Advertisements
Chapter 1 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 107

1 to 3K   out of 320.4K words

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
BOOK 2 paid book

Note!!!!
This book is a paid book, duk wacce ta karanta ba tare da ta biya ba akwai hakkina akanta, i put so much of my effort into this, sannan masu sharing,kuma dai kusan da cewa akwai hakki akan ku, a kiyaye.



chapter 56


Update!!
Ahankali siririn hawaye ya soma zarya akan fuskanshi yana kallon cikin idanunta, kokari yake yayi magana ya kasa,haka zalika jikinsa kamar an zare duk wani sassa dake dawainiya da kuzarin sa, yanda take magana ya tabbatar mashi da tanada sa hannu a cikin wanannan qalubalan daya tsinci kansa, babu abunda yake sai inna lillahi a zuciyarsa,duk yanda yaso ya daga hannunsa ya kasa, yanaji yana gani ta miqe ta fuce daga dakin cikin yan mintuna kalilan ta dawo da wayarta, anan gefensa ta zauna ta kunna record din, gaba daya conversation din da sukayi da mutalib daga farko har karshe babu abunda yayi saura hatta waya da yayi da qalam da yanda yaso ya fada mashi kan evidence din daya samu is recorded, saida suka gama saurara tass ta kashe, tana kashewa ta kalleshi, “kana mamaki ko?, well let me tell you, duk wani movement dinka yana kan idanuna jamid kuma nasan abunda kake shiryawa, wato kana tunanin wannan’’
tayi mashi nuni da drive din kafin ta nunfasa tare da sauke murmushin da ita kadai tasan ma anarshi tace ‘’kana tunanin wannan ne zai dakatar da kudirina?, kana tunanin wannan ne zai kawo karshen duk shirin dana yi shekara da shekaru?,where you planning on bringing me down?, meysa?, ni fa matarka ce, why cant you support me?, why, shin kasan irin kuncin da nake dauke dashi a raina shekara da shekaru?, daga ranar da taj ya bayyana a rayuwarmu duk wani farin ciki ya kaurace mana kuma yayi sanadiyar mutuwar ummu, akan idanuna baqin cikin yaron nan ya kawo karshen nunfashin ta,’’
idanunta yayi jaa sosai ta sauya fuska gwanin ban tausayi bayan ta karashe harda hawaye akan fuskanta, 

 jamid ko babu abunda yake sai kallonta,ganin irin kallon da yake mata yasa ta kece da dariya 

hahahahahah’’ saida tayi mai isarta lokaci guda kuma ta tsagaita idanunta yayi jaa sosai tace ‘’  duk wanda ya shugo gonata saina kau dashi koma waye, meysa baka tsaya a matsayinka ba ka zuba idanu kawai?, maysa zakayi interfering?, yanxu kaga consequeces din hakan?,.., bari na fada maka the most interesting part’

sake matsowa tayi dab da kunneshi yanda dagashi sai ita ne kawai zasuji abunda take fada tace ‘’cikin abunda bai wuce minti daya ba tak and with just few money na sa akabi ta kanshi da mota, deep down i wanted him to be dead saidai idan na barshi haka nayi ending dinshi ta sauqi, wannan yasa na chanza plan, I’ve never regrets doing that,i want him to suffer, bazan kasheshi ba ayanxu amma saina nakasa rayuwarshi, saina maidashi mara galihu, kamar yanda nayi alkawari tajudeen bazai taba samun jin dadin rayuwa ba har ya mutu indai ina raye, i will make sure that he suffer, i will makesure that ko dabba ta fishi gata,in fact duk abunda zan mashi bana tunanin zai taba goge tabon dake danqare a zuciyata har sainaga karewar nunfashinsa and i mean it’’


tana kaiwa nan ta miqe jikinta har yana tsuma ta juya, ba karamin tashin hankali jamid ya shiga ba musamman dayaji da bakinta tayi admitting itace tayi sanadiyar accident din taj din, ga kalaman da take furtawa babu imani ko kadan a cikin su kuma ya tabbatar saita aiwatar da abunda ta fada, innalillahi wa inna ilaiahi rajiun, rayuwar taj da sabeeha tana cikin matsala saboda allah kadai yasan me ta shirya yanxu, da kyar ya samu ya bude bakinsa dake karkace ba ya soma magana a rarrabe abun tausayi, ga hawaye na zarya akan fuskanshi., ‘’Al…llah..ba…zai…ta..ba..bakiii..iko ba’’
ya karashe yana rintse idanunshi, chak ta tsaya ta gama sauraronsa kafin ta fuce daga dakin gaba daya ma.



