Advertisements
Chapter 52 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   52 / 107

153K to 156K   out of 320.4K words

abunci.
“Hadiza meya kaiki sama inace aikin ki a kasa kawai yake.”
Rai a bace hadiza tace “banida ikon yin aikin daya wuce na kasa ne? Ke kinsan matsayina kuwa a gidan nan?”
“Menene matsayin naki? Inace aiki kikazo yi ana biyanki? Kinada wani matsayin ne bayan wannan bamu sani ba? Ki fada min dalilinki na zuwa sama inva haka ba na sanarwa da hajiya, babu amsu zuwa saman sai wanda aka yarje masu kuma bana jin kina cikin waenda akace su dunga hidima a sama”
Hadizq tajji zafin maganar rabi amma haka ta hadiye ta danne tace “ba komai ne ya kaini dama ba, jikar hajiya ce ta buqaci a kawo mata juice da parpesun kaji shine na hau saman”
“Ba aikinki bane idan tana buqatar wani abu zata nema wajen masu girki ko ta kirani”


“Ke kuma asuwa?? “
Suka jiyo muryar maya daga bakin kitchen din, juyowa rabi tayi ta kalleta, tana daure da towel a kirjinta ko me tazo dauka a kitchen din allah kadai ya sani,
“Daga yau duk abunda ya shafeni ita ce zatayi min, karki sake questionining dinta, banason iyayin banza da wofi, kema ba yar aikin bace ba har kinada ikon fadin yanda za ayi da abunda baza ayi ba”
Sunkuyar dakai rabi tayi, gaba dayansu zasu haifi uku ta wallahi amma yanda take magana kwata kwata babu respect a ciki.
“Mteww…ke yama sunanki?”
Ta nuna hadiza da hannu, binta da ido hadiza tayi, sai kawai wani murmushi ya kufce mata ta kasa magana saida mayan ta kara cewa “baki..”
Cikin sauri hadiza ta katse ta “hadiza..sunana hadiza”
“Inason smoothie yanxu kafin ki gama pepper soup din”
“Tohm an gama yanxun nan kuwa za ayi maki sai kuma me kikeso? Ki fada kin ayi maki yanxun nan”
Dan tabe baki maya tayi tana jin wani irin dadi aranta amma ta basar tace “ya isa”
Ta futa rabi ta girgiza kai aranta tace “futsararriyar yarinya”
Hadiza kuwa ta bi rabi da kallo tayi kwafa sannan ta fara kokarin yi mata smoothie data buqata.

Ahankali akayi knocking kofar kafin a shugo da sallama, nanne ce zaune akan gado cikin irin maroocan gowns dinnan mai hula, tana ganin anne tayi saurin sauke kafafunta daga kan gado ta aje takardun dake gabanta da glass din dake hannunta.
“Wa alaikum salam! Anne!! Lafiya dai dakin bari nazo ay keda kike fama da kafa” nanna tayi magana tana kallon yayar tata.
Takowa anne tayi ta zauna gefen gado inda nanna ke zaune tace “nazo dubaki ne, ya zazzabin?”
“Alhamdulillah anne doctor yazo dazu ay dan zazzabine fa, alhamdulillah ya sauka ma, ina wuni ya fama da iyali”
“Toh alhamdulillahi,”
Shuru ne ya dan biyo baya kafin anne tace “hajara!”
Nanna najin yanda ta kira sunanta tasan akwai magana.
“Na’am yaya”
“Nayi magana da doctor dazu, ba zazzabi kadai ke damunki ba harda hawan jini kuma nasan damuwa ce tasa maki shi, Hajara ina ganin lokaci yayi daya kamata ki waiwayo rayuwarki ta baya….”
Murmushi nanna tayi ta kalli anne tace “wallahi babu abunda ke damuna babu wata damuwa anne, kawai stress din aiki ne ba wani abu ba, ina gab da retire nima na huta abarma yara suyi”
“Hajara kinsan abunda nake nufi, bazanyi forcing dinki ba tunda kin nuna bakyason ayi maganar, bazan iya sanin abunda kike ji aranki ba amma inaso ki sani ni yar uwarki ce hajara bakida kamarni, nice uwa a gareki kuma nice uba, bana fatan rasaki hajara don ayanxu ne nafi kowa buqatarki, babu wanda yasan gobe da abunda ke cikinta, kiyi hkuri hajara, bazan fasa baki hkurin nan ba kinji, ki aje komai a gefe ki nemi…”
Hawaye ne suka fara neman ambaliya akan fuskarta tace “Anne please..dan allah dan allah badan halina ba mubar zancen nan,”
Shuru anne tayi sannan ta kama hannunta tace “shikenan hajara na bari, allah ya rufa asiri allah ya sawaqe, tunda kince ba damuwa bane, amma kiyi kokari kina gujema stress din”
“Insha Allah.. ya kafan ki?”
