Advertisements
Chapter 112 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc Hausa Novels
Advertisements

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   112 / 138

333K to 336K   out of 412.8K words

safe da raWe-raWen sunan haihuwa da aka samu a ?auyen har guda uku. Yara dake cin uban gudu suna ihu ne suka fara fargar da manya gari halin da ake ciki. Dan kuwa sojoji ne har kusan su hamsin sukaima ?auyen Giro dirar mikiya. A take kuma suka dinga kama mutane ana zubawa a motoci. Hankalin mata ya tashi matu?a gaya, ga tsoro sunata afkawa Wakuna suna kulle kansu ga tashin hankalin anata kame musu maza da yara matasan gari. Dan kuwa dai basa Waukar mata da kannanun yara sam. Da al'amarin yakai kukan kure har cikin gida suke shiga saboda wula?anci da tozarci ana za?ulo mazan da suka samu Suya da matasa. Ta wannan hanyar ne suka Wauki Babu dake fama da kansa dan zuwa yanzu jiyya yake mai tsananin gaske. Suka kuma haWa da Gwaggo da Sailu dake kuka da ihu da kururuwar a taimakesu amma basu sami wannan taimako ba kam. Haka aka jefa su a mota aka wuce da su cikin babban birni, ashe al'amari babbane, ba nan za'a tsaya da su Gwaggo ba su. Dan sauran mutane an zubesu anan amma Gwaggo, Babu, Sailu an wuce da su birnin tarayya Abuja.
Dan danan kuma aka saki Update wai an samu criminals da suka shiga garin Giro, dan haka jami'an tsaro sun za?ulosu kaf yanzu haka suna a hannun hukuma. Kafin kace mi labari ya fara yawo a media tamkar wutar jeji.......

__________&

Azaba tayi matu?ar isar Mabera da Sille a cikin rami. Shima kansa Maberan ganinsa neman gushewa yake saboda azabar ciwon kai. Da ?yar ya iya kama Sille suka fito ta cikin motar, babu zato jami'an tsaron dake ata kusa da motar sai gani sukai tana motsi. Dan da nan sukai shirin kota kwana duk da a farko sun tsorata da tunanin ko wani makamin ne mai fashewa. Sai da kukan Sille dake kiran a taimakesu ya ratsa kunnuwansu sannan suka shiga matsawa bindigu a Wane. Cak suka tsaya suna kallon mutanen da suke wahalar nema tsahon kwanaki amma babu ko alamarsu. Dan nan suka zagaye motar, sai kuma aka fiddosu. Nan fa aka fahimci daga inda suke. Motar aka janye sai ko ga rami. Ai babu Sata lokaci jami'an suka shiga binciken irin ramukan sai gasu da yawan gaske harda ?aton ramin da suke tara gawarwakin mutane idan sun kashe.
Babu Sata lokaci sukai kiran IG. Kafin wani dogon lokaci jejin ya cika da jami'an tsaro da ?an jarida masu ?arfin hali. An tattare su Sille akayo gari da su domin kaisu asibiti, gari kuma ya Wauki labari kamar wutar jeji. ?an jarida tuni sun fara sakin Update a media tako ina.
Matu?ar tashin hankali mara misali iyayen gidan su Sille sun shiga. Burinsu kawai samun jami'an tsaron da suka kamasu su basu kuWaWe masu nauyi dan gama musu da su kawai kafin ma aje asibiti dasu. Sai dai ina hakan ya gagara sakamakon maganar ta girma da yawa balle shugaban ?asa da kansa ya saka baki, ya kuma Wora alhakin controlling Win case Win ga IG da kansa ba sa?o ba ko haWa wani kwamiti..
General hospital na Abuja aka wuce da su kai tsaye. Aka zagaye jami'an tsaro da Wakin da aka shiga dasu a tare. Sai da ya zam hatta likitocin da zasu dubasu zai da Jami'an suka tantance suka kuma bincike sannan suke shiga Wakin. Dan danan aka rufu a kansu su duka biyun dan duk suna a cikin mawuyacin hali mai firgitarwa...

