Advertisements
Chapter 9 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 138

24K to 27K   out of 412.8K words

ba daga gareta, musamman idan yay dubi da wayewar yan gudansu ta tsiya. Sai dai kuma mahaifinsu mutumin kirki ne, dan tsaye yake akan tarbiyyarsu babu wasa. Hakama Yazeed yana nasa kokari kasancewarsa babba kuma namiji.
Yaso taimaka mata amma taki yarda, dan haka yay ficewarsa yabar mata dakin ransa fes.
Kuka bana wasa ba Huznah taci, daga
karshe tai kiran wayar Hajiya Basariyya.
A lokacin Hajiya Basariyya na zaria tare da kawarta cikin wani kauye wajen wani malaminsu. Sosai gabanta ya fadi jin yanda Huznah ke kuka. A rikice tace,
"Ke dan ubanki
minene zakisa zuciyata ta buga".
Kasa magana Huznah tayi, sai da ta sake jan wani kugin kukan sannan ta ce, "Ummy fyade yamin".
"Fyade kamar ya?"
"Wihy Ummy fyade, ina barci a daki kawai yazo ya haike min, nayi duk yanda zanyi na kwaci kaina amma na kasa. Kuma da yake shi tsinanne ne ya fita yana min dariya. Wlhy ji nake kamar na kashe shi Ummi, gashi nan ko tashi na kasa yi wata irin azaba nake ji a jikina".
Jagwab Hajiya Basariyya ta kai zaune, kafin ta ce, "Amma dai wannan yaro anyi matsiyaci dan iska. Munafiki sum-sum da shi. Wlhy Huznah kin cucemu kin cuci kanki. Yanzu duk fadi tashin da nake na ganin kin baro wannan kurkukun gidan kin koma inda daula take ki huta muma ahalinki mu huta shine kikai saken da matsiyacin yaron nan ya kwace abinda shine kimar taki. Yanzu ubanmi zaki kaima AA Darma din to?"
Kuka sosai Huznah ta sake fashewa da shi mai karfi ma kuwa tana fadin, "Na shiga uku Ummi, wlhy ina sonshi, bazan iya hakurin rasashi shi ba. Ki taimakeni ALLAH ba laifina bane ba, kullum rufe masa kofa nake kamar yanda Aunty tace nayi shine munafikin ya dawo da rana azzalumi dan ya cutar dani. Ummi dan ALLAH ki taimakeni kada na rasashi...." kuka ya sarketa. Kasa magana Hajiya Basariyya tayi, sai Maman Yaseerah ce ta amshi wayar....

Mamaki ne sosai ya kama Maanal ganin inda
AS ya kawota. Wato sabon Office da aka bata kafin tafiyarta hutu, ita sam tama manta da batunsa. Office ne madaidaici da aka kawata aka kuma hada mata komai daya kamata da zata iya bukata. Kujerar zamanta da desk mai dauke da computer guda daya, sai visitors chairs dake gaban desk din. Ta gefen damarta hadaddiyar kanta ce ta show glass da aka shirya kayan bukata irin wanda mai zane zai bukata..., Hatta da pensul gasu nan tari-tari kamar a shagon sai dawa. Sai daga dan gaba yan kujeru guda biyu suma da visitors zasu iya zama ko ita idan tana bukatar hutawa, daga bayansu akwai fright da wata yar kanta karama an ajiye dispenser da coffee machine sai kofuna a cikin glass kanta din na shan shayi dana shan ruwa. Office din a cikin jerin officers na Designers Directors yake. Daga floor din nasu kuma sai nasu oga kwata-kwata dake a floor din karshe. A tsakaninsu ma ba sai ka hau lifter ba su steps ne kawai.
Sallama AS yay mata bayan sake tayata murnar sabon office duk da a waccan ranar duk sun mata. Karan farko tai guntun murmushi tare da amsa masa. Yana fita ta sakama kofar key, sai kuma ta jingina a jikinta tana murmushi.
Wannan fa shine DARE DAYA ALLAH KANY!
BATURE. Tayi wata biyar kacal matsayin Junior watch designer yau gata a wanan matsayin. ALLAH kaine abin godiya, kai ke maida bawa sarki, kai ke badawa ga wanda kaso a lokacin da kaso. Kai ke sauya al'amura daga wautar tsarinmu zuwa kyakykyawan ikonka. Ya rabbi ka cigaba da jagorantar rayuwata bisa ikonka ba wayona ko dabarata ko tsarina ba...
