Advertisements
Chapter 125 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   125 / 138

372K to 375K   out of 412.8K words

ba gaskiya, da nasan haka ne dana ajiye ki a Sangarenki daban na saka ?yaure yanda dan uban mutum dole su barni na sha?ata. Amma bari kiga gari na wayewa yanda kika san kajin bashi haka zasu ishemu da kaya-kaya gida da sai kace ana bikin suna mtsowww. Yoni ace tun farkon aurena irinki na samu banga abinda zai sa na ?ara aure ba. Wannan al'amari haka cakwai malam. Ai babu abin faWa ga wannan miji naki sai ALLAH ya shi mishi albarka... duk fa wannan surutu yana yi ne yana danna nama a baki. Kafin ya kai ?arshen labaran nasa na rashin kangado yakai ?arshen kajin biyu tas sai kasusuwa. Sai kuma ya hau salati da faWin,  Oh ni Balala, kinga dai Basari na cinye miki kajin sayen bakin yo dama yunwa nake ji, matan nan najin haushi na yau babu wadda ta bani tuwo. Kinga taso ki suWe ko ?ashin ne na miki al?awarin gobe zan kawo wasu. Idan ma tsiren Hashibu kike so sai na haura gobe na sayo miki a Ingawa.
Ko motsi Hajiya Basariyya batayi ba, haka ya daddafa ya tashi da ?yar yana tura ciki gaba ga hakki da nishi ya sake Ware gado inda take.  Haba basariri na wai fushi kike na cinye kazar? Kwantar da hankalinki kinji ai nace zan sayo wata . Yana maganar ne fa yana ?o?arin sake haike mata. Itako abinda ya tokare mata ?irji ya hanata ko motsi. Haka ya sake bidirinsa babu batun yin wanka ko yin alwala ma balle addu'ar kasancewa da iyali. Dama Wazun baiyi ba.
Kafin wayewar gari Hajiya Basariyya ta sake tabbatar da Annabi Isa ba Wan ALLAH bane. Daddy kawai take tunowa tana rusar kuka dayin dana sanin wautarta, bata taSa sanin rabuwa da Daddy zai zame mata masifa da bala'in rayuwa ba irin yau. Sai yanzu nasihar Kawu Manu ta wancan karon ke dawo mata a rai da zuciya. Ashe gaskiya suke gaya mata ta dawo a hayyacinta kafin lokaci ya ?ure mata. Gashi ko ya ?ure matan, Daddy ya mata saki uku wani ?aton banza ?aton ?auye ya aureta. Haka tasha kuka da rashin barci, ana kiran sallar farko ya tattara kayansa ya Wauki butar ta ya fita. Daga haka bata sake jin Wuriyarsa ba. Itama dai haka taje tayo wankan ranta duk tsantsamin banWakin dana Alhaji Balala data kwana a ciki. Sai ko da tayi amai taji daWi. Ai gidan Kawu Manu gidan ?an gayu ne sosai, dan ko ina shafe yake da siminti sai wajen dabbobinsa kawai. Sannan banWakinsu tsaff yake dan iya akwai tsafta. Balle ma basu da yaran da zasu Sata musu. Bayan ta idar da salla barci Sarawo ya Wan saceta a wajen. Kawai zuwa can gari yayi shaaa sai taji kawai an faWo mata Waki. Firgigit ta buWe ido tana tashi. Wata busashiyar mata ce a kanta kayan jikinta idan wankewa za'ai saci omo jakka biyu. Tana wani yamutse-yamutse ta ce,  Sunana Deluwa, uwargidan Alhaji Balala. Munji shiru ne baki fito kin Wora Wumamen tuwo ba ga yaranmu sun fara kukan yunwa .........
'?