tana futa ta shige study room dinta tare da janyo laptop din dake kan table din ta saka drive din a jikin laptop din har yayi connecting, 
danne danne ta soma yi har tayi locating inda file din yake, da farko tayi mamaki ganin babu password don yawanci irin wannan files din boyesu akeyi, tana kokarin dannawa daidai nan wayarta ta soma qara, cikin hanzari ta daga wayar tare dakaiwa kunnenta, ta soma magana, ‘’bring him in’’ tana kaiwa nan ta ajiye wayar, daga nan zaune cikin yan mintuna qalilan head maid ta shugo study dinta, tare da wani mutumi biye da ita, yana sanye da green uniform tare da farar hula.,kallon inda head ke tsaye hidaya tayi tare da daga mata hannu alamun ta wuce, tana futa hidaya ta mashi nuni da  kujerar dake facing table din da take zaune, cikin sauri kuwa yabi umarninta ya zauna tare da ajiye jakarshi a gefe ‘’good day madam’’
ko kallon inda yake batayi ba saima relaxing datayi akan kujera ta kare mashi kallo daga sama har kasa, ma’aikacin gidan mahaukata ne, shima kana ganinshi yanda kasan wani burkitacce, daman ta buqaci a samo mata wanda zata iya toshe bakinsa don ta samu abunda take buqata ba tare da wata matsala ba, yanxu ta zabi tayi komai da kanta tunda taji maganar  yanda doctors din datayi hiring don suyi mata aiki suke 2 timimg sunayima khaal aiki ba tareda saninta ba.
hannunta ta bude ta mashi alamun ya miqa mata abunda yake tafe dashi, ganin haka yasa ya bude jakar daya shugo da ita ya zaro wasu robobin magunguna guda uku harda wata kwalba ya ajiye aganbanta ‘’madam ga abubuwan da kika buaqata’’
yana gama ajiye mata su ya fara kokarin yi mata bayanin yanda zatayi amfani dasu, bata ma tsaya sauraron sa ba ta dakatar dashi tare da bude drawer table dinta ta d`ebo bundles din kudi riyals ta ajiye kan table din sannan ta tace ‘’yanda zanyi amfani dashi ba matsalarka bace,you’re dismiss’’
jiki na rawa ya miqe ya kwashi kudin da jakarsa ya juya ya nufi hanyar futo a tsorace, yana tunanin hadarin magungunan daya kawo mata yawanci mahaukata ake bawa kuma akwai particular dosage da ake basu kan tsari idan ya wuce hakan yana burkita kwakwalwa sosai amaimakon a samu sauqi sai komai ya tabarbare, koma dai menene shidai wannan ba matsalarshi bace tunda ya samu kudi sosai.?
yana futa hidaya ta dauka robobin ta juyasu, tare da ayyana abubuwa aranta, duban laptop din da batayi ba kenan ta miqe ta fuce daga study room din da robobin a hannunta.

sabeeha dake tsaye a bakin kofar shugowa part din hidayar daga ciki aka budo kofar, saurin yin baya tayi, gaba daya ta burkice don ta dauka hidaya ce zata futo sai taga akasin haka,take jikinta yayi laushi sosai, tunda aka dawo da jamid daga asibiti take son ganin shi saidai tsoro yasa ta kasa zuwa wajen ganin hidayar ta hana kowa ganinshi, yanxu hakan ma neman hanya take ta shige cikin part din ko da a boye ne.
Tana nan tsaye mutumin daya futo daga part din ya wuce ta gabanta har zata juya saiga fadwa ta hauro saman, saurin sauke kanta tayi kasa har fadwa ta karaso inda take a tsaye, kallon ta tayi daga sama zuwa kasa kafin ta kauda kai ta sanya hannunta kan handle din kofar, tana shigewa ciki sabeeha ta juya jiki a mace ta koma part din su.

