Advertisements
Chapter 86 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   86 / 107

255K to 258K   out of 320.4K words

hadiza, marasa dadi da yasata ta yarda, dubaga abubuwan dataga hadiza kema yarinyar, abunda yasa ta kara yarda ma shine ranar da allah yayi zataji wani conversation din da maya sukayi da hadizar inda hadiza ke fadama maya ay sabeeha ba yarta bace, da farko bata dago kan zancen nasu ba don suna tsaka da yin maganar tazo dakin, harta bude kofa basu san da mutun a wajen ba, abun ya tsaya mata arai lokacin ta kasa gane inda zancen ya dosa sai a yanxu ta gane, dalilin da yasa ta yarda da zancen jamilar ma kenan, yanxu kuma Saita shiga confusion ganinsu tare.

Suna shiga daki hadiza ta wani rufo kofar rufo, jamila ko aka baje kan gado ta wani turo daurin nata gaba dakyau.
“Kai wallahi nasha wahala jiyan nan, ke wallahi badan ke ba wallahi bazan je wannan kasurmugun dajin ba”
Washe baki hadiza tayi ta zauna tana fuskantar jamila tace “allah yabar min jamila”
Suka wani tafa, “ke ay ni kasa barci nayi jiya wallahi da ban jiki ba, na kira layinki ma kwata kwata baya shiga” hadiza tayi mgana
“Yoh ina zakiji ina chan inda babu service” ta karashe tana bude jakarta.
Gyara zama hadiza tayi kafin tace “toh yaya???? Na matsu wallahi naji yaya? An fara aikin?”
“Haba waa kinsan bana wasa hadiza,” jamila ta fada tana fiddo da wata leda da wasu layu guda biyu kafin, hadizq ta wani washe baki, “aiki ne akayi babba, kuma wallahi wallahi ba karamin aiki bane, matso kiji”
“Kinga wannan?”
Ta nuna mata layar tace “wannan layar bakar ajiyace, ba a yi mata ganganci, ba a ajeta sai an daidaici awannin da ko wanne mai nunfashi ke kwanciya, zaki ajeta a kasan abun kwanciyarta da kika tabbatar zata saka kanta a wajen, da zarar ta aza kanta babu ita babu nunfashi…Kamar yanda kika buqata a yau yau dinan zaki shafe labarinta cikin sauqi”
Baki bude hadiza ta karba, wani irin dadi ya lulubeta,”kai jamila dame zan saka maki?kin biyani da komai”
Kallonta kawai jamila tayi a bayyane tana murmushi a zuciyarta kuwa ita kadai tasan abunda take qissawa.
Dayar layar jamila ta miqa mata tace “wannan ta mallaka ce da kikace kinaso,amma baki fada min me zakiyi da ita ba”
“Kema kinsan in na buqaci abu dole akwai dalili,”
“Dalilin kanki ne kona diyarki?, hmm tunda nake zuwa baki taba hadani da ita ba naga yar tamu yanda ta girma”
“Hmm tana chan bangaren shegiyar nan”
“A gaskia ya kamata na ganta nima,”
Wani irin kallo hadiza ta mata tace “zaki ganta karki damu jamila yanxu dai mu kauda wannan dmauwar tamu tukunna”
“Haka fa, yauwa ga wannan ma,”
Ta dauko wani kullin baqin gari kamar charcoal ta miqama hadizar,
“ wannan garin, bakar guba ce mai hadari,”
“Shima wajenshi kika samo??” Hadiza ta tambayeta tana karbar ledar.
“ah ah wannan tawa gudumawar ce, kinga wannan abar da ita nayi amfani wajen…kauda wannan tsohon mijin nawa cikin sauki, sai ganin gawar shi akayi kawai, a ruwa ake zubawa ko a lemon, da zarar mutun yasha cikin abunda bai wuce minti talatin ba saidai a bada tarihin mutun wallahi,”
“Kaiiiiii…ke ko wannan zan bata ne ta fara sha kawai?”
“Ay duk wanda yafi maki sauqi kawai kiyi amfani dashi, shiyasa ma na kawo maki solution biyu”
“Kai jamila allah yabarni dake, wallahi banida kamarke jamila, kin gama min komai,“
Dan murmusawa jamila tayi tace “ameen, in kina dani bakida case, zadai a bani tukwici dai ko?” Tashi tsaye hadiza tayi ta kama gefen zaninta ta qulle layar da kullin maganin kafin tace 
“Sosai ma kuwa bari na kawo maki lemo da ruwa ki kashe kishi”
Tana kaiwa nan ta miqe tsaye, ta futa daga dakin, kitchen ta shiga ta hado mata lemo da ruwa sannan ta futo, ta tunkari dakin,daidai nan maya ta futo daga bedroom din nata, daman ta shiga nemanta bata ganta ba,tuni hadiza ta soma washe baki, “hajiya karama, kwana biyu bkaya nemana albishirinki?”
Hannu maya ta daga mata ta dakatar da ita, don yanxu batada time din shirmen wannan matar, “kinga ba surutunki ya sauko dani ba, ki turomin wannan yarinyar zata gyara min part dina”
Jiki na rawa hadiza tace “toh!! Toh!! Yanxu zata zo, ay in gaya maki na samo..”
Tuni ta wuceta vata tsaya sauraronta, dakin hadiza ta shiga, jamila na daga zaune tana taunar chewing gum, hadiza ta aje mata lemo a kasa.
“Hala wannan ma yar masu gidan ce ko?”
Dariya hadiza tayi kafin ta mata rada a kunne,
Tuni jamila ta gwalo idanu,  tace “ke da gaske?”
Hadiza tayi dariya kafin tace “Wallahi kuwa…”