“Kufa kuke wani damuwa da kafa, wallahi garau nakejinta yanxu, abun kunya ni ban samu hawan jini ba da shekaruna gashi ke saboda tunani zaki jefa kanki a halaka”
Girgiza kai kawai nanna tayi don yayar tata tasanta ciki dabai, duk falewar da zatayi bazata taba yarda ba don ta san duk wani condition da take ciki.
“Toh anne za a rage tunanin,”
Mumrushi tayi mata sannan sukayi sallama anne ta fita.
Wata nayyayyiyar ajiyar zuciya nanna ta sauke,idanunta sunyi jaa sosai take taji kirjinta na mata wani irin nauyi, tayi hanzarin daukan pills dinta ta sha sannan ta kwanta.
Daki anne ta koma ana mata tausa hamad ya shugo suka gaisa, wuraren past 7 don anan idar da sallah ya shugo, hira suka danyi jefi jefi ya danci tuwon da aka kawo ma anne sannan ya mata sallama kan zai dawo anjima.
Yana sauka kasan yaga yan aikin gidan nata faman shirya dinner a dining duk bai buqata saiyaje ya diba.
Sai a lokacin sabeeha ta fado mashi yasan by this time an daukota, amma rashin ganinta da baiyi ba dazu sai yaji babu dadi gaba daya, gashi bazai iya sqwa a kirata ba, toh akirata yace mata mene? Saboda mene? A wani dalili kenan? Saurin watsar da zancen yayi ya wuce gida.
Yana parking a part dinsu ya shiga daga ciki.
Kai masha allah, gaskia anty fadila badai gayu ba, itama gidanta mansion ne mai zaman kanshi baikai nasu anne ba don shine family house dinsu amma shima badai girma ba gari guda.
Ko’ina yasha adon gold and off white, parlor ga wani katin frame na hoton su su hudu, laila hamad then babansu sai mamansu.
Daidai zai shugo yaci karo da laila data debo abunci zata wuce sama, hartasa yar aikinsu ta kawo mata tanajin sallamarshi ta karbe karyayi mata fada, irin waennan kananun abubuwan kamar irinsu gyaran gadonta da gyaran wardrops dinta ita keyi, ba’ayarda yar aiki tayi ba saidai wanke toilets da shara, saboda kar shagwabewar tayi yawa, sometimes ma itake girki a gidan, dakin mamansu kuwa itake gyarashi tass.
Gaskia an basu tarbiyya kam mai kyau, babu raina na gaba musamman na kasa dasu.
“Hello ya hamad!”
“The next time kika kara cemin hello saina mareki, baki iya gaisuwa bane”
“Sorry ina wuni how was your day”
“Alhamdulillah ya amsa ta” ta turo baki tare na bin hanyar stairs ya dakatar da ita.
“Kinje ta koya maki?” Ya jefa mata tambaya daman yanason yaji ko yaushe sabeehan ta dawo.
Damn gabanta ya bada, tsakani da allah dazun nan ciwon mara ya riketa sosai tunda ta kwanta take barci bata tashi ba sai yanxu shaf ta mance da batun driver daya kamata ta fada ma anne.
Ganin yanda tayi tsuru tsuru yasan bata da gaskia, “are you dumb?”
“Innalillahi wallahil azeem yaya ciwon mara nake dazu sai yanxu na iya tashi”
“Is that the question that i asked you?”
Ganin ta sunkuyar dakai yasa shi zaro ido don sai yanxu ya fuskanci inda ta dosa, “what!!!!!! Bakida hankali???? “
“Yaya wallahi mantawa nayi”
Ko sauraron baiba don kamar ya kwada mata mari haka ykeji ya fuce daga gidan a fusace kamar zai tashi, yayi hanzarin shiga motarshi ya juya akalar motar.