fadwa na shiga part din bata tsaya ko’ina ba sai study room din hidaya don yawanci anan take zama musamman a daidai wannan lokacin,bangaren hidaya bata dade da futa daga study room din ba ta sake dawowa tunawa da drive din data bari jikin laptop, tana kokarin shiga daidai nan fadwa ta tunkari kofar itama a furgice kamar wata mara gaskia, kusan saura kiris su buge juna, dagowar da zatayi taga fadwa a tsaye tana zare idanu kamar wata mara gaskiya,bata kawo komai a ranta ba saidai ganin yanda ta tunkari kofar tana kokarin futa ne yasa ta zuba mata idanu sosai, ‘’me kike yi anan?’’
‘’uhm daman nazo nemanki ne,’’
maida idanunta tayi ga laptop dinta dake kan table din tayi kafin ta dawo da kallonta ga fadwa din tace ‘’kin taba laptop dinchan?’’
‘’ah ah, yanxu na shugo fa,’’ tabe baki hidaya tayi ta nufi wajen laptop din, ‘’are you sure baki taba ba?’’
jin haka yasa fadwa dakatawa tare da juyowa inda hidayar take tace ‘’akwai abunda bai kamata na gani cikin laptop din ne ba ukty?’’
banza da ita hidaya tayi kafin ta zauna kan kujerar tare da shutting system din bayan ta zare drive din tace ‘’karki sake shugomin nan without my consent,’’
tana kaiwa nan ta fuce ta barta tsaye, ran fadwa ya baci sosai haka ta fuce daga bangaren nasu ta sauka kasa.
tana shiga part dinsu ta tadda tareeq kwance yana barci, ganinshi kadai ma yasa ranta ya kara baci sosai, ganin yana barci yasa ta fito daga dakin ta shige dayan dakinta ta kullo kofar.
‘’tunda ta shugo dakin take faman sintirya tsakanin dakin tana cije lebe, hidaya is trying her patience,duk abubuwan da takeyi tana sane da ita kuma zargin da takeyi akanta ya tabbata, tunda ta fara boye mata wasu abubuwan.


***
Yau da sassafe ta futa daga gidan tun wajen karfe 8, sboda manyan bakin da zasuyi a taheel Kamfani, ko breakfast batayi ba, already barad an samo mashi driver da zai dunga kaishi school don haka ita kadai ta futa yau.

Zaune take a office, fuskan nan radau tasha jan baki, yanxu bata da suran damuwa, duk wani abu datasan zai kawo mata matsala yanxu is under her control.

gabanta mnyan partners din taheels din ne da suke investing cikin kampanin, yawanci za’ace sune tallafin tattalin arzikin taheel, don suna bada any amount wajen investment, bama a kasar suke ba, , a ynxu hiday tafi buqatar su sosai saboda duk wani harkar dazai kawo mata kudi yanxu bata sanya dashi kwakwata.
Maganganu daya shafi business suka gama bayan sunyi yarjejeniya sukayi sighing papers din kafin ta miqe.
“Thank you mr benjmin”
Ta karashe tana mika masu hannu “its my pleasure “
Baturen ya bata ansa,
kafin su fice daga office din nata, kallon papers din tayi tana murmushi kafin ta ajiyesu cikin locker safe dinta, nan idanunta ya sauka kan flash din nan, sai a lokacin ma ta tuna da falsh din don haka ta dauko shi tare da kunna laptop din dake gabanta ta saka flash.
file din dake wajen tayi clicking tana shiga taga wayam empty babu komai, cikin tashin hankali ta zaro idanunta tare da miqe wa tsaye, saurin cire file din ta yi tare da sake maidawa tayi clicking for the second time ay tuni ta buga table din da hannunta idanunta na juya ta soma magana ‘’whats going on?, wha…..wha..’’
‘’empty drive?,’’ gaba daya ta gama furgicewa da mamaki, shin daman empty flash ne wannan agent din khaal din ya bama jamid ko kuwa? ko jamid ne ya sauya flash din? haka ta dunga tambayar kanta babu wanda zai bata amsa, hannunta na karkarwa ta dauki wayarta ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma magana , ‘’na baka nan da 24hrs ka nemo min duk inda wannan agent din yake a raye, i want him alive’’ tana kaiwa nan ta kashe wayar tana nazari, tabbas wannan ne drive din da agent dinnnan ya bama jamid, yanxu shes caught up in between, shin wannan agent din karya yayi ne ko jamid ne ya sauya flash din tun kafin ya samu paralyse? tama rasa tunanin da zatayi gaba daya kanta ya gama kullewa, don tabbas flash dinne kuma da hannunta ta shiga cikin motarshi ta dauko bayan an kaishi asibiti, 
‘’jamid!!!!! ta furta tana mai kallon drive din,  

