Advertisements
Chapter 92 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   92 / 138

273K to 276K   out of 412.8K words

Besty na ba raguwa bace ba . Ya faWa a cikin kunnenta. Murmushi tayi itama tana Wagowa, da wani sassanyan kallo ta kashe masa ido Waya. Tare da faWin,  Ashe dai ka gane .
? ?? Murmushi ya sake saki, ya kamo fuskar tata cike da shau?i da soyayya ya manne lips Winsa akan nata, idanunsu cikin na juna ya fara sumbatar ta, sai kuma ta lumshe natan a hankali dan bata iya jurar kallon cikin idanunsa sam. Suna da wani sirri na musamman mai ruguza nata dukkan kuzari a duk lokacin da ya tsareta da kallo da su. Sunyi matu?ar shagala a falon har sun kai wani matakin da basu farga sun kai ba, sai da ?urar ta lafa ya tasata da tsokana da dariya, itako tana masa shagwaSa da faWin ya gama da ita, dan abin kunya a falo. Cak ya Wauketa sukai bedroom yana dariya cike da ?eta. Dan bawai bata jin jikin bane ba a hannunsa, ba kuma tana iya dauriyar bane ba har yanzu, kawai dai Babynsa na taimaka masa ne wajen samunta yanda ya kamata batare data farga ba, sai daga baya kuma ta dasa masa rigimar tata, shiko baya gajiya da lallashi.....

__________&

? ? ?? A lokacin da nan Maanal da AA ke faranta rayukan junansu, a Sangaren Saheeba abin duniya ne ya isheta. Yau kwanan amarya tara kenan a gidan, ta gama kwanakinta bakwai tun shekaran jiya. Haka ta zage tai gyara da tunanin mijinta zai dawo gare ta a ranar amma sai Babban Yaya ma ya tsiri tafiya Kano. Sai yau da Ameerah zata sake amsar girki duk da basu zauna sun tsaida kwana bibbiyun ba sai ga shi ya dawo da yamma. Kuma tana jin lokacin da yake kiran Ameerah Win ya sanar mata ai masa sakwara, dan suna a sashen Oum da yanzu ta dage da zuwa ita da Nuratu yay kiran. Da farko Ameerahn tayi kamar bazata tashi tai aikin ba sai kuma zuwa can bayan sun dawo sashen nasu taga ta shiga kitchen tana aikin. Tafasa zuciyarta taketa mata, har tana jin bazata iya ha?uri ba sai taje ta samu Ameerah.
? ? ? ? Mi?ewa tai ta sauka downstairs Win, dan tunda akace Ameerah keda ?asan bata zama. Iyakarta bi ta fita. Ameerah na aikinta bluetooth a kunnenta tana jin karatun Alkur'ani Saheeba ta faWo mata kitchen Win. Da farko ita tsoro ma taji, dan har sai da ta sauke ajiyar zuciya ma. Sanin babu mai shiga harkar wani tsakaninta da Saheeban yasa ta maida kanta ta cigaba da aikinta. Hakan ya ?ara saka zuciyar Saheeba zafafuwa. Dan haka cikin kaushin harshe ta ce,  K bakiga mutane bane? .
? ?? Banza Ameerah tai mata, duk da kuwa ta jita sarai. A fusace Saheeba ta Wan fincikota baya ta hanyar kama mata veil. Sai kuma a fusace ta ce,  Amma ke ?ar rainin wayo ce ko? Ina magana kina wani shareni .
? ? ? ? Kallonta Ameerah tayi ido cikin ido, sai kuma ta girgiza kanta cikin nutsuwa ta ce,  Ai bamma yi zaton kin san akwai mutum a kitchen Win ba, sannan da kika shigo ke kikace ni kuma nasan ba ?arki bace ta fari. Zan baki shawara kodan mu kasance muna ganin mutuncin juna ki dinga sanin ta yanda zaki mu'amulanceni kamar zai fi miki sau?i. Sunana Ameerah, sannan in zaki shigo inda nake ko ya kasance muhallina ki min sallama. Na tabbatar miki zan amsa, kuma zan darajaki har na cigaba da kiranki da sunan dana saba wato Aunty Saheeba .
? ? ? ? ?? Wani irin kallo Saheeba ke mata, sai dai ta kasa magana dan mamaki, Ameerah dai data sani mai shiru-shiru ce bakinta ya buWe haka. Lallai ai dama barewa batai gudu Wanta yay rarrafeba ai, jinin Hajiya Shuwa ce fa....
? ?? Dai-dai nan kira ya shigo wayar Ameerah daya zama sanadin katsewar tunanin Saheeba. Ganin yanda Ameerahn tai wani ?ayataccen murmushi da faWin,  Amincin ALLAH ya tabbata a gareka My!. Badai har ka sauka ba? .
? ? ? Daga can Babban Yaya ya ce,  Gani ma a gida My Soha .
?? Wani kalar waro idanu Ameerah tai da faWin,  Are you serious Yayana? .
? ? ? ?? Babban Yaya dake murmushi har Ameerah na jiyo sautinsa ya ce,  Le?o ki gani .
? ? ?? Fittt Ameerah ta fice a kitchen Win cike da farin ciki tabar Saheeba da ?amshinta baki a buWe.........
'?



