Advertisements
Chapter 93 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   93 / 138

276K to 279K   out of 412.8K words

.
Da sauri ta Waga masa kai. Ya ce,  Shike nan, gashi nayi recording zan ajiye, zan kuma turama Oum da Yaya Fawzan ma su ajiye dan sune shaidun mu. Tashi ki haWa min shayin bara naje balcony na motsa jiki kwana biyu jikina na ciwo ban motsa shi yanda ya kamata ba .
? ? ? ?? Fuskarta cike da murmushi ta ce,  Ina ?aunarka Besty .
? ? ?  Nima haka Bestyn Besty, a yanzu kune duniyata mai girman gaske ke da unborn Wina . Yay magana yana kamo ?ugunta ya matso da ita gabansa ya sumbaci cikinta. Sai kuma ya Waura kunnensa a kan cikin, murya ?asa-?asa ya furta,  Ko waye kwance a wannan wajen mai albarka ALLAH ka albarkace sa, ya rabbi ka kare min shi ko ita da mahaifiyarsa, ALLAH ka bamu tsahon rayuwa, ka kashemu tare ni da matata dan in Waya ya tafi yabar Waya bazamu iya jurewa ba ya rabbi. Ya ALLAH kasa itace matata har a aljanna .
? ? ? ?? Murmushi mai faWi Maanal ta saki, tare da rungume kanshi a saman cikin nata sosai, sai kuma tai ?ar ?ara tana sassautawa saboda zafin da taji. Da sauri ya Wago ya kalleta tare da faWin,  Meya faru? .
? ?? Murmushi ta masa tare da jan hancinsa ta ce,  Zafi naji kaWan dana danna ?aton kan nan naka .
? ??  La'ilah yanzu Besty mijin naki ne mai ?aton kai. Jama'a kuzo mu tayata istigafari dan ALLAH .
? ?? Dariya sosai Maanal keyi, ta dungure masa kai.  ALLAH ka iya sharri wani lokacin, wanda bai sanka ba sai yay ta yabonka ana kiranka shiru-shiru basu san hali bane ba .
? ? ? ? Murmushi yayi shima har ha?oransa na bayyana, ya ce,  Oho dai, kema naga ai hakan kike ko. Gwara ma ni ai .
? ?  Wace gwarar kullum fuska a haWe, magana kamar ana maka dole. Ai wlhy sai na koya maka surutu .
? ?  Yo miyay saura kuma ALLAH na tuba Besty, tsabar maganar da kike sakani a gida da office kullum yawo nake da kwalin paracetamol a gida da office da mota .
? ? ? ??  Kai Besty kaji tsoron rabbu .
??  Kema beaty kiji tsoron rabbu .
 Shike nan bara dai naje na dawo zakayi bayani, badai yau lahadi ba ko nan da falon ?asa bazaka sauka ba yau sai kaga asalin koyan surutu mai saka ciwon kai .
? ? ?? Hannu ya kai zai cafkota ta zille ta fita da Wan gudu.  Ki tausaya min ki daina gudun nan dan ALLAH Wan tayima bai gama zama mutum ba .
? ?? Sarai ta jisa, dan ya Wan Waga murya, sai dai bata amsa masa ba, ta dai Wora hannunta a saman cikin tana shafawa da murmushi. Baza'ace ya fito yanda kowa zai fahimta ba, amma ?asan mararta ya mata tauri sosai ta yanda ita kanta zuwa yanzu tana sake yarda da eh lallai akwai gudan jinin Bestyn ta a wajen...