Gudu yake sosai gabanshi na faduwa, yanajin kamar yayima laila dan banzan duka, ya za’aui ta manta and ya bata strict instructions akan ta fadama anne asa cikin drivers available one yaje ya daukota, gaba daya saiya fara jin wani irin rashin dadi da tausayi sabeehar yanxu haka shes stranded batasan ya zatayi ba innalillahi wa inna ilaihi rajiun.
Yana isowa school din ya wuce direct wajen department dinsu hankali a tashe, duban duniya yayi mata bai ganta ba, gashi duk securities daya tambaya sai suce basu ganta ba don ana yi shifting na rana sun tafi.
Haka nan ya zagaye school dinnan gaba daya da securities ana nemanta, har akayi sallar isha’i, cikin ikon allah wani tunani yazo masa ya nufi masallacin mata, bai shiga ba yasa daya daga cikin securities mata suka shiga ko za a ganta.
Tana shiga saigata kuw sun fito tare, tana daga kwance chan sakon masallaci ta jigata sosai ga gajiya ga yunwa, sallah kawai takeyi ta koma kwance.
Tana ganin hamad ta sunkuyar da kanta feeling so sad, wallahi yarinyar nan ba karamin kashe mashi jiki take ba haka kawai yake jin tausayinta bayason ganin ta cikin kunci ko kdan, yana hango tsananin damuwa da rashin farin ciki cikin idanunta, kamar someone that is lonely and longing for something.
“Dauko littafanki”
Komawa tayi jiki a mace ta dauko ta fito suka wuce taba biye dashi a baya har suka iso mota ya bude mata seat din baya ta shiga ta zauna ya rufe
Kunna motar yayi ya saka ac kadan sannan yayi reversing ya futa daga school din.
Shi shuru ita shuru aka rasa wanda zaiyi magana.
Shi wani irin rashin dadi yakeji, how can he be so careless, dayayi tunanin kiranta yayi confirming kota dawo da duk haka bata kasance ba.
“Kayi hakuri ya hamad, ka dawo saboda ni, wallahi ba laifina bane, bansan kazo da wuri ba dazun da bazan bata maka lokaci ba,”ta fada cikin sanyi, zuciyar sa kam ta karaya dajin furucinta sannan ga abunda ya biyo baya da bai fuskanta ba.
“Why are you sorry? Daman ba extra lectures kika tsaya yi ba?”
Nanata abun tayi a ranta batason cewa komai yanxu data fuskanci kamar akwai dan misunderstanding.
Ganin taqi cewa komai yasashi cewa
“Now tell me meysa kika bata min lokacin”
“Daman class rep dinmu ne yace min lecturer dinmu na nemana shine naje, bayan naje kuma yace min ba nemana yake ba saidai ko wani lecturer ne bashi ba,“
“And sai kuma akayi yaya? Ya nemi karin bayani.
“Shine na sauko kasan don banga rep dinmu ba kamar ya tafi, anan ne naji wajen wani security cewa kazo kun jirani harkun tafi, kayi hkuri hakan bazata kara faruwa ba”
Shru yayi bayan ya gama sauraronta tass, a cikin maganganun nata ya fuskanci abubuwa biyu, na daya babu wani extra class datace ma laila da maya zasuyi, secondly kuma batasan cewa shima kanshi da wannan wrong info din yabi ba.
“Bakiyi laifi ba, but next time ki dunga kirana idan abu ya faru dake, kamar yanxu this is very wrong for a lady ki zauna, and im sorry bansan cewa driver bai biyo sahunki ba yazo daukanki i should have called you naji ko an maidoki”
“Insha allah”
Suna karasowa gida yayi parking ta wuce bayan sunyi sallama sannan ya wuce part dinsu.
Yana parking ya wuce ciki dirwct zuwa dakin laila yana shiga yayi knocking tana zaune tayi zuru avun tausayi don tasan yau zai sauke mata, kuma harga allah bata kyauta how can she forget this.
Yana shugow ata moqe tsaye kamar zatayi kuka “yaya don girman allah kayi hkuri wallahil azeem banqi fada ba da gangan”
Tass ya kwashe ta da mari, “meysa kikamin karyan extra class da kikace zasuyi?”
“Answer me” ya daka mata tsawa ganin tayi shuru, ta fara daburdabur, “wallahi ban maka karya ba, meysa zan maka karya yaya, tare mukayi statistics class da ita kuma a gabana lecturer yace zaiyi extra class”
“Ita da bakinki tace maki zata tsaya yi?”
