Author : Queenmerh Category : Complete Novels
wanda yasa ya mashi bincike akanta, gaban wajen yayi parking yana kallon gate din mataccen prison din,wayarshi ya daga ya kira mai yin binciken ya shaida mashi ya iso, sai gashi kuwa ya futo daga cikin wannan prison din ya shiga dashi, tunda ya shiga yake yatsinw fuskanshi, wari, bola, datti, ga ginin ya banbaro, kai komai ma akwai a wajen, prisoners din ma kamar mahaukata, gaba daya wajen dai sa a hankali.
Wani dan office mai kyan gani suka shiga inda ogan dake kula da wajen yasa aka kira wanda suke nema.
Wani dan sanda ne ya taho dashi wanda suke nema din gaba dayanshi ka ganshi kamar kwarangwal, ya bushe ya jeme.
Idanunshi daya ma kamar ya lalace don har wani fidda ruwan wari yakeyi.
Kallonshi investigotor din yayi bayan a zaunar dashi sannan yace “ya sunanka”
Ya fada masu, “sunana iliya”
Hoton sabeeha suka nuna mashi ya kalla ya sake kalla sukace “ka santa”
Yayi dariyar yan wii yace “tsakani da allah oga ina zanga wannan a rayiwar nan?”
Tsohon hotonta investigator din ya fidda sannan yace “wannan fa?”
Tuni kawu ya gano wa suke nufi ya jarbi hoton yace “kai wannan yar yayata ce ay, fati”
“Munsan dalilin kawoka da akayi nan saboda satar dakayi kuma baka biya kudin belli ba aka kawo ka nan ko?”
Girgiza kai yayi investigator din ya cigaba, “munyi maka alkawarin fitar dakai dagana indai zaka bamu hadin kai”
Cikin sauri ya girgiza kai yace toh yallabai.
“Mecece alakarka da ita da mahaifiyarta? Sannan ina ne aka haifeta? Waye asalin mahaifinta.
Shuru ya danyi kafin yace “mahaifiyar babarta da babata uwarsu daya ubansu daya, ni kuma kawunta ne, kuma a gaskia lokacin da inna ta dauko ni ta kawo ni nan habuja tun tana karama ne, nadai san babarta tayi aure anan habuja kuma anan aka haifeta, mahaifinta kuma dan taxi ne,shima garinmu daya dashi,”
“Ya alakar ta da mahaifiyarta take”
Rarraba idanu ya somayi yana taoron yin magana amma ganin yan sandan nan akanshi yasa shi cewa “ban gane ba yallabai?”
“Kasan me nake nufi karka bata min lokaci mana, ya alakarsu take?
“A gaskia nidai na taso naga yanda take tsangwamarta, kuma bata barinta tana futa ko’ina, dan ko makaranta dakyar ta bari ta karasa primary,”
“A ganinka me zaisa tayi haka?ko ba yarta bace?”
Shuru kawu yayi yana nazarin yanda yarinyar ke shan wahala wajen hadiza, a gaskia kowa yaga haka zai rantse ba yarta bace.
“ nidai ban taba jin wannan zancen ba, nadai san gaskia yanda ta taso ba haka kowa ya taso ba, don gaskia bata da gata”
Dan nunfasawa investigator yayi, duk wani bayanai da suke san sani sun kasa gano komai, daga kan inda aka haifeta ma.
“Kasan inda aka haifeta?”
“Eh anan habuja ne”
“Zaka iya fada mana wani asibiti ne?”
“Gaskia ban sani ba, kamar yanda na fada maku, tana da shekara biyar inna ta kawoni habuja, don lokacin danazo ma sun tashi daga tsohuwar anguwarsu inda aka haifeta,”
“Zaka iya fada mana inane taohuwar anguwar?”
“Eyy a gwagwalada ne, cikin anguwar rodi”
Da dan wannan bayanan da suka samu daga bakin kawu investigator din ya cigaba da bincike, bayan yayi ma taj bayanin komai sannan sukayi sallama.
Washe gari ta kama saturday, tunda safiyar allah hadiza ta dokama jamila kira,ta tambayeta ya jiki jamila tace da sauqi yauma zataje wajen bokan.
Da haka sukayi sallama hadiza dadi kamar ya karta.
Bangaren su bahijja tun ranar sataje wajen anne sukayi maganar auren hadi da takeso a hada maya da taj bata sake dago da maganar ba amma fa tana kan bakarta.