To gafa Hajiya Deluwa uwargida ran gida ta iso jama'a =??>? ?.
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
AJIYAH A DUHU

197

........Mamaki ne ya nema kashe Hajiya Basariyya, yo gari fa bai gama wayewa ba ma. To wai ma ita da aka kawo jiya ake jiran ta fita ta saka Wumamen tuwo ne komi ma. Maimakon tai magana sai ta zubawa matar ido kawai tana kallon ta, ALLAH tsabar ramarta tasan idan kamata zatai sai ta karyata. Yo ai tayi biyar Winta. Takaici ya hanata bata amsa ta maida kanta kawai ta sake kwanciya.
Cike da rashin hankali matar ta ce,  Ikon ALLAH, yoke haka keyi ki shige da miji Wakin tun farkon dare har ketowar alfijir amma ace ki fito kisa ma mutane abinci a wuta kiyi banza. Ke mu fa nan babu ruwanmu da wata ?ar masu kuWi ko hajiyanci daka mace zamuyi wlhy. Idan Kinga bazaki iya ba ce ya sakeki kiyi gaba mu tafi nono fari a wajenmu. Aikin Sur inji tusa. Kina son nuna birnancin naki miya hanaki zama gidan mijinki lafiya da kishiyoyi, su can sun rabu da ala?a?ai munan kuma an kwaso an kawo mana. To wlhy mu basu bane ba bazamu Wauka ba ehe. Garama ki shirya ki Waura Wamarar zama gidan Alhaji Balele sai jaruman mata . Ta wani buga labule ta fice abinta.
Eh lallai yau kam Hajiya Basariyya taga mata, ashe Hajiya Yaya Sayyada ce, Asiya ko ai sai dai a kirata waliyya. Tofa, wai yanzu akan wannan kucakin mijin ake wannan tada jijiyar wuyan? To ita wlhy bataga mata ba anan. To jama'a shifa ?auyen ma nada ?auye, wannan ai sune asalin ?an ?auyen ga jahilci ga rashin sanin ciwon kai. Yo idan ?an ?auyen su Kawu Manu na kiran nan ?auye sai taita mamaki, ashe-ashe sunada hujja. Babbar bala'i ALLAH ya ji?an Hajiya Yaya da Asiya badan sun mutu ba. Tana a cikin wannan jimami sai ga Alhaji Balala da wani tsohon kofin silba da leda. A gabanta ya ajiye yana washe baki da faWin,  Tashi amar sugun-sugun tashi na sayo miki shayi da burodi ne da ?osai, har fa garin kawunki naje yanzu da safen nan nine Wibar farko a tukunyar shayin nan. Sabi'u nasa ya kaini a mashin ai nasan kin kwana da yunwa bakici komai ba .
Gaba Waya maganarsa hawa mata kai yake yi, dan haka tace,  Nagode . Daga haka taja bakinta tai shiru.....

=??>? ?Gaskiya Basari kina cikin ?aulani, nace dole na baku First night na Alhaji Balala da Basari bazanci amanarku ba=?? sai ku tabbatar kun min godiya da sanya albarka, dan bana son harkar shiru anan tom>?#?=??.