? ? ? Coffee mai daWin gaske ta haWa masa ta juye a ?ya?y?yawan butan shayi na ainahin chainawan farko. Cike da ?yawun kallo ta jera a saman ?aramin tray ta haWa da ?ananun cups na butar shayin ta Wauka. Saman ta hauro, sai dai a maimakon bedroom yanzu ainahin ?aton glass window Winsu da ya cinye bango guda na bangaren balcony Win saman ta nufa. Sai da ta danna wani button labulen wajen ya shiga zuge kansa biyu a slowly ya koma gefe-da-gefe. Sai ga gilashin da ko bullet baya iya fasawa ya bayyana. Tar-tar daga nan ma kake iya hango ainahin gidan musamman sashen Yaya Fawzan dake makwaftaka da nasu. Ido suka haWa da AA dake Push-up ya jiyo yana kallon ta. Kayan data barsa da sune dai a jikinsa. Wando 3quater da riga armlass dukansu na kamfanin nike. Ba ?aramin ?yau da kwanciya a jikinsa kayan sukai ba, sun kuma fidda ainahin surarsa musamman damtsen hannunsa dake a murWe masha ALLAH. A saman table Win da ke a tsakkiyar kujeru biyu dake wajen ta ajiye, AA ya dakata yana kallon ta, dan itama tayi ?yau sosai cikin wandon jeans dake jikinta da ?ar top mai gajeren hannu. Yanda bayanta da ?irjinta suka sake cika dole ta birge idanun mai kallo....
? ? ??  Besty kallon ya isa mana, kada ka cinye ni .
? ?? Murmushi yayi da faWin,  Dama zan iya haWiyeki ai da nayi hakan ko zan samu sau?i daga abinda nake ji a kanki Besty . Yay maganar yana juyawa ya cigaba da Push-up Winsa. Baki ta Wan taSe tare da sakin murmushi ta na ?arasowa inda yake. Yana kaiwa ?asa ta haye bayansa tana faWin,  Tun yaushe ka gama haWiyeni Besty, ai saura kawai ya rage maka .
? ? Murmushi yayi baice komai ba, tana akan bayan nasa yana cigaba da Push-up Win sa tamkar baya jin nauyinta. Daga ?arshe ma sai ta zame ta kwanta rigingine a bayan nasa a haka ya cigaba dayi, harda saka caca wai idan yayi sau Wari da hamsin yau zata fita da shi yawo ta bashi atm Winta duk abinda yake so ya sayo koda na duka kuWin ne.
? ?? Dariya yayi ya ce,  Okay fara ?irga .
? ?? Haka ya fara ?irgawa kuwa, a mamakinta ba Wari da hamsin ba sai da ya kai da saba'in, a hakan ma ita ta dinga ro?onsa ya dakata wai ya gaji shiko yana mata dariya.......

_________&

? ? ? Duk wannan abun dake faruwa a idanun Nibras dake ma?ale a window Win bedroom Win Wakinta ne tana kallon su. Dan ta saitin nan Win window Win nata yake. Duk da kuwa ta inada suke badan daga Bedroom Win take kallo su ba da babu yanda za'ai idan tana nasu balcony Win ta gansu. Da farko ma Fawzan ne a balcony Win zaune yana aikin office, yana ganin AA ya fito ya fara motsa jiki duk da bawani ganinsa yake sosai ba ya tashi ya shige dan yasan in har kaga WATA dole sai kaga ZARA. Ilai kuwa yana shigewar Maanal Win daya tashi dan ita ta fito wajen...
? ? ? Hawaye ne masu zafi ke fitoma Nibras, musamman data ga yanda duk style Win da AA zai yi Maanal na jikinsa suna hirarsu da dariya cike da farin ciki. Wani lokacin ma su har?ume kokawa, bawai ta danben tsiya ba, irin dai ta ma'aurata mara hayaniya da cutarwa. Sun jima a wajen yayinda ita kuma ta jima tana kallon nasu dan rashin aikinyi. Har suka sha coffee Winsu Maanal ta kwashe kayan ta shiga da su, ta sake dawowa tana rigimar AA sai ya goyata ya du?a kuwa ta haye suka shige ciki abinsu basu ma san da ita ba....
? ?
? ? ? Labulen ta saki tana rushewa da kuka mai ciwo da zafafa zuciya. Yayinda shaiWaniyar zuciyarta ke ayyana mata abubuwa masu yawan gaske akan AA. Ciki harda tunkararsa da abinda ke ranta dan ita kam ta gaji da haWiyewa. A yanzu takai gaSar da take jin komai zata iya yi domin AA, kamar yanda komai zata iya yi domin Fawzan. Gaba Waya zuciyarta ta kasa banbance wa take so a cikinsu. Dawa take bu?atar yin RAYUWA.
? ?? Sai da taci kukanta ta gode ma ALLAH ta fito domin neman breakfast Dan wata irin yunwa take ji tazo kuma ta taras da wata soyayyar mai ainahin gudana a ?asa tsakanin Yaya Fawzan da Najma. Suna kitchen suna girki a tare cike da farin ciki. Ga dariyarsu na fita cike da nishaWi. Tai tsaye cak. Sai kuma ta jiyo Najma na faWin,  ALLAH bazan yarda ba sai na rama love.
? ? ? ? ? Shi ko Yaya Fawzan na dariya da faWin,  Ashe zaki rame ?ar Zaria. can sai gasu sun fito Najma na binsa da spoon Win girki na katako. Shi ko yana dariya da zizzile mata. Ko kusa ko alama basu ga wata Nibras ba ma su sabgar gabansu suke. Aiko da gudu ta koma sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ma tana kuka. Ta faWa saman gadonta da rabonsa da gyara yau kwana uku kenan sai idan dare yayi ta haye a haka ta sake kwanciya tana kiran,  Na shiga uku ni Nibras, shike nan babu WAN babu KANIN, mayu sun mamaye ko'ina. ALLAH sai na kashe Maanal da Najma, sai na kashe su..........
'?

