Advertisements
Chapter 65 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc Hausa Novels
Advertisements

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   65 / 138

192K to 195K   out of 412.8K words

aikin nan wata ala?a bata sake haWamu ba .
Ji Mamy tai kamar ta zandara ihu. Amma ta danne da ?yau zuciyarta sai bugawa take. Cike da damuwa ta ce,  Lallai akwai matsala Momyn Nuratu .
 Amma ni sai nake ganin abun duk mai sau?i ne. Ki zauna da shi Ajwaad Win mana. Nima kuma zan bincika inda Ra'iz Win yake
 Zama da Ajwaad ba shine mafita ba shiyyasa ma ban masa ko zancen ba har yanzu. Kin san wannan matsiyacin yaron Rafeeq ne ya baza musu zancen yarinyar virgin ce. Ina da tabbacin koshi Ajwaad Win babu wanda yay maganar da shi akan hakan har yanzu, alamun akwai abinda suke shiryawa. Nasan su wanene wannan family Win Turai, wlhy akwai damuwa. Gashi na saka a bincika min Dr Tofa Win ma har yanzu babu wani bayani. Idan nace kuma zanje Kanon da kaina a yanzu akwai damuwa .
 In dai dan wannan ne ki kwantar da hankalinki, daga yau zuwa gobe zansa a bincika mana Dr Tofa Win shima .
Mamy ta Wan ji sanyi a ranta, amma zuciyarta a birkice take fiye da farko. Tana ajiye wayar zufa na keto mata. Gadai Hajiya Turai ta tabbatar mata yaron da suka saka aiki ne akan Maanal. To miya haWashi da Junaid kuma? Sannan Junaid bai san da zaman jaririn can ba taya za'ai hotunan su su kasance tare a wajen mutum Waya? Yau ta shiga uku mike shirin faruwa da ita? Ga batun Abah na Waga mata hankali. Kada dai ace abubuwa ne zasu rikice mata a gaSar da take ganin nasararta zata fara, ?a?anta da komai nasu zai dawo tafin hannunta. Mijinta da take ganin ta gama nasarar wawashe zuciyarsa gaba Waya zuwa yanzu amma zai suSuce mata. Wai wanene wannan mai tura mata sa?on? Wanene shi? Miyyasa zai shigo duniyar ta a gaSar samun nasararta da ribantuwa da wahalhalunta da ha?uri da juriya da tai na shekaru aru-aru. Mafita Waya gareta a yanzu ta sanin wanene shi? T kuma yarda su gana kamar yanda ya bu?ata, to amma idan ta amince lokaci guda zai Wauketa shashasha. Bari ta Wan latsashi na wani lokaci kamar bata damu ba. KuWi kuma bai isa ya ci su ba....

__________&

Gaba Waya Yazeed baya gane komai a yanzu sai umarnin mahaifin matarsa. Ji yake ko wuta yace ya faWa zai faWa domin faranta masa. Nazeefa kuwa wata irin soyayya yake nuna mata kamar ya cinyeta. Balle da maganar cikin jikinta ta bayyana. Ita kanta sai abinda tace yayi yake yi. Dan haka take mugun tatsarsa kuWaWe, tana daga kwance shike mata tausa shine fita sayo mata abinci, shine mata wanki kai komai daya kamata tama kanta, tai masa matsayin matar gida yanzu shine keyi. Ga itama Sabuwa na zuba nata capacity Win a gefe. Sai da suka tabbatar sun gama samunsa a yanda suke so, sannan suka dawo gida Nigeria. Dawowar tasu kuma ta kasance rana Waya da dawowar su Ammie da Daddy suma.
Sosai Daddy ya zubama Yazeed ido, yaron ya rame yayi duhu daka ganshi kasan baya a cikin hayyacinsa. Ji Ammie tai ?walla sun cika mata ido, dan a wannan dambarwar dai shi Yazeed shi aka cuta wlhy, tana ?aunar Yazeed tana tausayinsa, dan yaron ya taka rawar gani a rayuwarsu suma, kuma in sha ALLAHU ta Wauki aniyar taimaka masa a wannan gaSar, bazata so cigaba da ganinsa a wannan yanayin ba. Daddy kam bazaka taSa fuskantar komai a fuskarsa ba. Amma shima al'amarin Yazeed Win na matu?ar damunsa a zuciya. Sai dai ya zuba ido ne dan Hajiya Yaya taji a jikinta. Sai dai tabbas bazai yafe mata ba, dan ta cutar masa da yaro. ?ansa babba abin sonsa, mai hankali da nutsuwa ga jin ?an iyaye ta zama sanadin da aka maida masa shi ?ar?ashin ikon mace..