__________&

Canjawar Sageer a gidan ta saka Huznah a matu?ar tashin hankali. Gaba Waya sai taji duniyar da komai basa mata daWi. Babban tsoronta kada ya gayama Daddy abinda ke faruwa ma. Tana son yi masa magana amma tana jin tsoro dan ya?i bata fuskar yin hakan. Zaman gidan ma kwana biyu ya rage yi, baya dawowa sai dare sosai, baya cin abincinta. Komai zai sayo ya ajiye kamar yanda ya saba amma ya barta da su. Daga sallar asuba idan ya fita baya dawowa sai sha Wayan dare. Daga sannu idan tai masa ya amsa ciki-ciki baya ?ara kulata. Sai ta shiga wata irin rama. Idanunta kullum a kumbure alamar kuka. Ta tattara wayarta ma ta kai Wankinsa ta ajiye duk dan ya gane ta ha?ura da komai amma ya?i kulatan dai. Hatta Wansa da yake ?ulafuci da bama kulawa kwana biyun nan ko Waukarsa baya yi.
Bata taSa tunanin hakan zata kasance da ita akan Sageer ba. Rayuwa kenan, wannan shine ashe magabata ke cewa kayi hankali kafin duniya ya koya maka karatunta. To ita dai ta koya daga duniya a tsakanin nan kam. Karo na farko ta yanke shawarar tunkarar ?anwarta Madeena da matsalarta. Bayan ta kammala gyara gidan dan yanzu kam zagewa take tayi ta shiga Wakinsa, inda ta ajiye wayarta tana nan a wajen har yanzu bai taSa ba tabbacin fushin yake da ita sosai. Ajiyar zuciya kawai ta sauke. Ta Wakko wayar ta fito. Fodio na a falo kwance a ?ar katifarsa yana barci itama ta zauna a ?asan. Wayar ta kunna, ta sayi kati a account Winta harna dubu biyu yanda zai isheta sannan tai kiran Madeena. Sai da ta kusa tsinkewa ta Waga, cikin muryar barci tace,  Aunty Huznah .
Murmushi Huznah tayi tausayin ?annen nata na ?ara kamata, dubesu a gidan mahaifinsu babu cas babu as na wahala sai dai suci suyi barci a binsu, su suna ganin gata ne sai an kaika gidan wani ka gane ALLAH Waya ne. Cikin sauke ajiyar zuciya ta katse tunanin nata da faWin,  Madeena har yanzu baki ma tashi ba? .
Mi?a Madeena tayi tana tashi zaune da Wan jan tsaki, ta ce,  Wlhy jiya ban kwanta da wuri bane ba. Fatan dai lafiya kema kira da safen nan ina Daddyn mu? .
 Gashi yana barci, magana na kira muyi Madeena. Dan haka ina son ya kasance ke kaWai ce a wajen .
 Babu damuwa ni kaWaice a Waki na kuma kulle ina jinki.
Komai Huznah bata Soyema ?anwar tata ba saboda akwai sha?uwa sosai a tsakaninsu. Babu abinda Madeena ke nanatawa sai kalmar innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Kafin tace,  Amma wlhy ban san har yanzu baki da wayo ba Aunty Huznah. Yanzu dan ALLAH dama baki cire tunanin bawan ALLAHn nan a zuciyarki ba har yanzu. Haba aunty Huznah haba dai kamar wadda bata da ilimin addini. Ki daina biyema Ummi fa wlhy kina dai ganin yanda ta kasance mata. Jiya Uncle ke gaya min wai tayi aure a ?auyen gaba da su Kawu Manu.....
 Aure kuma? .
