Author : Queenmerh Category : Complete Novels
ita dutsen habuja achan kawai a daura auren jamilu ya zama waliyyinta, daga nan kawai dahiru ya kara gaba ita.
Toh gashi dan iskan nan yana neman raina masu hankali, wayarshi ma a kulle take.
Ko mutunci amsa ta bata samu ba balle ta tambayi ko ya makarata irin dai ta nuna ta damu da ita, saima wucewa datayi daman allah allah take maya ta dawo tasan yanda zatayi ta ganta, kwana biyu kenan rabonta da ganinta, ko tanacin abunci kuwa? Shin tana buqatar wani abu da gaggawa ne?.
Chan bangaren su maya ko sai wajen 5 driver yazo ya daukesu, tana ta murna don a tunaninta taj ne zaizo harta fada ma friends dinta.
Salim yaso ta fito su hadu amma fitik taki yarda saboda kwata kwata batasan ya hada yanda da taj.
Her personal life should be kept personal yanda babu wanda yasan da irin rayuwar datake yi.
Koda akazo daukansu suna fitowa suka shiga mota suka kamo hanya, laila har zatayi maganar sabeeha saitaja bakinta tayi shuru gudun kar maya taji haushinta don batason tana maganar sabeeha kwata kwata tun lokacin nan da hamad yace ta sauka daga mota ta kullaci maya da hamad din akan sabeeha.
A gajiya ta shiga part dinsu, da basira taci karo data dawo nan bangaren don taimakawa maman maya da aiki.
“Sannu da zuwa”
Ko kallonta maya batayi ba tace “hado min green smoothie ki kawo min sama”
Tana fadun haka wuce sama sai dakin mummynta direct tana shiga ta taddada bahijja zaune da laptop kan cinyarta suna yin wani emergency meetung da team dinta.
“Mummy…” maya ta fada, dagowa tayi ta kalleta kafin tace “excuse me for a minute. Tayi mutung call din, maya ta karaso inda take tare da ture laptop din ta zauna kanta tace “mummy na gaji”
“Sorry Baby meeting nakeyi, go to your room”
Tashi tayi kamar zatayi kuka ta futa daga dakin a fusace.
Girgiza kai bahijja tayi, ta koma ga meeting dinta, maya ko tana futowa daidai nan basira ta hauro sama da smoothie din, maya ta kalleta kafin ta karba tasa a baki, kurba daya tayi ta watso shi fuskar basirar tare da sakin cup din ya fashe tace “mey wannan?” Ta soma balbale basira kamar zata duketa, duk takaicin rashin dawowar taj ne yasa take wannan masifar.
Futa tayi daga part din gaba daya ta wuce main part, tana shiga ta wuce kitchen daidai nan ta hango sabeeha dake tsaye, da mamaki take kallonta don tasan ba tare suka dawo ba, yaushe ta dawo?
“Keeee!!!” Ta kira sabeeha, sabeeha tayi banza da ita
“Keeeee!!!” Sai a lokacin sabeeha ta juyo ta nufi hanyar futa da abuncinta a hannu, maya na ganin haka ta watsar da plate din nata “ba dake nake magana ba? Ke wai jin kanki kike wata shegiya ko?”
Rai a bace sabee tace “mey haka ya zaki zubar kin da abunci na? Wannan almabazaranci ne”
“Abuncin na ubanki ne ko ubanki ya say? Mutun bai iya samun waje ba mteww”
“Karki sake zakin ubana, ki zageni son ranki amma karki sake ambaron ubana”
“Me zaki iya yi? Na zagi uban naki idan kina dashi fa kenan”
Hannu saveeha ya daga zata sauke mata hadiza tayi ha zari karasowa ta wanketa da maruka, har uku, “ko da wasa karki sake kiyi tunanin taba ta dan ubanki, ta zagekin idan ta zagekin zai futo ne a jikinki? Kunada uban ne da zagin nasa zai maki zafi? Shegiya???”