Takawa ta cigaba da yi cikin office din a nutse har zuwa kujerar zamanta mai laushi da kyau tanata sheki na sabunta. Sai da tai addu'a sannan ta zauna, ta lumshe idanunta tare da yin wani kalar juyi tana dariya kasa-kasa. Sai kuma ta tura kujerar jikin desk din sosai ta dauka wayarta. Sai da ta duba taga Didi Shahidah da Amaal da Ammie duk a online sannan ta shiga group dinsu tai video call. Babu ko bata lokaci duk suka shiga yin joining. Sun san da zaman office su duka, amma basu taba ganinsa ba.
Aiko ta shiga nuna musu komai daki-daki. Sai da aka gama murna sannan Ammie ke tuhumarta miyyasa ta dawo aiki haka da wuri, kwana tara fa kenan.
A shagwabe ta ce, "Ammie su Oum ne fa
sukace na dawo".
"Shi Ajwaad din fa?"
Shiru tai ta kasa cewa komai. Ammie ta ce,
"Humm. Maanal nidai zan baki shawara kibi mijinki, abinda ya faru ya riga ya faru, kar kiga Aban Fadeel nata baki kariyar nan kice kin samu damar bijirewa kema. Bance kada kibi umarninsa ba, amma ki kyautata alakarki da mijinki kinji".
Sosai idanun Maanal suka cika da kwalla.
Muryarta na rawa ta ce, "Amma Ammie shike nan komai da yay min yasha ruwa? Har yanzu fa babu wata nadama a tattare da shi. Ganin komai yake tamkar ma dolene a tsakanina da shi. Idan shi dake namiji bai sauke girman kansa ba Ammie sai ni na zubar da kaina a garesa?"
"Ni bance ki zubar da kanki ba. Amma ki kula da duk abinda zai dinga kasancewa a tsakanin ku. Maanal kawai kinki yarda ne, amma Ajwaad ya jima da yin nadama, sannan yana sonki fiye da zaton kowa. Bafa dole sai namiji ya bude baki yace ma mace yana sonta bane zata yarda. Irin su Ajwaad a aikace suke nunawa musamman idan akai dubi da yanayin shakuwarku"
Baki sosai Maanal ta tura gaba, "Ammie kawai dai baya laifi ne a wajenki".
"Oh haka kikace? Shike nan nayi shiru.
ALLAH ya daidaitaku cikin sauki. Ni bara naje gidan Nene zanje ALLAH ya sanya albarka. Sai a sake rike gaskiya a kumayi aiki tukuru".
Kai ta jinjina tare da fadin, "In sha ALLAHU
Ammie".
Ammie na fita Amaal da Shahidah da suke sauraren fadan Ammie suka shiga tsarama Maanal abubuwa. Dan suma dai suna goyon bayan kada Maanal ta sake tayi sake har sai ya kwantar da nashi kan. A cewarsu ita Ammie bata san halin mazan zamanin nan ba ZUMA NE SAI DA WUTA. Balle ma irin su AA miskilai ga giyar kudi na hura su.
Kiran wayar da akai ya saka Maanal tuna a office take, haka suma su Shahidahn duk suna wajen aiki. Ai babu shiri sukai sallama akan idan sun koma gida ayi zaman. Wayar ta daga, Director Mustapha ne. Bayan sun gaisa yake sanar mata akwai meeting nasu na designers zuwa 12 inji HOD. Yanda yake mata magana da girmamawa sai ma abin ya bata dariya. Itafa su rufa mata asiri suna oganninta bai kamata suna mata haka ba. Maganar aiki daban da matsayin da suke kallonta da shi yanzu. Dan haka ta dauki aniyar yin maganar a wajen meeting din in sha ALLAHU.
Ganin akwai sauran lokaci ta fara duba ayyukanta na baya, wanda ta fara bata karasa ba da wanda zatama gyara. Sosai take aikinta a nutse, cike kuma da shauki. Akwai aikin da suka fara fa Yaqub, basu kuma kammala ba, tana ganin kafin aje wajen meeting din kuma va kamata su kammala shi. Kan waya ta dauka bayan ta duba cote din department dinsu tai kira. Bayan an daga tare da gaisheta batare da tasan wanene ba ta bukaci ganin Yaqub a office dinta, ba kuma tare da jiran amsa ba ta ajiye..
