Advertisements
Chapter 8 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 138

21K to 24K   out of 412.8K words

Yanzu kam bata musaba ta bishi, dan hakan zaifi mata sau?i ita kam. Duk da dai a ranta bata son binsa office Winsa department Winsu take son wucewa. Suna shiga elevator ta wani sauke ajiyar zuciya tare da janye hannunta dake a cikin nasa. Dariya ma shi kam ta bashi, dan haka ya taSe baki da faWin,  Matsoraciya, nine kika raina kawai .
Kallonsa tai baki a tunzure ta ce,  Waye matsoraciyan? .
Kamar wasu masu faWan yara ya juyo yana ri?e ?ugu idanunsa ware a kanta ya ce,  Ke mana .
Itama juyowar tai tana matsowa gab da shi idannunta cikin nasa da yanayin harara hannayen nata a ?ugu kamar yanda sukeyi a da in suna faWa ta ce,  Niba matsoraciya bace sai dai idan kai .
Matsawa shima yay ?o?arin yi gabanta sosai idanunsa a cikin nata. Baya ta shiga ja yana binta har suka dangane da bangon elevator Win. Sai da ya tabbatar ya matse mata ko'ina ta yanda ko numfashinta a sar?e yake fita sannan ya Waura hannunsa Waya a bangon shima ya sake mata rumfa, still dai idanun nasa na'a cikin nata da take mar-mar da su na alamar tsoro amma a zahiri a dakenta take. Ran?wafawa yay a kanta da ?yau tsahonsu ya dai-daita, kafin ya sake matsar da fuskarsa gab-gab da tata tamkar zai haWe bakinsu waje guda. Gaba Waya sai Maanal ta rikice, fuskarta tai ?o?arin maidawa gefe cikin in-ina da sar?ewar harshe ta ce,  Wa....w. wai miye haka kake yi? .
Cikin son ?o?arin hanata janye idanunta a cikin nasa tamkar mai raWa ya furta,  Kulawa da ?ar Abah mana. ya ?are maganar yana hura mata iskar bakinsa akan idanu.
Baki ta Wan tura tana ?o?arin tureshi da yin mar-mar da idanun saboda iskar da yake hura musu,  To ni nace maka ina so? .
 Ai basai kin faWa ba, Abanki ma haka yake so naga .
Kasa cemasa komai tayi, ga idanuwanta sun fara tara ?walla. Dai-dai nan ?ofar elevator Win ta rabe biyu ta buWe kanta. Daburcewa Manaal tayi ganin mutane har kusan uku tsaye saboda itace ke facing ?ofar, shi kuma ya juya musu baya. Ai babu shiri takai hannu gefen cinyarsa ta mintsina cikin rawar murya da raWa ta ce,  Mutane fa .
Idanu ya Wan lumshe dan har yanzu hannunta na'a jikinsa ta?i sakin mintsinin data masa sai ma sake matsewa take sosai. KaWan ya waiwayo kansa ya kalla ?ofar elevator Win. Sai kuma yay wani kalan luuu da idanun cike da basarwa ya mi?e tsaye da ?yau. MaSallin rigar suit Winsa ya shiga sakawa tare da kallon hannunta dake a jikinsa har yanzu. Silently ya ce,  Sai fatan ya cire ne Besty .
Da sauri ta janye hannun nata, sai kuma ta yun?ura zata fice ya cafko hannunta. Cike da takunsa na nutsuwa da ?asaita tamkar komai bai faru ba ma ya fito, su HOD dake wajen suka shiga musu barka da dawowa cikin girmamawa.  Thanks you . Kawai ya faWa a ta?aice ya jata suka bar wajen kanta a ?asa ita dai.
Sai da suka Sace a wajen gaba Waya Director Steven ya kalla HOD da CFO fuska da murmushi ya ce,  Uhm dama haka boss yake .
Dariya HOD ya sanya, tare da faWin,  Ai irinsu daman yan babu sau?i ne ina gaya maka. Ai kowa ya shirya, dan sai an mana ?urmus a companyn nan da soyayya .