Sabeeha bata taba ganin hadiza cikin wannan yanayin ba sai yanxu, gaba daya rayuwarta,
Juyowa hadiza tayi tana kallon maya tace “yi hkuri hajiya karama,dan allah kar ranki ya baci saboda yarinyar nan”
Tabe baki maya tayi tace “da kin barta ta tabani wallahi da bazaku kwana gidan nan ba dagake har ita”
Hadiza taji abu ya doki ranta tace “ko a mafarki bata isa ta bata maki rai ba ta sha, kiyi hkuri kinji, bana son ranki ya baci, da naki ya baci gwara nawa ya baci sau dubu”
“Hadamin abu mai sanyi insha ina sama”
Cikin jin dadi hadiza tace “toh” jikinta na rawa, maya na futa hadiza ta kalli sabeeha, wata iriyar tsantsar tsana takema yarinyar.
“Futa kafin na kasheki na huta” hadiza ta fada da karfi, jiki na rawa sabeeha ta futa, rabi dake labe jikinta duk yayi sanyi.
A gabanta sabeeha ta wuce daki da sauri ta hau kan gado tana kuka rabi tabi bayanta cikin lallami ta soma bata hakuri.
Maya na kwance hadiz ata kawo mata abu mai sanyi, “bude wardrop dina a kasa zakiga wani kwali dauko min”
Maya tayi magana.
Budewa tayi ta zaro mata kwalin, lbatasan kwalin menene ba amma tana kallo maya ta bude ta zaro guda daya wata yar takarda ta nannade ta zuba a juice din sannan ta kai bakinta ta shanye tass, hadiza tace “hajiya jarama menene wannan?”
“Ina ruwanki? Idan gulmq zaki dunga yimin zan hanaki shugowa inda nake wallahi”
“Ah ah yi hkuri, bari na making tausa naga kin gaji”
Ta karashe tana danna mata kafafunta, cikin abunda hai wuce minti biyu ba kawai ta mangare sai barci.
Hadiza na lura da tayi barci ta tashi taaye ta nufi bakin gado ta zauna tana kallon fuskarta tana murmushi, a hankali ta soma magana “diyata….kinfi kowa, zan iya komai akanki, zan baki duk gatan duniyar nan, bazaki taba wahala ba indai ina raye, zan juri ganinki daga nesa indai zaki samu komai na duniyar nan, gata da dukiya, kuma bazanyi kasa a gwiwa ba saina tabbatar kin dawwama cikin arziki har karshen nunfashina, banida kowa saike…“
Toh fah…..
Ta dade tana tare da maya har ana gab da sallar magrib, kafin ta futa daga dakin.
Bahijja na gama meeting ta wuce dakin maya, ganin batanan yasa ta suako kasa basira ta shuada mata ay ta futa, tasan duk inda zataje bazai wuce part din su laila ba ko main house wannan yas ata tsaya domin daura dinner.
Bayan futar rabi daga dakin ta kawo mata wani abuncin taci tasha panadol kafin ta futo suka daura sanwar dare ita da rabi.
Dake hannayen taimakon gyaran gidan da girki ya ragu saboda basira ta tafi dayan bangaren yasa suka fara da wuri kuma cikin ikon allah suka gama da wuri.
Ta koma daki ta dauro alwala tayi sallah, tana idarwa ta tashi ta futa zuwa kitchen, tun kafin rabi ta idar da sallah ta futo ta deba dinner dinshi a tray ta futo ta backyard.
Anatse take tafiya kamar wadda kwai ya fashema, gaba daya jikinta ya gama mutuwa da alamarin taj, bayan ya mata maganar hamad kan cewa wai ta daina kulasa ya dora da yanda ta faro gyaran part dinshi dole ta dawo yi, abuncinsa breakfast lunch dinner shima dole saita kawo mashi wannan yasa ta hado ta fito.
Tana gab da wuce apartment din dake gaba da nashi bahijja ta futo sanye da lullubinta.
Macece kyakyawa, sai kamshi takeyi, tundaga nesa ta hango sabeehar, dake akwai haske a compound din wanna yasa tana ganinta ta ganeta.
Gaba daya hankalin sabeeha yayi nisa kwata kwata bata lura da ita ba saida tazo dab da zata wuceta ta dago suka hada ido cikin sauri ta sauke nata idanun ta dan duqa cikin biyayya tace “ina wuni hajiya”
Ba yabi ba fallasa bahijja tace “lafiya!!” Sannan ta wuce
Sabeeha ma ta wuce har zuwa part dinshi, dan dakatawa bahijja tayi tare da juyowa ta ganta ta shige part dinsa.
