Advertisements
Chapter 121 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc Hausa Novels
Advertisements

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   121 / 138

360K to 363K   out of 412.8K words

su Uwangale sune suka koma sakata aiki a gidan. Haka zata dinga gungura kekenta tana musu hatta girki. Mopping da shara ana idar da sallar asuba suke tasota, haka takeyi tana kukan zuci dan babu damar yin na fili Uwangale da bulala. Sam RK bai san wainar da ake toyawa ba. Dan barci kawai ke kawoshi gidan. Gari na wayewa yake shiri ya wuce asibiti sai kuma wani daren. Idan ya shiga duba Mamy kuma da safe tsaff yake samunta dan suna dai-daita lokacin shigowarsa ne su killafata waje guda, wani lokacin ma su haWa kayan daWi a gabanta Nuratu na mata tausa Uwangale na kai-kawo, Saheeba na bata abinci a baki. Yana fita Saheeba da Nuratu sai sun bata maruka suce ta sauka tai musu abinda sukai mata. Haka zata sakko jiki na rawa tayi dan in ba haka ba taci duka a hannun Uwangale.
Tashin hankali yasa jininta kullum a sama yake, ga zuciya ta kumbura sosai har sai da dole RK yasa aka maidata asibiti. Ya zauna yay mata nasiha dan shi a tunaninsa har yanzu tana nan da mugun ?udirinta ne a rai bai san ?aniyarta take ci wajen su Saheeba yan boko haram ba>?#?=??. Satinta uku a asibitin dan dole Aunty ta dawo ta zauna da ita. Ji Mamy ta dinga yi kamar kar a sallameta, gashi ta kasa gayama Aunty abinda ke faruwa saboda tsoron Uwangale da su Saheeba. Suna komawa gida kuma kwannan Aunty biyar kawai su Saheeba suka zugeta akan taje abinta zasu cigaba da kula da Mamyn, kuka Mamy ta sanya bata son Aunty ta tafi, sai abin ma ya bama Aunty mamaki sosai. Wai yau Kamila ce da kuka bata son ta tafi, lallai mata sun fara laushi ashe. To ita dai Aunty lallashinta tayi akan tayi ha?uri zatai ?o?arin dinga zuwa akai-akai, haka ta tafi tabar Mamy na kuka.
Kamar jira su Nuratu suke Aunty na wucewa suka kama Mamy suka lakaWa mata duka wai tana son tona musu asiri wajen Aunty. Haka taita rantsuwa da basu ha?uri. Bayan sun ja mata dogon gargaWi suka barta da jiyyar ciwon jiki. To wannan irin azabobi fa Mamy ke fuskanta tunda su AA suka tafi, idan kaga ta samu sassauci sai Aunty tazo kwana biyu. Tana tafiya ake Worawa daga inda aka tsaya. Da ace wani zai duba jikinta sawun bulalaine kaca-kaca dan sun zame mata tabo.
Yau tunda sukai waya da Oum tace mata sun kusa dawowa ji Mamy tayi kamar tai ihu dan murna. Har yanzu zuciyarta bata ?aunar Oum, amma tasan dawowarsu gidan zai zame mata rahama ta wani fannin, dan zata samu sau?i daga cin ubanta da take a hannun su Uwangale da Saheeba da Nuratu.....

=??=??=??>?#?>?#?>?#?=??=??=??Hajiya Kamila tamu, waya gaya miki barno gabas take>?q?=??>??