“Masha allahu burinki ya cika hadiza”  ta fada a bayyne a cikin zuciyarta kuwa babu abunda take sai tunanin yanda mayar ta shugo daki, kana ganinta kaga futsararriya kangararriya, kuma idanunta a bude yake, babu ladabi da biyayya balle girmama na gaba, dan ko kallon mutunci batayima jamila ba.
Suna cikin magana wayar hadiza dake ajiye gefe tayi ringing, tama dauka ko maya ce ke kiran tana ganin mai kiran tayi saurin daukar wayar ta kalli jamila tace “ina zuwa”
Tana fadin haka ta futa, jamila ta bita da kallo.
Dakin da sabeeha ke zama ta shiga kai tsaye, bin ko’ina ta soma yi da kallo ganin dan kwalin sabeeha gefen gadon, tasan yanxu basira bata kwana anan so basically sabeehan ce kawai a dakin, daidai nan sabeehar ta futo daga bathroom, tana ganin hadiza tayi saurin karasowa inda take kanta a kasa, “ay namayi kokari dana barki har kikakai e yanxu, bazan bari ki bata min shiri na ba, ko ki shiga tsakanina da yata, zuwanki duniya da haihuwar ki a banza,” duk a cikin ranta take wannan maganar.


“Wuce kije sama bangaren maya ki gyara mata shi tass yanxun nan”
Da toh ta amsa mata sannan ta dan raba gefe ta futa daga dakin, hadiza na tsaye saida taga futanta sannan ta aje wayarta gefwn gadon sabeehar ta fidda kullin datayi ma layun da ledar, haka ta dauka layar nan ta daga pillow sabeehar tasaka a ciki sannan ta aje pillow din, tana ajewa ta sauke ajiyar zuciya, ko irin dar dar dinan bataji kwata kwata, Rashin imani kenan zuciyarta ta rigada ta koma baqa, bata da imani ko digo daya.
Tana kokarin daukar wayarta da sauran abubuwan nata wayar ta sake ringing, “kai wannan wani irin naci ne”
Ta fada tana dagawa takai kunneta, “dan allah ka daina kirana a daidia lokacin da bai kamata ba, yanxu dana bar wayar da adaki jamila ta dauka fa?”
Jamilu najin ta ambaci jamila yayi saurin cewa “tamu ta kare hadiza, shikenan,wallahi jamila bazata barki ba”
“Ban gane ba me kake nufi?”
“Jamila ta san muamalar dake tsakanin mu hadiza, kuma ta dauki alwashim saita dau fansar cin amanarta da mukayi, da alamu dai ta cin maki don wallahi bazata barki ba”
“ ka natsu kamin bayani.. me kake nufi?”
“Ke bkya kwashewa ne? Ta san komai, ranar da kikazo ta kamamu,kuma dazu da bakinta ta fada min bazata barmu ba dagani har ke, ke kuma ina kiranki bakya dagawa”
“Kana nufin jamila tasan muamalarmu?”
“Kunnanki nawa ne hadiza??? Kinfi kowa sanin jamila wallahi bazata barmu ba,saiki shirya”

Take gaban hadiza ya wani bada damm, tayi shiru kanta ya kasa processing komai, idan har maganar da jamilu ke fada gaskia ne tabbas jamila bazata zauna haka ba, dole saita dau fansa don tasha fada mata abu daya ne zaisa ta tona mata babban sırrınta, idan har ta sake taci amanarta, ay bata taba tsammanin ta jirga shirme ba na biyewa jamilu da son zuciya sai yanxu, kar tasan kar ne ita da jamila, bazata taba barinta ba, jamila annobar macijiya ce, zata iya kai mata sara ta bayan fage don makirace ta karshe ta iya makirci, dole ta kauda jamila kota halin qaqa ne don sirrinta ya rufu, don idan ta tona mata asiri shikenan ta gama yawo.

