Advertisements
Chapter 136 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   136 / 138

405K to 408K   out of 412.8K words

?o?arin su suma na faranta musu. Ga ciki suna fama amma basa nuna gajiyawa da kulawa. Tsakaninsu da Oum da Abah tamkar iyaye ne da ?a?a ba surukai ba da iyayen miji. Duk abinda basu fahimta ba haka Oum ke zama ta koya musu yanda zasu gane. Kamar yanda suke kiran iyayensu da ?an uwansu haka suke kiran Mamy suna gaisheta da Aunty, tun Mamyn bata sakewa har dai ta sake Win. A haka suka shiga watan haihuwa, dan tsakaninsu babu wani nisa sosai. Gaba Waya sai kulawarsu ta koma ?ar?ashin Oum da Maanal. Mazansu da ?an uwa na binsu da addu'ar sauka lafiya.
Alhamdullahi Ameerah ce ta fara haihuwa Wiya mace. Zo kaga murna wajen a halin Darma dana Hajiya Shuwa da dangin babanta na Katsina. Dan danan hoton yarinya mai kama da babanta ya baje ko ina. Kowa farin ciki yake da annashuwa. Anama Baby addu'a anama mai jego. Anama su Oum barka. Lokacin da Mamy taga hoton Baby harda hawayenta. Ita Aunty ma wlhy yanzu tausayi ?ar uwar tata ke bata.
Sati Waya da haihuwa aka sakama yarinya sunan Oum, sunan Anum ke nan, sai dai ita suna mata la?ani da Zarah. Duk da ba ?asarsu ba AA yace sai sunyi shagali. Haka kuwa akayi, suka haWa Wan walimar cin abincin dare suka gayyaci abokan arzi?i na ?asa da ba?in haure irinsu. Akaci akasha aka Wan rausaya. ?an Nigeriya sai videos sukaita gani kawai da sanya albarka. Maijego tayi ?yau har ta gaji, hakama Baby da ?awayen maijego su Maanal, su twins yayu da sukai Sul-Sul abinsu dan har sun fara koyon zama ma sun sha ?yau.
Sati uku tsakanin haihuwar Ameerah data Najma, itama ta sulluSo yar budurwa mai kama da Yaya Fawzan. Yara dai duk sun rantse gidansu zasu Wakko. Ya suhanallah wannan haihuwa ta musamman ce a zuri'ar Darma baki Waya. Danda nan itama hoton Baby ya fara yawo, finally Yaya Fawzan yaga jininsa a duniya. Ga yarinya ?atuwa Masha ALLAH. Mutane sun so azo Nigeria a yi suna, sai dai yanzu ma ha?uri su Oum suka basu, dan su fa da gaske so suke su bama Nigeria iska sosai da sosai. Nan ma AA bai ha?ura ba yace sai fa sunyi bikin suna. Haka kuwa sukayi shi tamkar na haihuwar Ameerah. Yarinya ta ci suna Khadijah. Nan ma anci an sha an yi wada?a sai dai mu babu damar cin banza wannan karon an barmu a Nigeria >?-?>?q?. To ALLAH ya sanya albarka bazamu fasa addu'a ba ai.........
'?
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? !2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
AJIYAH A DUHU

215

........Sosai Oum ta tsaya akan masu jego sukai jego mai ?yau da kulawa. Bawani batun wanka ko gargajiya amma komai Alhamdullah. Ga yara sunata ?yau abinsu kamar ka lashe. Bayan sunan ne AA da Yaya Fawzan suka je Nigeria. Satinsu Waya suka dawo, sai dai sun biya ta saudia sun Wakko Naufal da suka samu hutu. A zuwa sun nan sosai zuciyar Mamy ta karaya, dan ta gama yarda dai ?a?anta ba nata bane ba na Fateema ne. Mijin ma nata ne. Duk da nadama ta mamayeta ta gagara Waga baki ta nema gafarar kowa har yanzu. Sai aikin kuka, su dai su AA sunta lallashinta da mata nasiha iya iyawa. Sannan suna mata dukkan gatan daya dace akan komai tsaye suke a kanta. Kai bama su ba ko Baba Sardauna da su RK hidima sukema Mamy sosai, kawai dai sunan bata a gidan Darma ne yanzu. Sai nakasan ?afa data ido data zuciya dake zagaye da ita. Idan akai dubi ta wani fannin kuma data gangar jiki saboda HIV. Amma da yake tana shan magani bama zaka gane ba.
Zuwan Naufal yama kowa daWi, yaro ya ?ara girma ya fara zama Wan saurayi, kamaninsa da su AA ya fito tsaff kamar sunyi kaki. Abin mamaki ko tambayar Saheeba baiyi ba. Sai ma farin cikin ganin su Oum da sabbin ?anne har huWu daya samu. Duk motsi sa kuwa yana manne da yaran nan. Yay hutunsa ya gama Abah da Oum suka maida shi Saudia, suma sun Wan huta na sati uku sukai umrah suka wuce Nigeria dan Baba Sardauna baya jin daWi. Sun duba shi aka gaggaisa da ?an uwa da abokan arzi?i, har gidan Mamy Oum taje. Taji daWin kuma ganin yanda Mamyn take cikin kulawa mai tsafta da nagarta. Suka sha hira Mamy na faman kukan zuci. A yanzu ma ALLAH bai bata damar ro?on Oum gafara ba. Girman kai da taurin zuciya na hana bakinta buWewa akan hakan. Satin su Oum biyu a Nigeria suka koma abinsu....