Dariya suka sake sanyawa a karo na biyu, banda CFO da zuciyarta ke mata zafi da raWaWi saboda kishi. Tsahon lokaci take jin son AA a ranta duk da ta girmesa a shekaru, sai dai tana matu?ar ?o?arin dannewa ta yanda kowa bai taSa fahimtaba a companyn. Shi kansa ta fahimci kamewarta ya sashi bata amanna kai tsaye, dan duk wadda zata nuna masa tana sonshi in har tana a kusa da shi duk iya aikinta sai ya canja mata waje. Hakan data fahimta yasa ita tazo da sabon tsarin kame kanta. Ita Win bazawarace, mijinta rasuwa yayi shekaru biyar kenan, bata taSa haihuwa ba. Bata sake wani auren ba kuma har yanzu. Tun randa akai musu interview a companyn ta Waura idanunta akan CEO taji duk duniya shi kaWai take so. ?ya?y?yawace itama ta gaske, gidansu kuma gidan kuWi ne ?warai da gaske, tayi karatu mai zurfi, ko aikin nan tana yinsa ne dan ra'ayi kawai bawai dan bu?atar albashi ba, duk da dai AA mutum ne mai ?o?arin kamantawa ma'aikatansa albashi mai tsoka dako gwamnati albarka musamman daya kasance ?asar tamu zalunci yayi gaba ba'a wadata ma'aikatan da albashi mai ?yau..........
'?

*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*
*_Typing=???_*









*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
........Cike da farin cikin aikar da Mamy tai mata ta fito, dan dama hanyar da zata fita a gidan take nema sai kuma ga mafita ta samu cikin sauki. Abinda ya kara mata dadi da Mamyn tace ta hau taxi tunda drivers din gidan duk sun fita. Daya ya tafi kai yara makaranta, daya ya tafi da Abah dayan AA. Ita kuma tana bukatar akai mata sakon ne yanzun nan. Ba komai Haule ta fahimta akan Mamy ba, amma ta dade da gane wasu abubuwanta a gidan musamman akan fuska biyu ga Oum, kawai dai ba abinda ya shafeta bane shiyyasa bata gaba dadara kanta da kasa ba. Sai dai duk wani aiken Mamy ita take sakawa, ta yarda da ita dari bisa dari. Tasan kuma hakan nada nasaba da kasancewar Maman Nuratu ce ta kawota aidan. Sai dai abinda Mamyn bata sani ba
Maman Nuratun ta kawota ne dan tai mata aiki a gidan, yayinda ita kuma Maman Nuratu bata san Sille takema aiki ba a kansu su duka da AA.
Can gaban wani tsohon Company Haule tace mai taxi ya sauketa. Ta zaro kudinsa ta basa sannan ta tura kai ciki babu ko dar. Kai kawai mai taxi din ya girgiza zuciyarsa na sosuwa da ganin yanda yaran mu na hausawa suka lalata kansu. Kowa yasan wajen nan maboyar yan daba ce da manyan kasa ke amfani da su wajen ta'addanci, shiyyasa ko anzo an kama su basa wuce ranar ake sakinsu su dawo. Ya tabbatar yarinyar nan kodai kayan shaye-shaye zata saya ko kuma mu'amular banza. Shi dai yaja taxi dinsa yay gaba.
Tunda Haule ta shigo cikin tsohon companyn sosai yaran Sille dake zaune daba-daba wasu na shaye-shaye, wasu na wanki, kai kowa dai na hidimar gabansa tamkar wanda suka samu aida suketa gaisheta dan kowa a cikinsu yasan yarinyar oga ce. Ita ko cike da jin kai take amsa musu harta dangane da idan dakin Sille yake. Bacher ce ta langa-langa, daga ciki kuma katako, sai dai an fenteshi tsaf ta yanda bazaka taba yarda katako bane ba. Dakin babbane sosai, akwai gado a ciki da kujeru set guda, sai freight da television harda speakers harda AC.
