Advertisements
Chapter 69 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   69 / 138

204K to 207K   out of 412.8K words

shi Winne kwantar da hankalinki baki da matsala dani. Duk abinda kike tunanin dai-dai ne ?ofa a buWe take kiyi abinki. ya ?are maganar da raSata zai wuce. Da sauri ta ri?o hannunsa tana fashewa da kuka. Fisgewa yay ?o?arin yi ta ri?esa da hannu biyu duka da iya ?arfinta kuma.
? ??  Amma kin san zan iya marinki ko? .
? ?  Gara ka marenin, wlhy gara ka mareni da wannan fushin dai da kake yi dani. Ka tausaya min dan ALLAH ka duba min, wlhy ji nake kamar zuciyata zata tarwatse. kuka mai ?arfi ya sar?eta. Shiru kawai Abah yay yana kallonta. Kamar wanda ya fahimceta sai kawai jitai ya zare hannunsa yay gaba. Sai da yaje zai shiga bedroom a kausashe ya ce,  Ki gayama ?an uwanki akan wannan bikin wlhy-wlhy duk wanda ya nema Waga hankalin iyalina nima sai na Waga nashi. Ba kuma lallai dole bane sai ?a?ana sun zauna da ?a?ansu. Hanawa su Wauki wani mataki akan yaran adalcina ne, amma a wannan gaSar duk wadda tace zata kawo musu shirme zan basu damarsu ta Waukar matakin da duk sukai niyya dan ina son farin cikinsu. Dan ko kece kika ce zaki Waga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu. Idan kunne yaji jiki ya tsira .
? ? Yay shigewarsa. (Dan ko kece kika ce zaki Waga musu hankali sai dai ki bar musu gidan ubansu) Wannan kalma tai matu?ar dukan zuciyar Mamy da girgiza mata duniyarta. Ta kuma fahimci eh lallai da gasken gaske Abah yake yi. Itako ta shiga uku, shin mike faruwa ne? Anya kuwa? Anya ganin da Abah yay musu sun fito a sashen Ajwaad ne kawai matsalar kuwa? Kai da mamaki gaskiya, akwai lauje cikin naWi. Dole akwai wani abinda ke a ?asa. Batun Ajwaad da Maanal ya faWo mata a rai. To kodai binciken da take tunanin zasu iya yi suka yin ne?. To amma ta ina? Inma zasu bincika ai Doctor ne kwai, jiya jiyan nan kuma Hajiya Turai ke sanar mata a binciken da tai Dr Tofa ma baya Nigeria kusan shekara biyar kenan. To kodai munafukar matar can ce tai mata wani ?ullin?. Zuciyarta tafi tsayawa a hakan, sai dai hujjar ta mata rauni da yawa. Amma ko akan batun auren nan ta tabbata akwai saka hannun Fateema. Kenan dai Fateema ta cita wasa. Ajwaad ya auri ?ar ?awarta, Fawzan ?ar ?anwarta, ga Fadeel ma zai auri ?ar ?awarta. Shike nan ya?inta na shekaru ya tashi a banza. Tunda ga Saheeba nata auren na rawa, Nibras ma bata sakata a sahun mata ko wanda take amfana. Auren Nuratu na tangal-tangal. Tana a ruwa fa kenan har yana shirin zuwa mata wuya idan bata tashi tsaye ba. Ga wancan batun duk da tana ?o?arin hidden Winsa yana nan daram a ranta, yana kuma cimata zuciya.....