________&

Rayuwa mai daWi da nagarta ta cigaba da wanzuwa a cikin zuri'ar Aliyu Abubakar Darma. Hankalinsu ya kwanta matu?a yanzu. Ga yara sunyi SulSul da su su twins na gudunsu da magana ras. Zarah da Khadee ma na fara koyon tafiya. Yara masha ALLAH kamar ka lashe dan ?yau da kulawa. Su dukansu basa ma banbance iyayensu saboda haWin kai da iyayen ke da shi. Kowa ya yarda shi uba ne, kowacce ta yarda ita uwa ce. Yanda zata kula da wanda ta haifa, haka zata kula da wanda bata haifa ba. Mafi yawan lokaci ma a wajen Oum suke kwana. Suna da shekara Waya a Chaina Maanal, Ameerah, Najmah suka zo Nigeria halartar bikin yaran gidan su Ammie da zagaya dangi. Kowa ya gansu sai ambaton masha ALLAH. Yaransu kamar a cinye dan so. An sha biki daya amsa sunansa biki, dan kuwa Daddy yara takwas ya aurar a rana Waya. Hajiya Basariyya tazo abin tausayi, ta haihu tuni yaron ma ko isashiyar lafiya bai da shi sikila ne. Gaba Waya sai ta tsangwami kanta, ta kuma gigita da ganin irin daular duniyar da su Ammie ke ciki yanzu. Da itama bataima kanta mugunta ba da harda ita anan fa. Amma gashi nan masu aikin gidan ma sun fita fasali da ?yawun kallo. Da taga Maanal kuwa ai sai ta ?ara sakin baki. Yarinyar ta girke abinta ta zama cikakkiyar mace komai yaji, ga ?yau ga gayu ya ranta abin sha'awa masha ALLAH. Ko wajen events Hajiya Basariyya bata iya zuwa saboda kunya. A hakan ma Huznah ta mata Winkuna masu tsada, amma kayan daban jikinta daban koda ta saka. Duk sanda idonta ya sauka akan Daddy sai tayi kuka dan tausayin kanta. Sai ma taga kamar an ?ara masa wani ?yau da ?uruciya shi da matan nashi. Haka dai akasha biki amare aka kaisu gari daban-daban, Khadijah kawai aka kawo Abuja gidan Yaya Yazeed.
An kammala biki da kwana biyu ALLAH yay ma Gwaggo rasuwa. Dama su Maanal nada planing Win zuwa Giron sai kuma ga dalili. Haka suka shirya suka tafi ita, Amaal, Shaheeda da Ammie sai Nene, dan Aunty Sakina mijinta ya hana itama da yake tana aure yanzu anan cikin Abuja. Duka harda yara suka tafi. Sun ko samu tarba ta girmamawa, haka akai zaman uku da su, Gwaggo dai ansha jiyya sosai, dan ita duk da tana shan maganin HIV Win abin ya haWa mata da tsufa shiyasa ta jigatu. Babu dai Alhamdullah, sai Sailu ce dai duk ta rame tayi ba?i, kodan abin ya mata yawa ne ga ba?in cikin Ha?ilah da Wanta, dan ta haihu namiji yaro kama da ubansa Temo sak. Kaida ka ganshi kaga Wan ?abilu, ga cin masifa kamar jaki. Bai fi shekara Waya da rabi ba amma cizon ?a?an mutane da yagushi ba'a magana. Idan akai magana Ha?ila ta tsige mutum tas. Yawonta kuwa babu abinda ta fasa sai tai kwana uku bata gida, haka take barma Sailu Wan kuma dole ta kula da shi, idan ta dawo kuma tai ta mata tujara kamar ba uwarta ba. Shi dai Sule ALLAH ya taimakesa, yana cikin Sokoto yanzu haka yana karatunsa na addini dana boko. Idan ka ganshi kamar ba shi ba, ya nutsu sosai masha ALLAH. Hakan yama su Maanal daWi suma, sun kuma tabbatar masa yana kammala wannan makarantar Saudia zasu nema masa gurbin karatu. Aiko yayta murna da farin ciki. Ha?ila kuwa da sukai ma faWa ganin tana neman musu rashin kunya sai suka ?yaleta suka ma fita sabgarta har akai uku suka baro garin. Suka bar Babu da kuka da kewar ?an jikokinsa. Har yanzu zuciyarsa ta kasa sabawa da rashin Ammie, a kowane motsinsa cikin tuna rayuwarsu ta baya yake da nadamar kuskurensa. A wannan karon ma haka yayta neman gafararsu har su Maanal.