__________&

Ba Mamy bace kawai ke amsar sakamakon abinda ta shuka, anan ?auyen su Kawu Manu ma Hajiya Basariyya na amsar nata sakamakon ne. Bana duka ko zagi ko hantara ba, wannan karon ko aiki ma babu mai sakata a gidan su Kawu Manu sun kawo ido sun zuba mata. Azabar canjin abinci dana canjin waje kawai ke ?ona zuciyarta da rayuwarta. Tana gama iddarta kuma kawai wani mutumi dake mutunci da Kawu Manu a can ?auyen gaba da su yazo wai yana son aurenta.
Mutumin shine mai anguwar ?auyensu, yana da shanaye da gonakin noma. Dan haka a yankin ?auyukan yana cikin masu kuWin da ake lissafi da shi. Suna huWWa sosai da Kawu Manu dan abokinsa ne na amana sosai. Matansa uku da yara kusan ashirin da takwas. Yaje makka dan Alhaji Balala ake kiransa ma. Karku Wauka dukiyar tasa yana da wani haWaWWen gida ne. A'a sam ba haka bane, gida ne dai irin na ?auye jar laka. Sai dai ?aton gaske ne dan duk yaransa maza idan sunyi aure anan suke yankar waje suyi Waki su kewaye. Hakan yasa ma gidan albarka sosai ya zama family house, dan a?alla yaransa maza bakwai nada iyalai. ?akunan matansa a jere suke reras guda uku falle Wai-Wai sai doguwar baranda. Abinda ya Wan Wara gidan Alhaji Balala dana sauran ?auyen filastar da yay ma Wakunan matansa da wannan doguwar baranda aka kuma shefe gaban Wakunan nasu suma da simintin. Sai kuma na tsakar gida dake iyakar tsahon barandar da faWinta. Ba'a abincin safe a gidan Alhaji Balala balle na rana. Tuwo ne ake yi ?atuwar tukunya duk bayan kwana biyu a raba kowacce ta Wauki nata dana ?a?anta ta adana taita Wumamensa. Da yake tuwon anayin wadatacce kam sai kwana biyun ma ya cika wata bata gama cinyewa ba, abinda ya rage Win saita shanya ya bushe ta adana kayanta, randa suke jin kwaWari ta dafa da barkono da manja da Wan magi kamar shinkafa dan sai an dakashi sannan. Shine mutanen ?auye muke kira da (Dabuwa. Ku wlhy akwai daWi=??). To wai a hakan mutane ke ganin gidan Alhaji Balala wadace yake da abinci, dan sauran gidaje wasu ma sai suyi sati basu Waura tukunyar ba musamman idan damina ta gabato an cinye amfanin gona.
Lokacin da Iya ke sanarma Hajiya Basariyya batun Alhaji Balala hankalinta tashi yayi, ta shiga wassafo Alhaji Balala data san yana zuwa wajen Kawu Manu duk bayan kwana biyu a cikin idanunta. Kawu Manu ya fishi shekaru, amma shi ?ato ne da ?ibarsa ga tsayi masha ALLAH. Kullum zaka ganshi cikin manyan kaya na yadi mara fasali shi adole ga Alhaji. Amma wuyan rigar kawai ka kalla da hularsa dauWar dake jikinsu sai ta sakaka amai. Bakinnan ba'a magana dan yana cin goro. Ga uban gashi ya tara a fuska babu gyara duk ya ?ududune yay ?uda-?uda sai kace dole sai ya ajiye sajen a fuska. ?afarsa ko faso ba'a magana sai kai ajiyar ?wandala a wani ramin ta zauna abinta tana hutawa. Yana da arzi?in kudin ?auye sai dai fa ba'a ci sai iya cikinsa, dan kuwa kullum yana ?auyen su Kawu Manu wajen mai shayi da tsire dan su babu a nasu ?auyen. Shiyyasa ?aton cikinsa ba'a magana, idan yana tafiya har nishi yake kamar mai shirin haihuwa. Ji Hajiya Basariyya tai amai na shirin taho mata, ta fashe da kuka tana faWin,  Haba Iya, nice wannan kucakin mutumin zai ce yana so har azo ana gaya min, wlhy ALLAH ya kiyaye, ai ko a Wan aikin gidana ba zan iya Waukarsa ba .