? ? ? Tir?ashi, ashe su oga AA an kusa yin takaba=??.



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________


............ Barka da zuwa Baa! .
? ??  Barka dai Son. Fatan na sameka lafiya? . Mabera ya faWa yana bin Wakin bacha Win sille da kallo. Shima Sille Wakin yabi da kallo, sai kuma yay ?ar dariya da faWin,  Normal ne Baa.
? ?? Mabera ya jinjina kansa, kafin ya kafe Sille da ido.  Yanzu Son bazaka bar cikin tsohon companyn nan ba ko? Na gaya maka zama a wajen nan akwai haWari, sannan kowane jaki da doki zai maka kallon wani ?as?antacce ko karen ?an siyasa ne. Amma ka kasa fahimta ta. Kaje ka kama hotel na shekara guda yafi min .
? ? ??  Hummm Baa! bazaka gane bane. Shifa mugu shine yasan makarantar mugu. Idan naje hotel na zauna ya zan yi da waWan nan karnukan farautar nawa ne? Idan na barsu su kaWai anan ALLAH kowane banza ma zai kawo musu hari ne musamman waWan nan masu ba?a?en kayan. Kawai ka barni anan ina samun yanda nake so, kallifa Wakin nan, minene marabarsa dana hotel Win. Ac yaji, solar taji, daga waje ne kawai zaka Wauka bacha, amma a ciki ko Wakin Kamila ai albarka .
? ? ? ??  ALLAH ya shirya min kai Son, Kamila fa itace ta kamilo min kai duniya tun karana bai kai tsaiko ba.
? ??  Hhhhhh!! Kai Baa, kuma fa kun tsula tsiya a ?arninku dai-dai gwargwado. ALLAH dai yasa tuban da akai yanzu ya zama kaffara ce. Muma ALLAH ya maidamu danshin ku mu tuba a dai-dai muna cika 45, dan kasan shifa walakirin lahirar nan ba gajiya suke da Wimar mutane ba. Kar muje ana hayya-hayya a aljanna mu muna ?ofar gate ana bamu horo, ai al'amarin baiyi daWi ba wlhy. Koda yake koda rinto da wawa ai sai munje kusa da MANZON ALLAH .
? ? ? ?  (S.AW). ALLAH to yasa. Amma gaskiya to, ba'ace komai ba dai Son, kasan nima dai nayi islamiyyar nan kiranyen sheWanne kawai kasan shi mai rabon wahala yake Wauka. Amma dai kai, anfayi al'amura, koma ace ana kan yi, amma dai gab muke ai da tuba ba komai. Yanzu yaya kuke ciki da Kamila?.
? ? ?  Hhhhh sai da kai Baa! Langa-langa mugun ?arfe, ?an gwangwan na rainaka amma shine uwar cinikinsu. Rumfa makara Waki, ko baki kare Wan kwarai ba ?ya kare shege, yo shima ai shegen da ubansa tunda ba'a ruwa ko a tuwo uwar ta shawosa ba ko taci. Kaga ?wan jimina ba'a ganinka sai gidan masu kuWi, coge takalmin mata gajeru na rubibinka dogayen ma sakawa suke dan su ?ara tsayi. Marfin tukunya mai rufe sirrin ?azamar miya koda arniya ce ta rufu, kaga Junaid, baban Junaid mijin Sabuwa baban Nazifa da Sa'adatu. Ogan Kamila kota amsa ko jiki yay tsami ..
? ? ?  Son baka da dama ALLAH yanzu mike tafiya a wajen Kamilar? Menene shiri ka kuma .
? ? ? ?  A gareni komai normal ne, a gare ta kuwa tana can tana haukar nemana yanzu haka. Dan na toshe ko'ina. Sai dai ina samun imformetion Win komai a wajen Turai  .?
? ? ? ?  Turai? Son har yanzu kana tare da Turai ken nan? .
? ?? Kai Sille ya sauke ?asa yana shafa keya. Ya ce,  Baa matar nan fa nada amfani sosai a garemu kaima ka sani. Kayi ha?uri ka yafe mata wancan kuskuren da tai....
? ? ??  Amma kasan wacece Turai ai ko .
