Advertisements
Chapter 25 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   25 / 107

72K to 75K   out of 320.4K words

bai yarda da ita ba.
“Fatima!!!” Ammu ta kirata, “nasan tunanin da kikeyi, inaos kisan wannan abun ba haramun bane agareki harma dashi saboda ke matarshi ce, dalilin dayasa na kawo wannan maganar kuwa shine, idan kika samu cikinsa komai zaizo mana da sauko fatima, koda kuwa ya gano gaskia abun zaizo mana da sauqi, ke kanki rayuwarki is secured around him, bazai taba bari a cutar dake ba, at the same time allah zai nuna mashi komai,fatima yaron nan maraya ne, ya taso cikin kadaici da maraicin uwa da uba, yaronnan tun yanada shekara biyu ya rasa uwarsa, an rabashi da uwarsa, baisan dadinta ba, baisan kamshin uwa ba balle duminta, inaji a jikina kece zaki bashi farin cikin daaka danne mashi, nayi imanin khaal bai zabeki a matsayin matarsa ba don ki cutar dashi saidan ki zame masa alkhairi,”

Dan dakatawa yayi da karasa shugowa kitcehn din, jin abunda ammu ke fada, bazaka taba iya tantance yanayin da yake ciki ba kwata kwata, futawarsa kenan ya farka daga barci bai ganta ba ya kasa sukuni, harya futo daga wanka ya shirya babu motsinta wannan yasa ya futo don ganin me takeyi.
Maida dubanshi ya sakeyi da kofar shigowa part din, daidai lokacin daya futo ya kura da giftawar abu a wajen kamar mutun saidai bazai iya tantance koma menene ba.
Sauke ajiyar zuciya kawai yayi yana nanata maganar ammu aranshi, “fatima yaron nan maraya ne, ya taso cikin kadaici da maraicin uwa da uba, yaronnan tun yanada shekara biyu ya rasa uwarsa, an rabashi da uwarsa, baisan dadinta ba, baisan kamshin uwa ba balle duminta, inaji a jikina kece zaki bashi farin cikin daaka danne mashi, nayi imanin khaal bai zabeki a matsayin matarsa ba don ki cutar dashi saidan ki zame masa alkhairi,”
Iya daidai nan allah ya bashi ikon jin maganganun ta daya taba mashi zuciya, tabbasa dukda abunda ake tuhumar khaal dashi yanaji a zuciyarshi akwai wata a kasa, ya kasa yarda kwata kwata, kuma duk yanda akayi akwai wata a kasa, this story is unfold, and its time for him to decide on finding out his instincts.
Cikin hanzari ya koma daki ya dauki wayarshi ya fara dialing number dayayi dialing da gym buddy, ana dagawa suka gaisa cikin kamala kafin ya soma magana…” uhm pleasei need a favor”
“Okay sir..just say it”
“Please do you know anyone from SCID? (Saudi Crime investigation department)”
Shuru mutabblib yayi yana sauraron sa, jikinshi na bashi yanason ya fara buncike ne.
“Yes sir..but is everything okay?”
Shima dai dan dakatawa yayi, yana contemplating yayi conversation din da mutabblib din ko karyayi saidai kuka bazai iya shuru ba don mutabblib ne kawai mutun daya sani anan haffaen dan kasar, shima ma, abocin abota ba, rayuwar gaba daya ba a nan yayi ta ba, mutabble is the only person da zai saka cikin maganar nan”