Suna dawowa Abuja da kwana biyu su Maanal suka fara shirin komawa Chaina, dan mazajensu fa sun dame su. Najmah na Kano, dan haka Ameerah da Maanal suka shirya suka sameta acan suma. Sun zagaye ahalin Darma har Yola wajen Gwaggo Khadijah. Har gidan Huznah suka je itama akai zuminci. Maanal taji daWin ganin yanda rayuwar Huznah ta canja, dan sun sake gida ma yanzu ga ?an yaranta uku gwanin sha'awa. Daga ?arshe suka yada zango a gidan Mamy.
Mamy taji sun zo ?asar, amma bata san suna Kano ba. Yau tunda ta tashi bata jin daWi, ga Aunty ta fita biki a dangin mijinta. Sai ita kaWai a gidan sai mai aikinsu. Tana tsakar gida tana shan iska Ahmad da Muhammad suka shiga gidan da gudu, Najma na kiransu amma ina basu dakata ba. Suma Zarah da Khadee na ganin yayinsu sun yi ciki sai suka bisu da nasu gudun. Gaban Mamy sosai ya faWi, ta dinga bin yaran da kallo dan Muhammad dake gaba na shigowa kawai ya fara zagayeta Ahmad na binsa suna dariya, su Zarah ma sukabi layi.
Zuciyar Mamy na bugawa tana musu magana amma basu kulata ba sunata dariya da gujegujen su. A haka su Maanal sukai sallama suka shigo. Sai da kan Mamy ya nema fashewa. Ganin wasu cikakkun mata ?an gayu ?an ?walisa da kallo Waya zakai musu kasan nera ta zauna a jiki da suturarsu. Ga wani ?amshi na girma ya cika tsakar gidan. Sai da Ameerah tama yaran tsawa suka tsaya cak sannan Mamy ta dawo hayyacinta. A nutse suka ?arasa shigowa fuskokinsu da murmushi suna mata sannu. Fahimtar kamar bata ganesu bane yasa Najmah faWin,  Mamy Maanal ce da Ameerah da Najma. Sai jikokinki .
Gaba Waya sai lips Win Mamy suka fara rawa, idonta ya cika da ?walla. Da ?yar tai musu jagora zuwa cikin gidan. Sunata kallon ko'ina su dai. Bayan sun shiga sun zauna mai aiki ta kawo musu ruwa. Cikin girmamawa suka gaida Mamy, ita ko tana amsawa da rawar murya. Maanal ta harari yaran da suka tsaya suna kallon Mamy kamar sun sami magiji.
 Wai baku iya gaisuwa bane ba yaran nan .
Da sauri Muhammad ya kama kunensa ya ce,  Sorry Mie-mie . Ganin haka shima Ahmad ya kama nasa kunnen, hakama su Zarah, suka haWa baki suka ce  Sorry Mie-mie bakuna a taSe abinka da ?an madara>?q?. Maanal ta ce,  Oya naji a gaida Mamy . A tare yaran suka matsa inda take cike da ladabi bakinsu a haWe sukace,  Mamy good afternoon .
Yawu mai kauri Mamy ta haWiye. Tana murmushin ya?e ta ce,  Kuna lafiya? .
Kansu suka Waga mata dan suna jin hausarsu tsaff. Ganin tayi shiru Ahmad ya ce,  Baki ce ya Grandpa da Grandma, da Daddy's Winmu ba? .
Mamaki ya kama Mamy, ga shi su duka huWu sun wani tsareta da idanunsu sak irin na Aliyu da Fateema da su AA. Sai kunya ta kama su Maanal. Najmah ta ce,  Ta tambaya a zuciya, oya azo a zauna .
Mamy zatai magana sai ga Aunty, yanda Aunty ta nuna farin cikin ganinsu ta kuma shiga kiran sunan yaran Waya bayan Waya da buWe musu hannaye alamar suzo sai sukafi sakin jiki da ita. Da gudunsu kuwa sukaje suka shige jikinta suna dariya kamar sun santa. Dan su basu da wahalar sabo, in dai zaka jasu a jiki yanzu zasu sallama. Sai abin kuma ya dami Mamy taji kunya sosai. Sai bin yaran take da kallo dake nane da Aunty, itako sai nannan take da su kamar zata cinye. Basu sake kula Mamy ba kuwa. Ana haka sai ga AA ya kira video call. Yaran suka shiga Woki suna kiran Abie-Abie. Shi ko sai murmushi yake musu cike da kulawa da soyayyarsu. Labarin abinda Aunty tai musu suka shiga bashi, su Zarah bakin bai gama nuna ba sai murmushi suke saka shi.........
'?
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
AJIYAH A DUHU