Hadiza na zaune tana expecting call din jamila maya ta shugo part din, dakin hadiza ta nufa kai tsaye, hadiza kamar ta rungumwta don dadi.
“Ya ake ciki?”
Maya ta tambayeta?
“Karki damu hajiya karama bani na maki alkawari ba yau yau dinann ba sai gobe ba Insha Allah zata bar gidan nan”
“Ay kuwa dai gwara ki san yanda zakiyi inba haka ba wallahi daga ke har ita zan sa a koreki”
“Toh shikann, bayan wannan ma akwai wani abu da kikeso ne? Koma menene ki fada min”
“Me zaki iya min kona fada maki?”
“Zan iya maki komai, kawai ki fadi koma menene”
“Kina tsibbu ne????”
Wata dariya hadiza tayi tace “ah ah ba tsibbu nake ba, amma inada makaman da zan iya yin komai dasu, shiyasa nace ki fada min duk abunda kikeso kamar yankan wuka zakiga komai”
Gyara tsayuwa maya tayi tana nazari kafin tace “wani nakeso amma na kasa samunshi…”
Hadiza ta karashe mata “kinason ya dawo tafin hannunki?”
“Eh…”
“Zan iya sanin waye wannan mai sa’ar?”
“Uncle taj, wannan balaraben”
Tafawa hadiza tayi tana murmuahi tace “kamar kin sameshi ne hajiya karama, indai ina nunfashi sainasa ya biki yana lasar kafafunki”
Ay maya najin haka ta samu waje ta zauna, abunda hadiza keso kenan, “da gaske kike?”
“Wallahi zan iya maki rantsuwa,”
“Toh amma ya avun yake? Me zakiyi?”
“Akwai wani malamin bugu, kina fada mashi damuwarki shikenan, ki bari zakiga example akan wannan yarinyar in takai safiya ba sunana hadiza ba”
Wani irin murmushi maya tayi mai kayatarwa tace “ki fada min ko nawa kikeso, indai zan samu abunda nakeso zan baki kinji, Gaskia kinfi mun mommy, na fada mata inason shi kuma inason na aureshi amma taki yin komai akai,karshe ma cemin tayi wai na hakura dashi, ni kuma wallahi saina mallakeshi, danni aka haifesa wallahi”
“Kingani ko, da tuntuni kinzo kin sameni baki samu wacchan mummyn taki ba ay da tuni an wuce wajen, ke har kulle masu baki duka zanyi duk wanda ya nuna bayason hadin nan,kuma haka zai haukace maki”
“Allah da gaske?, kai nagode” maya ta fada tana rungume hadiza, hadiza baki har wuya, murna kamar ta kasheta.
“Ay babu abunda bazan maki ba hajiya karama, yanda nake son farin cikin kamar nunfashi na”
Maya tayi murmushi tace “daga yau komai ya tsaya tsakaninmu,”
“Toh shiknan,amma ki dawo nan bangaren mana tunda kin saba kawai”
“Mummy bazata yarda ba”
“Kice mata kinfi son nan kawai, ko kinfiso ki zauna achan din? Nan baifi ba mu dunga maganar mu cikin sirri”
“Aiko haka za ayi, bari zanje na fadi mata, nagode hadiza na yarda dake sosai”
Maya na futa hadiza ta soma kulle kullenta, yanxu da farko dai ta kauda sabeeha na biyu kuma faduwa tazo daidai da zama, jini jini ne, ashe ashe mayan ma tana son shi, chap ay yanxu ta samu babbar dama kuwa, kuma dole ta koma bin jigajigan malamanta akan wannan alamari, yanda ta samu yardar maya kuma da alamu zata juyata san ranta idan har ta bata avunda take so ay shikenan, haka nan zata zame mata uwarda bata samu ta zama ba shekara da shekaru.
Wani irin dadi takeji aranta ba kadan ba.
Misalin wajen jarfe shifmda saiga kiran jamila, hadiza na duka tace “akwai matsala hadiza yanxu haka ina hanyar dawowa daga wannan tsiburin kauyen kinji kukan tsintaaye ko?”
Hadiza tace “naji, meysa zaki dawo an samu dacewa ne?”
“Inafa dacewa, wai ya dade da mutuwa wannan tsohon”
Hadiza ta dora hannu a ka “na shiga uku, jamila ya za ayi”
“Kwantar da hankalinki akwai wani chan dana sani, ammafa yafi dayan gaskia, don shi wannan tantirin mugu ne na karshe”
“Toh zakije gobe dan allah?”