 Na sani Baa, kar kuma ka damu dan a tafin hannuna take wlhy, a yanzu haka komai daya shafi mijinta har mutuwarsa na sani, shiyasa ko War bana ji a kanta dan har yanzu abinda naso ta sani kawai take sani. Kamar yanda kai treating Winta a baya nima haka nakeyi yanzu. Kasan mugu shine ya san makwantar mugu.
? ? ? ??  Hakane. Shike nan ina jin ka.
? ??  Yauwa normal ne Baa. Kamar dai yanda na gaya maka tsarin wasan a baya shine...... tsaff ya sake maimaita masa komai da suka tattauna a waya ranar. Mabera ya jinjina kai da sauke ajiyar zuciya.  Tsarinka duk yayi, sai dai dole ne mu canja dukkan wasan. Dan a yanzu mun zo wata gaSa ne bata hawainiya ba gudun barewa zamuyi. Kamar yanda ka faWa yaron nan Ajwaad shege ne. Kasan iya buge-buge na har yanzu mun gagara sanin ina ?anwarka take da Yazeed. ?an sandan ma suna neman maidamu mahaukata. Yanzu haka zancen da nake maka Sabuwa na kwance a asibiti kwana biyar kenan. Daga ni har ita Chalawa ya hana a barmu mu shiga gidansa, ?an sanda ma ke gadin gidan. Hakama yaransa makarantar boko da islamiyya jami'an tsaro na tare da su. Matansa ma idan zasu fita haka ne. Matarsa ce ta tsakkiya ce dai ma jiya kaWan ya rage na cafketa a asibitin doctor Dev.. sai kuma na fasa dan na fahimci akwai abinda take ?ullawa. Kasan shegiya ce itama, kuma ta hasala ?warai da gaske akan kwasar kayanta musamman da Yazeed Win bai iya kwaso na amaryar ba sai take tunanin da sanya hannunta a ciki. Shiyyasa a yanzu haka na shirya yin aiki da ita, kuma nan da kwana biyu kacal nake so ta shigo tarko na.....
? ? ? ?  Sai da kai Baa! Shiyyasa bana gajiya da maka kirari dan ka cancanta, ALLAH kuwa ubana yafi na kowa dan nawa kowace SaranSarama ya haWa. Ga ilimin bokon gana arabi amma yafi jahili jahilci. Ka tafka tsiya a ?ar?ashin ?asa a zahirin rayuwa ko damo baya nuna maka ha?uri sai jinin Mabera tushen aiki...
? ? ? Wata dariya Daddyn Nazeefa ya sanya mai ?arfi, Sille na tayasa da iya iyawa, sai kuma suka cafke. Cike da so da ?auna ya ce,  Son ALLAH yay maka albarka, in dai bakin iyaye nada tasiri akan ?a?a koda kuwa iyayen tantirai ne to kai dai bakai babu taSewa. Dan kamar uban kamar Wansa, idan kaji ana ainahin TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE to Mabera ne da Wansa, wato Junaid Wan Junaid  .
? ? ?  Yess Baa! Sai da kai. Fitaaaa manaaaa! .
? ??  Tuni na fice Son. Dan haka bayan wancan shirin nawa naka wasan na haWaka ne ni da kai. Manta da wannan video Win bazai baka kuWin da kake bu?ata ba aiki zamuyi mai Wungum a lokaci guda da zai mallaka mana Alhaji Usman Chalawa da da tsohon Ambassador kuma Wan kasuwa Alhaji Aliyu Abubakar Darma, abokin ?uruciya kenan, rayuwar jami'a ai ba wasa ba, wannan abotar tamkar ?an uwan taka take. Lokaci yayi da zan maida murtani da ?arfin ?wanji, sannan da ?arfin basira. Ta ?arshe Kamila, itace zata fi kowa amsar sakamakon wannan wasan, dan gaba Waya ma wasanta ne, Aliyu Darma ya biya nashi tuni harda gyara, yanzu albarkacin ta zaici shima shi da ?a?ansa
? ? ? ? Wani irin cafkewa sukayi kamar ba uba da Wa ba. Daga haka Mabera ya fara tsarama Sille bayani filla-filla.....