“Ah ah,”
“Then how did you conclude zatayi?”
“To ay naji maya tace zatayi extra class ne sainayi tunanin class din zatayi”
Saida ta fadi hakan ya gane inda gaba daya akayi misleading dinsu, wannan kafurar yarinyar futsararriyar ce, kuma saiya koya mata hankali.
“The next time kika kara bani wrong information saina tattakaki”
Hamad nada sauqin kai sosai amma in aka taboshi bashida sauqi.
Yana kaiwa nan ya fuce ya barta da kama kunci, anty fadila data fito daga part dinsu ita da oga don su ne a sama da maya kasan is for hamad tana ganin yanda ya futa tasan sunyi rikici kenan da qanwar tasa.
Bedroom din laila ta shiga ta taddata tana kuka shabe shabe.
“Menene kuma me kika masa? Nasan kece mara gaskia”
Cikin shesheka tace “mami wallahi ba laifina bane, kinga maya ce tace wai sabeeha zatayi extra class shine nayi tunanin class din zatayi ashe bashi zatayi ba shine shine muka tafi muka barta a school, toh dazun daya dawo damu yace na fada ma anne asa driver yakaita ni kuma bayan nasha maganin ciwon mara yasa ni barci na manta gabadaya shine yazo yanxu..”
Tun kafin takai aya fadila tace “innalillahi wa inna ilaihi rajiun karkice kin yarinyar nan kuka vari a makaranta tun da yamma har zuwa yanxu, amma bakida hanklai, are you mad?what sorr of nonsense is this? Eh”
Haka ta dunga balbaleta itama hankalinta ya tashi, abun babu dadi.

Sabeeha na shiga part dinsu ta tadda dakin kacha kacha, daman ita ke gyara wa duk sanda ta dawo daga school to yau ko zanin gado hadiza bata daga ba.
Wata iriyar yunwa takeji wannan yasa ta fuce zuwa kitchen ko zata samu wani abun da zata kaima cikinta.
Tana shugowa taci karo dasu rabi da hadiza a kitchen din anata faman gyare gyaren kwanuka na dinner da akayi.
Gaishesu sabeeha tayi sai a lokacin hadiza ta tuna da ita, batace mata komai ba sai binta take da ido tana girgiza kai.
Ganin irin kallon da hadiza ke mata na tuhuma yasa taji yunwar ma ta tafi gaba daya ta juya zata cire kayan jikinta dan tazo ayi aikin da ita daidai nan sukayi karo da maya data sauko kamar zata tashi sama, a kufule saboda yanda hamad yazo saura kiris ya mareta akan wannan yar wanke wanken.
Wani irin turata baya maya tayi kamar zata fadi ta daidaita tsayuwarta, “wallahil azeem da ya hamad ya mareni saboda ke wulaqantacciya yau da sainaga jini a bakinki, haka kawai saboda kin tafi yawanki na iskanci sai yazo ya balbaleni? Banza barauniya, asarraru, yar wanke wanke, gaba dayanku wahalace ta maku yawa tsabar Samun wajen har kin isa kisa yazo kamar zai dukeni? Ke a wa? Who’s your father? Ke yar uban wacece? Wataqila ma wajenshi kika gado sata”

Rabi dataga abun yayi yawa ne yasa tace “haba maya, me ta maki? Ya zaki mata kazafin sata?”

Hadiza na daga tsaye tana wanke wankenta ko tak bata ce ba ranta in yayi dubu yayi mugun baci sosai, saida taji anyi batun sata ne yasa ta juyo ta kalli sabeeha, maya dataga haka tace, “ki daina yi mata wani kallo, inta sato ke zata kawowa ay ba wani ba mteww rubbish”
Tana fadin haka ta juya tabar wajen hadiza ta fizgi hannun sabeeha zuwa backyard, ta kama hannunta sosai kamar zata ballata tace “dan abu kaza kaza…..”ta kundumo mata ashariya tace “koda na tura ki chan wata kasa daman sata kika koyo??? Eh????”
Tana shekar kuka tace “wallahi mama ban taba yi ba, wallahi da gaske nake”
“Zata maki karya ne???? Wallahi bazaki Jawo min magana ba, gwraa na tattaraki gaba daya ki koma chan wajen dangin ubanki lafia”
Tana kaiwa nan ta bar wajen kamar zata tashi sama.
