Advertisements
Chapter 63 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   63 / 138

186K to 189K   out of 412.8K words

yanda kike so, ni kuma ZAN DAWO a gaSar da ?afafunki da gangar jikinki har ma da zuciyarki da ?wa?walwa suka gaji. Dan kinfi kowa sanin JUNAID baya barin BASHIN GABA)_.
Dummm kanta ya yi, zuciyarta na rawa da bugawa. Dan a wancan lokacin sam bata Wauki kalamansa da wani muhimmanci ba face cika baki da kirarin banza irin na wanda akaci wasa. Amma sai gashi a yau fa kamar kalamansa na neman kama hanyar tabbata ne. Kai ina hakan bazai yiwu ba. Bama zai taSa yiwuwar ba sai dai idan a cikin yaran Junaid Win ne wani ke son mata barazana da son tatsarta kuWi tunda gashi ya ambata a yanzu. To aiko zata nunama ko wanene ita Win ba ?aramar ?ar wasa bace. To amma kuma minene ya ala?anta yarinyar nan Maanal da wancan AJIYA A DUHUN nata na tsawon shekaru da babu mahalukin daya sani. Hoton nan dai na Maanal tabbas itace ta bada shi da Maman Saheeba da Hajiya Turai a lokacin da suke son ai musu aiki. Kuma idan bata manta ba a lokacin Hajiya Turai ce ta haWasu da yaron da zai yi aikin, dan lokacin suna zaune ne a Lagos, sun zo ganin gida ita da mijinta da Nuratu da zata girmi Maanal kaWan, kasancewar basu san wazasu samu ya musu yanda suke so ba saboda gudun mizai je ya dawo sai Nana tace ta bari ta shawarci Hajiya Turai Win dan tasanta itama ?ar ?unar ba?in wake ce. To bayan sun tattauna da Hajiya Turai Win shine tazo wajen bikin da saurayin da zaiyi kusan sa'a da AA a lokacin tace Wan ?anin mijinta ne, tace ya zauna wajen su Fawzan har a gama biki dan sun san AA bazai shiga harkar shi ba dan shi babu ruwansa da kowa sai Maanal. Fuskar yaron ce ke son dawo mata, amma ta kasa tunashi da ?yau. Sai tai tunanin duba hotunan ranar. Closet Winta ta nufa, ta buWe wani box dan tun suna asibiti tai kiran Haule tace ta kulle mata Wakinta saboda hotunan, Haule najin haka ta gane, sai ta kwaso hotunan daga inda ta Soye ta ajiye mata su saman gado sannan ta kulle Wakin. Koda aka sallamosu suka dawo gidan bata yarda an buWe Wakin ba shiyyasa ma ta zaSi yin jiyyar a nan ?asa sai jiya ta shigo da kanta da za'ai shata ya kwaso su taSoye sannan. Shine yanzu Win ta Wakkosu a inda ta Soye. Hoton matashin yaron nan ta ciro, ta maida sauran ta ajiye. Bakin gado ta dawo ta zauna ta zuba masa ido, tsahon lokaci zuciyarta na tabbatar mata shine wani sashe na cewa a'a. Da taga dai tana neman rikicewa sai tai kiran Maman Saheeba a waya tace ta shigo ta sameta..........
'?