________&

Su AA na hanyar tafiya gida daga asibiti da suka bari a fusace suka sami labarin. Dan Uncle Najeeb ne yay kiran Babban Yaya yace sunga abinda ke faruwa kuwa a media yanzu-yanzun nan? .
Babban Yaya yace masa a'a. Ya ce ku duba maza. Koda ya yanke wayar Yaya Fawzan yay parking a gefen titi kowa sai ya fiddo wayarsa. A tare suka saki murmushi da sauke ajiyar zukata. Babban Yaya yace ma Fawzan.  Juya mota maza mu koma asibiti Fawzan .
Babu musu Yaya Fawzan yayi hakan. Lokacin da suke dawowa suma su Oum labari ya iso musu ta hanyar gani a television. Ga kuma Mamy dasu RK suka rufu a kanta sai hankalin Oum ya rabu biyu. Koda su Babban Yaya suka shigo kallo Waya tai musu ta Wauke kanta. Suko ai ita suka nufa suka rungume a tare. Dan wlhy ba ?aramin farin ciki sukaji da zancen kama matsiyacin mutumin nan da akai ba. Sai dai suna cikin wannan murnar kuma sai ga wani sabon labari akan abinda ya faru a ?auyen Giro. Lallai babbar magana kenan....

________&

Maanal na tsaka da bibiyar labarin kama Mabera da Wansa taci karo da bada?alar Giro kuma. Ai babu shiri ta tashi zaune daga kwancen da take cikin kujera a falo dan bata jima da baro sashen Oum ba su duka su suna tare da su Umma saboda ?an anguwa dake zuwa yin gaisuwar rasuwar Anum da jajen abinda ya faru. Tunda babu Oum sai su Umma ba?i dole su suke zama. Da farko dai komawa Maanal tayi kamar wadda ta suma a tsaye sai ga kiran Shahidah ya dawo da ita. ?asa Waga wayar tayi harta tsinke aka sake kira sannan. Shahidah dake kuka ta ce,  Manaal kinga abinda ke faruwa kuwa? .
Sharr hawaye suka shiga rige-rigen sakkoma Maanal. Wato shifa tushenka dai tushene komi akai maka na bakantawa a cikinsa tuwo sunansa tuwo, sannan jini sunansa jini. Murya na rawa Maanal tace,  Na gani Didi, amma wlhy ni naji a raina wannan zancen ba gaskiya bane. Kaf asalimu babu Wan ta'adda akwai abinda yake ba dai-dai ba dai .
 Tabbas maganarki nakan hanya, amma duba videon dana tura miki ta WhatsApp sannan .
Kafin ma Shahidah ta rufe baki Maanal ta katse kiran, WhatsApp Win ta shiga dama data Winta a buWe take. Videon ma har ya buWe. Koda ta shiga nutsuwa tai tana kallon yanda ake Wibar mutane kamar an samu wasu dabbobi. Da farko bata fahimci komai ba face ganin yanda ake tozarta musu ahali dan taga waWanda ta sani sosai a ciki harda ?an gidansu duk da wahala tasasu canjawa daga yanda ta sansu a shekaru tara baya. Shahidah tai kiranta tace,  Mi kika gani? .
 Banga komai ba Didi sai cin mutunci da tozarta ahalinmu .
 Ba shine sa?on da nake son isar miki ba Maanal. In ce dai baki manta da yaron tsohon mutumin nan da yace hana sonki ba har ya Wakko su Gwaggo ya kawo Kaduna shekara Waya data wuce? .
 Tabbas zan iya mantawa da shi Didi, dan bawani kallon tsaff nai masa ba a lokacin hatta shi kansa tsohon banzar. Amma kimin bayaninsa mana? .
 Ba bayaninsa keda amfani ba, tabbatar da shi Win ne ko bashi bane mai amfani. Ki ?o?arta dai bari na amsa kiran Amaal ina zuwa . ?itt Shahidah ta yanke kiran, dai-dai Maanal na kaiwa zaune jagwab sai ga AA ya shigo. Kai tsaye inda take yayo yana faWin,  Are you okay? .
Kanta ta jinjina masa kawai, sai kuma ta mi?a masa wayarta tana faWin,  Besty zaka iya gane yaron mutumin nan Sen... Bukar dan ALLAH? Ba Wansa na cikinsa ba, wanda muka taSa haWuwa da shi a ?ofar Mawaad harda su AS randa kuka fara Waukata a mota? .
AA dake kallonta ya ce,  Sosai ma kuwa, duk da ba yaron da kowa ya sanshi da shi bane sai ta hanyar neman matan banza da yake masa ni na sanshi dan a kanki ma har kamashi sasa anyi yay kusan sati biyu a police station sai shi Bukar Win ne ya fitar da shi .
Sosai Maanal ta sauke ajiyar zuciya, tare da faWin duba videon ka gani dan ALLAH  .
Komai bai sake cewa ba ya amshi wayar ya buWe videon, nutsuwa yay ya kallesa daga farko har ?arshe duk da kuwa da tsawon mintuna biyar ne. AA ya jinjina kai tare da dawo da videon baya yana nuna mata fuskar Rabilu daya tsayar dai-dai shi, abin mamaki yana sanye da kayan sojoji shima.  Tabbas wannan shine, hakan na nufin wannan abun shirine ke nan? Amma taya akai Bukar yay amfani da jami'an tsaron soji haka? .
 Ta hanyar makirci mana in har ta tabbata shi Win ne da hannunsa a ciki. Zai je ya shirya musu abinda basu sani ba, kuma su basu da laifi, a halin da ?asar nan ke ciki musamman ta yankin namu ko yaya wani magana zai fito akan bara gurbi jami'an tsaron mu zasuyi kowane irin yun?urine su, kuma basu da laifi dan aikinsu ne yin hakan a garesu kuma shine dai-dai ..........
'?