Yaya Yazeed kam sai yaji kunyar ganin Daddy da Ammie, dan ko wancan dawowar har suka sake barin ?asar bai bari sun haWu ba duk da gida Waya suke kwana suke tashi. A mamakin Nazeefa sai taga yaje yana gaida Daddyn da Ammie. Wannan abu ya mata zafi, fuuu ta wuce sashensu batare data gaida Daddyn ba ita balle ma Ammie da bata saka rai ba. Sai ko Yazeed ya zabura ya biyota yana kira kamar zai faWi dan sauri. Hawaye suka zuboma Ammie. Daddy kam sai ya ma kauda kansa gefe.
?annensa da komai ka faruwa akan idonsu cike da ba?in ciki suka nufi sashen su suka sanar ma Hajiya Yaya. Aiko sai gata ta fito kamar zata tashi sama. Kai tsaye sashen Yazeed Win ta nufa, tana tura ?ofar kuwa ta buWe. Ta wani bugata da iya ?arfinta ta shiga falon. Turus taja ta tsaya hakama ?a?anta da suka biyota ganin Yazeed dur?ushe a ?asa yayi kneeling yana bama Nazeefa da tai wani zaman ?asaita ha?uri. Itako sai danna waya take tana taunar cingum kamar ma bata san da shi ba. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un.
Sarai Nazeefa taji shigowarsu amma sai ta watsar da su kamar bataji ba, sai ma cike da rashin mutunci ta dakama Yazeed tsawa.  Dalla malam yimin shiru, shashasha kawai dabai san ciwon kansa ba. Kai ko kunya bakaji ba zagam-zagam ka tafi gaida ubanka sai kace wani uban kirki. To wlhy ka jama kanka yau sai kaji a jikinka a gidan nan. Dalla tashi ka mana shara kana ganin waje duk datti .
Jiki Yazeed har rawa yake ya mi?e kuwa. Ko kallon su Hajiya Yaya baiyi ba ya nufi inda suke ajiye kayan shara ya Wibo...........
'?

Tofa Hajiya Yaya da alama anzo dai-dai wajen>?q?.

*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*

*_=???AJIYA A DUHU....=???_*

*_Bilyn Abdull ce >??
*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_BOOK 2_*