Kasan dakin kuwa tils ne tsaf. Zaune yake a kujera ya wani barbaje gabansa kwalaben giya ne har uku, sai dai ba giyar yake sha ba taba ce a hannunsa kunnesa makale da waya alamar magana yake, daka gansa kuwa kaga Sillen na gasken gaske, dan sirrine sosai tamkar zai karye ko in iska mai nauyi zata iya yin gaba da shi.
Tunda ta shigo ya zuba mata ido, tana karasowa gabansa yasa kafa ya tadota ta fada a kansa, matseta yay a jikinsa tare da manna mata kan tabar hannunsa a damtsen hannunta. Yar kara tai da kankame jikinta saboda zafin wuta, sai yay murmushi da yarda tabar a kasa ya shiga shafa mata wajen da har ya dashe dan ya konata. A haka ya kammala wayar, ana yankewa daga can bai wani tsaya komai ba yay wurgi da ita gefe ya dauka Haule cak ya nufi gadon dakin da ita.....
Sai da suka gama masha'arsu sannan ta mike a dan rikice tana fadin, "Baby bara na wuce. Aikana matar can tayi gidan su Nuratu nakai sako". Ta mika masa wayarta tana cigaba fa fadin, "Gashi na dakko maka yau da safe, dan ita da shi duk sun koma aiki".
Kamar yanda bai tanka mata ba tun dazun yanzu ma batare daya ce komai ba ya amsa wayar daga kwancan da yake. A zabure yay wani kalar tashi zaune yana waro idanu waje. Sai kuma ya nufi drawer din dake a dakin karama ya bude, kayan ciki ya shiga watsowa a kasa har ya samu damar ganin abinda yake nema. Ita dai Haule tsoratama tayi da yanayin nashi, da sauri ta mike tsaye tana kallonsa. Juyowa yay inda take idonsa akan wani hoto daya dakko. "K duba min nan ko idona ne? Data cikin hoton nan da wannan duk mutum daya ne?". Karo na farko kenan dayay mata magana cikin budaddiyar muryarsa mara dadin saurare da tafi gangar jikinsa girma. Amsar wayar tata tayi da hoton ta zuba musu ido itama. Sai kuma ta dago tana kallonsa. "Baby tabbas wannan duk mutum daya ce, kawai dai anan bata karasa kaiwa mace bane ba. Dama kasan matar AA din?"
Bai tanka mata ba, sai wani irin naushi daya kaima bangon katakon dakin yana fadin, "Yanzu ne yakin na gaske zai fara"..
Sakare Haule tai tana kallonsa. Sai dai ko kallon inda take bai sake yi ba ya nufi bayin dake dakin dan karami na wanka, wanda shima dai din na langa-langa din ne.. Wanka yake yana dariya sosai kamar mahaukaci sabon kamu.
Jinsa yake a wani irin nishadi mai girman gaske daya dade baiji a zuciyarsa ba. Ajwaad ya auri Maanal fa? Eh lallai yanzu ne za'ai wasa mai zafin gaske tsakaninsa da shi. Tabbatacen alwashine wannan a garesa sai ya nakasta Ajwaad da Maanal. Dole ne yayi RAMUWAR GAYYA DA TAFI GAYYA zafi. Shine fa Sillen karan gero mai wuyar tsagewa, idan kai nasarar tsagewar baka yanke ba kai mai nasara ne.
Uban daba yake a yanzu mai kujerar karfin iko.
Ajwaad! Maanal! Ku jira sakamako....
Ya kwashe da wata shegiyar dariya yana kaiwa bangon langa-langan duka har sai da Haule dake shirin tafiya ma ta firgita. Hakama yaransa dake can ta waje duk sai da suka kallo dakin da mamakin minene ya saka ogan nasu nishadi haka ne?...
Tofa, mike faruwa ne? Wanene kuma Sille?