*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*

*_=???AJIYA A DUHU....=???_*

*_Bilyn Abdull ce >??
*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*

______________

.........Babu jimawa Maman Saheeba kuwa ya shigo, kusa da Mamyn ta zauna, ita tama yi zaton wani sirrin zasuyi, amma sai taga Mamyn ta mi?a mata hoto. Amsar hoton tayi tana kallo, tsahon mintuna ta Wago tana kallon Mamyn.  Aunty waye shi? .
Numfashi Mamy ta fusrzar, sannan ta amshi hoton ta ce,  Zaki iya tuna fuskar yaron nan da Hajiya Turai ta kawo yay mana aiki a shekarun baya? .
Jimmm Maman Saheeba tayi, sai kuma ta ce,  Kai ai shekarun da yawa ne Aunty, kuma kinga yana gama aikinsa ai bamu sake ganinsa ba. Amma muga hoton nan ALLAH kamar shi fa a nan . Ta jima tana kallon hoton, sai kuma ta Wago da sauri ya kalla Mamy.  Kai wlhy aunty yaron nan shine. Ina kika samo hotonsa? .
 Kin tabbatar shine? .
 ALLAH babu kokwanto shine, kuma a kira Yaya Turai, ai ita dai bazata manta ba tunda ita ta kawo mana shi. Amma tabbas yaron nan shine Ra'iz .
Sosai zuciyar Mamy ta shiga karkaWawa, amma sai ta ce,  Bari dai a sake turama Hajiya Turai Win mu sake tabbatar wa . Tai maganar tana Waukar waya ta Wauki hoton, ta WhatsApp ta turama Hajiya Turai, kafin tai kiranta a waya. Sai dai harta tsinke bata Waga ba. Sake kira tayi, nan ma ba'a Waga ba. Sai ta ajiye wayar yana faWin,  Maybe bata kusa, nasan in ta gani zata kira .
Maman Saheeba ta ce,  Hakane, amma Aunty miya kawo kuma zancen yaron yanzu? Kodan ance yarinyar nan virgin ce? Ke ba?ya ganin duk shiri ne kawai dan su wanke yarinyar. Ko bayan wancan maganar kin sake jin sun tada maganar. Washe gari ma dangin nasu ba tafiya sukai ba kuma basu zauna da Ajwaad Win ba kamar yanda suka ce zasuyi .
Kai Mamy dake kallonta ta jinina, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da faWin,  Hakane dukkan zancenki Nana. Amma akwai abinda na sani game da mutanen wannan family Win dake baki sanshi ba. Dama kai tsaye bazasu zaunar da shi su tambayesa ba a lokacin dake kike zato, sai sun gama munafunce-munafuncensu ke kin ma manta da al'amarin sannan su dawo da shi. Haka kawai kuma nake ji a jikina bincike sukeyi, dan haka dole muma mu dawo da tunanin mu baya akan duk wanda keda ala?a da aikin nan a wancan karon mu binciko shi musan ina yake a yanzu? Mi yake yi? Musamman shi yaron nan da yay aikin da kuma Doctor. Sai ma?wafciyarmu .
Cikin gamsuwa Maman Saheeba ta ce,  Kuma tabbas hakane, ai sai yanzu na dawo hankalina. Wlhy duk zatona sun bar zancen ne. Amma abin na matu?ar damina a zuciya. Taya za'ace ba'ama yarinyar fyaWe ba bayan shi Ra'iz ya tabbatar yayi, shiyyasa ma shi Ajwaad Win ya ari laifin ya Waurama kansa dan a barshi ya aureta .
 Nana zuciyata ta fara bani akwai abinda ya kamata mu sani. Ni na haifi Ajwaad na sanshi nasan halin wannan yaron. Wlhy hatsabibi ne na gaske, babu abinda ya baro na ubansu. Shiyyasa kikaga ina kaffa-kaffa da al'amarinsa, na kuma fito na bayyana masa wacece ni kai tsaye bakamar sauran ba. Idan kin san kalmar bahaushe ta KAMAR KAYI KAKI KA AJIYE to haka ne tsakanin Ajwaad da ubansu, tamkar yayi kakin ne ya ajiye. Da da ban bayyana masa wacece ni ba akan waccan banzar matar shi zai fara ganoni, amma yanzu hakan da nayi kamar na kama lagonsa ne. Tsohon shekaru bai iya faWa ba, duk kuma wata hanyar da wani zai fahimci ni Win wacece hatta da sauran ?an uwansa cikin tosheta yake. Wannan shine dalilina nayin garkuwa da shi.
Sosai Maman Saheeba ta fahimta, ta kuma gamsu da bayanin Mamy Win. A ?asan ranta kuma tana jinjina mata da jin lallai dole itama ta sake shiri kenan. Dan ?ar uwar tata ba kanwar lasa bace ba ashe. Karma ya zamto tana mata kallon kitse ne ita tana mata na rogo. Daga ?arshe maimakon ita ta ajiyeta a duhu ita sai ta ajiyeta. To itama dai Mamyn kusan kalar tunanin nata kenan. Dan dariya take a cikin ranta da faWin (Nana kenan, a zatonki ba kallonki nake ba. Duk wani kai-kawonki a tafin hannuna kike wlhy. A tunaninki amfani kike dani wajen cimma burinki akan ?a?ana da dukiyarsu. Baki san nice nake amfani dake ba wajen cimma nawa burin. Amma muje zuwa dan irin wannan wasan na birgeni, kuma yana min daWi)

=??Tofa babbar magana, wannan fa shi ake kira da ainahin AJIYA A DUHU. Wayaga kafin biri yaga ayaba, ayaba ta ganshi>?#?. Kumuje zuwa mutanena yanzu ne zamu warware ainahin ma'anar AJIYA A DUHU =??=?M?.