______________

.......Muryar Hajiya Yaya na rawa ta ce,  Yazeed! .
Yanzun ma baiko kalleta ba sharar sa ya fara ma. Ta ?ara kiranshi cikin tsawa. Ko gezau baiyi ba. Dariya Nazeefa ta shiga tuntsurawa. Sai kuma ta wani mi?e cike da gadara da raini taje gaban Hajiya Yaya ta tsaya, kallon sama da ?asa tai mata fuskarta da murmushin ?ularwa ta ce,.  Kima daina wahal da kanki, dan in dutsen arfa zaki hau kiyi ihu bazai taSa ya jiki ba. Dan yanzu shi Win ba naki bane, nawa ne nan, dama kin rainar min shine Hajiya Sadiyya .
Ta kira ainahin sunan Hajiya Yaya.
Hannu Hajiya Yaya data gama kaiwa wuya ta Waga ta Wauke fuskar Nazeefa da mari. Marin daya farfaWo da sauran ?a?anta da sukai sumar tsaye tunda akace yayansu yay shara. Gigitaccen ihu Nazeefa ta fasa da kiran sunan Yazeed. Bawan ALLAH tamkar ?yaftawar ido har yazo inda suke. Yay ?o?arin kama Nazeefa yana tambayar miya sameta? HankaWashi tai baya ya tafi taga-taga zai faWi saboda a bazata ta turesan. Ta kallesa hannunta ri?e da kuncinta Wayan ta nuna Hajiya Yaya da yatsarta manuniya.  Wannan jakar ce ta mareni, kuma wlhy idan baka rama min ba sai na tafi gidanmu yau....
Ai baki ma Nazeefa bata gama rufewa ba Yazeed ya zabura tare da Waga hannu zai sauke ma Hajiya Yaya a fuska. Ammie da ihun Nazeefa ya sata nufo sashen saboda sashen su Yazeed Win shine kusa da nata, duk tana iya jiyo hayaniyar tasu caraf ta ri?e hannun Yazeed Win. ALLAH sarki Hajiya Yaya harta rufe idanu tana jiran saukar marin Wanta a fuskarta=?%?. Abinda zai baka mamaki suma sauran yaran kowa ya kasa yun?urin komai sai idanu kawai suka rufe dan suma su Sabuwa ba ?yalesu sukai ba=??=?M?.
Kai Ammie ta shiga girgiza masa hawaye cike da idannunta. Muryarta na rawa ta ce,  Karka sake ka taSa wannan gangancin Yazeed. Komu da muke matan uba bama fatan ALLAH ya jarabceka da aikata hakan a kammu balle ita. Yazeed bakai data haifa ba, ko mu da muke ?ar?ashin miji Waya bazamu so taSa kwatanta haka ba gareta kodan shekarun da ALLAH ya bata a kanmu. Haba Yazeed Mamma ce fa...
ALLAH sarki, a mamakin kowa sai Yazeed ya risinar da kansa a hankali. Itama Ammie sai ta sakar masa hannunsa. Sum-sum ya wuce yabar wajen kansa a ?asa ya koma ya Wauka tsintsiyar daya yarda ya cigaba da shararsa. Ko kaWan ba haka Basariyya dake laSe jikin window tana le?e taso ba. Sai taji wani irin haushi da takaicin Ammie ya sake kamata. Cikin ?us-?us tace,  Munafuka ta hanamu kallon show. Ai mu irin wannan wasan muke so .
Ko kallon Nazeefa dake cika tana batsewa Ammie batai ba. Sai ma hannun Hajiya Yaya ta kama. Cike da lallashi da kwantar da hankali ta ce,  Yaya kiyi ha?uri muje .
ALLAH sarki rayuwa, Hajiya Yaya ko musu bataima Ammie ba. Ta sake kallon inda taga Hajiya Basariyya dake laSe tun Wazun ta janye idanun ta dake cike da hawaye. Suma yaran Ammie tace,  Ku wuce muje . Suma babu wanda yay musu. Har falo Ammie takai Hajiya Yaya, ta taimaka mata ta zauna sannan ta dubi yaran ta ce,  Ku bani ruwa mai sanyi .
Amrah ce dake hawaye taje ta Wauka mata. Koda ta kawo Ammie ta buWe ruwan Hajiya Yaya ta ba, nanma bata musa ba ta amsa ta sha, dan ji take tamkar zuciyarta zata fashe mata a cikin ?irji. Sosai tasha ruwan, dan Wan kaWan ta rage. Kamar dama ruwan take jira tasha kawai ta saki kuka. Yaran duk sunyo kanta a zabure zasuyi magana Ammie tai musu alamar suyi shiru. Duk komawa sukai suka zauna, sai da Hajiya Yaya tai kuka sosai sannan Ammie ta ciri tissue ta bata ta kuma sake bata ruwan tasha. Bayan wasu mintuna ta sake natsawa Ammie ta fuskanceta.