________&

? ? ?? Anan Sangaren Oum kam shirye-shiryen biki suke hankali kwance. AA ya riga yay order Win kayan lefen Fawzan tuni, yanzu kuma gana babban Yaya. Duk da zai iya yin hakan shima saboda kawai yaje ya Wan huta da tashi amaryar sai suka tsiri tafiya Dubai wai haWo lefe shi da RK da Maanal da Nuwaira. Sarai Oum ta fahimcesu, dan haka batace komai ba face binsu da addu'a. Shima Abah koda suka faWa masa addu'ar yayi. Dan daga shi har Oum Win ?an ba ruwa na ne.
? ? ? Haka kuwa suka shirya suka tafi, suka bar su Oum kuma anan Nigeria suna shirin fara gyara amare ita da Hajiya Shuwa. Sai dai ita Najma ma can wajen Ammie zata zauna nata gyaran. (Kun san dai itama Ammie tsohuwar mai gyaran jiki ce) Dan haka Hajiya Shuwa data haWa duk abinda ake bu?ata aka aikama Ammien, itama kuma daga can Ammien ta aiko musu da tata basirar da za'ama Ameerah da Maimoon da itama ta dawo nan Abujan amma a sashen Oum zata zauna dan ba'ayi abin kunya suruka Hajiya Shuwa tayi gyara ba..
? ? Babban Yaya da Yaya Fawzan kuma sai suka maida hankali a gyaran sassan nasu. Amaren zasu zauna a downstairs kafin a gama musu nasu ginin. Amma duk da haka sai da aka gyara duka sashen biyu. Hakan yasa Nibras komawa sashen Oum da zama. Saheeba dama har yanzu tana a sashen Mamy. Duk da dai sunata zuba rikici ita da Mamyn, dan kota sakata abu yanzu batayi. Mamanta da itama ta tadama Mamy hankali tace Saheeba ta taho gida amma Saheeban tace babu inda zataje, dan Babban Yaya ya rantse mata indai ta fita a gidan ta fita kenan na har abada.
? ?? Hajiya Turai ce da ?yar ta sasanta Mamy da Maman Saheeban. Ta kuma nuna musu illar bari kan nasu ya rabu. Acewarta a yanzu ne ma ya kamata kansu ya haWu suyi ya?i na gaske dan abaya wasan yara sukayi. Fargarwar tata ta shigesu, dan haka suka sasanta Win itama Saheeban mamanta ta ?waSeta. Ita kuma ta bazama gidan bokaye da malamai neman sa'a...

_______&

? ? ? Rayuwa a Dubai ta sati Waya kacal rayuwa ce mai tsayawa a zuciya da Sargon jiki tsakanin Maanal da AA. Hakama Nuwaira da RK ba'a barsu a baya ba. ?ara'in amarci akai sosai mai kuma ?ayatarwa. Sunyi wani fresh abinsu musamman Maanal data fara shiga wani yanayi na biyema fitinar AA. Shi kanshi har mamaki abin ya fara bashi. Tana shan wahalar amma tana nane da shi yanzu ba kamar da ba. Takai wani lokacin ma ita da kanta take takaloshi koda zatai masa rakin daga baya. Ranar dai suna hira shi da RK Maanal da Nuwaira kuwa sun fita kasuwa dan yau su AA Win sunce sun gaji sukam, sai AA ke Wan yima RK tambaya akan hakan. Murmushi RK yayi dan shikam tun a Nigeria ya fahimci Maanal nada shigar ciki. Amma rashin tabbas ya sashi yin shiru tunda mata nada abubuwan ban mamaki a tattare da su.
? ? ? Cikin nuna rashin tabbas RK ya ce,  Ciki zai iya saka mace hakan, dan wani lokacin idan suna da ?aramin ciki sukan bu?acemu a kusa da su fiye da ko yaushe. Dan a farkon aure gaskiya mune zaka samu muna zalamarsu amma su ba sa jin daWin yanayin gaba Waya wahala tafi yawa. Shiyyasa sukafi son a tsaya iya romancing kawai. Wata macen zata iya maka haihuwa uku sannan ta fara sanin muhimmancin yanayin. Wata Waya, wata biyu wata ma har biyar. Idan kuma ba'a haihu da wuri ba zakaga an Wauki shekaru, bawai basa so bane gaba Waya, a'a badai kamar mu ba, doke zaka ga dai sai sunja shekarun nan sannan komai me daidaita musu. Sai dai idan suna shan ?wayoyin saka ?arfin sha'awa ne ko wannan kayan nasu na mata
? ? ? Cikin gamsuwa AA yake jinjina kansa. A ?asan zuciyarsa kuwa wani irin farin ciki yake ji da fatan ALLAH ya tabbatar da hasashen RK Win na batun cikin ne bawai shan maganin Maanal keyi ba duk da dai bai taSa gani ba. RK da duk ke lure da shi ya ce,  To amma fa kaima sai ka Wan sassauta a irin wannan yanayin. Dan in har hasashenmu ya zama gaskiya cikin ne ALLAH zaka iya Saro shi. Ka aikata hakan kuma ba yafe maka zamuyi ba .
? ? ? Harararsa AA yayi, sai kuma ya Wauke kai gefe da faWin,  Shiyyasa bazan taSa Kawu da kai ba dan kawun banza ne anan .
? ? ? ?? Dariya RK ya shiga yi. Dole AA Win ya tayashi da murmushi.