Dariya ma abin yaba iya, ta ce,  Lallai samun wuri, ina ma laifi da kika samu Alhaji Balala Win? Mutumin kirki abinci baya yankewa a gidansa. Ke har mafarkin samun wata daular rayuwa da tafi wannan kike yi? To ai saiki matsa kiyita jira .
Da harara Hajiya Basariyya ta raka bayan iya tana ?un?uni. Kamar magana ta wuce kawai bayan kwana biyu Kawu Manu yace mara taje soro su gaisa da ba?o. A tunaninta Daddy ne ko wani dai daga birni, kawai taci karo da Alhaji Balala shirim a zaune cikin wata daddauWar shaddarsa datai uban squeezing, ga wata shegiyar hularsa a karkace shi a dole yazo zawarci. Jitai amai na neman taso mata, ta kauda kai tana zubar da yawu. Shi ko sai faman washe mata baki yake ha?ora jazur da goro.
Ganin ta?i yin magana ya ce,  Hajiyata an fito? Ina fatan kina cikin ?oshin lafiya? .
Maimakon amsa masa gaisuwar sai cewa tai  Miya kawoka wajena? .
 Haba Hajiya Basari, (Basari>?#? Alhaji Balala ya iya saka suna fa) duk namijin da kika gani yazo gun mace kamarki ai alkairi ne ya kawoshi, alkairin ma na aure. Mu ba yara bane dan haka babu wani batun kwana-kwana aure ya kawoni, kawunki ya sanni, ya kuma san wanene ni. Kai duk kewayen ?auyukan nan kikace Alhaji Balala ko yaron goye in dai yana magana zai ce miki ya sanni. Dan haka babu wasa a lamarina, zan ri?eki amana kuma zan hidimta miki gwargwadon iko......
 Mtsowww!! Kai nifa ka isheni da magana. Karma ka wahalar da kanka ni bana sonka, jibeka, kai banda ?addara ko a hanya ka ganni ka isa min magana ma. Dan maigadin gidana ma ya fika komai wallahi wawa ba?auyen banz......
Bata ?arasa ba taji saukar lafiyayyen mari a kumatunta. Juyowar da zatayi taci karo da Kawu Manu. Fuskarsa na nuna matsanancin Sacin rai da fushi ya ce,  Yanzu Alhaji Balala Win kike zagi Basariyya? Saboda ki nunama duniya ke mara tarbiyya ce. Da shekarunki da komai amma sam baki da isashen hankali. To bara kiji auren Alhaji Balala babu fashi, dan nima na gaji da zama min da kike a gida wawuya kawai. Alhaji kaje ka shirya nan da kwana uku kacal ka turo magabatanka ..
Kuka sosai Hajiya Basariyya ta fasa da faWin,  Wlhy dana auresa na gwammaci na gudu kuwa . Tai cikin gida fuuu. ?wafa Kawu Manu yayi da faWin,  Shike nan Alhaji in dai da sadaki a tare da kai muje masallaci yanzun nan, dole ne na nunama yarinyar nan bata isa ba kuwa. Duk da itace da damar zaSar mijin aure bata da cikakken hankali ni zan zaSa mata dan bazan sake bari ta koma birni ta sake fanWarewa ba.
Bakin Alhaji Balala a washe ya mi?e yana faWin,  Ai ko babu yanzu zan aika gida a Wakko Malam, ALLAH ya saka da alkairi ya bada kadan zuminci ...........
'?

