Advertisements
Chapter 106 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   106 / 107

315K to 318K   out of 320.4K words

dan duqa a gabanta.
“Fatimaa…!!!”
Nunfashinsa yasa ta tashi tsaye ta matsa daga inda yake, zata juya kenan ya rungumeta ta baya.
“Ahap…ay na sani dama…” tana fadin haka a zuciyarta taji gaba daya she’s disappointed in him,wallahi taj baya sonta kuma batajin zai taba sonta jikinta kawai yakeso.
“I’m sorry…I’m very sorry please…i need you in my life, let’s put an end to dis fight silly fight please uhmm..”
“Okay…” ta bashi amsa yayi saurin sakinta tsabar murya ya juyo yana kallonta, ta cigaba da cewa “ka sakeni kawai…hmm bazaka iyaba ko?? Cause you have not had enough of my body right? Okay then…zo kayi abunda kakeso, zo kayi abunda kaga dama…”
Ta fashe da kuka, “ban taba tsammanin haka daga gareka ba, i loved you i cherish you tun baka cikin hayyacinka,…”
Cikin Sauri ya sanya yatsa akan lebenta, “can you say that again??”
Ta bangaje hannun, yayi wata iriyar dariya mai kyan gaske data karama fuskarsa annuri, “you loved you????”
Ranta ya kara baci ganin ya maida abun wasa yana dariya, gashi ita ranta a bace yake, and she doesn’t mean to say she loved him in a romantic way, just for who he is, tana kokarin yin magana ya dagata chak sama har zuwa lokacin dariya yake, wani irin farin ciki ne kwance a fuskarshi….
Unexpectedly taji yace “i love you more”
Wallahi yanda yayi magana saida taji abun har kwakwalwarta, “i love you fatimaa yes you…”
Yana fadin haka yayi pecking kumatunta yana murmushi, i love you dinan ya ahige ta fa amma gani take kamar aaboda yanason abu daga gareta ne.
“And kana tunanin zan yarda dakai ne…?ay bazan taba yarda da maganarka ba, cause you broke my trust twice…”
“I dont care ko ki yarda ko kiqi yarda…”
Yana fadin haka ya nufi gado da ita…
Acahn gida ba laila data dawo ta wuce part din mummy ta shaida mata komai tayi mamki soaai, saidai kuma hankalinta bai tashi ba tunda ta tabbatar suna tare.
Saida taga wajwn karfe sha biyu shuru nanfa hankalinta ya tashi, ta soma kiran sabewha a kashe gashi bazata iya kiran taj dinba saboda kunya.
Haka nan ta kwana zuciyarta fal babu dadi.

Bangaren au sabewha tun tana nokewa harta hkura data tabbatar ba gida zai maidata ba.
Batasan ya akayi ba sai jinshi kawai tayi ya rungumwta suna barci lokacin wajwn karfe uku na dare.
Tana jin nunfashinsa da kamahinsa, saita tuna sanda suke rayuwa a saudi,…
Washe gari tunda asuba ta tsiri sabon kuka, ta hana kanta natauwa, yayi rarrashin yayi rarraahin harya gaji, gashi yana jin wani shauqi sai lallabata yakeyi.
Basu ne suka bar hotel ba sai wajen 12, lokacin kowa yasan basa gida harda su anne, inda anne tace inaa cikin satin za ayi bikinsu kawai kudi ba matsalanau bane, infact other bigger apartments da suke available a cikin estates din taza azo a fara gyarawa.
Bayan sun dawo da kyar ta yarda suka hada idanu da mummy sai faman sunkuyar dakai take, bahijja tace au dama ashe duk wannan batasonshi bata son aurenshi, ta tsaneshin datake yi duk a baki ne,.
Batace mata komai ba ta kyaleta ta zuba mata idanu kawai.
Sabewha batasan abunda ake ciki ba, ashe ashe shiri ake maga babba, an hado lefe uban ubansu tattaki daga dubai, komai babu abunda ba a saya ba.
In 5 working days suka iso, duk wani abu da tradition ya tanada anyi mata.
Ji taj ko tunda anne ta shaida mashi plan dinsu kai tsaye yace masu baisan ayi komai,infact yanason su koma saudi ne for the mean time cause akwai it is very important ya tafi da ita.
Basuyi queationing dinshi ba suka yarje.