Dan jimmm bahijja tayi na yan mintuna kafin ta maida hankalinta zuwa cikin main house.
Da sallama sabeeha ta bude kofar, babu kowa akasan kuma ko’ina fess fess babu datti sai kamshi da sanyi.
Aje abuncin tayi bayan ta jera har ta juya zata futa sai kuma ta dan dakata tare da wucewa sama, tana karasowa tayi knocking, shuru daga ciki ta sake knocking, shuru nanma saitayi tunanin koya futa ne wannan yasa ta dan bude kofar ahankali, ko’ina duhu babu haske wannan yasa juya har zata rufe kofar ta soma jin nunfashi sama sama, dan dakatawa tayi don tabbatarwa aiko taji nunfashin na hauhauwa, cikin sauri ta kunna fitilar bedroom din, take hasken ya bade ko’ina ta jefa idanunta ga bedroom din, a kwance ta taddashi amma jingine jikin board din gadon ya rufe idanunshi yana fidda nunfashi kamar wanda ke zazzabi, tundaga nesa ta soma dola sallama, yaji shugowarta amma ya kasa bude idanunshi saida ta doka sallama.
Dan karasowa tayi cikin dakin ta budeshi daga nesa nesa tace “na kawo dinner yana kasa”
Baice komai ba saida ya dauka wajen 2 minute kafin yace “okay thanks”
Harta juya zata futa taji wani irin aranta, alamunshi kamar baida lafiya tace “are you okay?”
Baice mata komai ba yayi shuru, ta sake cewa “bakada lafiya?”
Sai a lokacin ya sake bude idanunshi yace “zaki iya futa”
Ya fada a hankali, saitaji wani iri, daga yanda yake magana zakasan bashida lafiya don idan ta tuna yawanci haka yake idan yana zazzabi, saboda tsabar yanada strong blood yasa yake shan wahala.
Abunda yafi bata mamaki dazu fa suka rabu? Kuma bataga alamun rashin lafiya a tattare dashi ba.
Kokarin tashi ya somayi, sai taga kamar zai fadi ya koma ya zuwna tayi saurin takowa inda yake ta tsaya gabanshi tace “ka fadamin idan wani abun ne ke damunka zanje na fadi ma nanna”
Dagowa yayi ya kalleta yace “please step out..”
Jin haka yasa ta dakatar da zuciyarta ga avubda take raya mata, “tsayuwar me kikeyi? Ki fita kawai, ina ruwanki dashi? Idan kika nuna kin damu dashi shine zai bashi damar yi maki abunda yaga dama.
Aiko tana gama shawara da zuciyarta tayi fucewata kawai bata waiwayeshi ba.
Taba futowa daga part din nashi daidai nan kuwa bahijja ta sake fitowa, for the second time suka sake haduwa, data shiga ta ganta da tray saita dauka abunci zata kai ta futo immediately amma daga ganin lokacin data futo ya wuce ace abunci kawai ta ajiye, don daga shigarta zuwa main house har ta shiga dakin maya anyi wajen 20mins, saitaji gaba daya yarinyar ta kara fuce mata akai, daman what did she expect jinin hadiza?? Hmm”
Fuska anty bahijja tayi kamar baga ganta ba ta wuce part dinsu.
Tana shugowa ata tadda dady harya dawo, ya tambayeta ina maya ta shaida mashi taba main house achan zata kwana.
Chan bangaren oga taj kwana akayi a zaune, anata fama da abu daya, zazzabi ya rikeshi wanda urge dinshi ya jawo mashi.
Washe gari da safe duk suka fito, suka tadda driver ne zai kaisu, su maya suka shiga baya while sabeeha ta wuce gaba.
Suna isowa kowacce ta wuce class dinta banda maya data tsaya tayi bolt, ride dinta na isowa ta kira salim ya tura mata address dinshi ta kara gaba.
Ba itace tabar wajen salim ba sai ana gab da tashinsu ta dawo, tana dawowa kuwa driver yazo ya daukesu.
Rabuwarta da salim yasha tambayoyi akan taj, ya akayi yasan taj, menen relation dinsu da take ganinsu tare kuma tayaya suka san juya, dukda ya fada mata tun farko amma haka ta tado da maganar, yanda yaga tanayi yasashi suspecting ko sonshi takeyi, don gaskia hes a big catch overall all kuma relative dinta ne.