Na ha?ura AA aci uban kawuna a wannan gaSar>?q? *_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
.......... Lallai maganarki na kan gaskiya kam, kuma bana raba Wayan biyu shine ya shirya komai, wato abinda akai musu a asibiti shekaran jiya shine zasu juyashi akan bayin ALLAH da basu ji ba basu gani ba. To lallai banga ta zama ba. Dole ina bu?atar ganawa da shugaban ?asa yanzun nan .
 Amma Besty kai kasan hakan bamai sau?i bane. Haka nan Sakatatan rana tsaka kaje kace zakaga shugaban ?asa duk da kusancin da kake da shi a tsakaninku .
 Na sani Besty, amma wannan maganar bata waya bace ba. Dan haka bani wayata a Waki, cikin bed side drawer  .
Mi?ewa tai da sauri, dan wayar itace yake da ajiyayyun numbers na manyan mutanensa, baya kuma fita da ita ko ina daga office sai gida. TaWan fara haye stairscase da Wan gudu yace,  Please bar gudun nan tafi a hankali .
Juyowa tai ta kallesa, sai kuma ta koma yin tafiyar batare da tace komai ba. Babu jimawa ta dawo masa da wayar, yana tsaka da rubuta massage da zai turama shugaban ?asa sai ga su Babban Yaya da Fawzan har ma da su Baba Sardauna. Hijjab Maanal ta Wauka ta saka, sannan ta nufi ?ofa ta buWe suka shigo. Cike da girmamawa ta gaishesu bayan sun zauna. Jaje sukai mata na abinda ke faruwa, kanta a ?asa tana share hawaye Baba Sardauna yace,  Ba abin kuka bane kinji yarinyata ?ar albarka. Addu'a zamuyi kuma ALLAH na tare da masu gaskiya komai zai warware, in har basu da laifin komai za'a sake su.
 Ai bama su da shi, shiri ne kawai wannan abun Baba . AA ya faWa dai-dai yana gama turama shugaban ?asa text. Da mamaki duk suke kallonsa. Ya Wauki wayar Maanal ya latso musu hoton Rabilu.
Babban Yaya ne kawai ya gane Rabilu, ya kalla AA yana faWin,  Ajwaad wannan ba yana cikin tawagar yaran su Bukar Kaugama ba kuwa? .
 Tabbas yana ciki Yaya, dan yaronsa ne ma na kusa sosai. Idan ka kula bai san ana Waukar wannan video Win ba.
 Lallai bai sani ba kam, to miya haWa shi da kayan soji kuma? .
 Wannan shine Abin tambayar kuma abin nazari, amma idan zamu kalli al'amarin ta wata fuskar zata iya yiwuwa yaje musu matsayin wanda keda information Win ne, ko kuma su sojojin bana gaskiya bane ba...
Baba da yay shiru yana nazari ya ce,  Bazasu tura sojojin daba na gaskiya suyi wannan Wanyen aikin ba, akwai dai abinda yake ba daidai ba dole. Amma ina zuwa bara nai kiran mataimakin gwamnan nasu. Dai-dai nan Maanal dake hawaye ta dawo Wauke da basket data zubo gorinan ruwa. Sai kuma gasu Umma sun shigo harda Oum data baro asibiti da Ammie da suka iso ita da Hajiya Yaya. Karo na farko kuma da Hajiya Yaya tazo gidan Darma. Duk da halin da ake ciki kallon ko ina take tana faman jinjina kai....