Tana barin wajen sabeeha ta duka anan dakalin wajen ta saka kanta tsakanin cinyoyinta sai hawaye, kuka take sosai bakajin sautin ma sosai sai kadan kadan.
Jin alamun an dafata ne yasa tayi saurin dagowa ta miqe tsaye, nanna ta kalleta ganin tana saurin goge hawayen dake fuskarta kar a gani.
Saukowanta kenan kasa, daman tana zama ne a balcony dinta dake sama saiya kasance yana daga wajen backyard din, kaf conversation dinsu taji, wannan yasa ta sauko.
“Ina wuni Hajiya akwai abunda kike buqata”
Kallon fuskanta nanna tayi hawayen sun kasa tsayawa, ba karamin tausayinta taji ba ga muryanta ya soma dishewa, irin wannan ba tuhumar mutun akeba zama ake dashi a tambayesa akan komai bawai a yanke mar hukunci ba,
Hannu nanna tasa ta share mata hawayen a maimakon ta daina sai kawai ta fashe da hawayen sosai, nanna batasan lokacin data rungumeta ba ta soma padding bayanta, “shiii, ya isa haka”
Tana fadin haka ta zarota daga jikinta sannan tace “share hawayen”
Ta gogesu tass sannan tace “now tell me
Meya faru?meysa akace kinyi sata?
Kujerun dake wajen nanna taja masu suka zauna tana fuskantar sabeeha.
“Wallahi hajiya banyi ba, sharri ne,”
“Zan yarda dake idan kika fada min meya faru”
Ajiyar zuciya sabeeha ta sauke tana jin wani irin sanyi aranta tace”Daman dazu ne a school muna zaune ana lectures sai kawai maya tace anyi mata sata, tayi reporting to lecturer din saiyace duk wanda ya dauka ya futo dashi ko yasa a shigarda report, duk sai naga suna kallona bansan meya faruba wallahi, sai wata daga cikin students tace wai a duba jakana,im the suspect,nace masu ni banida jaka ma don littafaina ma a hannu nake rikesu,sai lecturer yace na fito zuwa stage zaiyi questioning dina, wallahi hajiya ina tashi bansan ta inda agogo yafito ba sai kawai suka fara ihu wai gashi nan nice na dauka, shine aka kira securities, sukazo za akaini disciplinary, sai wata sabuwar student ta dakatar dasu ta fidda same watch din tace ay wanda ya fito a jikina ita ta bani na aje mata ga nasu nan a wajenta lokacin data shugo class ta tsinta, toh kinji yanda akayi”
“Toh ita din da gaske ta baki ki ake mata?”
“Wallahi ah ah, banka santa ba wallahi ranar na fara ganinta a class din”
“She saved you?
Da mamaki sabeeha ke kallonta “yes she saved you, duk yanda akayi na hannunta shine nata na asali wanchan dayan kuma its possible ko wani ne yaso yayi maki sharri, you should be thankful to her”
Sabeeha tayi mamakin maganar nanna sosai don sai yanxu ta fuskanci hakan, “sunanki fatima ko?”
Ta girgiza mata kai alamun eh, “na yarda bake kika dauka ba kinji, sannan next time ki dunga lura da mutanen dake kusa dake, wanda ke kusa dakai shike da damar cutar dakai”
“Tohm hajiya nagode sosai”
“Karki sake yin kuka kinji ko? Tunda bakiyi ba me zaisa kiyi kuka, now give me a big smile”
Take kuwa ta sauke mata murmuhshin ta mai kyan gaske, nanna ta dunga kallon idanunta tana tunanin ina ta taba ganin ta ko me kama da ita.
Kallonta da nanna keyi yasa itama ta kura mata idanu tana tunanin ina ta taba ganin ta, sai kawai tayi zumbur ta miqe tsaye “laa hajiya kece wallhi kece, kece wadda kika taba bani kudi da yawa dana baki jakarki da kika yadda a masallaci”
Tunani nanna ta farayi yaushe event haka ya faru, “hajiya wallahi kece, wajen masallacin gidan man salbas dake kan Hanyar wajen gari? Shekara biyu da suka wuce? Kika mance purse dinki a masallaci harna biyoki da jakar lokacin zaki wuce”
Kama baki nanna tayi set of hakoranta suka fito rass tace “allahu akbar kece wannan yarinyar? Yar amana? Kece mai robar kwai ko?”
“Eh nice hajiya

52 / 107