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________


........A kofar babban falonsu kuwa Ameerah ta samu Babban Yaya, ai bama tasan ta wani daka tsalle ta ma?alesa ba. Dan wlhy da gaske tayi kewarsa kwana biyu kacal. Wani irin farin ciki mai narka zuciya ya mamaye zuciyar Babban Yaya. ALLAH kaWai yasan yanda yake son yarinyar nan, dan akwana goma kacal datai a gidansa ta dasa wata soyayyarta mai zafi a cikin zuciyarsa. Tana riritashi da masa dukkan abinda yake so daga matarsa. Duk wani gurbi da giSi da Saheeba ta bari yake masa ciwo da jin ?ishirwar samu a cikin rayuwar aure Ameerah na ?o?arin kwaranye masa su a cikin kwana kaWan. A cikin kunnenta ya raWa mata,  I miss you my Soha .
? ? ?? Maimakon bashi amsa sai ta ?ara ?an?ameshi kawai. ALLAH ta manta da wata Saheeba a kitchen. Sai da Babban Yaya ya Wagota yana ?o?arin sumbatarta Saheeba dake fitowa karaf a idonta zani ya harWeta tana neman faWi, sai dai ALLAH ya taimaka ta dafe bango da ?yau a maimakon faWuwar tata sai flower base ta faWo daga inda akai ado da ita a hanyar fitowa kitchen ta faWi, hakan ne ya fargar da Ameerah da Babban Yaya. Kallon ido cikin ido Saheeba da Babban Yaya sukama juna. Harga ALLAH baiso hakan ya faru ba, koda yake fushi da ita da son hukuntata babu tsarin cimata fuska irin haka a ransa. Dan haka yanzun ma sai ya janye idanunsa a cikin nata slowly, kafin ma yay wani yin?uri itama Ameerah da hakan bai mata daWi ba dan bazata so ai mata ba harta zame jikinta daga nashi. Sai dai kafin ta fita gaba Waya Saheeba ta wuce sama da sauri-sauri. Sai kawai baban yaya ya wani basar ya sake ri?o Ameerah ya rungume.
? ? ? ??  FaWa min sau nawa kikai missing Wina? .
? ? Ganin ya basar itama Ameerah sai ta basar, cike da shagwaSa ta ce,  Sau dubu Wari ba adadi .
? ??  Anya babu ojoro a wannan lissafin my Soha .
? ? ? ? ?ar dariya tayi da faWin,  Da gaske fa .
? ? ?  To ina godiya. Muje nai wanka sauri-sauri kinga ana kiran magrib .
? ? Babu ja'inja ta ce,  To amma fa ina girki, ai min afuwa kaje yanzu zan ?arasa na sameka .
? ? ? Cikin gamsuwa ya ce,  Okay tauraruwar mijinta. yay maganar yana ja mata hanci. Murmushi tayi tana sumbatar hannunsa. Shima sai ya murmusa kamar ba Babban Yaya ba ya nufi hanyar upstairs. Ita kuma tai kitchen...