Miyake nufi da yanzu ne wasan zai fara? Menene tsakaninsa da AA ko nace Darma Family da har ya shafi Maanal yake ajiyar hotonta?. Hummm kumuje zuwa kudai cakwakiya ce ta gaske fa *
Suna karasa shiga cikin office din Maanal ta kwace hannunta daga cikin na AA. Babu musu shima ya saketa. Bai kuma ce komai ba ya nufi kujerarsa. Koina a tsaftace yake kal an office din.Ga wani kamshi mai kwantar da zuciya na tashi.
Files din dake a table din nashi tule yabi da kallo, sai dai an ajiyesu a tsare dan kowa yasan shi ya tsani ganin waje rakwacam ba tsafta. Hannu ya kai a hankali ya kunna computer din saman desk din, kafin ya dago idanunsa ya zuba akan Maanal dake a tsaye har yanzu. Kallonsa take yi itama, sai dai yana dagowa ta kauda kanta.
Baki yadan tabe, sai kuma ya dauka kan waya ya danna 1 tare da kaiwa kunnensa. Dai-dai an dauka. A takaice ya furta, "Zo ciki". Bai jira amsa ba ya yanke kiran. Maanal ya kalla fisha ya dauke idanunsa, ciki-ciki ya ce, "Malam sit"
Harararsa ta danyi, sai kuma taje ta zauna dan bata son wanda taji yace yazo ya shigo ya ganta a tsayen kodan nasihar da Oum da Abah sukai mata na darajta kanta ga ma'aikatan companyn. Bawai tazama mai girman kai ko wulakanta kowa ba. A'a ta mutunta kanta da kame kanta yanda ya dace dai matsayinta na matar ogansu. Inba haka ba mutane da yawa zasu fara amfani da ita a yanzu domin cimmasa a ciki da wajen companyn. Hakama mata dake kulafucinsa a ciki da waje zasuji shakkar nunata koda da zundene balle isa gabanta.
AS ne ya shigo bakinsa da sallama bayan yayi knocking AA din ya bashi damar shigowa ciki. Batare daya kalleta ba saboda girmamawa ya wuce sum-sum kamar munafuki inda boss yake. Hankalin AA a computer shima, batare daya dago ba ya ce, "Daban kiraka ba bazakazo kamin bayanin abinda ya dace ba kenan Haneef?".
"Ayi hakuri sir, naga kana tare da Auntynmu
ne shiyyasa. Amma ai min afuwa".
Komai AA bai sake cemasa ba. Sai tulin documents din dake zube ya kalla. Matsowa AS yayi kusa da shi domin fahimtar abinda yake nufi. Cike da nutsuwarsa ya shiga masa bayani yanda ya kamata. Shi kuma yayi shiru yana saurarensa. Hakama Maanal dake latse-latse a waya kunnenta na kansu ne tsaf. Fin minti ashirin kafin su gama magana da AS ya fita. Dan haka ta dago ta kalla sashen da yake zaune.
Ganin zai fara aikinsa kamar ya manta da ita yasa ta mike. Wayarta ta saka a handbag dinta sannan ta nufesa, batare data karasa inda yake ba ta ce,
"Nifa zan tafi".
Yi yay kamar baijita ba tsawon sakanni kafin ya dago ya kalleta. Ganin yanda ya kafeta da idanu yasata dauke nata tana sake tsuke fuska.
Shima janye nasan yay ya maida ga aikinsa yana fadin, "Nace miki na gama dake ne?".
"Amma kasan fa aiki nazo ko. Kuma Abah
yace ka fita harkata".
"Hakane Aunty Maanal yi hakuri yar gidan
Abah".
A yanda yay maganar tasa ta dan hararesa. Dan irin gatsen da yake mata kenan ko ada can idan tace yay abu kota takura masa idan yace bazaiyi ba sai ya dinga kiranta da Aunty......