Gaba daya saita furgice, Ay batasan sanda ta katse wayar ba, jikinta na rawa kamar tsohuwar kamu, kallon baqar gubar dake hannunta tayi, batada wani shiri dole saidai tayi amfani da abunda take dashi, yanda ta mata fuska biyu ta nuna kamar batasan cin amanarta suke ba ita da jamilu haka zata mata itama, zatayi amfani da wannan damar itama takai mata sara.

Jikinta na rawa ta futo daga dakin zuwa dakinta databar jamila, tana shiga taga wayam, take gabanta ya wani bada damm, dagowar da zatayi kuma saitaga kofar bandaki adan bude sai kuma karar saukan ruwa dataji, tuni ta sauke ajiyar zuciya cikin sauri ta dubi lemon da jamilar bata taba ba, ta dubi kofar toilet din, kafin ta maida hankalinta ga lemon, cikin sauri ta soma kunce zaninta inda ta kulle baqar gubar nan ta fiddo da ledar sannan ta bude, hankalinta na ga kofar tana sauri ta maido da dubanta ga lemon ta zuba gubar a ciki, lemon kwali ne wannan yasa ba a ganin abunda ke ciki, tana gamawa ta girgiza lemon sannan ta ajeshi sannan ta soma kokarin kulle ledar daidai nan taji saukar ruwan fanfon ya tsaya, tsabar rudu saida ledar ta fadi cikin sauri ta dauko daidai nan jamila ta futo daga bandakin, ta mata kallo daya ganinta a furgice, sai kawai ta sauke murmushi, lallai sai yau ta tabbatar hadiza jaka ce ta karshe, “kin dawo?” jamila ta fada tana karasowa bakin gadon.
“Eh… ashe kina bayan gida,”
“Wallahi daman a matse na shugo gidan ne”
Yaqe hadiza tayi sanan tace “ga ruwa ga lemo fa”
“Ay kuwa bani na kora makoshi na”
Cikin sauri hadiza ta miqa mata kwalin lemon, “babu kofi ne na yan gayu na tsiyaya?”
“Kedai kawai ki kafa baki kisha, wake ta kofi? Ni wani sa’in ma nafison inasha daga kwalin” ta karashe tana murmushi, allah allah kawai take tasha.
Jamila ko aka gyara zama aka bude cover juice, hankali kwance ta daga takai kurba daya, sanyin lemon ya ratsa ta ta sake kurba, hadiza ko kifta ido batayi ba tunda ta kafe jamila, sai kawai ta sauke wani murmushin jin dadi, “tunda kika gano abunda ke tsakanina da wanchan lusarin mijin naki nasan abu na farko da zakiyi shine yunkurin tona min asiri, ni kuma bazan taba bari ki bata min shiri na ba tunda har nakawo wannan matsayin,daga ke har ita idan na kaudaku banida sauran matsala” hadiza ta fada a zuciyarta
ganin irin kallon da hadiza ke mata yasa tace “Yaya dai wannan kallon da kikemin??”
“na tuna yanda muka taso ne jamila” hadiza ta bata amsa
“Haka aka ganmu kuma haka za a barmu ba”
“Kina ganin mai zai bata wannan amincin namu? Jamila?” hadiza tayi magana tana kallon ta
Sake kora juice din jamila tayi kafin tace “cin amana, kinsan yanda na tsani aci amanata, indai bazakici amanata ba toh bakida yar uwa sama dani”
“In kuma naci amanar taki fa??? “
Chak jamila ta dakata da shan juice din, ta kure hadiza da ido babu kiftawa, yanayin fuskanta ya sauya tace “ke kinsan me zai biyo baya,bana yafiya, musamman idan aka shiga gonata da bai kamata a shiga ba”
“Zaki iya kasheni kenan???”
“Kafin na kasheki saina dandana maki zafin radadin cin amana a bakinki tukunna” tana kaiwa nan kwai ta fashe da dariya, kamar batasan komai ba, yanayinta ya sauya zuwa normal tace “ay nasan ma bazaki taba cin amanata ba ko hadiza?, mubar zancen nan ma, ke kinsan ni da zafi”
hadiza dai mamakin dadin bakinta take da yanda take mata fuska biyu, da gayya ta tambayeta idan taci amanarta me zatayi, bariki kenan, yanxu badan tasan halin jamilar ba da abunda zata iyayi ay bazata taba yarda da ta gano taci amanarta ba.