“Eh in allah ya kaimu..”
Ditto jamila ta kashe wayar ta dauka remote din tv dinsu ta rage karar tashar data saka, tayi dariya tace “Allah ya kaimu goben hadiza,”
Baiwar allah uta wadda ake wannan shirin tsuburin don a illatata, kwana biyu addua kawai take, kwana take tana sallolin dare, allah baya barci.
The next day ta kama sunday, kusan gaba daya kowa ya hallara dining, nanna, taj ne, harda laila, sabeeha ce ke serving dinsu, tana gamawa nanna tace ta zauna, da har zata qi zama saita zauna kuma tana fuskantarshi don kujerarta na facing tashi.
Laila tayi saurin yima maya message, sai gata kuwa cikin pj, tashi ta kenan daga barci tana gama brush ta fito taji karar notification tama dauka salim ne saitaga laila.
Kannan babu dan kwali anyi packing gashin a tsakiya.
Tunda ta karaso take aikama sabeeha harara, cike da mamaki badan laila tace mata nanna ce tace ta zauna ba ayda ta kora mata, kuma ga taj a wajen bazata iya ba.
“Maya karaso mana zoki zauna” nanna tayi magana tana kallon mayar data shugo kamar a furgice.
“Good morning nanna, good morning uncle taj”
“Morning” nanna ta amsa ta.
Maya taja kujerar kusa da taj din ta zauna.
Itadai sabeeha tunda ta zuba abunci kasa ci tayi, gaba daya she’s so uncomfortable.
“Ci mana fatima”
Nanna tayi magana sabeeha ta danyi yaqe kawai, ta cigaba da chakalar abunci, zungurin kafarta da akayi yasa ta dago tana kallonshi, sai kuma taji yatsanshi na yawo a fatar kafarta, cikin furgice ta kalleshi ya basar kamar baisan tanayi ba, yanda yake tafiyar tsutsar yasa ta soma jin futsari, gashi babu damar tashi, maya na ankare da sabeehar da yanda take kallonshi gashi sai mutsu mutsu take, gashi suna facing juna, tana cikin kallonsu batasan cewa wayarta data dora kan cinyata ba ta sulale ta fadi kasa, wannan yaza ta dan duqa, karaf idanunta ya suaka kan kafafun taj dake yawo ga na sabeeha kamarma yakai wajen cinyanta, wani irin kundumemwn ashariya maya ta antayo tare da mikewa har tana buge kanta, sabeeha tayi saurin tashi tayi baya gabanta na faduwa, maya na kallonta tana kallon maya.
Nanna tace “maya what sort of an insults is this? This is bad table manners dont do that again”
“Nanna wannan yar iskar yarinyar kafarta na gani kan ta uncle taj, she’s trying to flirt with him, daman nace maku yar iska ce, wallahi har maza tana bi”
Nanna ta dubi mayar sannan ta dubi sabeehar tace “maya…wannan wani irin strong allegations ne? Eh?? Kinada hankali kuwa”
Gaba daya kamar mahaukaciya haka maya ta koma, shidai bai dago ba ya cigaba da cin abuncinsa sabeeha ko jikin na bari duk ta furgita.
Maya tayo kanta zata watsa mata mari yanda ta saba ya daka mata tsawa gaba daya sauda wajen ya girgiza, daga kan nanna har bahijja data shugo parlorn gaba daya mamaki ya gama cikasu, ranshi a mugun bace ya dubi maya yace “don’t you dare lay your hands on her”
Kawai sai maya ta fashe da kuka, “na rantse da allah saikin bar gidan nan, daman ba tun yanxu ba take min baqin ciki, ita ba kowan kowa ba, yar aiki ce fa kawai, duk abunda aka mana sai an mata shiyasa take baqin ciki dani, yanxu ma shi da nakeso so take ta kwace shi, ba tun yanxu ba take shiga part dinshi, tana kokarin jan hankalinsa”
Bahijja ta karaso dining din rai a bace tace “whats going on here??”
Nanna dai shuru kawai tayi ta kasa cewa komai, shi da baijin hausa baisan zanjen da take ba,
“Bahijja jata kuje gida please,”
Janta bahijja tayi idanunta sunyi jaa sosai har suka fita kallon sabeeha take da tsana.
Nanna ta dubi sabeeha daketa hawaye tace “jeki abunki”
Sabeeha ta juya ta wuce bedroom shi kuma taj nanna tace ya sameta a daki.