“Meet me at that mini ba in 2hours”
“Yes sir” mutabblib ya amsa shi cikin respect.
Kashe wayar taj yayi yana jujuyata,iyalan khaal ne suka zo mashi aranshi, how can he locate them? Yanason ya gansu, he definitely wants to have a conversation with them.
Da sallama ta bude kofar ahanankali ta shugo cikin kamala, kanta a kasa ta ruko dan mini tray, sanye take da doguwar riga mai kyan gaske daidai jikinta ta dan kamata don ga shape dinta ya futo nan, shes so small yet so attractive, well shaped and curvy, sai wani irin glowing takeyi,dago da fuskanta tayi ta sauke akanshi, nan take idanunsu ya sarke dana juna yayi saurin dauke nashi, irin kamar an kamashi dinnans
Takowa tayi cikin natsuwa ta karaso inda yake ta ajiye mashi coffee din gefen bedside kafin ta dan duka cikin ladabi tace “sabahal khair”
Daga yanayin yanda take magana da yanda jikinta yayi sanyi ya tabbatar mashi da akwai abund ake damunta arai, yayi mamakin yand aya karance ta tass, kuma yaji a jikinta tabbas haka dinne, muryarta ta kaste mashi tunanin da yakeyi, “ga coffee bismillah”
Tana fadin haka ta juya zata bar wajen ta dakata jin muryarshi, “bibi….”
Dam gabanta ya bada jin sunan da yake kiranta dashi a baya for the first abakinshi ayanxu, take taji gabanta na faduwa kamar zatayi hawaye, ashe bai manta ba, Kuma sai taji kamar exactly yanda yake kiranta da sunan abaya yayi ayanxu, ahankali ta juyo, idanunta na tsatsafo da hawaye, tunawa da maganganun ammu akanshi, ashe maraya ne, daman she keeps wandering ina shi mahaifiyarshi? Meysa yake rayuwa tsakanin waenda basa qaunarshi.
Nuni yayi mata data zo, ahankali ta soma takowa daidai wajen kafafunshi daya sauke a kasa don zaune yake kan gado ta zauna a kasan tana mai kallon doguwan kafanshi, mai yatsu zara zara farare tass,kanta a kasa
ta kasa cewa komai, shima ya rasa me zaice mata,
Da mamaki ta dago jin abund aya fada “daga wace kasa aka kawo ki nan? how did you end up here?“
Bakinta na karkarwa ta soma amsashi, “daga nigeria nake,”
Shuru tayi bata sake cewa komi ba saida ya sake jefo mata tambaya, “ how did you end up here?”
“Aiki nazo yi,”
“Why? What was the reason??” Ya sake jefo mata tambaya, she the fact that yar aiki ce ita abun yana bata mashi rai sosai, shi he don’t like the idea of turo yara aiki kwata kwata,
Rasa amsar da zata bashi tayi, toh mema zata ce mashi? Mamanta ta turo ta aiki? Saboda dalilin da bata sani ba? Ko mamanta ta saida ta zuwa wata uwa duniya da batasan kowa ba sai Allah?.
“Waya kawoki nan?i want to know everything….”
Nanma shurun ta sakeyi tanata saqawa tana warwarewa da zuciyarta, me zata ce mashi yanxu? Abu daya tayi ma zuciyarta alkawari, cikin any conversation dinsu bazata taba yi masa karya ba, karyar datayi masa na wannan cikin ma kadai ya isa wannan yasa ta nunfasa ta soma mashi bayani.