 Yaya kuka ba shine mafita ba, na barki kiyisa ne dan ki samu nauyin zuciyarki ya ragu. Kiyi ha?uri idan na shiga hurumin daba nawa ba. Amma Yazeed ba kuka ko biyema yarinyar nan ai rikici al'amarinsu ke bu?ata ba. Hasalima Wauke idanu daga garesu shine yafi alkairi, idan ba haka ba komai zai iya faruwa, saboda Yazeed baya a cikin hayyacinsa gaba Waya. Yanzu shi yana a wani matsayine da baya banbance fari da ba?i sai wanda yarinyar nan ta nuna masa kawai. To idan muka ce ta ?arfin tsiya zamu sakashi ya gane akwai babban matsala, dan maimakon ya gane Win sai ya sake rikice mana ne kawai, idanunsa su sake makancewa daga ganinmu. Dan haka dole zamuyi ha?uri da kauda kai na wani Wan lokaci, mu shanye zafi da radaWin da muke ji akan wannan sabon yanayin nashi tunda mun san bayin kansa bane. Ita kanta yarinyar mu barta ta rin?a jin tamakar ta gama samun dukkan nasarar da take bu?ata sai mu samu damar gayama ALLAH damuwar ya warware mana ita cikin sau?i kuma. Amma tankawa da nuna damuwar kai tsaye a yanzu tamkar sake zaburar da ita ne ta cigaba da sabon shiri a kansa, shi kuma dama illar sihiri Waura wani aikin akan wani, yakan sa asha wahala sosai kafin a raba mutum da shi. Wannan shine mataki na farko da zai taimaka mana. Mataki na biyu addu'a, Yaya Addu'a Yazeed yake bu?ata daga garemu baki Waya. Kuma taki ita ce mafi ?ololuwar daraja a gareshi, itace kuma tamkar yankan wu?a. Kasancewar ta a hakan kuma bazai samu ba sai kin daure kin sanyaya zuciyarki, kin yafe ma Yazeed kurakuransa. Ki rage barci, ki tashi cikin dare ki gayama ALLAH damuwar ki masa kuka ki masa bagiya shi mai ji ne mai gani, kuma shine ke raba abinda duk duniya babu mai kwatantawa. Yaya da zakiji wahalhalun da na fuskanta a rayuwata data zuri'ata da kince wannan na Yazeed ba komai bane ba. Amma wlhy ban taSa zuwa gaban wani na du?a nace ya taimakeni da garin magani ba. UBANGIJINA na fuskanta, shi kaWai na amince zai yaye min damuwar da ?uncin. Na ajiye maganar barci gefe, na sadaukar da rabin nema na a sada?a, na maida harshena da laSSana a ambaton UBANGIJI ne a koda yaushe. Na rungumi ?ishirwa da yunwa a kowane yini. Na sakama zuciyata jarumta da tunatar da kaina akwai fa wanda suka fini shiga ?uncin rayuwar, akwai wanda idan zanga halin da suke a ciki nawa ba komai bane ba. Na dinga tuna ANNABAWAN ALLAH ma an jarabcesu. SAHABBAN MANZON ALLAH sun sha gwagwarmaya da jarabawoyi kala-kala. Amma da sukai ha?uri wace irin riba ce basu samu ba. ?arshen dai wahala da faWi tashin bawa shine ya samu makoma mai ?yau ta aljanna. To su tun ma suna duniya akama mafiya yawansu albishir da aljannar, sakamakon ayyukansu na alkairi da sadaukarwar ya?i a bayan MANZON ALLAH. Wannan abubuwan sun ?arfafani matu?a, na kuma saka yarana suma suka dage, dan nasan yanda tasirin addu'ar uwa take akan Wa haka addu'ar yara nada tasiri matu?a. Dan haka Yaya ki jure, ki gwada ki gani in sha ALLAHU zakiyi dariya nan bada jimawa ba, al'amarin Yazeed zai zama tamkar labari ne. Muma kuma ba zama zamuyi ba in sha ALLAHU. ALLAH ya baki ha?uri ya sanyaya ranki. ta juya ga yaran suma da duk suka nutsu suna saurarenta.
 Kuma ina muku nasiha da ku kauda kanku akan al'amarin Yayanku, komi zaku gani tsakaninsa da matarsa dan ALLAH ku daina zuwa kuna faWawa mahaifiyarku. Ba wannan Yazeed ke bu?ata ba, addu'a yake bu?ata, idan ba haka ba maimakon mu tsamoshi a wannan masifar sai dai mu sake bada hanyar sakashi a cikin wani. Kunga dai abinda yaso faruwa. Da taci nasara ya mari mahaifiyarku kunga ya sake shiga wata masifar ne ai ko. Ku kwantar da hankalinku mu haWu mu tayashi da addu'a, sadaka, komai zai wuce .
Daga haka Ammie ta mi?e abinta. Harta kusa kaiwa ?ofa Amrah dake kuka sosai ta ce,  Ammie! .
Tsayawa Ammie tayi, tare da juyowa tana kallon ta, sai kawai Amrah ta taso da gudu ta rungumeta tana sake fashewa da kuka da faWin,  Mun gode Ammie, mun gode, in sha ALLAHU ke ?ar aljanna ce. Dama nace ke mai ?aunarmu ce da zuciya Waya amma ba'a fahimtata.....
Murmushi Ammie tayi, tare da Wagota, cikin katseta ta ce,  Amrah ya isa haka kinji, mu dukanmu in sha ALLAHU ?an aljanna ne. Kuma ba fahimtarki ne ba'ayi ba. Kowace rayuwa da nata ?alubale ne kinji .
Amrah zata sake magana Ammie ta hanata, sai ma share mata hawaye datai tas sannan ta maidata ta zaunar ta fice...