aikin da bata kaarshe ba kenan ta dawo gida hankali a tashe, koda ta karaso saman ta wuce part din su, lokacin nurse din dake kula da lafiyar jamid na tare dashi tana gyara mashi gadon sa, hidaya na shigowa dakin ta umarci ta futa daga part din, tana futa kuwa ta karaso inda jamid din ke kwance, yanda yake kallonta haka take kallonshi, 
‘’jamid!!’’ ta kira sunanshi, ‘’ina kakai file dinnan?, wheres the file’’
confusely yake kallonta don bai gane inda ta dosa ba, 
tana ganin haka tayi saurin bude jakarta ta zaro flash din tana mai kallonshi tace ‘’jamid youre trying my patients, ka fadamin inda ka kai file din cikin drive dinnan?,after all youre still tryig to protect him huh?, what did you do with the file ehhhh answer me’’ ta daka mashi tsawa.

idan ya gane inda ta dosa file din dake cikin drive din is missing but ya akayi haka?, ko dama chan agent dinnan empty drive ya bashi?, how is that possible?, bazai iya tantance hakan ba saboda shi kanshi baisan ko akwai file a ciki ba ko babu don mutallib na bashi file din ya fuce daga motarshi, shi kuma baiyi tunanin ganin abunda ke ciki ba kawai dai yayi deciding koma menene a ciki zai bama qalam abokinsa dake dss crime office, kuma hakan bai samu ba saboda a ranar matar qalam ta shiga labour wanda hakan yasa bai samu ya bashi ba wannan yasa ya nemi safe waje a cikin motarsa ya boye don baiyi tunanin wannnan kaddarar ciwon barin jikin zata samesa ba.

‘’this is your doing ko?, jamid the more kake kokarin ganin downfall dina the more nake jin urge din ganin karshen taj, ka fada min inda file dinnan yake?,’’

jamid yanda yake kallonta yana hango tsantsar fargaba a tattare da ita don wannan file din kadai zai iya kawo karsheta, kuma zai ruguza duk wani plans din, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama karantar komai, ba karamin dadi ne ya ziyarceshi ba daya lura wannan file din bai shiga hannunta ba, daman tashin hankalinsa dayaga file din a wajenta kuma yasan zata bunne gaskiyar alamari ne kuma allah kadai yasan abunda zatayi nan gaba don bazata taba bari asirinta ya tonu ba shi baima damu da inda file din yake ba, dadin shi daya dabai shiga hannunta ba, tambayar daya dunga ma kanshi kuwa itace ina file din yake kenan? yadai san wannan mutabblib din bazai bashi empty abu ba bayan bayanan daya mashi game da abubuwan datayi kuma da evidence din da khaal ya nemo akanta.

ganin yayi mata shuru yasa ta tunkaro bakin gadonsa tana facing fuskanshi tace ‘’youre forcing me to do the worst jamid, as this stage youre still willing to protect him,’’
bakinsa na karkarwa ya kalleta idanunshi yayi jaa sosai ya soma magana ‘’do…your..worst..ba..zan..taba..contri..but..ing wa..jen..za..linci ba,’’
saida ta sunkuyar da kanta sosai taji abunda ya fada kuma yana kallon cikin idanunta yana hango tsagoran fargaba da rudani a cikin idanunta, ko ba komai ya barta a haka yasan bazata taba samun sukuni ba siata samu file dinnan, saidai kuma tunawa da mutallib yasa ya soma fargaba don yasan saita nemeshi duk inda yake.

rai a bace tabar shi kwance ta fuce daga gidan ma gaba daya.