“Shekara daya da rabi da suka wuce aka kawo ni garin nan, ta hanyar kamfanin dake kawo ma’aikata, domestic workers agents, nayi aiki a gidaje uku wannan ne na hudu,…, kamfanin ne suka kawoni,lokacin danazo ni bansan aikin da zanyi ba, nadai san an kaini fannin kula da yara da kuma marasa lafiya,..”
Shuru tayi bakinta na karkarwa tanason ta fada mashi yanda khaal ya kawota gidan a matsayin yar leken asiri, saidai from the look of ever an gama corrupting mind dinshi, gashi kuma tuhumar da akema khaal, idan gar tayi kuskuren fada mashi komai zai iya tabarbarewa, yanxu ya zatayi? Zai yarda cewa yar leken asiri ce ita kenan, kuma khaal ne ya kawota, how can she explain everything to him?, duk sai tabi ta rude tayi zuru.
“Khaal ne ya kawoki gidan nan ba tare da saninki ba?
Wannan tambaya tashi ta girgizata sosai, at that point kawai amsawa da abunda zuciyarta ta fada mata zatayi, “eh da farko ban sani ba, amma daga baya…”
Dakatar da ita ya sakeyi, “why?..saboda kudi? Saboda dukiya da abun duniya? Why?”
Calmly yake maganar wannan yasa bata tsureba, kuma ta kasa yi masa karya, don yana karantarta tsaf.
“Ah ah,..”
“Then why? Give me damn reason..”
Ya dan daga muryarsa ganin taqi bashi amsar da yake nema gashi he’s eager to know.
“Wallahi tunda nazo gidannan banzo da niyar cutar da kowa ba, kuma aikin sa aka bani badan na cutar dakai bane, wallahi auren nan ma ba a son raina akayi ba, hasalima bansan da zancen ba sai a ranar,kuma wallahi khaal bai taba kudircewa cutar dakai ba, harya mutu, ni bansan dalilin dayasa ya maida dukiyarka karkashina ba amma wallahi nayi imanin baiyi dan ya cutar da kow aba saidan yayi protecting dinka, harya mutu kokarin shi bai wuce na ganin ka samu sauqi ba, ko aranar da akayi kidnapping dinmu shine ma yasa jamid ya kaimu inda ake maka therapy kuma..kuma shine…”
“Therapy? What therapy wani kidnap din?” Saurin miqewa yayi tsaye, wato dai akwai abunda bai sani dinba,
“Aranar da akayi kidnapping dinmu nida kai munje monthly therapy din da ake kaika, uncle jamid ne ma ya kaimu, bayan an gama mun fito sai muka shiga motar da mukazo da ita, kwata kwata bamu lura ba uncle bane ke tukin motar, daga nan bamu sake sanin meya faru ba, har saida muka farka cikin kasa, kwananmu daya a wajen,…”
Tana fada memory din abun na zuwan mashi, kwata kwata batayi gigin fada mashi komai gameda abunda hidaya da yan uwanta sukeyi ba, tayi imanin ba huruminta bane wannan kuma idan tayi gaggawar fada mashi zai iya zame mata matsala, amma idan ta fada mashi waennan abubuwan dole zai dasa aya akan maganganun ta.
Said ata gama labarta mashi tass iyakacin abunda ta sani kafin ta dakata, lokacin fuskanta yayi jeme jeme da hawaye.
He has not gotten his answers yet, he needs more of this information, kuma he can sense akwai abunda taqi fada mata masa, musamman abund aya shafi rayuwar da yayi a cikin gidannan da yan uwan nasa.