Shuru hadiza tayi bata ce komai ba saida jamila ta sake dagowa taga ita take kallo cikin ido,da alamu ma nazari takeyi da tunani, yanayinta bai sauya ba kwata kwata.
sai kawai kuma ta fara tafa hannayenta biyu tana kallon jamilar,
“hmm jamila kenan, jamila bakar kunama dafinki yafi harin ki zafi, toh Wasan kwailwayon ya isa haka,…badan na iya takuna ba saiki hallakani ta fuska biyu,” tana fadin haka ta miqe tsaye jamila ta bita da ido, irin bata gane ina zancenta ya dosa ba.

takowa hadiza tayi zuwa gefenta ta zauna kafin tace “Nasan kinsan cewa naci amanarki ammafa Karkiga laifina, nifa aminiyarki ce, munsan sirrin juna, sainaga ba laifi bane don munsan namiji guda daya, ni ban dauki wannan a matsayin cin amana ba da har zaisa kiyi tunanin zuwa nan don ki tona min aisirin da muka binne..kina tunanin zaki raina min hankali????? Hahah kin manta ni hadiza kenan? Nida akewa laqabi da kanwar shedan???Ni da ke Karr tasan karr fa jamila''

Tunda jamila ta kafa mata idanu ko kiftawa batayi ba,sannan bata nuna wani reaction basaida hadiza ta dubi kwalin lemon hannunta sannan tace ''a tunaninki zaki raina min hankali ko? sai gashi da hannun ki kin kawo min sauqin matsala cikin ruwan sanyi''

take jamila ta dubi kwalin lemon da take sha, tsoron da bai bayyana ba a fuskarta ya bayyana, jin kalaman hadizar, hannunta ya soma karkarwa ta dubi lemon datake rike dashi a hannun nata, batasan sanda ya sulale ba a kasa, kalar lemon ya koma baki, gashi dai taste din bai chanza ba, take ta gane cewa hadiza ta zuba mata bakar gubar nan a cikin lemo.
“……Ha..diza ni zakici amana????ni?”

“Ah ah banci amanarki ba,bazan bari ki ga bayana ba dole koni ko ke, jamila ke kin sani, ko ban kasheki ba nasan saikin tona min asiri na”
Tuni jamila idanunta ya soma ja ta fara kakarin amai, “gubar nan kika saka min???“
“Kwarai kuwa, jamila in ban kasheki ba bazaki barni ba, ni nafi kowa sanin koke wacece”
“Allah ya isa tsakanina dake…. Duk da kinci amanata banyi tunanin ksheki ba, sannan ban fasa nemo maki mafuta ba, amma ni zaki….” Ta kasa karasawa jin cikinta na wani murdawa, tana hawaye,”
“Da dai ban sanki bane jamila, bazaki taba kyaleni ba saikin dau fansa, allah ne ya bani sa’ar jifar tsuntsu biyu da dutse daya, kinada sauran minti ashirin daya rage maki, ina fatan zaki amfana da su”
Tuni hawaye ya wanke fuskan jamila harda majina, ta jawo mayafinta kamar mahaukaciya ta nemi futa daga dakin.
hadiza aka daura kafa daya kan daya, babu abunda take sai murmushi, tasan yanxu yanda hankalin jamila ya tashi dole makarin gubar zata fara nema, kuma tana da tabbacin kafin ta samu lokaci ya kure mata, don gubar bata wuce minti talatin a jikin mutun take kashesa,shiyasa ake kiranta da baqar guba.

***
Shugowar bahijja main house kenan ta soma jin ihu daya karade ya cika gidan gaba daya, hankali tashe ta dubi sama jin daga nan ihun yake, rabi ma tayi saurin futowa da sauri, bahijja kamar kafafunta zasu harde tsabar tashin hankali, tana haurowa ihun ya tsananta sosai wadda yasa gabanta faduwa don muryar maya dataji.