_________&

? ? ? ?? A can Sille da ubansa na ?ullawa, anan Kamila ma ?ullawar take yi. Dan shiri take yi sosai na wasan ?arshe akan Oum, Abah, da yaranta uku zaratan mazaje. Plan b Nana da ?a?anta. Sille da mahaifinsa sune plan c Winta in har ta tabbata Junaid na a raye dolene ta maidashi gaba da inda ta aikashi a baya. Dan haka a yanzu shiri ne na gaske, dan ta shirya karSa daga rasa Aliyu Darma amma kuma dole ne ta tsira da Fadeel, Fawzan, Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Dan bazata yarda tai 2-0 ba. Sai dai Fateema ta Wauki wannan makin wlhy. Dan tabbas in dai tana raye dole ne Fateema ta rasa ALIYU DARMA, da ?a?an ALIYU DARMA. Ita zata mallaki ?a?an, Aliyu ya mutu, Fateema ta ?arasa rayuwarta a ciwo. Dan bazata taSa rayuwa a wannan duniyar Aliyu Darma na raye shima a wannan duniyar ba tare da wata ba ita ba. Dan haka kowa zai rasa, sai dai ita zata tashi da ?a?an Aliyu Darma kamar yanda ta faWa.
? ? ? Tai wani makirin murmushi, fuskarta data gama lalacewa da rama na sake bayyana tayani muninta a fili.....

________&

? ? ? ??  Mama magani ya iso yau da safe yaya tsarin yake ne? .
? ? Saheeba ce mai maganar tana le?e-le?e gudun kar wani ya jita. Daga can Nana ta ce,  Duka kowa akwai tsarin da zaki bashi nashi batare da fahimtar kowa ba. Amma yanzu zaki fara da matar Ajwaad ne. Dan zubar da cikin jikinta zai saka hargitsi da tashin hankalin mutanen gidan ta yanda zakiyi amfani da ruWewarsu ki ciyar da sauran nasu tsarin. Saheeba kada kiyi wasa. Ki nutsu dan ALLAH kiyi abinda ya dace. Kinga kayan nan kaf abinda na tara na kadara da wanda kema kika saya ne dana Nuratu harda aron kuWi na sake yi a wajen Hajiya Turai duk na haWa. Dai-dai da sar?o?in ki na gwal da jarin sana'arki duk suna a wannan kayayyakin, to ku lura ke da

93 / 138

Chapters