216

..........Haka dai ya biye musu sai da kowa ya gama bashi nashi labarin su duka huWun sannan ya gaisa da su Aunty, godiya yay mata sosai, itako tana harararsa da da?uwa. Wai dan mi zai mata godiya ita da jikokinta. Mamy ma ta amsa suka gaisa. Yanda batai masa maganar yaran ba shima bai mata ba. Haka yaran suka ?ara amsa suka koma gefe sun hana iyayen. Dama haka suke musu, wataran har gori suke musu idan sukai magana. Musamman Ahmad ya iya faWin  Ai Daddy's Winmu ne dai .
Suko suce ikon ALLAH ai mu daga sama muka faWo. Haka AA ya biye ma yaran nan sunata shiririta har Babban Yaya da Yaya Fawzan suma suka samesa suka Wora, da ?yar suka yarda sukai musu sallama Khadee harda kukanta sai da Maanal ta goyata aka samu lafiya. Yaran nada sha?uwa sosai da iyayensu bata wasa ba. Koda su kaWai suka taso suke gani sai kakanni su oho.
Anan gidan suka kwana, washe gari suka shirya komawa Abuja Manaal bata jin daWin jikinta. Aunty ta haWa musu shatara ta arzi?i. Mamy kam sai kukan zuciya. Amma ta buWe baki ta nema gafararsu suma ta gagara. Haka suka koma Abuja. Kwannasu biyar da dawowa suka fara shirin wucewa. Maanal ta ziyarci Mawaad Company har sau kusan uku. Ta duba komai yana tafiya dai-dai yanda ya dace. CFO dai ta ajiye aiki tuni. Su Zaharadeen sai wani bata girma suke. Yaqub daya kara samun girma a yanzu yana matakin Designer director shima har gidansa taje sukai zuminci da matarsa mai kirki, haka taita girmama Maanal taima Khadee da Zarah kitso dan dasu taje....

&& Randa suka dawo Chaina mazan nasu ne da kansu suka je tarbosu. Ba kunya suka rungume su sannan suka koma kan yaransu. Sun iso gida Oum ta shirya musu beta dan yanzu sun canja wajen zama. Suna a gidan dake Waukar family ne gaba Waya. Sun sami Naufal yazo hutu, sai dai sunyi ?ar tafiya shi da Abah sai dare suka dawo. Tuni yara suka tare wajen Oum da Abah da Naufal. Su AA suka sami filin sharafin baje soyayya dan sunyi kewa. Maanal ma dai dauriya kawai take dan bata jin daWi. Sun dawo da sati Waya jikin nata ya takura mata AA ya Wauketa suka je asibiti. Gwajin farko aka gane ciki ne. Zo kaga murna wajen Abah, Oum, Babban Yaya, Yaya Fawzan da uban gayya AA. Haka Ameerah da Najma ma. Kowa addu'a sauka lafiya yake mata. Wannan karon dai kam laulayi take sosai tun a farkon cikin, sai da ya shiga wata na huWu ta samu lafiya da ?arfin jiki. Haka suka cigaba da rainon cikin nan kowa na bata kulawar data dace. Gefe AA na kasheta da soyayyarsa mai tsayawa a zuciya. A haka ALLAH ya kaita watan haihuwa, wannan karon ma aka ciro mata baby girl mai kama da iyayenta. Hotunan baby ya cika wayoyin dangi, washe gari RK da Nuwaira suka isa Chaina da yaransu biyu suma kyawawa. Sosai su Oum suka farin ciki da zuwansu, nan fa suka haWu aka sha shagalin haihuwar Baby. Bakin AA ya kasa rufuwa dan farin ciki. Ranar suna yarinya taci suna Ru?ayya, zasuma ce mata Urwa. Wannan karan kam RK ya shirya walimar da akaci aka sha aka gagije. Bayan suna maijego ta cigaba da jegonta kafin a koma filin daga. Suma su Ameerah suka fara nasu laulayin kuma.
Ai a wannan gaSar Mamy tama rasa nacewa, UBANGIJI ya tabbatar mata shine maiyi da tsarawa bayinsa rayuwa. Ga dai masu cikama ?a?anta burinsu nan da ?a?aye. Wani lokacin a Soye take saka hoton yaran su shida

136 / 138

Chapters