_______&

A nan kuwa Babban Yaya ne ya samu Oum da batun Ameerah dai yau kai tsaye. Matu?ar mamaki ya kama Oum, farin ciki kuma ya mamayeta har idannunta na tara ?walla. Ta kamo hannun Babban Yaya cikin nata.  Fadeel da gaske kake wannan maganar? .
Murmushi Babban Yaya yayi, cike da kulawa ya ce,  Oum girmanki da kimarki ya wuce nazo miki da kalmar wasa a wannan bigiren. Nace zan rabu da Saheeba kun hanani ke da Abah, ni kuma na gaji da banzayen halayen yarinyar gaba Waya. Shiyyasa naga kawai gara nayi irin na Fawzan na ?ara auren. ?ari bisa Wari kuma na gamsu da tarbiyyar Ameerah, na kuma tabbatar zan samu yanda nake so. Hakan kuma dazan ma Saheeba shine zai zama hukuncin laifinta har naji na huce .
 Alhamdullahi, Fadeel ALLAH yay maka albarka. Na kuma baka goyon baya Wari bisa Wari.
 Nagode Oum, ALLAH ya ?ara miki lafiya da nisan kwana mai albarka. ALLAH ya cigaba da tsare mana ke, ALLAH ya cigaba da baibayeki da farin ciki da kwanciyar hankali .
 Tare daku baki Waya Fadeel. ALLAH yay muku albarka. Yasa kuma ace gwara da aikai. Yanda Auta ya samu farin ciki haka nake fatan kuma na ganku kai da Fawzan .
?ar dariya Babban Yaya yayi, ya ce,  A Oum autanki kam sai dai muce Alhamdullah. Kina ganin wata ?iba ma da yake yi sati uku kacal da tarewa. Idan naga yana murmushi sai naita kallonsa .
Dariya itama Oum Win tayi. Ta ce,  Kaima haka nake fatan naita ganin wannan murmushin a fuskarka. Dan haka ma ni bazan iya ha?uri ba yanzu zan je na samu Hajiya Shuwa. Idan zai yiwu ma wlhy a haWe dana Fawzan nan da sati biyu kenan. Dama itama Hajiya Shuwan ta sameni akan Maimoon, Ameer ya sameta da batun yana son Maimoon kasan abin nasa ya fara sauka kwana biyu jiya ma matar ta tafi gida wai tayi yaji .
 Ikon ALLAH, Oum dama shi komai lokaci ne, musamman irin wannan sihirce-sihircen. Haba shiyasa naga kwana biyu ya koma fita aiki, sannan zai tsaya mu gaisa yana wani du?e-du?en kai. Dan jiya da magrib har gidan nan ya shigo neman Fawzan, to kin san Wan naki akwai sau?in kai amma idan ya birkice yafi kowa daru. Sai cayayma maigadi yace baya nan .
Dariya Oum tai da faWin,  Oh ni FaWima wato Fawzan ko. To ka barni da shi zan zauna da shi, ai tunda ya dawo sai yay ha?uri komai ya wuce tunda mun san bayin kasan bane ba .
 Ato ya dai kamata Oum ....

&Kamar yanda Oum ta faWa batai ?asa a gwiwa ba ta samu Hajiya Shuwa da batun babban Yaya. Ya subahannallah farin cikin da baiwar ALLAHr nan ta nuna har sai da Oum tai mamaki. A take tace wlhy ko yau Fadeel ya shirya ta yarda a aWaura masa aure da Ameera koda Ameera bata so kuwa. Balle dama taga kwana biyu wani mutunci na yawaita tsakanin Ameera da babban Yayan har tanata mamaki, ashe ashe sun san mi suke ?ullawa...
Shima Aba a ranar Oum ta bashi labari a waya. A mamakinta shima farin ciki sosai ya nuna. Harda tabbatar mata washe gari zai dawo gida. Dariya ma abin ya dinga bama Oum, dan ta fahimci Gadanganta ya huce kenan. Yajin da akai musu kuma ya ?are. Aiko ya ?are Win, dan washe gari sai ga Abah ya dawo. AA ne yaje ya Wakkosa a airport shi da RK da sassafe. Ita Oum ta zata Abah ya sanarma Mamy, tunda da dare sukai maganar washe gari kuma sai gashi itama bata san da safen zai dawo haka ba sosai. Dan bama tasan AA yaje Waukarsa ba shi da RK, tunda RK banan yake kwana ba yana gidansa dake cikin asibitinsa shi da matarsa, sai dai kusan kullum Nuwaira na nan gidan saboda laulayi. AA kuwa yau weekend batai tsammanin ganin idonsa da wuri ba ma sam...
A lokacin da su AA ke shigowa da Abah gidan ne kuma su Mamy ke can suna tattaunawa ita da Maman Saheeba akan batun hoton Ra'iz, suna kuma tsumayen kiran Hajiya Turai amma shiru.. sai kawai ga Saheeba kamar an jehota tana sanar musu ga Abah can ya dawo. Mamaki ya kama Mamy da Nana, amma sai Mamyn batace komai ba tunda tasan mike faruwa tsakaninta da Aban. Koda Maman Saheeba ta Wakko zancen ma sai ta basar ta hanyar Waukar waya tana faWin,  Bara dai na sake kiran Hajiya Turai ko ina ta shiga haka .....