 Eh wlhy, yo in ba ?auyen ba wazai yarda ya auri Ummi da wannan halin nata. Ai taima mutun nasiha da nuna masa gaskiya amma ya dinga rufe ido ya?i fahimta. To wlhy ki dawo hayyacinki kar ki zama mai irin wannan halin. Aunty Huznah ALLAH ya miki gata, ya baki miji mai sonki da kula dake, kalla yanda yake rawar jikin kiyaye dukkan ha??okinki, wlhy Wan zaman da mukayi haihuwar fodio bakiji yanda zamanku ya birgeni ba, sai naji ina addu'a ALLAH ya bani miji ko bai kai Yaya Sageer ba. Dan ba auren mai dukiya bane ke nuna ka more aure, masu auren masu kuWin nawa ne a cikin bala'i da masifar rayuwa, mazan ma basu da lokacin su kullum suna yawon ?asashe, kuma bazasu iya tsare rayuwarsu ba sai sunbi wasu matan. Wanda kuma ke ma yawo a iya Nigeria ko Africa shima zaki samu ?alilan ne masu iya ri?e kan nasu. Gamu nan an ce mu fito da mazan aure munma samarin magana duk sun tarwatse kamar anyi ruwa an Wauke, ka rasa ubami ke kawosu gunka da idan ba auren ba. Amma ke kin samu mai tattalin rayuwarki mai sonki kina wasa da damarki kuma akan haramun ma son wani a gidan aurenki. Haba aunty Huznah ni wlhy duk sai ma kika bani kunya, nazata ai a wuce wajen zuwa yanzu. Ni dai shawarar dazan baki ki koma ga ALLAH, ki koma gayama UBANGIJI kukanki ki shirya tsarkake zuciyarki da rayuwar aurenki ALLAH zai dafa miki ya cire miki Yaya AA a zuciyarki, ya kuma saka miki son mijinki. Shi yana can yana farin ciki da matarsa, Maanal gashi har ta haihu jiya twin's ke kina nan kina Sata ?ya?y?yawar rayuwar da ALLAH ya baki. Kiyi ?o?ari ki bama Yaya Sageer ha?uri ki nema yafiyarsa, dan wlhy ko Yaya Yazeed kika bari ya gayawa sai ya Sata miki rai balle Daddy. Ki cire ZUCIYARKI daga wannan AJIYA A DUHUN ki maidata cikin haske ALLAHU zai haskaka ki ya haskaka rayuwar aurenki ya haskaka jikinki da zuri'ar da kuka fara tarawa...
Sosai Huznah ta sauke ajiyar zuciya mai ?arfi,  Nagode sosai Madeena, Nagode da tunarwarki, wlhy wani lokacin rashin mai gayawa mutum gaskiya shike sake dulmiye tunainsa a wahalar rayuwa. Na jima da son jin ina son na cire soyayyar AA Darma a raina amma na rasa tayaya zanyi hakan, ta ina ma zan fara. Amma yanzu kam kin haska min hanya, kin cireni daga duhun dana shiga nakai zuciyata AJIYA A DUHU. In sha ALLAHU zan dage da addu'a, dan wlhy nima nasan na fara son Yaya Sageer, amma wancan ke danne zuciyata. Amma ina sha ALLAHU zan canja, zan canja daga waccan Huznah fandararriyar zuwa Huznah nagartacciya jinin Usman Chalawa.
 ALLAH ya tabbatar Aunty Huznah ki daina kuka. Nima zan tayaki da addu'a kuma zan saka a islamiyya a tayaki a kuma yi miki saukar Alkur'ani. Amma kema ki dage da addu'a jarabawace in sha ALLAHU zaki cinyeta. Nima zan kira Yaya Sageer na bashi ha?uri  .
 Nagode Madeena idan kikai min hakan kin taimakeni ?ar uwa ta. Ngd sosai. In ce dai baku da wata matsala? .
 Wlhy Alhmdllh babu matsalar komai, Mamma da Ammie na iya ?o?arin su a kammu, hakama Yaya Yazeed. Shima Daddy, Dan yanzu haka ma ni na dawo sashen Ammie ne .
 ALLAH sarki ALLAH ya saka musu da alkairi. Amma da Ummi tasa muyita zaginsu da kallonsu mugaye, gashi yanzu bata kusa kuma sun ri?eku da zuciya Waya. ALLAH yasa wannan auren ya zame mata izina itama ta canja .
 To amin .
Sun jima suna hira da tattauna abubuwa akan mahaifiyarsu kafin sukai sallama. Sai Huznah taji nauyin zuciyarta ya ragu sosai sai sauke ajiyar zuciya take yi.......