Yana zuwa ta tambayeshi abunda maya tayi magana akai, sai a lokacin yasan kanun zancen, lallai yarinyar nan bata da hankali, ay ba sabeeha kawai ta jefa da adultery allegations ba hardashi, ranshi yayi mugun mugun baci.
Nanna tace “she will stop whatever shes doing a part dinka from now on to avoid any problems”
Take ya kalli nanna yace “no nanna, she will continue her job, i will not tolerate such nonsense behavior from this girl,”
Nanna dai tayi shuru batace komai ba, daga maganganun da naya tayi ta fuskanci kamar son taj takeyi.
Tunda suka shugo part dinsu ta bi ta tayarma da bahijja hankali, ta ind atake futa ba tanan take shiga ba, gaba daya sai bahijjar taji ta tsani sabeehar wallahi, kuma ta yarda da maganganun mayar tunda tagani da idanunta itama, yanda yarinyar ke yawan zuwa part dinshi yayi yawa kuma wallahi bazata taba bari yar hadiza ta shugo gidan nan ba su tsaya a matsayinsu da tanada yanda zatayi ay da ta koresu daga uwar har yar gaba daya.
Har yau bata iya manta abunda hadiza ta mata ba, har yau kuma dashi take ganinta, shiyasa kwata kwata hadizar bata taba yarda su hada ido.
Chan bangaren jamila haka ta shirga hadiza da zancen ta futo fa, kuka tana isowa wajen malamin zata fada mata.
Drop hadiza ta hau direct mai ac ma kuwa daga dutsen habuja zuwa nan maitama, taci kwalliya abunta fess fess, hardasu jambaki, sannan ta aza chewing gum a bakinta, ta futo asalin jamila bala’i yanda ake kiranta a da, sai wani qas qas takeyi, suna isowa bakin gate ta danyi yan daba runta na jikakkun ya bariki ta samu ta shige, drop bai tsaya da ita ba sai daidai gidan, ta biyashi kudinshi sannan ta sauko, tana saukowa ta dubi estate din gaba daya kafin ta maida dubanta ga apartments din santura’ki’s…..”gani nan tafe hadiza, nazo maki da gagarumar tsaraba….
Toh fa, me jamila ke shirin yi? Lokaci yayi ne????? Ku biyoni don jin yanda zata kaya….
MATAR TAJ (destined with you)
Written by
Queenmarh
Book2
PAID
Chapter 106
Kai kana ganin yanda take tauna chewing gum dinna tana juya ido kasan bata zo da alkairi ba kwata kwata, nan bakin gate dinsu da shima ba a shiga sai an nemi izini daga ciki ta tsaya, ta gaisa da securities din wajen sannan ta shiada masu wadda take nema.
Saida suka dakatar da ita don sai an kira daga ciki kafin ta shiga.
Rabi na daga zaune tana ninke kayayyakinta data wanke wayarta ta soma ringing voo voo, tana ganin daga waje ne tayi saurin dauka don normally ita ake kira idan za ayi baqi ko idan mutane zasu shugo,
da sallama ta daga security din ya soma magana, “theres a visitor who’s here for rabi”
“Sorry who???” Rabi ta tambayeshi
Kallon jamila yayi yace
“Madam your name”
“Jamila..” jamila ta bashi amsa
Ya maida wayar kunenshi yace “jamila..”
ganin irin kallon da yake mata don wayar har zuwa lokacin tana kunnensa yasa tayi saurin cewa
“Dan allah ko zaka bani ita muyi magana.”
Har zai katse wayar don rabi ta shiada masu babu baquwar da suke expecting ya bawa jamilar wayar.
“Hello!! Hello kina jina, dan Allah ki futo yanxu cikin gaggawa, abu ne mai muhimmaci zan fada maki”
“Wacece wai wannan din?” Rabi tayi magana, “kiyi gaba wata kila kinyi mistake banan gidan bane.” Rabi ta sake magana
“Ki dan dakata kiji, ni kawar hadiza ce, wadda nazo kwanaki,” jamila ta tari nunfashinta cikin gaggawa.
“Toh ay saikiyi bayani yanda ya kamata, bata fada min cewa akwai wadda zata zo ba” rabi ta bata amsa
“Ay ba wajenta nazo ba wajenki nazo, ki futo kona minti biyu ne dan Allah abu ne mai mahimmanci nake tafe dashi”
dan jinkirtawa rabi tayi tana nazarin mezaisa kawar rhadiza ta kirata kuma wai tazo ne saboda ita? kodai wani abun hadiza tayi? ko fada sukayi da kawar tata don daga yanda ranar datazo ta ganta ta gane suna da kusanci sosai, don da farko ma ta dauka yar uwarta ce.
