Author : Queenmerh Category : Complete Novels
sabeeha, daidai nan taj ya sauko daga sama daman hidyaa ta kirashi a waya.
Duk kusan a tare duk suka karaso, yana zuwa ya zauna kan kujera ya daura kafa daya kan daya, hidaya dai tana mamakin yanda ya dan fara sauyawa, gaba daya attitude da bai taba yi ba take ganin yanayi yanxu,bama wannan ba tukunna, maganar yarinyar nan da afiya ta tsorata su ne a gabansu inda tace masu ay a dakinsa ta kwana, kuma barinta around him is vwry risky, he could easily trust her once again tunda itace wadda ta kula dashi lokacin da baya cikin hayyacinsa.
Sabeeha na futowa tundaga nesa ta hango cirko cirko, ga sonata ga afiya ga fadwa a zaune hidyaa ma a zaune sai taj shima yana daga zaune, tareeq ne dai baya nan.
Tunda ta karaso gabanta ke dukan uku uku,
Hidaya na kallon taj din babu wasa kan fuskanta ta turo mashi divorce paper tace “sigh this up”
Daukan paper yayi ya soma karantawa, takarda ce ta yanda akeyin saki irin nasu achan kasar, yanda addini ya tanadar, aaida ya karance paper tass kafin ya dago ya kalli hidayar, “dis what i should have done already,we wouldn’t know whats she might come up with, tunda wanda ya kawota baya raye, i don’t trust her, yanda yayi kokarin cutar dakai itama zata iya yin haka”
Sabeeha najin haka gabanta ya bada wani dam, tunda hidaya ta soma magana take kallonshi, shi baika san tana wajen ba kwatakwata,
Idanunshi na kan paper,
“Maybe ma harda ita akayi planning kidnap din,” fadwa ta karashe tana mata wani mugun kallo,
ta ajiye mashi pen agabanshi, daman kamar jira take tamafi kowa kosawa tunda afiya tace mata idan har sukayi wasa wani abu zai iya shiga atsakaninshi da yarinyar.
Gaba daya binshi suka dunga yi da idanu ganin yaqi motsawa,sabeeha kuwa a daidai wannan lokacin babu abunda take sai hawaye, wato abunda suka kulla kenan, su maida abun zuwa khaal, sun kulla mashi duk sharrinsu akanshi, yanxu sa sukaga taj din zai iya ganowa shine suka maida kan khaal kenan, ita kuma da khaal ya aura mashi ita dole za ayi zargin bakinsu daya da khaal tunda ya bata property din taj, bayan wannan ma tasan hidaya ta gano cewa khaal ne ya kawo ta gidan ba tare da saninsu ba, so they want to use that against her, “innalillahi wa inna ialiahi rajiun” ta furta ahankali, kunnsshi ne kadai ya jiyo mashi furucinta,sai yaji presense dinta a jikinshi,allah allah take ya dago ya kalleta amma yaqi, baiyi wata wata kawai ya dauka pen din ya sanya hannunshi kan paper din, yana kokarin rubuta saki kawai sukajiyo muryar ammu data futo, barci takeyi amma wani ikon allah haka kawai ta farka a daidai wannan lokacin gabanta na faduwa, wannan yasa ta fito kuma taji gaba daya abubuwan da sukace, tsayarwa datayi tana hangosu jiran decision din taj din kawai take.
“Karka sake ka rubuta komai kan paper nan”
Gaba daya dagowa sukayi suna kallonta,fadwa ce tayi saurin miqewa tsaye tace “why? Saboda me ammu?”
Ko kallon inda take batayi ba ammu ta karaso inda sabeeha take tace “bazata bar gidannan ba, she can never, ko kun raba aurensu abunda ke tsakaninsu zai maido su”
Da mamaki duk suka juyo suna kallonta, hidaya data kagara da zancen ranta idan yayi dubu ya baci da maganganun da ammu keyi, tace “i have said it all, yarinyar nan yau zatabar gidannan, dama chan we have never accepted her she can never be part of this family”
“Well yanxu dole kuyi accepting dunta tunda she’s PREGNANT!!!!!!”