Rabi data biyota a baya tabi sahunta,cikin sauri bahijja ta karaso bedroom din don kofar na bude, take gabanta ya fadi dammm ganin maya tsaye, rike da hannunta ga jini na malala duk ya bata rigarta, ga kuma sabeeha a gabanta rike da wuka, jikinta sai kyarma yake hankalinta a tashe, komai ya faru cikin gaggawa ba tare da ta ankare ba.

maya na ganin shugowar bahijja ta sake kwala kara a gigice ta wani yi yuuu zata fadi bahijja tayo kanta jikinta na rawa, “innalillahi wa inna ilaihi rajiun'', gaba daya ta rikice lokaci guda don batasan takamaimai daga ina jinin yake ba.
rabi ta dora hannu a ka,hankali a tashe tace “na shiga uku ni rabi” a dubi sabeeha dake rike da wuka ga jini a hannunta.

Hankali a tashe sabeeha ta soma girgiza kanta tana duban hannunta dake karkarwa, ta kasa cewa komai don gaba daya jikinta ma rawa yake tsabar furgici.

“maya!!!!! Maya!!!  Meya samekiii na shiga uku innalillahi wa inna ialaihi rajiun….jinin menene wannan? meya sameki”

Maya dake wani kif kifta ido kamar wadda za a zarema rai,kai kace yanke mata wuya akayi ta daga hannu tayi nuni ga sabeeha dake tsaye in so much shock.

Bahijja ta maida dubanta ga sabeehar, “ita ce…kasheni zatayi..”

Tuni hankalin bahijja ya tashi ta saki mayar tayo kan sabeehar, tana karasowa batayi wata wata ka sauke mata lafiyayyin maruka kusan guda shida a jere both sides of her faces, bata hkura ba ta dago idanunta ya sauka kan wani wire ta zarota, tayo kan sabeeha dashi wadda ta sulale tunda ta wanketa da maruka, kamar wadda aka aiko haka ta dunga zabga mata bulalarnan, bataji bata gani,rabi me zatayi banda ihu, duk yanda taso ta kwace sabeehar ta kasa, yarinya ta nemi rasa nunfashinta maya ko daman zubewar karya ce tayi tuni ta tashi zaune tana murmushi, “hajiya ya isa, dan allah kiyi hkuri, karki illatata, tsautsayi ne”
“Yimin shuru rabiiii” ta dakawa rabi tsawa, “kafin ta kasheta ni bari na kasheta”
Rabi ta kara kai hannu zata karba igiyar ta sake daka mata tsawa “matsaaaaaaa!!!!”

Tana fadin haka ta sanya hannayeta biyu ta dago sabeehar da gaba daya wire nan ya soma fasa mata hannu da jiki ga shatin bulala, dake fara ce saita koma jajawur kamar jan kosai, ta wani irin fusgota kamar tana jan kayan wanki, rabi tayi saurin bin sahunsu,
maya ko ta miqe a guje ta bi bayansu itama, dazu ka ganta zakace batada sauran nunfashi, ashe daman abun nata drama ne.

Haka bahijja take jan ta har zuwa kasa, rabi nata roko amma bahijja bataji bata gani, bata saki sabeeha ba har tsakiyar compund din gidan, tana sakinta ta soma kwaloma securities kira, dima diman sojojin dake tsare gate, aiko sai gasu radada su uku sun taho,
bahijja na haki tsabar tsananin bacin rai ta dubesu tace “ku fitar min da yarinyar nan kafin na illatata, let me not ever see her foot step a cikin estate dinnan”

Maya najin haka ta kyakyale da dariya, yanda ba kowa zaiji ba, plan dinta work out yanda ta tsara, burinta ya cika yau dinan.

Sojojin nan su uku haka suka zagaye sabeeha, rabi ta dora hannu aka tana innalillahi, “hajiya kiyiwa allah kiyi hkuri, yarinya ce karama, kuma macece karsu mata wani abun dan allah”

Rabi na kuka, idanun bahijja ya rufe gaba daya bataji bata gani, gaba daya ta gama tsanar yarinyar ko ganinta bata kaunar yi, yanayin yanda taga maya ba karamin tashin hankali ta shiga ba sai a lokacin ta tuna da mayar data gani a sama unconsciously.

Jikinta na rawa zata juya kenan aka bude tafkeken gate din, manya manyan motocin gidan suka soma shigowa, kamar convoys, babu wanda ya lura da abunda ke faduwa tsakar gidan

86 / 107