& Satinsu Waya suka dawo Nigeria, a kallo Waya kuma Oum ta tabbatar da hasashenta akan Maanal. Dan komai na jikinta ya ?ara canjawa a sati Wayan nan. Sai wani mahaukacin ?yau takeyi da haske. Sai murmushi ya kasa barin fuskar Oum, duk motsinta addu'a take na ALLAH ya tabbatar da hakan. Da ?yar ta iya danne zuciyarta bata gumtsawa Abah ba........
'?





*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*09032345899*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________


....Washe garin da suka dawo wasu cikin ?an Kano suka iso Abuja. Dan za'a kai lefen Najma Zaria. Koda Maanal ta nuna zataje AA yace bai yarda ba. Dan tunda RK ya masa kanta farga yake wani kaffa-kaffa da al'amarin Maanal Win duk da ba tabbas. Koyaya yaga zatai wani aikin da zai jijjiga mata jiki yanzu zai amshe gara shi yayi. Tunma yana yi a su kaWai harya kasa daurewa bai iya kawaicin hakan ko a gaban Oum. Ita ko Oum babu ruwanta, irin wannan abubuwan kawaicema yaran nata take tayi kamar bata gani ba. Dan farin ciki hakan ke bata akan kulawar da suke bama matan nasu.
? ? Kamar wasa rigima ta kacame akan zuwa Zaria. Dan AA ya dage kuma ya Sata rai a yanda Maanal Win bata taSa gani ba. Ita kuma ta rigime akan sai taje sai masifa take masa kamar dama jiranshi take yi. Kuma tana masifar tana kuka. Takaici ya sashi yin?urin baro mata sashen gaba Waya. Amma sai ta biyoshi yana gab da fita ta ri?eshi wai wlhy bazai fita ba.
? ? Tsayawa yay yana kallonta, fuskarsa babu alamar wasa ya ce,  Sakeni .
? ? ??  An?i Win .
Ya faWa a fusace. Sai ma ya rasa mi kuma zai yi. Dan kallon ma abin yake a matsayin rainashi ta farayi ne ko mi bai san yazai fassara ba. A wani kuma gefe na zuciyarsa yana ?ara yarda lallai mata zuma ne ga za?i ga harbi. Duk yanda kake da su idan suka kuma maka wani takaicin sai kaga kamar basu taSa ma saninka ba. Wannan yanayin dakan gitta lokaci zuwa lokaci shine iyaye kullum ke tisa mana kalmar ha?uri a kansa, sai anyi ha?uri da mata sai anyi ha?uri da mata. Idan ka fusata ka zafafa su kuma matan su kalleka a matsayin namiji ba Wan goyo ba. Jiba fa ?ar ficiciyar yarinyar nan daya raina da hannunsa ce yau take neman birkita masa lissafi gaba Waya. ?iri da muzu yace baza'ai abu ba tace sai tayi. Yayi yun?urin bar mata gidan yaje ya Wan huce ta masa Waurin goro tana mazurai wai bazai fita ba kai kace itace Oum. Oh shi Wan Aliyu da Fateema yau yaga takansa.
? ?? Kallonta ya sake yi, yanda take hura hanci wlhy saika Wauka duka zata lakaWa masa. Anya a duniyar nan akwai wanda yakai mata ?arfin hali kuwa. Ka gansu abu ba abu ba amma fitinarsu da rikicinsu yafi na ya?in basasa girma. Nan kuma anjima fa idan ta huce sai ta rungumeshi ta masa kiss ?auna ruwa-ruwa. Nisa'u na rijalu kenan.....