__________&

Duk kiran da Mamy kema Hajiya Turai akan idonta ne. Dan lokacin tana jikin Sille kwance ya gama Sille ta tas. Yau kwanansa biyu a gidan tare da ita, shiyyasa dama take son tura Nuratu gidan su Mamyn dan tafi samun isashen lokaci da Sillen. Cikin Wan yamutse fuska ta nunama Sille fuskar wayar da faWin,  Mamarka fa ta daman. Kuma bazan Wauka ba dan nasan sotake tace Nuratu zata dawo gida. Ni kuma bana bu?atar haka ban gaji da kai ba .
Cike da iskanci Sille yay dariya da faWin,  Ke dama kina gajiya dani ne. Shekaru sunja amma kina ?ara kangarewa. Ya kamata ki Waga kiji minene, kin san daren jiya na tura mata sa?o na san kuma ya risketa zuwa yanzu. A nawa hasashen ta zurfafa tunani akan hotunan dana fara tura mata, tana son sanin miya ala?anta hoton matar Wanta da sauran hotunan, anan ne zata fara tuna wanene Wayan hoton shima .
 Eh kuma fa hakane, ai bari ma na duba WhatsApp dan Wazu kuwa naga kamar ta tura min hoto kafin kiran nan ma . WhatsApp Win kuwa ta shiga, sai ko ga hoton Ra'iz. Da mamaki ta ce,  Baby na kaga kuwa hasashenka yayi dai-dai. Wai ya akai kasan matar nan haka da yawa ne? .
Mintsini mai zafin gaske ya bata cike da ba?ar mugunta har sai da tai ?ara. Kafin cikin raWa ya ce,  Karki manta ita Win UWATA ce, sannan irin tunaninta gareni ki kula ita Win SURUKARKI ce .
Hajiya Turai tasan halinsa sarai dan haka tai murmushin ya?e kawai. Shi kuma ya Wauka taba yana kunnawa da faWin,  Kice mata shine wanda take tunanin, idan ta tambayeki yana ina yanzu kice ta tambayi Wanta Ajwaad .
Cike da mamaki ta ce,  Amma Baby miyasa zanyi hakan? .
 Saboda haka na tsara. Dan komai nawa ni ina binsa daki-daki ne kema kin sani .
Kanta ta jinjina masa da faWin,  Kayi ha?uri na fahimta .
Banza ya mata, sai kuma ya Waura mata tabar a baki, dole ta zu?a. Aiko tari ya sar?eta dan bata iya sha ba. Sai idan yaso mata mugunta ne yake sakata sha dole ko ?wayoyi. Aiko tari take sosai idannunta sunyi jazur. Yako shiga balbala dariya cike da tsantsar mugunta har kifawa yake..........
'?

=?.?
=???Kai jama'a ALLAH ya rabamu da faWuwar ba?ar tasa. Ga kuma wata sabuwa. Shin miya ala?anta Hajiya Turai da Sille kuma>?#? AJIYA A DUHUn fa kenan kumuje dai zuwa
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*

*_=???AJIYA A DUHU....=???_*

*_Bilyn Abdull ce >??
*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*

______________

........Maanal na kitchen AA ya shigo, dan tunda taji yana waya da RK daya kirashi yazo su Waukesa Abah a airport ta martaye daga barcin da take yi tunda taji Oum ma bata sani ba. Sosai AA da ?amshi ya jawoshi kitchen Win mamaki ya kamashi, dan yasan shi dai barci ya barta tanayi. Hankalinta yayi nisa a harhaWa abincin yay gyaran murya, juyowa tai da sauri, sai kuma ta sauke ajiyar numfashi a shagwaSe ta ce,  ALLAH ka bani tsoro Besty .
Murmushi yayi, sai kuma ya ?araso inda take ya rungumeta ta baya kasancewar ta juya tana kwashe Irish Win dake cikin air pryer. Wuyanta ya sumbata tare da raWa mata,  I'm sorry. Yaushe kika tashi ke da na bari kina barci? .
?ayan hannunta takai ta shafo fuskarsa.  Tunda Uncle R ya kiraka na farka, kawai nayi shiru ne harka fita. Yaya Aban? .
 Abanki na lafiya gashi can a sashensa. Yanzu wannan kayan daWin duk na waye? .
 Na Abah mana .
Ta faWa tana juyowa bayan ta zuba wani dankalin.
 Mu baza'a sammana ba kenan? .
KaWan taja hancinsa da faWin,  Ko Wan guntu bazaku samu ba .
 Idan an hanamu wannan ai Ni sai a bani nawa abincin .
 Oh kana

63 / 138

Chapters