Kallon agogon hannunshi yayi ganin its over 2hours wannan yasashi kwasar wayoyinsa gaba daya ya fuce daga dakin ba tare da ya sake waiwayobta ba.

Driving yakeyi cikin natsuwa, cikin abunda baikai minti ashirin ba ya iso mini bar din, tunda ya fara drivinv yake nazarin maganganun fa sukayi shida ita, maisa maganganunta suka banbanta dana hidaya akan abundata fada mashi?meysa yakeji nata is adding up akan na hidaya?kodai zuciyarshi wasi wasi take mashi? First of all he needs to find out komai akan allegation din da akayi ma khaal.

Cikin kamala ya shugo bar din, daga chan nesa mutabblb na hangosa ya daga mashi hannu wannan ya bashi damar tunkarar wajen, yana karasowa ya ja kujara ya zauna.
“Barka da zuwa sir..how was your weekend”
“Hamdullah!”
Kawai ya amsa mashi dashi kafin akawo masu abun dan tabawa da mutabblib yayi order.
Yan danne danne taj yayi a waya kafin ya juyo da wayar saitin mutabbl kafin ya soma magana.
“Nasan kasan wannan scandal din about a year now ko?”
Dam gaban mutabble ya bada ganin rahoton khaal na mutuwarshi da abubuwan da aka zargeshi dashi, gaba daya sai hankalishi ya kaiga taj ya gano shine yaron khaal din,
“ thats my uncle…bana kasar lokacin da abun nan ya faru, so inason nayi bincike ne akan mutuwarshi,and i want to know about allegations din da akayi akanshi.”
Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya suake, kafin ya fuskanshi taj din yace “akwai wanda na sani a CID, and i think hes the one who worked on this case, zan iya karba maka all of the necess information da zaka buqata akai”
“Masha allah, i will be glad.. “
girgiza mashi kai kawai mutabblib yayi kafin ya dan nunfasa yace “so he’s your uncle…wow.. wait hold on.. that means..”
“Taheel.. yes Tajudeen Taheel” taj ya amsashi kai tsaye.
“Wow what a small world, ashe kaine the only heir na taheel kamfanin, ban taba tunanin zan hadu da someone powerful ba, no one can teel you are that person, but amma im so curious about something”
Kallonshi sosai taj keyi don jin abunda zaice,
“Why do i feel like something is not right akan wannan uncle din naka da akece yayi waennan laifukan?”
Daga mashi gira daya taj yayi don jin abunda zaice,
“We all know the crises of a family business, it got to be from 2 parties aiming for the seat, idan har he’s fighting for the shares to be his then definitely they got to be the order party whos aiming for the shares as well, im sorry to say this..”
Wannan magana da mutabblb yayi sako ya aika mashi a fakaice, kuka tayi tasiri a zuciyarshi don tuni ya fara nazari.
“Please i want this to be between us..”
“Baka da damuwa sir..amma please karkace na fiye tambaya kamar dan jarida lols…, akwai lokacin da akace the only heir of taheel ya samu tabin hankali, i even have the press conference..” yana kaiwa nan ya fiddo da wayarshi ya kunna press conference din da hidaya tayi a daidai lokacin da aka dunga yada cewa taheel heir ya samu tabin hankali.. cikin hanzari ya kunna ya tura mashi gabanshi.
Kallon video taj ya somayi, jijiyin kanshi sunyi rudu rudu, saida ya saurara kaf abunda ta fada, “heir of taheel bashida hankali, ya samu tabin hankali kuma he can not run the company family babu yanda za ayi a bama wanda bashida hankali wannan reponsibility din”
Aranshi ya fara wasee wasee da maganganunta, hidaya ta fadi haka da kanta? At firts he couldn’t believe din said ayaga tabbas online ne akayi post din about a year ago,.
Wani irin murmushi kawai yayi, yana mai kallon mutabblb din yace “thats true, i had an amnesia that time”
Ba haka mutabblb yaso ji ba, don kirikiri kana gani zakaga manufarta a cikin maganganun datayi, daman yasan it will very hard for him to start believing on this, amma atleast yanxu dai ya nuna mashi daga inda problems din suke, it got to be from the company, shiyasa ma ya fara mashi maganar khaal dazu kafin yayi maganar wannan ayanxu, dole yasan zaiyi tunani akan wannan.

Achan gida kuwa yana futa dakyar ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskanta, tana gamawa ta futo zuwa kasa don shaidama ammu maganganun da sukayi, tana futowa daidai nan barad ya futo daga part dinsu, yana ganinta ya taho da gudu inda take cikin murna, “anty…”
“My barad…how are you? I missed you? Meysa bana ganinka?”
“Anty bibi, i came back yesterday, munje school vacation”
“Ya dadyn ka?”
Tana fadin haka ya soma jan hannunta, har zuwa part din jamid din, yau kusan wata nawa rabonta da ganinshi, saboda anyi masu iyaka da shi, cikin dakin suka shiga har gabanshi suka tsaya, yana barcinsa kamar kullum, ta dade sosai tana kallonshi tana masa adduar samun lafiya aranta kafin su fito ita da barad din,
“Kaje kar mummynka ta ganmu tare kartayi maka fada”
“Bata nan ay, she travelled”
Da mamaki sabeeha ke kallonshi, shiyasa taga ya futo ashe, ita rabondata sanyata a idanu ma harta manta, kwanciyar hankalinta ne ma saboda dataga fuskar hidaya nan gabanta ke faduwa.
A tare suka sauko kasa wajen ammu, dake yan gidan yau karkaf basa nan saisu kadai wannan yasa sukasha hira sosai, barad dinma ya sake shima abunshi.

Misalin wajen karfe biyar suka shiga kitchen da ammu da sabeeha garda barad dinma, gaba daya ma’aikatan gidan ammu ta kora suka koma bangarensu, nan sukayi dinner lafiyayye.