? ? ? Koda ya haura saman kai tsaye sai ya nufi Wakin Saheeba dan bata a falo.? Sai da yay knocking, jin babu alamar za'a amsa masa balle buWewa ya tura ?ofar ya shiga. Zaune ya sameta a bakin gado tana kuka. Ya tsaya kawai yana kallonta tsahon minti Waya. Itama kallon nasa take tana hawayenta. Ganin ya?i ?arasowa inda take sai ta mi?e ita taje gareshi, gabansa ta tsaya ?i?am, muryarta na rawar kuka ta ce,  Yanzu Daddyn Naufal kana ganin na cancanci duk irin wannan wula?antawar daga gareka? .
? ? ? Sosai Babban Yaya ya sake haWe fuska, a dakensa ya ce,  Sai ki gaya min yaushe na wula?anta ki? Ko rungume matata ya zama laifi saboda kar ranki ya Saci Aunty na .
? ? ? ?  Kayi ha?uri ni bance haka ba, kuma ni ba Auntyn ka bace. Amma kaji tausayina kamin adalci Ya Fadeel. Nasan nayi kuskure amma nayi al?awarin gyarawa. Yanzu dan ALLAH ya kake so yarinyar nan ta Wauke ni? A ranar fa da zaka dawo wajena kabar garin nan, sai yau kake dawowa, maimakon kuma kazo ka sauke ha??ina sai ka tsaya a wajenta saboda tana amarya .
? ? ?? Sosai Babban Yaya ya taSe baki da faWin,  Look bana son damuwa daga shigota okay, sannan ki bama kanki dukkan amsar data dace ai, ki kuma duba lokaci yanzu nata lokacin ne, ruwanki ne ki gyara ki amfani da lokacin da zaizo nan gaba, ruwanki ne ki cigaba da shirme ki rasa gaba Waya. Dan ba damuwata bace na sake wata tafiyar a ranar girkin naki mtsowww!!!! . Ya juya ya fice abinsa. Rashin iya maganar Saheeba na ?ona masa zuciya. Sam bata san yanda ake tauna magana kafin a fitar da ita ga miji da laushi ba. Kawai duk abinda yazo mata kan harshe furtawa take, shi kuma baya son raini, shiyyasa ko iya zama hira da ita baya sonyi, amma wlhy da zata san irin maganar da zata dinga masa da mutuntawa data samesa fiye da yanda take so, dan duk da auren haWi akai musu zuwa yanzu jini ya gauraya da ruwa tunda ga ?a?a.......