Suna dawowa gida kowacce ta kama gabanta.
Sabewha da tunanin taj ta wuni dukda tana kanta, tabbasa karya ne tace bata damu dashi ba, karya ne.
Suna dawowa gida she use the opportunity if gyaran part dinshi taje, sai kuma ya kasance a lokacin shi kuma baya gidan, haka ta gyara part dinshi sannan ta futo tana ta tunanin yanda ta taddashi jiya da daddare.
Shikam a asibiti ya wuni ma, yaje shima doctor ya dubashi, to his greatest surprise doctor ya tambayeshi if yaga abunda ya sashi jin urge din having intimate interaction, don daga yanda yake mashi bayanin yanda yakeji ya gano kamun zaren, nan ya shaida mashi mace yake buqata a rayuwanshi tunda namiji ne mai lafiya, he’s healthy above all samun irinsu akwai wahala, shi bai taba experiencing wannan abun ba sai yanxu.
The very next day..
Duk suka fito gaba dayansu, shima ya fito walking majestically just like always, tunda hanad ya tafi nanna tasashi ya dunga kaisu tunda shi hes less busy, abunda ya danganci kaisu makaranta ba tun yanxu ba anne tace banda drivers saboda yaro zai iya hada baki da driver ya tafi inda ba a sani ba agida.
Daga maya har laila binshi suke da ido bare maya kamar zata cinyeshi suka hada baki wajen cewa “good morning uncle taj”
“Morning” ya amsa su kai tsaye, sabeeha ta sauke kanta kasa tace “good morning..”
“Morning ya amsata calmly, motar ya bude maya ta nufi gidan gaba ya dakatar ta ita.
“Let her seat in the front, u go back”
Da mamaki maya ke kallonshi yana kallon sabeeha kuma ta tabvatar ita yake nufi,take taji wani abu ya daki zuciyarta kamar ta tsala ihu, saitaji ta kara tsanar sabeeha sau miliyan.
“But uncle taj… ya za ayi ace wannan yar aikin ce zata zauna a gaba tare dakai?”
“Dont you dare make me repeat my self” ya fada rai a bace coldly, maya felt so embarrassed, she felt so bad, haka nan ta juya ta koma baya, da hamad ne data mashi rashin kunya taj ko ina zata iya.
Sabeeha dai sai yanda akayi da ita, ammafa hankalinta a tashe yake, tana tuna maganganun hadiza, idan har ran maya ya baci babu zaman lafiya.
Fatanta suna sauka ta bata hkuri kawai karta kullaceta.
Aiko suna shiga motar bini bini yake kallonta jwfi jefi, yana kokarin hana kanshi kallon surarta don akwai damuwa inyayi haka.
Suna isowa school duk auka bude kofar, laila tace “thank you uncle taj,”
Maya dai ta kasa cewa komai ya dubi sabeeha da batace komai ba, jira yake yaji me zatace tayi saurin cewa “thank you”
Har wata ijjiyar zuciya ya suake jin muryarta, muryanta ma yanxu junta yake so sexy.
Har zata bude kofa yace “seat for a minute”
Aiko ta rufo kofar, ya dago da kanshi ga maya suna hada ido tayi saurin bude motar kirjinta na bugawa, meysa uncle taj ke kallon yarinyar nan haka, badai sonta yake ba? Badai ya fara sonta ba? Menene tsakaninsu??? Haka ta dunga jefoma kanta tanbayoyin daga karshe ma dai kasa tafiya class tayi ta tsaya tana kallon motarshi.
Bayan futarsu ya dubi sabeeha sannan ya miqa mata wayar daya saya mata yace “when will your first ends?”
“In an hour or 2”
Ta bashi amsa kai tsaye, “your phone, i will call you after then”
Kallon wayar tayi gabanta na faduwa zatayi magana yace “take the phone…..”
Haka nan ta karba ta rike a hannunta, brand new Iphone 15 ne sak irin nashi, saidai banbancin color don nashi black ne nata kuma titanium color.
Futa yayi daga motar ya zagayo inda take ya bude kofar datake zaune, ta sauko ahankali gaba daya wani iri takeji ga idanu a wajen, sunkuyar da kanta tayi ta wuce department dinsu shi kuma ya shiga motar ya bar school din.