Ranar da bahijja ta fada mata abunda aka yanke kwana tayi tana kuka, saitayi dana sanin binsa datayi dinnan, don tasan tabbas shi yayi triggering maganar aurensu,gashi ta shaida mata yace zasu tafi saudiyya cikin kwanaki masu zuwa, sai bayan sun dawo ne sai ayi duk wani avunda tradition dinmu na nan hausawa fulani ya tanada.
Kiran duniya idan zaiyi mata a waya bata dauka, haushinsa takeji ba kadan ba,sai yanxu takejin shakuwa mai karfi sa iyayenta, sun dandana mata dadin aoyayyar iyayw and has not had enough of it, ayanxu nw take buqatarsu a kusa da ita.
Bahijja data lura shes getting depressed kullum fada take mata da addua, sannan tana kwantar mata da hankali kan cewa they will always be there for her.
Ta bangaren gyara bata bar diyarta haka ba, haka ta dunga gyarata sosai, kusan kullum sai laila ta rakata spa, zuwansu na karshe akayi mata kitso kannu masu kyau lalle ne dai na bikin haya bai futa ba saboda bata aikin ruwa.

Ranar da zasu wuce saudi bata iya barci ba gaba daya da zazAbi ta tashi amma ta daure,bahijja ta hada mata kayanta, tana kokari hana kanta shiga state din da zaisa ta karaya.

Tana kwance a daki misalin wajen karfe biyar na yamma mummy ta shugo ta mata nasiha sosai, sannan ta shaida mata da zarar sun dawo za ayi bikinsu yanda akema kowacce budurwa auren gata, karshe dai she couldn’t help it saida ta fashe da kuka sosai.
Suka futo tare daga gida don yima kowa sallama don flight dinsu bay 6:20.
Ta ahiga bangaren nanna ta taddashi zaune, nanna ta masu nasiha sosai, sabewha ta tashi da sauri ta rungume nanna, nanna ma saida tayi hawaye tana shi mata albarka, haka zalika wajen anne ma, ta saka masu albarka sannan sukayi mata sallama.
Suna fito suka wuce wajen anty laila, itama dai harda kwallarta laila kuwa wuni tayi tana kika itama bare kuma hamad shi futa ma yayi daga gidan.
Uncle sameer yazo shima sukayi sallama ta ahiga bangaren matansa suma, anty laila harda rungumarta, itama tayi la’asar dataga karahen maya a gidan.
Daddy ne last peraon da sukayi sallama, which shine da kanshi ya sata mota sannan ya zauna kusa da ita suka wuce airport bahijja dai ta kasa binsu don tanada karyayyiyar zuciya, saidai kuma adduar ta na tare da ita,taj ko tun jiya suka zauna, ta roki alfarmar ya rike sabeeha da amana, she trusted her in his hands.

Airport…
6:00pm daidai suka iso airport, tunda ta shiga motar take kuka a jikin dady, dukta jika mashi shaddarsa, zuciyarsa tayi masa nauyi sosai, yayi lallashi harya gaji ya barta.
Suna isowa ya kama hannunta ya fito da ita sannan ya fuskanceta.
“Ya isa haka kinji, promise me bazaki sake kuka ba, muna nan muna jiran dawowarku allah ya maki albarka my daughter, allah ya dawamar dake cikin farin ciki, idan bakyason fushina kinhoge hawayen”
Cikin sauri ta gogeshi tass yace tayi smiling tayi, da haka sukayi sallama, it was an emotional moment ya rabb aaida ya danji kwalla.

Suna shiga airport kai tsaye aka fara boarding, yana gaba da boxes dinsu tana biye dashi a baya sanye da pink abaya, duk tayi laushi.
Chan wajen stand din first class ya nufa ya bada passport dinsu aka gama komai shaf shaf sannan suka wuce lounge.
Mintuna kadan luxury motan da zai kaisu ya iso suka wuce sai saudiyyaaaaa…

The flight was smooth, throughout barci ta dunga yi, seat dinsu na kusa da juna, sai dan extension dake taakani.
Tayi kwanciyarta yasa aka kaqo blanket ya shinfida mata.
Hutu akwai dadi, inda suke zaune ma kamar daki, kamar ba a jirgi suke ba.