“Toh shiknan” rabi ta bata amsa sannan takashe wayar.
Ninke kayayyakin da rabi keyi ta dakata, tare da daukan lullubinta ta futo da wayarta a hannu.
Kai tsaye gate ta nufa dake akwai dan nisa daga cikin gida zuwa gate din gashi ana kwlala rana saboda ko sha biyu bata karasa ba rana ta futo sosai.
Jamila dai na daga tsaye allah allah akwai take rabi ta futo, har zuwa lokacin taunar chewing gum dinta take hankali kwance.
Rabi na futowa ta gyara tsayuwarta tana duban ta,daman daga dan nesa da security din ta tsaya wajen post din su tana ganin futowar rabi ta daga mata hannu,rabi ta karaso inda take.
“Sannu rabi..”
Rabi ta kalleta kafin tace “yauwa dai sannu,ina fata dai lafiya”
“Lafiyar ce ta kawo haka, da farko dai nasan zakiyi mamakin dayasa nace ki futo ko? Kuma ban nemi shiga wajen hadiza ba don bata san da zuwan nan nawa bama, taimako nake nema a wajenki”
“Toh…dame zan iya taimaka maki kenan?” Rabi ta tambayeta har zuwa lokacin kallonta kawai take
Gyara tsayuwa jamila tayi tana fuskantar rabi sannan tace ''ina tafe da wani babban alamari wanda nake da damar fayyace komai ayanxu kafin lokaci ya kure''
dan nunfasawa jamila tayi kafin ta cigaba ''so nake ki kaini wajen hajiya babba, mgana ce babba''
''toh fa, wace hajiyar kenan?'' rabi tayi magana tana mata wani kallo kallo.
''hajiya anne nake nufi''
''haka kawai saina daukeki na kaiki wajen hajiya? a wani dalilin ? saboda me kenan?''
chewing gum din dake bakinta ta fidda don zuwan rabi baisa ta cireba sai yanxu.
''banida lokacin yi maki dogon bayani amma inaso ki sani cewa wannan maganar ta danganci wannan ahalin''
''kinga bansanki ba, hadiza ce kawai ta kawoki gidan nan,a matsayin kawarta kuma a ganina idan alfarma kike nema ita zaki nema bani ba ''
jamila fa a qage take, so take kawai ta ganta gaban anne, gashi ita wannan datake tunanin zata samu hadin kai daga wajenta ta taimaketa tana neman fada mata maganar banza.
''kinga, bawai dan son raina bane nazo nan, abu daya nake nema wajenki shine ki taimaka ki kaini wajen hajiya anne, dalili daya ne yasa nazo wajen nan badan haka babu abunda yasha kaina''
''kinga babu yanda za ayi fa na kaiki wajen hajiya anne idan baki bani kwakwaran dalili ba, me kike nema daga wajenta?, kibani dalili saina ga abunda zai yiwu.''
cije labba jamila tayi wata dabara tazo mata kafin tace……..
Anan cikin gida apartment din su bahijja, da kyar ta samu ta lallaba maya tayi shuru, don kuka take wiwi, kamar zata zauce, ta inda take futa ba tanan take shiga ba, gaba daya ta tayar ma da bahijja hankali, sai a lokacin ta kara tabbatar da maya na son taj sosai.
“mummy wallahi inason shi, shi kadai nakeso kuma na rantse da allah bazan bari ya so yarinyar nan ba wallahil azeem, ni kadai zaiso ni kadai kuma zai aura…”
Kamo hannunta bahijja tayi da lallama tana mai share hawayen fuskanta tace “baby dan allah ki daina kuka ki natsu ki saurareni,”
Kallonta maya tayi idanunta sunyi jajawur tace “i trust you mummy kinmin alkawari, ni wallahi aure nakeso, idan baku auramin shi ba zan….”
Gaba daya yanda take magana she lost her manners, babu wani zancen kunya, idanunta ya rufe kawai.
Hankali tashe bahijja ta toshe mata bakinta don a tunaninta zata koma gidan jiya ne, don tayi mata alkawarin bazata sake yin abubuwan data kamata dasu ba.
“Ya isa…ni na maki alkawari kuma zan cikashi Insha Allah, zan fada ma nanna, nasan bazataqi wannan abun ba, ki daina kuka