Gaba daya dakin ya dauke wuta kamar mutuwa ta gifta, fadwa afiya hidaya sunji maganar ammu kamar saukar aradu,
“She’s pregnant for him”
Suka ne kawai sonata batayi ba don baqin ciki, hidaya kuwa idanunta yayi jaa sosai, shi mai gayya mai aikin gaba daya ji yayi kamar an toshe mashi kunne sai kawai ya saki pen din, idanunshi yayi jaa sosai ya dago suka hada idanu da sabeeha, take yaji kamar an zuba mashi ruwan dalma a zuciyarshi tsabar bacin rai, sabeeha kuwa baiwar allah kamar ta kurma ihu tsabar furgici, tama kasa karantar yanayinshi gaba daya mai wuyar fasaara, da kyar ta dauke idanunta akanshi ta maida kan ammu, saurin runtse mata idanu ammu tayi alamun tayi trusting dinta, hannunta ammu ta kama ta rike dake ta faman karkarwa, me ammi take nufi da abunda ta fada yanxu? Dauke idanunta tayi daga kan ammi ta maida kan mutanen dake parlorn sai suka dunga mata wani irin gizo, tana hango bala’i cikin idanun kowannensu…..itama ammu karfin hali ne yasa ta fadi hakan…….
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 66
Update!!
Unedited!
Fadwa ce tayi saurin miqewa taba kallon sabeehar sa ammu tace “no thats not possible, karya ne”
“Daman ana karya da ciki?” Ammu ta jefo mata tambaya kafin ta maida dubanta ga taj din dake zaune tace, “yanxu saikayi deciding, zaka koreta ne da cikinka a jikinta?”
“Ammu…..ya za ayi mu yarda nashi ne? What if ba nashi bane?” Fadwa ta sake jefo ma ammu tambaya, gaba daya kamar tama fi kowa rikicewa tsavar bacin rai,
“Ay gashi nan a gabanku, shi yasani idan ma nashi koma ba nashi bane, decision ya rage nashi to decide on that, saidai inason ka sani, all this while yarinyar nan tana tare dakai, kuma tare kuke kwana duk kun san da wannan,”
Tunda suka soma magana hidaya tayi shuru tama kasa cewa komai, she couldn’t believe abunda kunnenta ke jiyo mata.
Maido da dubanta tayi ga taj dake zaune yana kallon paper hannunshi, tunda ammu tayi breKing wannan maganar cikin dole ta tabbatar tukunna kafin ma akaiga koma menene, haka kawai tasan ammu bazatace yarinyar nan nada ciki ba
“How do you expect us to believe this? He was mentally unstable babu yanda za ayi ta samu ciki” sai a lokacin hidaya tayi magana, sabeeha dai har zuwa lokacin bata bar kallon taj dinba,
“Koda kuwa he wasn’t on his right mind namiji ne shi, kuma ga shaidar hakan nan ajikinta, Na kasa gane maku gaba dayanku, why do you keep insisting on cewa karya ne? Eh?,kaikuma kayi shuru,say something!!! No one should speak up for you”
Ammu na fadin haka suka maida dubansu zuwa ga taj din gaba dayansu, kowanne ya kasa kunne yanason jin abunda zaice, hidaya ko tama gama relaxing mind dinta opinion dinta zai buqata tunda already yana tafin hannunta sai yanda tayi dashi.
Bai dago ya kalli kowannensu ba, haka zalika yasan gaba daya jiran reponse dinshi suke, yyi nisa sosai wajen yi nazari, duba ga memeories dinsh tare shida ita daya dunga zuwan mashi na kusancin da suka samu yasa yaji tsoro da fargabar abunda ammu ta fada yanxu, idan ya karyata cikin ya koreta kuma yazo ya zamana akwai shi he will be devastated, indai tana da ciki to tabbas nashi ne tunda akwai aure tsakaninsu,koda kuwa she took advantage of him, saurin runtse idanunshi yayi sosai, he’s so embarrassed at that moment, sai yaji gaba daya ya tsani yarinyar sosai,yana ganin abun kamar she used him ne, har yayi concluding daman plans dinta kenan, tayi amfani dashi a lokacin da baya cikin hayyacinshi kuma shi ayanxu ya gama yarda da maganar da hidaya ta fada akanta, ya dauka wajen minti biyar kafin ya sauke ajiyar zuciya ya dago ya kalli ammu yace “idan har tana da cikin then I’m responsible,”
Yana fadin haka kowa ya bishi da kallo, ammu kuwa wani murmushi ta sauke, hidaya kam kasa daina kallonshi tayi, he didn’t even look at her balle ya bata damar yanke hukunci,lallai maganar fadwa ta tabbata, yarinyar nan zata iya zame mata babar matsala, bata ga hakan ba sai yanxu.