Sai wani nan nan yake da ita, duk wani motainta alan idanunshi, data farka ta cigaba da kuka sai ya dawo bangaren da take ya ahiga cikin blanket din nata yana rarrashinta a haka har barci ya daukesu.
Kowa na abunda kw gabansa allah yaso ma duk turawa ne a ciki babu wanda ya damu da wani.

Basu ne suka iso ba sai safiyar ranar, ya tasheta saboda dogon barcin datayi, sannan suka fito, baggage dinsu na biye dasu.
Tunda ta shaqi iskar kasar taji wani irin rahama ya shige just like sanda ta shugo kasar, ahankali ta furta “ni’imatullah..”
Tana sauke kafafubta Take abubuwan da suka faru da ita a kasar suka ziyarceta, kamar ba ayi ba komai ya zama tarihi allahu akbar.
Hannu ya miqa mata ganin ta taaya yana murmuahi yace “let’s go mrs tajudeen abdullah taheel”
Samun kanta tayi da miqa masa hannun suka wuce inda motarsu ke jiransu a harabar jirgin…..


Maya…
Rayuwa babu tabbas, yau in kaine gobe ba kaine ba, babu wanda yasan shirin allah, in kayi daidai kaga daidai in kayi ba daidai ba kaga ba daidai ba.
Watanta daya a asubiti babu wani progress, wayo allurar nan ta taba kanta ma, ga ciki mai laulayi ga cutar dake jikinta wa iyazubillah, in tana zaune saidai kaji tana saina kasheta na kasheta ma saina kasheta.
Nurse mata ko sun daina attwnting dunta sai maza tunda ta chaka ma wata nurse wata allura tafkekeyi ta dunga zubda jini, hamad baqan allah shike kula da ita, ya kashe kudi ba kadan ba wajen lura da ita da expenses din asibiti karahe daia akace psychatric za a kaita.
Bai musa ba ya bada approval, kuma babu wanda yasan da yanayin da take ciki sai nanna da hankalinta ya kasa lwanciya ga mayar, yarinya ce kankanuwa sandaiyar uwar data haifota duniya yasa ta shiga wannan kunci.

Watanta biyu a asibiti ta soma samun progress amma kuma ta shuga depression which lead to cikin ya zube daman gashi yana bata wahala ta rame ta qanjame sosai.
Bata magana kwata kwata ta zama kamar kurma kullum saidai ta kafe waje daya da kallo wani sa’in tana hawaye.
Hamad yana zuwa jefi jefi on the other hand ya bazama neman saurayinta dayayi contributing wajen lalata mata rayuwarta.
With the help from taj da shima ya shiga cikin masu kokarin taimaka mata bayan duk abunda tayi akayi locating salim, dukda taj baya gari yayi contributing wajen ganin dole idan ta samu sauqi salim ya aureta don tabbas anne da mummy bazasu taba barinta ta dawo gidan nan ba saidai ta koma gidan jiya.
Aiko baban salim dayafi kowa son kudi gudun karya rasa deal dinshi da TFord take yace ay kamar anyi an gama.

Laila ma an turo kudi, wannan saurayin nata dai da suke tare over 1 years hamshakin mai kudi shima yana zaune a dubai yana aiki.
Hamd ne dai bai shirya ba yanxu don hes still recovering from heartbreak dinshi na rashin sabeeha dukda ya rahamtama kanshi ita har abada.

Wajen su hadiza ansha azaba iya azaba, ana chan ana girbar abunda aka shuka.


Saudiyya…
Daga airport gidan da ya saya wani tamfatsetaw suka nufa, ya subhanallahi wane taheel residents innalillahi wa inna ialihi rajiun, aaida sabeeha ta tsorata ba kadan ba, tundaga waje balle ciki kuma, ga uban ma’aikata ta ko’ina gashi koina sai saidai san barka.