Kambu Hajiya Basariyya an shiga gidan Wan kande, wayaga Waurin goro >?#?=??.
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
AJIYAH A DUHU

191

.......Aure dai kam ya Wauru tsakanin Hajiya Basariyya da Alhaji Balala. Dan ana idar da sallar la'asar ya biya sadaki aka Waura. Sai ga Kawu Manu ya shigo da goro da sweet, sai kuWi dubu hamsin ?an Wari biyar-biyar. Wani irin kukan tashin hankali Hajiya Basariyya ta saki lokacin da Kawu ke musu bayani ita da iya. Ko kallo bata ishesa ba, sai ma mi?ewa yay yana faWa mata ta shirya gobe zuwa jibi zata tare ta bar masa gida, dan bazai iya zama da mai taurin kai da bijirarriyar zuciya irin tata ba. A gobe ma Alhaji Balala zai turo a fara kwashe kayanta zuwa can, dan haka iya ta nema wanda ta yarda dasu suje yin jere.
Suma ne kawai Hajiya Basariyya batayi ba a ranar tsabar yanda ta dinga zuba musu bori. Da daddare ta gama shirya kayanta tsaff da shirin guduwa sai dai ta makaro, dan kar Kawu Manu ke kallonta. Tana fitowa ma taci karo da shi zaune a ?ofar gida. Turus ta tsaya tana kallon sa kamar yanda yake kallonta. Sai kuma yay murmushi mai ciwo da faWin,  Oh guduwa kike shirin yi da aure wani a kanki? To kada ki fasa dan ALLAH ga hanya nan . Yay maganar yana tashi ya shige gida abinsa. Ga dai ?ofa a buWe ga kuma dama an bata amma ta kasa yin komai, sai ma rushewa da kuka tayi a wajen tare da zamewa ta zauna dirshan. Haka ta ?ara cin kukanta babu mai lallashi ta taso ta dawo cikin gidan....

__________&

KANO

Zaune take tana shayar da bebinta, yaro ?ya?y?yawa yay Sul-Sul gwanin sha'awa. Sosai yake kama da babansa, haske kuwa nata ne. A zahiri yaron take kallo, amma tunaninta baya tare da shi. Sageer daya shigo kusan mintuna goma ya fahimci hakan, dan ko shigowarsa da alama bata sani ba. Numfashi ya Wan furzar ya wuce kitchen ya ajiye kayan hannunsa ya fito. Sai da ga kai zaune har ya taSa sannan firgigit ta dawo tunaninta. Kallonsa tayi, shima ita yake kallon, sai ta sauke kanta ?asa kawai.
 Har yanzu jikin ne? .
Kanta ta girgiza alamar a'a.
 To mike damunki? .
Cike da son danne abinda ke ranta tace,  Babu komai fa, kawai dai na tafi tunani ne. Sannu da dawowa .
Amsa mata kawai yayi badan ya gamsu da abinda ta faWa ba. Itama sai ta mi?e tana mi?a masa fodio ta nufi kitchen. Babu jimawa ta dawo da ruwa ta ajiye masa. Ta Wan kallesa yanda yakema fodio wasa kamar yana yi da babba mai wayo.  Kawoshi kasha ruwan .
 No barci, Wan samin dai ruwan wanka na watsa ruwan nan yasa garin yin sanyi .
Kitchen Win ta wuce, ta Wauka kettle ta fita zubo ruwa a rigiya, koda tazo ta jona a wuta sai tai tsaye, sai kuma ta Wauki wayarta, tana dannawa screen Win ya kawo haske hoton AA ya bayyana. Yayi matu?ar ?yau cikin ?ananun kaya sai coat data kai masa har gwiwa fara sol mai gashi. Ya saki ?atuwar hular rigar bayansa ta kwanta. Akwai alamun kyakkyawan hannun mace dake a kafaWarsa alamar tana a bayansa ne, kod???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ai zooming hoton akayi, ko kuma yanke macen akayi. Yanda AA Win yay wani shegen murmushi idanunsa a lumshe gashinsu sun kwanta gazar-gazar ga murmushi akan ?ya?yawar fuskar tashi kaWan yaWan turo lips gaba yay masifar yin ?yau. Gashi ya fito tar-tar kamar kai magana ya amsa.