Ammu kuwa dadi kamar ya kasheta, ta dubesi daya bayan daya tace “toh yanxu kuna da magana? Are you still against it? Baku yarda ba?”
Hidaya da ranta ya gama baci tayi saurin cewa “yes, inason ayi test”
Ammu kuwa ko a jikinta ta daga mata kafada tace “okay then, gobe sai ku kira family doctor ku yazo yayi mata test din, saiku tabbatar da kanku”
Tana kaiwa nan taja hannun sabeeha suka bar wajen, suna barin wajen fadwa ta kalli hidaya tace “wallahi ukty karya ne, bazai taba yuwu ba, daman na fada maki yarinyar nan is a snitch..zata iya”
Saurin zungurinta afiya tayi sai a lokacin ta ankara da taj dake kokarin barin wajen, sonata kuwa tana daga gefe kuka take shabe shabe tsabar takaici, ko kallonsu bai sake yi ba ya bat wajen ya haura sama, shima abubuwa da dama sun tsaya mashi a arai.
“Ukty….say something mana, are just going to be silent?”
Rai a bace hidayar ta kalleta, “ya kikeso nayi then? Did you even see what just happen? Yau taj ne yayi making decisions da kanshi ba tare da ya kalleniba? Meke shirin faruwa kenan”
“Ay daman na fada maki, wannan yarinyar zata iya zame mana matsala, tun wuri na fada maki mu kaudata daga rayuwarshi kika tsaya kina ganin she cnnt be a threat to us” afiya ta fada tana mai kallonsu, ita abunma haushi yake bata, komai is about him.
Tsaki ta doka kawai tabar wajen rai a bace.
Acahn daki kuwa suna shiga daki ammu ta rufo kowa ta jata har gadonga ta zaunar da ita, har zuwa lokacin sabeeha batabar jin shock din maganar da ammu tayi ba, lallai akwai bala’i a gaban su.
Hannunta ammu ta kamo tana mai fuskantar ta, tun kafin tace” nasan you’re shock ko? “
“Ammu meysa kika fada masu inada da ciki, what if suka gano banida shi? What if…l”
“Listen to me fatima, i did that to save us time, wannan ce kadai hanyar da zaisa bazasu koreki daga gidan nan ba, daman nasan kece next target dinsu kuma bazasu barki, sabida suna tsoron karya tuna ki kuma ya fara yarda dake don ke kadaice kikasan irin rayuwar da yayi a gidan nan, kuma kinsan sirrin su,“
“But ammu what if suka gano gaskia?”
“Karki damu ive prepare for them, kedai kawai inaso kiyi pretending kinada ciki karki sake ki bari su gano, yanxu we have him on our side, kinga dai yanda baima kalli hidaya ba balle ya bata damar yanke mashi hukunci, he will never let anyone hurt you yanxu, tunda yaji da cikinsa a jikinki, bazasu iya korarki ba koda wasa, thia is our only chance, ta hanyar nan ne zaki samu damar earning trust dinshi ki fayyace mashi komai”
“But amma ammu idan ya gano duk karya ne he will be heartbroken, bazai ji dadi ba”
Kamo fuskanta ammu tayi ganin tana neman sarewa tace
“Dont think about that my dear,we are doing this for his sake,he will understand us kinji,”
Sabeeha dai bata gamsu ba, a cikin wannan tight position din shi take tunanin kawai, batason ta mashi karya, amma dole tabi abunda ammu ta fada idan har tana son ta cireshi daga duhun da aka sakashi,kuma bazata samu yin haka ba sai tana tare dashi, kamar yanda ammu ta fada she needs to be very close to him saboda ta samu damar samun yardarshi, kuma wannan ce damar da take da ita kawai wannan yasata samu karfin gwiwa tace “toh shikenan ammu, toh amma ya za ayi da ciki? Ni bansan yanda masu ciki suke ba” ta karashe a shagwabe, yanda tayi magana yasa ammi ta dan murmusa tana hango tsantsar yarinya a tattare da ita, “karki damu, kibar wannan a wajena kinji”
Jinjina mata kai kawai sabeeha tayi.