? ? ? ?  Ni ka daina kallona .
? ?? Maanal ta faWa tana fashewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke, cikin daidaita nashi yanayin ya kama hannun nata ya jata suka koma cikin falon, zaunar da ita yay shima ya zauna. Idanunsa na binta da kallo mai tausasawa ya ce,  Na zauna yanzu mi kike so ayi? .
? ? ? Sai da ta share hawayenta sannan tace,  Ni ka barni naje .
? ?  Besty kima daina Satawa kanki rai da batun tafiyar nan dan bayinta za'ai dake ba. In da ace jirgi ne sai na barki, amma tafiyar mota daga nan Abuja har Zaria badani ba wlhy. Ban shirya asara ba gaskiya. ZaSi dai wani abun .
? ? ? ? ?  Ni ba abinda nake so, Zaria kawai nake son zuwa. Da da nake tafiya a motar miya saman, sai yanzu zakace wani bazanje ba bayan kuma kowa zaije. A can Dubai wane irin yawo ne bamuyi a mota ba sai anan da yake kana jin mugunta..
? ? ? Wai yana jin mugunta abin dariya. Dannewa yay cikin lallashi ya ce,  Ki gane mana Besty, titin Nigeria dana Dubai ai ba Waya bane b.....
? ? Baima gama ba ta sake fashe masa da kuka tana faWin,  Ni ban yarda ba! Ni ban yarda ba. Kawai sai naje! Sai naje .
? ? ? Shi kam yau AA yaga bala'i ai ganin idonsa. Wlhy ta birkice masa gaba Waya kamar ba Maanal Win ba. Sai kawai ya zuba mata ido ma yana kallon ta. To sai kuma sabon masifa, ita dan mi zaiyi banza da ita. Dan mi tana magana zai yi shiru. Ita bazata yarda ba, ita miye-miye.
? ? ? ? ?? Da yaga abin bana ?are bane sai ya fara tunanin hanyar da zai gudu. Can dabara ta faWo masa. Sai yay Wan gyaran murya yana mi?ewa da faWin,  Bari na kawo miki ruwa ki sha sai muyi magana naga yanda za'ai tafiyar ta yiwu, in ma ni zan kaiki sai na kaiki da kaina .
? ?? Da farko ri?eshi tayi, sai kuma ta sake shi tana share hawaye ta ce,  Kuma mara sanyi nake so, ka haWo da fresh milk mai sanyi ka saka min inibi da dabino a ciki .
? ? ?  An gama Aunty .
?? Ya faWa yana nufar hanyar kitchen. HaWa mata duk abinda tace tana so yayi, ya buWe back door ya gudu. A can compound ya samu su Naufal na ball da yaran ma?wafta, sai ya kirashi yace yabi ta back door ya Wauka abu nan akan work table ya kaima Auntynsu falo tana jira. Shi kuma ya shige mota yabar gidan. Gara yaje ko zagaye gari yayi idan ta huce ya dawo.
??
? ? ?? >?#?>?#?AA bawan ALLAH yau Nisa'u sun nuna maka hali kenan=??? Maanal karfa kisa mu Aurama brozan su o'e Nuratu fa. Koda yake ki kiyayi ranar da suka Rijalu zasu murWa nasu kambun rigimar tommm=??.