Da gudu Maanal tazo ta shige jikin Oum, Oum ma ta rungumeta tana lallashinta saboda Baba Sardauna na waya da mataimakin gwamna, yana masa kuma bayani dalla-dalla ta yanda suma suke samun bayani a yanzu-yanzun. Dan ta Sangaren su shugabanni basu san komai ba suma sai yanzu da videos Win ke yawo, wanda aka samu wasu yara ne ?ammata suka Worashi a social media. Ya kuma tabbatar ma Baba a yanzu haka sun bu?aci ganin shugaban soji na jihar ma baki Waya. Sannan an sake tura jami'an tsaro garin Giro Win ma domin bama mata da yara da aka bari a garin tsaro.
Baba Sardauna na gama sallama da mataimakin gwamna ya ajiye wayar yana jinjina kai da faWin,  Lallai wannan ?ulli ya ?ullu. Dan haka bamuga ta zama ba dolene mu wuce Giro a yanzun nan. Sannan duk inda wannan yaron Kaugama yake a kamashi kafin suyi wani siddanarun makircin .
Dukansu sun gamsu da bayanin Baba Sardauna Win. Babu Sata lokaci Babban Yaya ya mi?e yana faWin,  Wannan aiki nane game da kama shi yaron Kaugaman, bara na nemi abokina Deen ......

_________&

Sen.. Bukar tare da abokan tafiyarsa na zaune cikin farin cikin nasarar da suka samu ga gasashen rago da drinks zagaye da su cikin katafaren falon da suke zaune. Babu abinda suke sai maimaita videon abinda ya faru da aka tura musu akai musu connecting Winsa da television suke suna kwasar dariya. Senator Mai-hula ya danna nama a bakinsa yana faWin,  Wato Kaugama kai shegen kanka ne, yanzu na yarda da maganar ka da kake cewa faWan fito-na-fito da yaron nan ba namu bane kodan siyasar mu, jiba cikin abinda bai wuce awa biyar ba ka sake hargitsa zukatan ahalin Darma gaba Waya, musamman shegen yaron nan mai taurin kai da izzar banza da wofi. Yanzu sai muga zai dawo da ubansa ne, ko zai ?wato yan garin surukansa, ko zai ji da kunyar mugun halin uwarsa. Wato matar nan fa da namiji ce itama shegiya za'ai a ?asar nan .
Dariya suka sake kecewa da ita. Alhaji Sallau ya amshe zancen da,  Ai ko yanzu sunanta ya shiga tarihin manyan jaruman shegun Nigeria, ni yanzu duk ba wannan ne damuwata ba ma, so nake kawai naji an sanar da mutuwar Aliyu Darma, sai kuma su Mabera suma naji jami'an nan sun kashe mana su shike nan ?urun ?us kan Wan Sera tatsuniyar ta ?are .
 Inafa zata ?are Alhaji Sallau. Ai in kaga ta ?are to shima wannan yaron AA Darma mun ?arar da shi. Idan ba haka ba fa zai kasance mana tamkar mun kashe MACIJI ne bamu sare kansa ba. Shifa wannan shegen yaron tamkar ubansa yake wlhy babu abinda ya bari nashi. Kaga kuwa ai akwai sauran tsalle idan har bamu kwantar da shi ?asa ba. Kawai ni abinda nake tunani mizai hana wannan wasan garin surukan nashi mu juyashi ya koma kansa kawai kunga mun jefa tsuntsu biyu da dutse Waya ko .
 Tabbas maganarka nakan hanya Hon... Ishaya Badikko. To amma ta yaya zamuyi hakan kenan? .
 Kowa ya Wanyi nazari na mintuna muga, idan bamu sami mafita ba sai mu barma gobe ko .
Duk sun gamsu da hakan, sai dai me a dai-dai lokacin da sukai shirun domin nazari a lokacin wayar Sen... Bukar ta shiga rurin neman agaji. Kamar zai share sai kuma ya Waga ganin Oler ne mai kiran sashi. Cikin harshen turanci Oler ya sanar masa akwai matsala fa. Ya duba media yanzun nan an sanar da kama Mabera da Wansa har ma an iso dasu cikin Abuja suna Genaral hospital. Tsabar tashin hankali ruWani da bugawar zuciya data samu Sen... Bukar a lokaci guda baima san ya saki wayar ?asa ba shima ya tafi luuuu yana neman zubewa sai da abokan nashi suka taroshi.
Tambayarsa suke miya faru, shi kuma faWi yake,  Mun shiga uku, na shiga uku shike nan an yanka ta tashi. Komai ya lalace wlhy .
 Wai mike faruwa Senator, Dan ALLAH ka gaya mana idan na tayaka kuka ne muyi tare, idan na taimakonka ne mu taimake ka. Amma kana abu kamar ba namiji ba .
Feettttt!!! Sen... Bukar ya fyace majina yana taba idanu da faWin,  Bazaka gane ba Alhaji Sallau, wlhy akwai matsala, akwai babbar matsala ne. An kama Mabera da Wan sa, Mabera da

112 / 138

Chapters