Duk wannan abun akan idanun maya, idanunta har wani jaja yakeyi tsabar bala’i,jikinta na rawa ta lalubo wayarta tama rasa wa zata kira, abunda take fargaba yana shirin faruwa akan idanunta.
After 2hours kuwa daidai saiga call dinshi ya shugo taqi dagawa saida ya sake kira ta dauka, ya tambayeta what time zaau gama tace mashi sai wajen 4 na yamma
4 nayi kuwa yazo ya daukesu, yanxu ma mayan ce tayi gigin shiga gaba ya sake ce mata daga yanxu karta sake zama a gaba fatima ce zata zauna a gaba,
Laila ko mamaki baisa tace uppan ba, ai ba komai bane don sabewha ta zauna gaba saboda idan hamad yana nan agaba take zama amma kuma saboda maya nason taj sosai yasa bata ce tak ba.
Suna isowa gida daidai nan mummy ta futo zasu fita tare da daddy zasuje dubo anne a asibiti don ana shirin dawowa da ita gida, cikin yan kwanakin.
Tana sanye da kaya na alfarma tayi kyau masha allah, tun daga nesa ta hangosu suna fitowa daga mota, ga mamakinta taga harda yar hadiza data futo daga gidan gaba, aranta tace lallai samun guri.
Ganin sabeehar datayi tare dasu laila saitaji kawai abun baiyi ba, gashi taj ya futo shima daga motar.
Maya na ganinta ta taho da sauri idanunta yayi jaa sosai kamar zatayi kuka tace “mummy…lets talk”
Ko gaisheta batayi ba ma, bahijja tace “baby…”
Laila ta karaso tace “mummy ina wuni”
“Lafiya lau laila ya school”
“Alhamdulillah”
“Me akayi ma baby ne taketa bata rai kamar zatayi kuka, kuje kuci abunci zamu fita da daddy dubo anne”
Rai a bace maya ta wuce ciki, laila tabi bayanta.
Bahijja saitaji babu dadi kamar tabita taji meke damunta amma ta kyaleta.
Karasowa tayi wajen motar dady daidai nan sabeeha ta karaso ta duka ta gaisheta, ta amsa ciki ciki, taj da futowanshi kenan shima ya karasa inda suke ya gaisheda bahijja da daddy kafin su wuce.
Already sabeeha tayi shigewarta don gaba daya taoron bahijja take tun ranar nan da wannan abun ya faru.
Maya na shiga gida ko zama batayi ba ta futo zuwa ga maim house, tana shugiwa ta antaya dakin hadiza, hadiza daketa zumundun ganinta kwana biyu, ganin yanda ta shugo yasa ahankalinta tashi sosai,
Tunda maya ta soma magana hadiza ta kasa zaune ta kasa tsaye,gaba daya ta rasa inda zancen mayar ya nufa.
Kawai dai tasan saboda sabeeha ne take wannan abun.
Zagi ko har hadizar saida ta hada ta zageta tass , tace “wallahi yafi karfinta, taj nawa ne ni kadai, yafi karfinta, i was so stupid for thinking kina bayana, ashe cin amanata kike kina tira yarki wajenshi ko kunga mai kudi, bari ku shugo cikin dangin mu, toh wallahi wallahi idan har na sake ganinta ta rabeshi saina kashe ta, saina illatata.”
Hadiza fa hankali ya tashi, ganin maya ta juya mata baya gani take kamar tana bayan sabeeha, “dan allah karki ce haka, duk abunda zaki mata kiyi mata, wallahi ni mai iya taimakon ki ne, bazata taba shugowa cikin danginnan ba ita da arziki har abada tayaya ma zanyi fatan ta shiga arziki ita da ba yata ba? Tsintota fa nayi a titi??? Yar sheggu ce, mara galihu, banida wata alaqa da ita wallahi ki yarda dani hajiya karama kinji, wallahi babu wanda yakaini son cigabanki, nafi kowa son nagnki cikin farin ciki”
“Wallahi sai kun bar gidannan nan dagake gar ita,… bana kaunar ganinta daman yanxu ay da kikaga asirinku ya tonu zakice ba yarki bace”
“Ki yarda dani, bakiga ko kamanni bamayi ba wallahi ba yata bace, ina riketa ne kawai don ta zame min kadara da zan dunga cida kaina”
Shuru maya tayi tana