Maids din da zasuyi dawainiya da ita kuwa sunkai su biyar, daga iyakacin part dinta, said aya rakata har part dinta sannan ya futa ya barta da maids dinta suyi hidimar ta.
Gaba daya kewar gida ya addabeta gashi tunda ya futa da safen bayan ya rakota daki bata sake ganinsa ba yama fuce daga gidan gaba daya.
Gashi batada sim da zata saka ta kira gida taji ya mummynta take.
Abunci da aka jera mata for just her yakai kusan potion goma, abun ya taoratata sosai gashi bata samu damar tambayarshi ina ne nan din ba don batayi tunanin gidansa bane, son yafi taheel resident to kuwa in yafi chan wani mai uban kudi ne haka keda nan, unkowning to her gidan mijinta ne nan Mr TFORD.

Bai zauna ba tun bayan isowar su ya futa, sannan bashine ya dawo ba sai wajen 11 na dare a gajiya, ga barci dake kan idnaunsa, dakinta kawai ya fara zuwa ya ganta kwance tana barci, ya sundumi kayarsa ta tashi furgigi, yayi calming dinta down sannan suka fito zuwa bedroom nasa, tun kafin su iso ta ishesa da tambaya.
Ina ne nan? Gidan waye maisa ya kawo ta nan.
Answer daya ya bata which is she will find out tomorrow Insha allah…

MATAR TAJ (destined with you)
   Written by 
          Queenmarh

Book2 
PAID
Chapter 119


The next day!
Misalin wajen karfe takwas ta fito daga bedroom dinsa da sauri bayan ta samu damar fucewa daya shiga bathroom, gaba daya ya hanata sakat, duk wani motsinta akan idanunshi.
Abunda yafi bata mamaki shine kwanan da sukayi ko kadan baiyi kokarin tabata ba, da farko taqi sakewa daga baya kuma saita sake abunta har barci ya sake daukanta.

Fast forward..ta gama breakfast already ta shirya tsaf abunta cikin wata shaqaaaiyar abaya dake cikin kayanta da mummy ta saya nata,tun kafin ma maids dinta su shaida mata breakfast is ready ta sauko taci.
Tana zaune sai gashi ya sauko shima, sanye da jallabiya da kundura akanshi, ya koma sak balarabensa na asali.
Samun kanta tayi da bunshi da kallo batama san tanayi ba, yayi captivating attention dinta gaba daya ya tafi da ita.
Badan badan kar Tayi downgrading kanta ba datace tabbas taj yafi karfinta, he’s charismatic, he’s handsome, kai komai ya hada.
Gyaran muryar dayayi ya dawo da ita daga duniyar data tsunduma, tayi saurin saukw kanta kasa saboda kunyar dataji, yayi dariya kawai sannan ya kashe mata ido daya.
Zama yayi ya buqaci tayi serving nashi batayi misu ba ta miqe tana zuba mashi abunci harta gama.
Tana gamawa zata koma mazauninta ya jawo ta ga cinyarsa ya soma cin abunci a natse, yana cikin ci wayarsa yayi ringing, very important call wanda hakan yasa ya ajiye abunciz
Yakai wajen 5mins yana waya, haka kawai ta dauka spoon din ta deba ta cigaba da bashi, abun ko ya mashi dadi sosai.
Bai gama ci dinba ya aje wayar hannunsa sannan ya sauke ta ya miqe shima tare da kama hannunta suka futa daga gidan.

Bayan sun shiga mota babu wanda yace da dan uwansa qala tana son ta mashi maganar sim amma kuma ganin yanda yake ta waya yasa ta dakata saiya gama.
Saida suka iso ya aje wayar sannan suka fito daga motar, gaba daya wajen she’s not familiar with it, ta daiga an saka saudi international court of justice, kuma gashi wajen is roudy da mutane soaai, ga yan jaridu da yan rahoto kowa yana rike da camera.
Mark daya karaso wajensu cikin sauri ya gaishesa sannan ya gaisheta itama, kafin daga bisani ya shaida ma taj din is better idan suka saka mask a fuskansu saboda masu daukan rahoto, yace mashi no need for that, don shi yana sanye da black shade a fuskansa su kuma attention din su ba a wajensu yake ba.