Da daddare wajen karfe tara ammu ta sake shugowa dakin nata ta kawo mata wata kwaya ta bata tasha, “wannan kwayar zata taimaka mana idan akazo gwaji, za a kina da ciki, zata dunga saka ki feeling nausea da amai, duk effect dinta ne,”
Jinjina mata kai kawai sabeeha tayi har ammu ta juya ta dan dakata tace “for now karki koma part din nashi, gobe idan anyi test saiki koma”
“Tohm ammu saida safe”
“Allahumma bareek aibnat bialnasab” tana kaiwa nan ta sauke mata murmushi kafin ta fuce.
Tana futa sabeeha ta sauke ajiyar zuciya tana hango gagarumin bala’in dake gabanta.
Chan bangaren afiya da sonata kwanan baqin ciki sukayi musamman sonata data gama ganin wulaqanci, yanda kasan karamar mahaukaciya haka ta dawo, harta sare ta yanke barin gidan gaba daya afiya ta zugota akan ta zauna, su tabbatr akwai cikin idan babu zasuyi ma sabeeha korar wulaqanci, imma akwai dole saisun san yanda suka zubar da cikin.
Chan bangaren fadwa kamar ma tafisu shiga tashin hankali, ahi tareeq da baima san meya faru ba gana daya ta gama daga mashi hankali, tund ata shige dakinta ta rufo kofa take ta faman fashe fashe, sai a ranar ya tabbatar fadwa nada wani irin hot temper, idan da yana gabanta zata iya illatashi ma.
A cikin dakin kuwa bayan ta gama fashe fashenta ta shige bathroom, cikin yan mintuna qalilan futo, daure da towel a kirjinta da alamu wanka tayi, takowa tayi bakin gadonta ta tsaya tana mai kallon hotunan data watsa akan gado, dubanwan da zanyi kawai naga hotunan taj, different types of hotunanshi ne burjik, mafi yawa sune wanda yake gym, he looks so breathtaking, wasu ma ba a kasar bane akayi hoton, ga wasu hotunan nashi da suit ya zauna akan mighty kujera aka dauka hoton unexpectedly wasu a beach ma ya dauka yana daga zaune kan kujerun beach ya saka sunglases mai kyan gaske fatarshi na glowing yayi smirking kamar murmushi, zama tayi bakin gadon tana murmushi tana kallon hotunan nashi sai kawai ta fara lumshe idanu tana shafa hotunan nashi at the same time tana sauke sighn of relief tana admiring picture din nashi ta dade a haka sai kuka naga ta chanza fuska take abunda ya faru dazu ya dawo mata arai, batama san lokacin data dunqule hotonshi ba a hannunta tace “idan bazan sameka ba then no one will have you as-well, babu macen data isa ta mallakeka ina nunfashi, saina kawo karshenta” lokaci guda kuma sai ta sauke wani murmushi ta kyalkyale da dariya kamar wata psycho, hoton nashi dake hannunta ta warware tana murmushi tana shafa fuskanshi ta kwanta akan gadon tana mannashi a jikinta.
***
Yana daga cikin bathroom bayan yayi wanka ya janyo towel yana kokarin daure kugunshi idanunshi ya sauka akan mr D, yana kallon wajen kawai yarinyar nan ta fado mashi arai, baima san lokacin daya doka uban tsaki ba tsabar bacin rai, yanxu shikenan yarinyar nan ta ganshi? She have him without his consent? Tuna wanna kadai ke sa ranshi ya sake baci, tun bayan daya hauro sama dazu ya kasa daina tunanin maganar cikin da akayi, gaba daya haushin kanshi yakeji sosai.