__________&

? ? ? ?? Sai da Rabilu yaci yay nak da abinci ya sha lemon kwali sannan hankalinsa ya dawo jikinsa ya fuskanci Sen... Bukar da ?yau. Sen... Bukar yay gajeren tsaki. Dan tun Wazun ya ?osa Rabilun ya kammala. Cike da takaici ya ce,  Kai idan ka kama abinci baka ji baka gani kamar wani jinin yunwa? .
? ? ?  Ranka ya daWe miye maraba? Ai jinin yunwar ne. Rabona da abinci lafiyayyen irin wannan tunda nabar gidan nan. Kai dai ALLAH ya rabamu da faWuwar ba?ar tasa kawai ranka ya daWe. Yanzu dai gani nayi darrr mikake so? Kasan ni ko wuta kace na faWa ALLAH kafin ka rufe baki na gama ma cinyewa a cikinta .
? ? ? Wata dariyar ?eta Sen... Yayi, ya ce,  Ja'iri, lallai kaji wuju-wuju Rabilu. Shiyyasa gaka nan ko'a ido duk ka zama wani kwashe wuya kamar mari?in lema. To manta dai komai ya wuce. Yanzu sabon aiki ne ya tashi, amma kuma tsoho ne daya kwanta za'a tayar.
? ?  To to ranka ya daWe yanda kace ai haka za'ayi, na gabashi ne? Ko kudanci? Ko arewaci? .
? ? ? ?  Batun yarinyar nan ce da Wan gidan Darma ya aura, ina son kayana su dawo hannuna koda tsiya koda tsiya-tsiya. Dan haka kawo shawara .
? ? Sosai Rabilu ke jinjina kai kamar tsohon ?adangare, sai zuwa can ya ce,  Tur?ashi, ranka ya daWe wannan fa tamkar tado da ya?in duniya na uku ne lokacin yinsa bai kai ba. Ka sani na sani wannan yaron ba ?yale bane ?yalle ne. Shifa baya tsoron TAHO MU GAMA! a mutu ko'a rayu akan mutuncinsa zai iya sallamawa rayuwar. Balle wannan yarinyar naji gagarumin tarihinsa da ita. Tsohuwar zuma ce, sannan renonsa ce ta ainihi. Dan tare uwar goyonsu ta goyasu, ta kuma yi musu tawai. Ba wannan bane ma matsalar, saboda yanda suke son juna bayan an musu sharrin rabuwa tazo sunyi shekarun da basa tare da juna da ciwon ZUKATA, amma suna sake haWuwa sai kaji lufff ko ciwon ?irji wani bai sake kukan yanayi ba a tsakaninsu. Kasan kuwa wannan ?auna takai ?auna. Danni in ma ba'a film ba wlhy ban taSa ganin irin wannan soyayyar a zahiri ba. Bawai fa ba'ayi bane ba. Anayin ma irin wadda tafi tasu zafi, amma sai kaga da anyi aure labarin ya canja salo, duk da dai suma har yanzu ba'a tsallake koda goma ta marmari ba balle mu tantance....
? ? ? ?  To kaima kaji ka bama kanka da kanka amsa, a wannan zamanin har wata soyayya ce tsakanin maza da mata in ba ta ina son kuWinka kana son jikina ba. Malam kuWi itama ta gani shiyyasa ta ri?e amana, shi kuma shegen kayan marmari ya gani shiyyasa. Dan haka wuta zamu bata iya wuta da kuWaWe na tabbatar da gudu zata saki wancan layin ta dawo namu....
? ? ? ?  Eh to ban musa maka ba ranka ya daWe, amma dai da zaka fahimceni ka kuma ji shawarata da ita Win an barta, mudai sake komawa matsayar ta inda aka hau tanan ake sauka. Wato can wajan ubanta, dan kasan su har yanzu fa zaman jiranka suke yi ka dawo azo a baka ita. A bincike mai ?arfi kuma da nayi har yanzu basu san tayi aure ba, tama auri Wan gidan Darma, dan kakar nan tata ta tsaneshi, da ace sun sani ai da yanzu wani batun ake ba wannan ba .
? ? ? ?  Ban?i ta taka ba Rabilu, amma kasan akwai ?an kuWaWena dama a jikinsu, kuma dama dole zan bibiyi kayana, sile bazan iya yafewa ba a ciki kaima ka sani .
? ? ??  Tabbas hakane Alhaji, nima ban baka goyon bayan yafewa ba. Kuma zan tayaka ya?in ?watosu. Shiyyasa nace mu sake komawa ta can wasan zaifi daWi. Zamu jefa tsuntsu biyu da dutse guda kenan. Mu haWa rikicin bala'i tsakanin su da Wan gidan Darma Win, mu kuma ce kuWinmu ko yarinya, dan na tabbatar a yanzu babu ko sisi a bishashar arzi?in nan da kai musu. Kasan mutumin ?auye idan yaga banza (ALLAH dai ya saka mana mu mutanen ?auye=?D?=??). Ya iya kwanciyar magirbi, sai dai kuma akwai tsoron Wan sanda, wuta zamu basu iya wuta muce kuWi ko ?a, ko ofishin ?an doka .
? ? ??  Kai banza ne, ka manta ubanta Wan dokar ne da kansa .
? ??  Eh kuma fa haka ne, to ranka ya daWe shirinmu zamuje da shi. Barikin sojoji zamuje ka samu gidiba-gidiba majiya ?arfi kamar guda goma zuwa ashirin, kawai mu Webesu atai kauyen nan a tattarosu .
? ? ??  Eh kaima ka kazo da magana anan Rabilu. Indai wannan wasan ya faWa fiye dana farko, a maimakon mota da kaci wancan karon wannan karon harda kuWi .
? ? ?  To ranka ya daWe ina godiya, amma motar ma fa ta waccan karon har yanzu ba'a bani ba. Kasan daka turani wajen Oler daga cewa sai an min sabon fenti har yanzu sai binsa nake baya ma saurarena.
? ? ? Dariya Sen ya kece da ita. Sai kuma ya bubbuga kafaWar Rabilu yana faWin,  Kwantar da hankalinka wannan karon hannu da hannu ni zan baka. Sai ma ka zaSa ka darje sannan. Kai ina ga ma harda ?yautar gida zaka samu. Dan ni kaWai nasan irin romon lagwadar demokradiyyar dana hango, kaga yarinya tako ina ta cika tai ciff-ciff rainon madara da lemon kwali, wato shegen yaron nan da alama akwai lafiya, dan yarinyar nan ?yawun daya ?ara badai shinkafa ba wlhy sai dai madarar kwalli .
? ? ? ?  ALLAH ranka ya daWe? .
??  Hummm ai Rabilu ba'a magana wlhy, dama fa mace ce iya mace a wajen nan. Kasan ba?a?en matan nan da muke rainawa kullum idonmu a nunar ranar nan, ?an bleaching ma sunfi yawa, dan shi farin usil farin so ne fa ?auna dan fenti ne daga ALLAH, amma ba?a?en matan nan ?a?an malam Shehu wlhy talaucin ne kawai amma kadara ce mai girman gaske. Yo hauka ake na ?ara auren fara .
? ? ?? Dariya sosai Rabilu ya kece da ita............
'?