Ajiyar zuciya Huznah ta sauke mai ?arfi, sai kuma hawayen da suka taru mata a cikin ido suka zubo sharr. Hannu tasa ta sharesu... Sageer da yaji shiru ya biyo bayanta kasancewar ta juya masa baya tsaff yaga abinda take kallon. Da farko sai da zuciyarsa ta buga, wani irin kishi mai zafin gaske ya turni?esa. Har ya buWe baki zai yi magana sai kuma yay shiru ya koma da baya-baya. Kasancewar hankalinta ba'a wajen yake ba ko motsinsa bata ji ba. Koda ya koma falon ma da ?yar ya iya nutsuwa yay controlling fushinsa. Bayan ruwan yayi ta Wakko ta fito, da kallo ya bita har ta shiga Wakin barcinsu. Bata wani jima ba ta fito tace masa ga ruwan can. Shima komai baice da ita ba ya mi?a mata Fodio ya wuce. Duk yanda yaso shiga wankan kasawa yayi, ya zauna bakin gado ya ciro wayarsa ya buWe data. Karo na farko ya shiga google ya fara searching sunan AA Darma da accounts nashi na media. A X kawai ya samu, sai facebook. Na facebook Win ya fara shiga, sai dai babu wani abun kirki a ciki ma, dan posting Win abubuwan da akai basufi goma ba, duk ma agogo ne. Amma kuma yana da followers sosai. Daya shiga ainahin profile Win account Win ma sai ya fahimci kamar ba ainahin AA Win bane. Fitowa yay ya shiga X, anan ne yafi gaskata AA Win ne da kansa, sai dai nan Win ma babu wani posting Win hotonsa ko guda Waya balle matarsa ko wani family member na Darma kaf. Hotunan agoguna ne manyan kai na manyan masu hannu da shuni kawai. Koda ya shiga comments na posting Win farko yaga kusan duk manyan mutane ne ke masa comments Win ma. Fitowa yay zuciyarsa na tunanin a ina to ta samu wancan hoton? Sai zuciyarsa ta ayyana masa brothers Winsa mana. Nan take ya koma neman account Win su Babban Yaya. Sai dai babban Yaya irin AA ne, shima twitter Win ce kawai yake da account kuma babu komai akai sai harkar business. Yaya Fawzan ne keda a Instagram da X Win, anan ne ya samu hotunan Babban Yaya, da AA Win har ma dana Abah. Mafi yawanci kuma hotunan salla ne, dana juma'a sai na Waurin aurarraki. Akwai wasu hotunan da dama na zuri'ar Darma, sai dai shima babu hoton mace ko Waya, kuma babu irin wancan hoton da yaga Huznah na kallo. Ajiye wayar kawai yayi ya shiga wankan, abubuwa da yawa zuciyarsa ke ayyana masa, ciki harda Huznah na charting da AA Darma ne ya tura mata hotunan da kansa. Sai dai zuciyarsa na ?aryatawa ta wani gefen, dan yasan labarin wanene AA Darma da halinsa akan mata. Kai har yanda Huznah ta dinga bibiyarsa da ?in kulata duk sai da ya binciko...

Har washe gari yana son ture abin a ransa amma zuciyarsa ta?i nutsuwa. ?arshe dai ya Wauki wayar tata ya fita da ita bata sani ba. Da yake tsakanin jiya zuwa yau ya saka mata ido sosai ya fahimci password Win data canja yana gwada sakawa wayar ta buWe. Haka ya shiga ya fara mata bincike daki-daki. Tun daga kan massages, bai samu komai ba ya koma WhatsApp, nan ma normal sai sisters Winta kawai take charting da su dan canja mata layi da yayi dama duk babu ?awaye yanzu. Ya koma facebook, bata buWe account tabi dokar daya kafa mata kenan, sai ya shiga Instagram. Sai ko kai tsaye ga hoton jiya tana akan shafin da hoton yake ma bata fito ba. Koda ya duba mai account Win sai yaga sunan Saleem Mahmud Darma. Ya shiga profile ya duba yaron tabbas da ganinsa kaga jinin Darma Win, koda ya shiga account Win sosai hotuna ne kala-kala na zuri'ar Darma. Akwai kuma na AA Win sosai a wajen, dan wanda ma Huznah Win ke kallo kwana biyu da Worashi, yanzu kam sosai hoton ya buWe

121 / 138

Chapters