&Baki Hajiya Basariyya ta ?yaSe. Tare da faWin,  Kai wannan kilakakkiyar mata anyi munafuka. Ita adole gata ALLAH. Yannn! yannnn! yannnn! Tana wani zabga wa'azi. Sai dai kuma a gayama wasu amma wlhy bamu ba. Ubanwa ye zai yarda wani kin tsaya a addu'a ne da azumi da mima tace. Waye wawa an gama tsaface mana miji, da samarin ?a?anmu sun aure ?a?anki .
Haka dai ta gama surutanta sai kuma ta gyara yanayinta ta nufi cikin falon Hajiya Yayan a Wan rikice. Har wani neman yin tuntuSe take zata faWi. Tadai dafe kujera tana kaiwa zaune kusa da kujerar da Hajiya Yaya ke zaune. Sudai kallonta suke kawai. Cike da makirci ta fara faWin,  Mun shiga uku, ina wanka yanzu Jannah ke sanar min abinda ke faruwa. Kai wannan yarinya anyi ibilishiya, ita yanzu dan bata da mutunci sai ta saka Yazeed ya mareki, kai ALLAH wadan naka dai ya lalace. Amma gaskiya dai ya kamata a kira Sabuwa a gaya mata wannan Wanyan aiki tazo tai mata faWa dan ba halin arzi?i bane ba. Yanzu haka ?awayen banza ne suka Worata a wannan hanyar mara Sullewa. Yo mara Sullewa mana kasa Wa ya mari suruka ina arzi?i. Ita bata tunanin zata haifa tunda ga cikin nan a gabanta itama za'ai mata wataran. Ai ni yaran nan baku ?yauta min ba da baku haWu kun lakaWama shegiya duka ba, har sauran ?an uwanku duk basai ku kira ba damu mu haWu mu ci ubanta ai daWi gidan yawan kenan dama ko .
Amrah da surutun ke ?onama zuciya ta ce,  Ai hakan baida amfani Ummi. ALLAH kawai ya shiryeta. Jarabawace watarana sai labari.
Kasare Hajiya Basariyya tai tana kallonta, ta zata wani zai sake magana ta samu point, sai taga kowa bai tanka ba. Hajiya Yaya ma mi?ewa tai abinta ta nufi bedroom. Sai suma yaran suka fara mi?ewa.. ganin fa zataji kunya sai itama ta mi?e tana faWin,  To ALLAH dai ya ?yauta. ALLAH kuma ya kiyaye gaba iyakarta kenan . Daga haka ta fito tana tsine musu a zuciya. Ganin nan babu nasara sai ta nufi sashen Ammie, Sakina da Waleed kawai ta samu, sukace mata Ammie na sashen Daddy. Nan ma ta fito cike da ba?in ciki, amma sai itama ta nufi sashen Daddy Win duk da kuwa Wazun taje ya korota..........
'?

>?#?Itafa Hajiya Basariyya tafi dacewa da haihuwar Saheeba. Kai ALLAH ya rabamu da munafunci gaskiya9&?.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*

*_=???AJIYA A DUHU....=???_*

*_Bilyn Abdull ce >??
*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*

*_BOOK 2_*

65 / 138

Chapters