Takaici ya saka Maanal dauke hankalinta daga gareshi gaba daya. Tsohon mintuna arba'in yanata aikinsa kamar ma ya manta da ita akai knocking kofar. Sai da ya kalla sashen da Maanal take sannan ya bada izinin shigowa. AS ne ya shigo yanzun ma. Batare daya kalletaba yanzu ma yay mata sannu. Maimakon amsawa saita samu kanta da harararsa, dan haushin ogansa ya shafe sa shima. Shi dai da yake ba kallonta yake ba baima san tanayi ba. Cikin girmamawa ya karasa gab da AA, murya a kasa yake masa bayani like ba'a son taji komai. Sai ta sake tunzura. AA ya jinjinama AS kansa, tare da fadin, "Shike nan kuje ka kaita, su kuma su bari after break na dan rage aiki"
"Okay sir". AS ya fada yana nufar inda Maanal take. Kansa a kasa ya ce, "Aunty bismillah".
Mikewa tayi batare da tace komai ba, sai dai ta kalla inda AA yake zaune cikin yanayin harara.
Sai ko akai sa'a shima ita din yake kallo. Gira daya ya dage mata, sai kuma ya kashe ido daya cike da neman rigima da son tunzurata. Aiko fuska ta yamutse tare da janye nata fuuu tabi bayan AS bayan ta zuba masa harara. Rakata yay da idanu har ta fice gaba daya. Guntun murmushi yayi yana mai lumshe idanunsa ganin yanda take cika da batsewa. A kan lips ya furta,
"Yar gatan Abanta kenan" yay wani murmushin shakiyanci yana datse lip da hakori........

*_Typing=???_*









*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
KANO
Ganin yanda ya shareta kwana biyu bai sake gwada son kwana dakin ba yasa yau ta saki jiki, balle ma daya shirya ya fita wajen aiki. Su uku ne kawai a gidan, ita sai kannensa biyu yammata da suka zo mata wai yini. Dan yana fita babu jimawa suka zo. Sune suka mata gyaran gidan tsaf da tsohon kwana biyu bai samu shara ba.
Dama dai yaran anguwa dake dan shigo mata take ritsawa su mata. Ko kuma bakin da sukazo ganin gida idan taga yan tagajan-tagajan ne sai ta saka su. Wasu ma danginsu ne, amma da yake su dama yan gidansu an musu shaidar girman kai da raina mutane bata jin ko nauyi take cewa su mata aiki koda sun girmeta. Su kuma da shegen kwadayi da neman gindin zama sai suyi din kuwa.
Kannen nasa ma sai faman
yamutse-yamutse take musu. Sajeeda sarkin zuciya har tace su tafi kawai, da kyar Khadijah ta lallabata. Aikin ma kinyi tayi sai Khadijan ce tayi mafi yawa a ciki. Huznah dai ana bedroom an bararraje ana barci, dan daga charting ta bingire a wajen. Ana idar da sallar Azhar Sageer ya dawo gidan. Yaji dadin ganin babu kowa sai kannensa, ga kuma mutuniyar tasa na sharar barci. Hankalinsa kwance ya kada su Sajeeda gida, yaje kuma ya kulle kofar gidan sannan ya koma ciki. Hajiya Huznah anji dadin fanka barci yay dadi sai taji hannu na yawo a jikinta. A firgice ta farko sukai ido hudu kuwa da Sageer. Wani irin bacin rai ne ya sata yunkurawa a masife, sai dai gogan yariga ya mata daurin huhun goro da jikinsa. Karfi kuma ba daya ba, dan ko motsin arziki bata iya tayi ba, tana ji tana gani kuma ya shiga yin yanda yaso da ita batare daya nuna damuwa da hawayen da take ba.
Cikin sauki da nuna mata mazanfa maza ne yay kidinsa yay rawarsa tare da more sadakinsa.
Itako tana faman kuka da zaginsa, zagi kuma na rashin mutunci. Nunawa yay bai damu ba, dan ta ceci kanta data kawo mutuncinta, harga ALLAH bai kumayi tsammanin hakan

8 / 138

Chapters