24hrs na cika gaba daya ta kasa samun natsuwa, babu bunciken dabatayi ba ta kasa samun wannan mutallib din, hankalinta ya kasa kwanciya musamman data san cewa akwai mutun daya da yake da abunda zai tarwatsa plans dinta kuma zai tona mata asiri.
babu irin threat din da batayi ma jamid ba amma yaqi fada mata komai.


8pm..
jamid na daga kwance kan gadon marasa lapiya anan bedroom dinsu bawan allah, babu abunda ya sauya a atttare dashi helplessly, yana kallon duk wani motsinta hartayi wanka ta shirya ta sauya kaya kafin ta tunkari bakin gadon nasa inda yake kwance, jamid na ganinta yayi rufe idanunshi, shi ayanxu babu abunda ya tsani gani irin fuskarta, daidai da inuwarta baya son kusanci da ita, yanajin motsinta harta karaso inda yake ta soma kwantar mashi da gadon nashi,don yanxu saidai a daga gadon sannan a kwantar tashi, saida ta daidaita mashi yanda zai kwanta din kafin ta soma magana ganin ya rufe idnunshi kuma tasan idanunshi biyu kuma yana sauraronta.
‘’abuh barad whats your take on drugs? kasan fentalyn, the most highly addictive and dangerous drug’’
yana jin haka yayi sauri bude idanunshi tsoro da fargaba sun gama durar mashi, ganin reaction dinshi yasa ta murmusawa tace ‘’ka kwantar da hankalinka this is not for you’’ ta kaarshe tana nuna mashi robar kwayoyin, yana jin haka tuni hannunsa ya soma karkarwar ya fara kokarin yunkurawa yana shure shure, babu abunda yake yunkurin yi sai kokarin kamo hannunta, tana ganin haka ta mike tare dayin baya robar na hannunta,’ bakinsa na karkarwa ya soma furta ’noo..noo’’
‘’save your energy jamid,don babu abunda zaisa bazan bashi maganin nan ba, inason naga wanda zaiyi protecting dinshi yanxu, ’’

tana kaiwa nan ta fuce daga dakin da robar maganin a hannunta, bata tsaya ko’ina sai bangaren su sabeeha, taj din kadai ta tarar a dakin wannan ya bata damar aywatar da abunda ya kawota, karasowa tayi inda yake fuskannan kwata kwata babu wani digon murmushi ko sakin fuska, hannunta na rike da robar maganin ta zauna inda yake.
murmushi yayi mata yanda ya saba yace ‘’hello first love’’

bata ma amsashi ba ta bude robar din hannunta ta deba maganin dake ciki har guda hudu ta miqa mashi, ‘’take your medications’’
karban maganin yayi daga hannunta ya kai bakinsa, ganin haka yasa ta miqa mashi bottle din ruwa yasha dashi,saida ta tabbatar ya hadiye kafin tace ‘’good boy’’ ta miqe tsaye tare da kakkabewa ta fuce daga dakin tana jinshi yana ce mata goodnight tayi banza dashi anan sitting room ta tadda sabeeha wadda ta yanko mashi fruit tana kokarin karasawa bedroom din, tana ganin hidaya kuwa ta dan rusina ta gaisheta, ko ta kanta hidaya batabi ba ta futa daga dakin.


kofar dakinsu ta bude inda ta shugo yanda tabar jamid  haka ta dawo ta taddashi sai faman shure shure yake helplessly, duk wannan kokarin da yake don ya hanata aywatar da kudirinta ne saidai ya makaro, yana ganin shugowarta ya fara kokarin fadowa daga kan gadon, tana kallonshi ta kauda kai ta karasa wajen gadon su ta ajiye robar maganin tayi kwaciyarta tare da kashe bedside lamp dinsu, tana jinshi yana fidda nunfashi helplessly taqi koda yunkurawa ne, saida sautin nunfashinsa ya isheta ta miqe zaune tare da

1 / 107