_______&

Anan gidan Darma kuwa tunda labarin haihuwar Maanal yazo musu tsakanin Saheeba, Nuratu, Mamy babu wanda baiji tashin hankali, ba?in ciki da hassada ba. Dan Mamy batayi kwanan gida ba a daren jiya sai asibiti. Sosai abu ya birkita mata zuciya sai aman jini. Haka aka kwasheta dan ALLAH ma yaso Aunty tazo Abujan ne jiya da safe, kamar yanda ta saba zatai kwana biyu ya koma. Sai kuma ga wannan al'amari dan AA da kansa yay kiran aunty ya sanar mata. Da yake kuma tana da babbar waya ya tura mata hoton yaran. Anan ne fa take nunama Mamy, su kuma su Saheeba a media suka gani.
Kawai Mamy na ganin hoton yara ta fara jan numfashi da ?yar, abu kamar wasa tari ya sar?eta sai ga aman jini. Ba Aunty kawai ba shi kansa RK da aunty taima bayanin komai mamakin ba?in zuciyar matar nan yake yi. Ya tabbata wlhy itace zata kashe kanta da kanta. Yanzu idan dukkan abinda ya faru bai zame mata izna ta koma ga ALLAH tana neman tuba da ro?on gafarar duk wanda ta zalunta ba mi kuma take bu?ata? To lallai kuwa aiki ya ganta. An tsayar da aman jinin nata da ?yar kuma sai ga sabuwar magana a gwajin da akai mata na jini dan doctor dake dubata yace a gwada ko akwai maleria a tare da ita. Sai kuma sakamako ya nuna akwai ciwon HIV...........
'?

Tir?ashi, wasu na murnar haihuwa. Wasu na kukan kabari ya tunkarosu. Wannan fa itace ainahin duniyar mutane na=?)?=?)?.
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
AJIYAH A DUHU

198

........Ba ?aramin tashin hankalin RK yayi ba da bayanin likitan, cikin rashin yarda ya ce,  Dr. Hamaad, how could you say that? She's my family. I can't believe this! This can't be true. Ta ina zata samo wani HIV? .
 I'm sorry Sir, shiyasa na fara samunka da maganar dan nima abin ya taSani sosai.
 No, I think it's the machines namu na lab na bu?atar canjawa. Amma kaga muje zan duba da kaina .
Ba musu Dr Hamaad ya mi?e suka fita tare, dan shi dai bashi da haufi aikinsa nakan dai-dai gaskiya. RK da kansa ya sake Wibar jininta ya wuce lab Win. Anan Win ma komai da kansa yayi. Abin mamaki result Win ne dai irin na Wazun yanzu ma ya fita. A rikice ya sake komawa Wakin da Mamy take tare da Nurse, yawunta suka Wiba, duk da a yanzu basa amfani da fitsari wajen gwajin HIV dan ya zama tsohon yayi haka yasa tayo fitsari. Nan ma aka sake gwajin yawu da fitsarin. HIV dai ta ?ara bayyana. Ya subahannallah mike shirin faruwa haka. Idan matar nan nada wannan ciwon a ina ta samu? Yayansa da Auntynsa kuma fa?. Karo na farko da a cikin aikinsa na likitanci ya ji abu mai girma da nauyi ya cushe nasa zuciya. A duk bibiyar Mamy da yake na tsawon shekaru da a?alla yanzu akai huWu bai taSa kamata da sabga ta bin maza ba, wanda tayi kafin aurenta daban. A wannan gaSar zai shedeta, bata bin malamai, bata bin maza. Tsantsar mugunta ce kawai a ranta da busashiyar zuciya. To a ina aka faWi a ragaya kenan?.
Kasa bayyana ma kowa wannan magana RK yayi, dan washe gari ma su Umma suka iso Abuja daga Kano ita da Gwaggo Khadijah. Sai ?ammatan family Win su biyar da masu aiki. Gidan Darma aka shiga gyarawa lungu da sa?o. Da yake Nibras na nan Umma tace ta gyaro Wakin Yaya Fawzan, su Lailah kuma suka gyarama Najma nata. Itama Saheeba ta gyara na babban Yaya, nan ma su Lailah suka gyara na Ameerah. Sashen su Maanal babu kowa, aka gyara falon sama sai ?asa zuwa bedrooms na ?asa da kitchen. Sai bedroom Win dake sama babu kowa ciki

125 / 138

Chapters