Cike da gulma daga can Zaharadeen ya ce,
"Matar boss ce fa da kanta.'
"
Kusan su duka idanu suka waro, Yaqub ne kawai yay kamar ma bai jisu ba. Zaharadeen ya cigaba da fadin, "Yaqub kai take nema, dan ALLAH idan kaje ka nema mana damar ganinta, dan ya kamata muje mu mika gaisuwa mu taya murna muyi ALLAH yasa alkairi ko ALLAH zaisa ta manta da abinda ya faru baya".
Mikewa Yaqub yayi yana mai girgiza kansa.
A fili ya furta, "Oh ko kunya ku bakuji ba yanzu ko ita da kanta tace kuzo s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ai kuje dan neman kusanci da ita".
"Da gudu ma kuwa. Ko tunani ka kai kadai
zakaci arzikin?".
Cewar Ema..
Murmushin takaici Yaqub ya saki, batare da yace komai ba ya nufi hanyar fita abinsa dauke da folder din daya hada drawing pappers din daya san zata nema a wajensa. Yana gama ficewa Jameel ya ce, "Dan bakin ciki, idan fa bamuyi da gaske ba guy din nan sai ya kankane komai ta yanda ko kallonmu bazata ringa yi ba balle ta tuna munrayi tare anan matsayin abokan aikinta. ALLAH dai yasa ta manta da abinda ya faru baya. Ni damuwata ma randa ta kamamu muna gulmarta ni da Teemo da Hafiz".
Caaa kowa yay yana fadar albarkacin bakinsa. Sai dai duk suna cikin fatan ALLAH yasa Maanal ta yafe musu sudai. Daga haka suka dora da gulmar ashe Maanal din tasan abinda ta taka akwai alaka tsakaninta da boss shiyyasa take musu girman kai. Gashi nan cikin kankanin lokaci tazo ta samesu ta kuma shallake abinta matsayin ogarsu. Kai kai wannan al'amari da taba zuciya yake.
ALLAH ya shirya yan gulma a duk inda suke.

*_Typing=???_*









*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
......A office din Maanal kuwa sai da taima Yaqub magana sannan ya dan saki jiki suka karasa aikin a dan gurguje saboda lokacin meeting dinsu yayi. A tare da shi suka fita a office din. Hakan yay dai-dai kuma da sakkowar AA daga sama, da'alama daga office ya fito.
Bayansa CFO ce da Bussines Director. Da alama suma wani abun zasuyi mai muhimmanci, dan elevator suke kokarin nufa. Wani irin zuba musu ido AA yayi dan guntun sakewar dake fuskarsa na bacewa. A ransa ko ayyanawa yake, (Yarinyar nan bazata fita sabgar yaron nan ba ko?). A zahiri kam yanda ya wani dauke kai sai ka rantse baima gansu ba. Amma ita Maanal tana gannin kallon banzar daya watsa mata na fisha ta kasan idon. Amma itama sai ta wani basar kamar bata gansu ba ta nufi hanyar conference room tana cigaba da wayarta. Dan magana take da Amrah data kirata suna fitowa.
Shi dai Yaqub dan matsawa yay ya gaishesu.
CFO ce kawai ta amsa da Bussines Director.
Boss yi yay kamar baiji ba ta shige elevator.
Kasancewar shi Yaqub ba kallonsu yake ba bai san yaya boss din yake ba. Sai da suka shige kofar ta rufe sannan shima ya nufi conference room din.....