Ana gab da magrib ammu tasata taje tayi wanka, don sun dade a kitchen din, ay kuwa taba hawa sama tayi wankanta fess fess ta nado jikinta da towel sannan ta futo,gaba daya hankalinta na gareshi, tunda ya futa wajen karfe sha biyu,fatanta dai allah yasa yana cikin koshin lafiya.
A gaggauce ta wuce closet room tana zuwa ta fara kokarin neman abunda zata saka, wata rigar ta jawo mai dan gajeran hannu ta saka rigar har gwaiwa take saidai tanada wando dogo mai kamawa.
Yaudai she just feel like ta saka bra, wannan yasa ta janyo bra da pant, saida ta mulke jikinta da turaren da ammu ta bata mai karfin nan kafin ta fara kokarin zame towel din dake jikinta, da mamaki take kallon din ganin dan jini jini, take gabanta ya fadi, daman daxu datake haurowa sama ta dan soma jin kafarta na zugi, those that mean period ne? Innalillahi wa inna ilaiagi rajiun, ya zata yi yanxu? What will she do?”
A gaggauce ta nemi pad a bathroom ta saka sannan ta saka kayan data fiddo, towel din kuma tayi gagagwar wanke shi tass sannan ta shanya kafin ta fito.
Tana fitowa daidai nan ya budo kofar dakin, kana ganinta gaba daya kaga mara gaskiya, cikin hanzari ta sauke idanunta, “sannu da dawowa” ta fada ahankali, batayi exeocting amsawashi ba saiji tayi yace “thanks” kafin ya gifta ta gefenta ya shige closet room yana mai shakar wannan kamshin dake fuzgar sa…

Bai wani dade ba cikin closet ya futo daure da towel a kugunshi, ya shige bathroom kai tsaye.
Tana ganin shigewarsa ta koma ciki tabtattare kayansa daya bari akan table din dake tsakiyan wajen, kayan basuyi wani datti ba haka ta sanya su cikin laudry basket, har zata futa wata zuciyar ta ingizata da fidsa mashi kayan fa zaisa na zaman gida,aikuwa ta fidda mashi su ta ajiye mashi sannan ta fito daga dakin.
Kasa ta sauka direct dakin ammu nan ta taddata zaune, “kin sauko,”
“Eh..”
“Ya dawo ne?”
“Eh yanxu..”
Kallonta ammu tayi ganin tana kame kame, “yadai fatima? Is everything okay?”
“Uhm..ammu period ne yazo kuma ina tsoron karya..”
Murmusawa ammu tayi kafin tace, “bazai ganeba insha allah, muje muyi dinner”
Atare suka futo, hakiman gidan duk sun zzzauna dare dare, banda hidaya datayi tafiya, tun kafin su karaso duk wanda ke wajen ke kallonta kamar zasu cinyeta, daga masu harara sai masu wulla mata mugun kallo, wasu kuwa dadin ganinta sukaji don ta hanyar nan ne kawai zasu cimma kudirinsu akanta na ganin sun zubda cikin nan.
Kallonta ammu tayi tace “jeki kirasa”
Juyawa sabeeha tayi jiki a mace ta koma saman, tana bude kofar ta taddashi zaune, ya saka kayaj data ajiye mashi, sautaga wani irin kyalli ma yakeyi saboda gyaran fuskan da yayi, takowa tayi inda yake kafin ta danyi gyaran murya.
“Uhm..ammu tace muje muyi dinner a kasa”
Dagowa yayi ya kalleta, ganin ta jujuya hannu kanta a kasa, baice mata kala ba haka zalika bai tashin ba itama bata motsawa ba saida ya dauka wajen minti biyar kafin ya tashi tsaye, ya nufi hanyar futa tabi bayanshi, ahankali yake tafiya tana biye dashi saiya zamana kamar atare suke tahowa, yana tunkarar wajen kowa ya dago yana mai kallonshi, fadwa ce ta riga kowa wulla idanunta gareshi saiya zamana idanunshi ya shiga nata, wani irin mugun kallo ya mata kafin ya kauda nashi idanun, sonata kuwa kamar ta cinyeshi, wajen daya saba zama ya nufa bayan ya shafa kan barad daya gaishesa sannan yaja kujera ya zaune ya gaisheda ammu, tareeq ko tsohon maye, tunda sabeeha ta shigo dazu yake bunta da ido, har allah allah yake ta sake dawowa ya ganta, ya dade bai ganta ba kwata kwata, shi alamarinta ma ya shafe shi, dake gaba daya zuciyarci ta kazance da lalaci wani irin mugun shawanta yakeji yanxu haryafi nada, kwadayinsa akanta ya tashi sabo fill, saboda ta chanza gaba daya kamar ba ita ba. Fadwa na ankare dashi, saima murmushi kawai datayi tana nazarin abunda take kulla wa wajen amfani dashi, daman yanxu

25 / 107