*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________



............ Ni ALLAH bana son kitso. Baga salla na zuwa ba saura ?an kwanaki ka bari zanyi .
? ? ?  Haba Besty! Wai kina son komawa ?azama ne, mata ai da kitso aka sansu, amma tsakani da ALLAH ke babu abinda ake kai ruwa rana dake a kansa sai kitso. Kanki wata kusan biyu ke nan babu kitso. Kullum sai dai mu taje a Waure diba har ya fara raguwa.
? ? Hawaye sosai ke ziraro mata, dan a duniya babu abinda Manaal ta tsana irin kitson nan, da ace fa an yarje mata suyi aski da itace zata zama shugabarsu. (Hhhhh wayaga su Bilyn Abdull >?#?>?#?adai rufe rufau kawai na Maanal ne ya fito filin subahana). Zuru AA yay yana kallonta, ?asan ransa ko dariya ke cinsa sosai. Kusan fa sati biyu kenan yana wannan faman da ita amma ?iri da muzu da yay magana sai ta hau ciwon ?arya. Shi kuma harga ALLAH yana mugun son ganin ta da kitso. ALLAH dai ya taimake shi idan Baby girl za'a haifa masa kada a haifo mai gudun kitso....
? ? ?  Besty .
Ta kirashi cike da shagwaSa tana girgiza masa hannu. Cikin sauke ajiyar zuciya ya ce,  Uhhyim Besty  .
? ??  Dan ALLAH ka ha?ura zaka bari sai sallar. Kaga kwana tara fa ya rage duka-duka. Kuma kace zamuje Giro da KD, basai kawai nayi kitson ba .
? ? ? ??  Uhm-uhm Besty, karfa lokaci yayi kice zaki saka min rigima .
? ?  ALLAH bazanyi ba .
 Kin tabbatar?

92 / 138

Chapters