Rafeeq na zune Nuwaira a jikinsa tana
masa hira amma shi hankalinsa na wani tunani daban. Maganar zuwan Najma Abuja ce keta masa kai-kawo a rai. Kodai zai yi amfani da wannan damar ya sata tai masa wani aiki. Wani gefe na zuciyarsa kuma na farin ciki da fatan tabbatuwar abinda yake hasashe a tsakanin Najma din da Fawzan. Dan auren wani karin GARKUWA ne ga aunty Babba bayan na AA da Maanal. Tun jiya yake son yin waya da Maanal, dan yana son su tattauna wasu abubuwa masu muhimmanci sai dai bai san a yanda zata kalli al'amarin ba. Sannan alakarsa da ita kafin aure zai iya saka AA yaji wani abu a ransa idan yaga kiran duk da yasan har abada Ajwaad bazai kawo mummunan abu a garesu ba, amma yana da kyau ya kiyaye. To amma a yanzu batun Najma sai ya zaburar da shi, a ganinsa hakan wata hanya ce mai sauki da sakon da yake so zai isa ga Maanal din dan ita kawai yake so a wannan gabar tasan hakan saboda ya yarda da ita dari bisa dari, ya kuma gamsu da tarbiyyarta da soyayyar da takema yar uwarsa, soyayya ce irin ta da da mahaifi.....
"Babie!"
Nuwaira ta kirashi a cikin kunne cike da shagwaba. Kallonta yay da sauri, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sakar mata murmushi ya sake jawota jikinsa. Hancinta ya kama ya dan ja.
"Kefa yarinyar nan
shagwababbiya ce. Minene kuma?"
Baki ta dan tura masa. "Bakai ne ka tafi tunani ba inata kiranka bama ka jina. Minene ke damunka wai? Ina lure da kai tun jiya baka da sukuni"
Sake lakace mata hanci yayi. Tare da fadin,
"Tunaninki nake fa".
Tai murmushi mai kayatarwa. Duk da tasan ba hakan bane cike da farin ciki tace, "Godiya nake Babie. ALLAH ya kara mana farin ciki da
kwanciyar hankali",
"Amin my angel, harma da soyayyar juna"
Ya fada yana kankameta a cikin jikinsa. Wata irin soyayyarta na ratsa jini da bargonsa. A tabbas har randa aka daura masa aure da ita zuciyarsa Maanal take so, amma ganin halin da suka samu AA ya sake sakashi daukar damarar yaki da zuciyarsa akan sadaukarwarsa. Dan ya sake tabbatar da AA ya fisa bukatar Maanal.
Shine kuma ya cancanci samunta din. Koda ya shigo ya samu Nuwaira a dakinsa matsayin mallakinsa baiyi wani yunkuri ko tunanin zasu sami juna ta sauki ba, sai dai kuma labarin ya canja saboda karfin tasirin nasihar iyayensu a garesu, gashi shi kuma yana a cikin wani hali na bukatar abokiyar rayuwa. Cikin kudirin samawa kansa sauki kawai ya yarda ya tunkareta, sai dai a lokacin da komai ya kankama sai labarin ya canja, dan tamkar ya shiga sabuwar duniya ne da zazzafar soyayyarta. Na biyu hakurinta da biyayyarta, Nuwaira bata da kwaramniya, ga saukin kai da kyakkyawar fahimta. A dan kwanakin da suka samu tare ya fahimci hakan sai soyayyarta ta kara tasirantuwa a zuciyarsa.
Dan haka yake baje kolin amarcinsa yanda ya kamata, itako tana nuna juriya da dattako..
Daukarta yay cak ya nufi bedroom. Zizzilewa ta farayi cikin dariya tana fadin, "My R please Aunty Rufaidah fa zanje na taya aiki a kitchen"
"A nan ma ai aikin zakiyi, yama fi na Aunty
Rufaidah lada".
". Ya fada yana tura kai cikin dakin
da sumbatar goshinta..
Tattaunawa ce sosai ta kasance a zaman meeting din na su Maanal. Domin abubuwane masu muhimmanci da suke son kawowa na gyara a matsayinsu na artists din companyn.
Daga karshe Director Mustapha ya sanar dasu batun da za'aje kasar Chaina a kansa. Wadda tun kwanaki CEO ya gabatar, ya kuma bada damar kowanne bangare su bada mutane biyu da zasu samu horaswar ta kwanaki goma kacal in sha ALLAHU. To zuwa yanzu kowane department na kokarin kai nasu, dan haka suma ya kamata sukai nasu din. Dan haka adan nazari da su manyan sukayi cikin satin daya gabata, da ayyukan kowa da suka duba da kwazonsa sun yanke wadanda suke ganin sun cancanci zuwa.