Harya shirya ya kwanta baibar tunanin event din daya faru ba daxu.
Washe gari da safe kowa ya hallara a dining area, gaba daya kowa yanayinshi ya sauya, su afiya da sonata jira kawai suke ayi test, sun shirya yima sabeeha grand wulaqanci da zarar aka gano babu ciki, idan ma har akwai cikin wanda basa fata ya tabbata to saisunsan yanda sukayi ya zube kota halin qaqa.
Shugowar sabewha da ammu yayi daidai da saukowarsa daga dining shima, ammu na ganinshi cikin rashin walwala ta tabe baki tace “kaji dashi kaima daya, ka tsaya mata suna juyaka yanda sukaga dama kamar wani kwallo”
Bai jita ba ganinta tare da sabeeha yasa ya wuce baima tsaya gaisheta ba don ko kallon sabeehar ma bayason yi don yana tuna mashi cewa ta sanshi a matsayin namiji, abun takaici ma maid dinshi ce, kuma karamar yarinya da ita for that matter.
Zama kowannensu yayi babu wand ayace da wani qala ko gaishe da ammu ma basuyi ba taj dinne ma kawai ya gaisheta da larabci sauran kuwa daman sun qullace ta yanxu don sun gano tana bin bayan sabeehar.
Sabeeha kuwa tana jin idanunsu akanta kamar zasu hadiyeta dan masifa.
Kota kansu ammu batabi ba ta kalli maid din dake serving dinsu ta vuqaci ta fara serving dinsu.
Maid din na bude warmer sabeeha tayi perceiving aroma din abunci taji cikin ta ya hautsina sai kawai wani irin amai ya taso mata tayi saurin miqewa tayi baya, ammu na ganin ta miqe tayi saurin miqewa itama tana mai kallonta tace “are you okay?”
Girgiza mata kai sabeeha tayi tana kokarin toshe hancinta, ammu na ganin haka ta kalli maid din dake kokarin zuba abunci a gabansu, abuncin na sauka akan plate ammu kawai amai yazo, cikin hanzari sabeeha tayi baya allah yaso akwai wash hand basin a dining tayi hanzarin tunkarar wajen ta fara kwarara ruwan amai, ammu ta biyo bayanta tana dabbing bayanta, yanda take aman kamar zata amayar da kayan hanjinta, daidai lokacin hidaya ta karaso dining din, tana ganin abunda ke faruwa tayi saqe, taj na daga zaune ko gizau baiyi ba kuma ya ga komai shima ta gefen ido.
Breakfast din da hidaya batayi ba kenan ta fuce daga wajen, yab uwanta suma don takaici suka bar wajen ya tage daga sonata sai taj da afiya a zaune,sonata kanar zatayi kwalla da baqin ciki, ganin taj bai motsa ba kuma bai dago ba yasa ta danji dadi aranta koba komai it looks like kamar he doesn’t care much.
“Sannu fatima, sorry, wannan morning sickness dinne ko? Zai ragu kinji ko”
Girgiza mata kawai sabeeha tayi tana langwabewa, suka bar wajen basin din,ammu ta mashi kallo daya ta kauda kai tana murmushi, ta lura tunda sabeeha ta miqe yake kallonta ta gefen ido,tana hango how restless he was lokacin data fara aman wannan ya bata tabbacin ya damu kenan daman tasan he dole aai hankalinshi ya dawo garesu dukda ta lura shima hes tough yabada kafiya.
Su Ammu na barin wajen sonata dake gefenshi ta fara kokarin kamo hannunshi, harda yar kwallarta “babe…don’t tell me you believe all of this, karya ne wallahi, so suke su qala maka wannan pregnancy din,”
Wani irin banzan kallo ya mata tare da kabar da hannunta ya miqe ya barsu a zaune, yana barin wajen sonata ta dubi afiya tana hawaye, “babe wallahi ciki ne, she’s pregnant ya zamuyi? Yanxu shikenan she will have him, banida chance kenan”
Afiya ranta in yayi dubu ya gama baci da maganar, tsakanin jiya da yau gaba dayan su kowa hankalinshi na kan maganar, sonata na tafi bata haushi.
Batama san lokacin data miqe ba tabar