________&

? ?? A lokacin da AA ke fita anan Sangaren Mamy ta fito wanka ne ta samu wayarta na ringing. Koda ta duba taga number ce kawai babu suna ajiyewa tai tana jan ?aramin tsaki. Sai dai me kiran sai ya cigaba da shigowa babu ?a??autawa harta ji haushi ta Waga a fusace. Tana fara masifa Sille ya wani kwashe da dariya daga can. Sai tai tsai tana saurarensa zuciyarta na bugawa dan ta gane sa. A ranta tace ubanwa kuma ya bama wanan Wan iskan number ta. A fili kam cikin ?arfin hali ta ce,  Malam waye kai? .
? ? ? ?  Ai kin san waye ni Mrs Darma. Karki wani yi pretending. A tunaninki kin kashe waccan wayar kin tosheni ke nan. To ai abinda baki sani ba ni kamar kurege nake bana hanya Waya. Hanyoyine dani kashi-kashi harta inda bakiyi zaton zan fasa ba. Ina muka kwana ina muka tashi? Bake ba kuWina mike faruwa? .?
? ? ?? Tsaki mai kauri Mamy taja. Cikin dakiya ta ce,  Kai bari kaji na fika iskanci wlhy, kai ubanwaye daka isa ka sani yin abinda banyi niyyar yi ba. An?i a baka kuWin, kuma an?i a yarda a ganka Win yi duk abinda kaga zakayi .
? ?? Wata irin mahaukaciyar dariya Sille ya sanya daga can. Tare da faWin,  Oh haka kikace? Shike nan zanko baki mamaki. Amma bisa wasu dalilai zan baki dama ta mintuna talatin yanzun nan kacal. Koki fito yanzu ki sameni a bayan gidanku da kuWina 10m, ko kuma yanzu na nuna miki ni bana magana biyu, dan zaki ganni har cikin Wakin barcin ki, sai ki fara ?irga lokaci.....
? ?? ?ittt ya yake kiran. Ba ?aramin bugawa zuciyar Mamy tayi ba. Tai shiru kamar mai nazari tsahon sakanni sai kuma ta taSe baki da faWin,  ?an iskan banza, su masu gadin dake gate Win wawayene irinka da zasu barka ka shigo har nan . Hankali kwance ta shiga shafa manta. Kafin ta mi?e ta nufi closet Winta dan saka kaya. Harda su kallon agogo kuwa tana sake jan tsaki. Ta gama shirinta tsaff ta fito dan gidan wata tsohuwar aminiyarta take son zuwa. Da bala'in sauri tai baya zata fasa ihu jikinta na rawa saboda ganin mutum zaune a bakin gadonta.
? ?? Sille dake kallonta yay wata shegiyar dariya da faWin,  Haba relax mana Mrs Darma. Sai kace bake Win ba.
? ? ? A rikice matu?a Mamy ta nufi ?ofa, ta danna mata key sannan ta dawo inda yake. Bakinta har rawa yake ta ce,  Ubanwa ya shigo da kai har nan? .
? ? ?  A ?afafuna mana. Ai na faWa miki ni bana magana biyu kamar ubana nake.
? ??  Waye uban naka? Kai wanene ma kai? Mi kake so a wajena? .
? ?  Tofa irin wannan tambayoyi haka wacce zan amsa a ciki . Sai kuma ya zame hular rigarsa data rufe masa fuska yana cigaba da faWin,  Kalla fuskar ba?ya bu?atar bayani .
? ? ? KaWan ya rage Mamy kuwa ta zube ?asa tsabar razana. Junaid fa take gani, Junaid dai Junaid. Amma taya Junaid zai cigaba da zama a iya wannan shekarun har yanzu. Wannan fa bazai wuce talatin da tara ba haka. Dan zai girmi Fadeel gaskiya kamar da shekara biyu ma. Jiri ke neman Wibarta ga numfashinta sai wani fisga yake da ?yar. Shi dai Sille kallonta kawai yake. Sai da yaga kamar zata sume sannan ya mi?e zai kamata. Hannunsa ta bige tare da faWin,  Karka taSa ni . Hannayensa ya Waga sama tare da ja baya ya koma ya zauna inda ya tashi, itama ta daddafa ta kai zaune cikin sofa, ruwan dake a saman table ta Wauka tasha tana hakki ga idanunta sunyi jazur. Da ?yar ta iya sake furta,  Wanene kai? Miya kawoka waje na? .
? ? ?? Murmushi Sille yayi mai haWe da dariya. Sai kuma ya taSe

69 / 138

Chapters