Aifa nan kowa ya shiga gyara zama da fatan ya kasance shine. Duk da kuwa wasu a cikinsu an taba zuwa dasu wasu kasashen akan irin hakan. Dan ba sabon abu bane duk bayan wata shida Company na irin wannan zuwa karo sanin kai da kai din dan karuwar ilimi ga ma'aikatansu. Director Steven ne ya mike yay bayanin wadanda suka samu wannan dama.
Wato Maanal Habib Giro da Yaqub Nuhu. Tuni fuskokin su Zaharadeen sun canja, ko tafin da akayi ma da kyar suka tafa. Maanal da Yaqub suka nuna farin cikinsu. Duk da ita dai Maanal bata so haka ba. Musamman data tuna maganar da AA ya taba mata akan tafiyar. Sai dai tana fatan ALLAH yasa bada shi za'ai ba.
Suna tasowa a meeting din yay dai-dai da lokacin break. Ransu Zaharadeen a bace suka wuce. Kowa naji a ransa akwai makirci a wannan tsarin. Dan a ganinsu kawai an zabi Maanal ne dan tana matar boss a yanzu, ita kuma ta zabi Yaqub saboda suna tare. To aiko lallai zasusha mamaki, dan ko zasuyi amfani da wannan damar akan Yaqub game da alakarsa da Maanal din sai yabar Companyn nan da kafafunsa. Ai sun san dai boss ba mahaukaci bane ba zuciyarsa ba dutse bace zaiji kishi...
Salla kowa yay kokarin zuwa gabatarwa.
Bayan an idar masu tafiya cin, abinci suka tafi, masu komawa office suka koma. Harda
Maanal kuwa a masu komawar, duk da yau batazo da abincin nata ba. Hankalinta kwance ta fito daga elevator tana danna waya fuskarta da murmushi dan kuwa charting take da su
Aneesa. Dai-dai ta danna zata ma Zeezah vn aka zare wayar a hannunta, da sauri ta dago idanunta, sai ko cikin na AA dake kallon wayar alamar karanta charting din yake. Hannu takai zata amshe wayar, ya janye jikinsa batare daya
daina karanta hirar tasu ba.
Kamar zata saki kuka ta ce,
, "Amma dai haka
babu kyau ALLAH"
Bai tanka mata ba bai kuma daina karantawar ba, sai ma fara tafiya da yayi, binsa tayi tana jinta duk a rude, dan tsokanarta su Aneesan keyi a kansa. Acewarsu har an gama cin amarcin ne ta dawo aiki. Amasar data tura musu cewar (Ai ba sai an gama a gida ba zasu cigaba da ci a office) yasa suka tasata gaba da shakiyanci irin na kawaye. Itako tana bama kowa amsa dai-dai shi. Dan tafi sakewa tai musu surutu a charting fiye da zahiri. Son amsar wayar yasa Maanal bata ankara ba har sun shigo office dinsa. Sai da yakai zaune a rukunin kujerun ta kara kai hannu zata fige wayar batare daya daina abinda yake ba ya saka mata kafa ta fado jikinsa sannan. Da sauri ta kalla inda take, aiko dai a cinyarsa take dare-dare babu karya. Mikewa tai yunkurin yi, yasa hannunsa ya sake rungumota da kyau, tare da saka idanunsa cikin tsakkiyar nata da wani salon dage gira sama.
"Bake kika ce za'aci amarcin a office ba!
Miye na pretending kuma amarsu ta ango?"
Yanda yay maganar kamar mai rada ya saka tsigar jikinta tashi, ga kunya na neman halakata tamkar ba tana tare da Bestyn ta dake goyata a bayansa ba ko bayan kekensa, wanda suke cin abinci a kwano daya. Wanda yasha yimata wanka da mata tsarki, wanda yasha wanke mata underwears harda masu jini a jiki batare da kyankyami ba. Wanda y..."
Knocking kofar da akai ne ya katse mata tunani, bama tasan ta daka tsalle ta mike daga jikin nasa ba gaba daya. Bai hanata ba, amma ya kamo hannunta ya zaunar a gefensa gab, kafin ya danna remote kofar ta bude a hankali ta hanyar rabewa biyu. Kallo daya AS yay musu ya dukar da kansa. A haka ya karaso gabansu ya ajiye basket din hannunsa yana fadin, "Sir gashi in ji driver".
'.

9 / 138

Chapters