Daidai nan wata katuwar mota bullet proof ta shigo harabar wajen da motar police na biye da ita har kusan guda biyar.
Aykuwa kamar jira suke masu daukan rahoton suka nufi wajen da sauri, police din suka zagaye motar, kai kace wani hamshakin criminal za a fiddo daga ciki.
Sabeeha dai zuba idanu tayi sosai tanason ganin waye zai fito daga cikin motar, bata gama nazari ba wasu mata masu sanye da kayan hukuma suka fito, da wata mace a tsakiyarsu an saka mata mask a fuskanta an rufe, take masu rahoto suka fara dauka da masu jefa tambayoyi…
Saboda yanayin tsaro yasa aka wuce da ita ciki, daidai nan kuma wata motar ta kunno kai zuwa harabar wajen, sabeeha bata lura da motar ba tana daga tsaye saiji tayi an kwalo mata kira.. dagowan da zatayi idanunta ya sauka kan barad da uncle jamid sai kuma khaal da mutallib.
Barad ya taho da gudu ya rungumeta har glasa din fuskansa na neman faduwa tsabar murna, cikin sauri itama ta rungumeta sosai farin cikin data ji ya lulubeta ya bayyana a fuskanta …
“Aunty fatima….”
“Barad….” Ta kira sunansa, ya dubeta kamar zaiyi kuka, “where have you been?? I missed you alot”
“I missed you more…” ta sake rungumeshi daidai nan su jamid suka karaso, ta kasa rike hawayen dake saukowa a fuskanta tsabar murna, uncle jamid take gani a tsaye ya samu lafiya ga khaal kuma ta tabbatar ma idanunta bai mutu ba….
Inda khaal ke tsaye ta tunkara tana sauke kanta kasa tana hawaye, she’s speechless gaba daya.
Khaal ya dafa kanta ta dago da sauri..
“Marhaban fatima…ina farin ciki da dawarki cikin rayuwarmu… allah ya maki albarka..”
Still kukan take bata iya cewa komai ba sai daga bisani kuma ta goge hawayen suka gaisa, ta maida dubanta ga uncle jamid daketa murmushi tace
“Uncle jamidd..ka samu lafiya?“
Suna cikin magana mark ya shaida masu time yayi wannan yasa suka nufi ciki.
Itafa har zuwa lokacin bata gane meke wakana ba ta daiga prosecutors da lawyers, da suka shiga court room din, anan ta tabbatar da shari’a zaayi.

Note!! Bansan ya ake shari’a ba so please bear with me.

Bayan an rufe kofar court room din aka gabatar da shari’a as the final day of judgement, da opening statement din trail din, lawyers din dake kariya na daga zaune haka zalika prosecutors.

Dago idanunta da zatayi kenan idonta ya sauka kan hidaya…dake zaune a gaba gaba wajen inda aka tanadar ma witness, ga lawyer a gefenta dGa dayan side din kuma wadda aka shugo da ita ne da mask daxu, cikin sauri ta juyo ta kalleshi haka zalika shima ita yake kallo, gaba daya ta nemi shiga shock ya kamo hannunta ya rike yana mai calming dinta down, yasan yanxu ta shiga confusion amma komai zai warware akan idanunta.
Judge ya buqaci a shugo da second witness wanda ya kasance shine accomplice din offender, daidai nan aka shugo da black da cuffs a hannunshi da kafafunshi gaba daya.

Bisa ga hujjar da aka gabatar da long term shari’ar da aka yi da investigation da akayi presenting sai kuma accomplince daya bada shaidu daya gamsar da judges din a dai dai nan aka yanke hukunci..
“I hereby declare The offender ms fadwa abdulbasit, found guilty of 3 charges, attempted murder twice, murder”
Daga nan kuma aka yanke mata hukunci kisa ta hanyar rataya wanda ya kashe a kashesa koda kuwa ubanta ne wanda ta kashe din.

Sai a yanxu sabeeha ta soma gano inda kanun zancen ya dosa a daudai lokacin kuma fadwa tayi saurin miqewa ta fuzge mask din dake kan fuskanta ta soma ihu, tana denying allegations din da ake mata.
judges din suka umarci tayi shuru amma inaa kamar wanda tayi karamin hauka.

Ita kuma hidaya aka yanke mata hukunci shekara biyu a prison na kidnapping abdallah datayi ba tare da wani kwakwararan dalili ba matsayinsa na civilian sannan aka wanketa daga allagetion din da ake mata na kashe khaal da fadwa tayi yunkurin yi bayan ta boyeshi na tsawon shekara guda gudun karya tona mata asiri, kai abubuwan da tayi da yawa, charges din nata ba daya

106 / 107