Advertisements
Chapter 95 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   95 / 107

282K to 285K   out of 320.4K words

da batayi mata ba, yan aikin gidan kuwa babu wanda bata zaga ba ta uwa ta uba, ashe ashe itama dai ba asalin kirki ne da ita ba, dole ta nema ma kanta mafita dole ne wannan.



MATAR TAJ (destined with you)
   Written by 
          Queenmarh

Book2 
PAID
Chapter 111



Kamar ana jan kafarta tana goge hawayen fuskarta hannunta na rawa tsabar bacin rai haka ta nufi part din taj, da wani kuduri aranta, as’usual part din na bude ta samu shiga kai tsaye ta wuce sitting room sannan ta haura sama, babu wani darr aranta.
Tana hawa saman tayi knocking daya biyu daga ciki ya amsa da come in don a tunaninshi ko me gyaran part dince.
Kai tsaye ta bude babu ko sallama, ya gama shirinshi kenan zai futa ya zauna bakin gado yana kokarin saka wrist watch dinshi akayi knocking din, bayan ya bada izinin shigowa baima dago yaga ko wayene ba yaji muryar maya.
“Inason magana dakai…
Ahankali ya dago da mamaki ya ganta tsaye idanunta sunyi jaa sosai, jikinta har wani rawa rawa yake,
maida hankalinshi yayi ga abunda yakeyi yayi kamar baisan da ruwan mutun a wajen ba, ganin haka yasa ta soma takowa “stop right there”
Ya dakatar da ita, “fadin abunda ke tafe dake daga nan”
Wani abu taji ya tokare mata a maqogaro, shima zai nuna mata iyakarta kenan? A harzuka ta soma takowa tana danne abunda ke taso mata ta hana kanta hawaye a daidai lokacin shi kuma ya miqe tsaye, ya mata wani irin kallo dayasa tasha jinin jikinta.
Abunda taso yi ta kasa kawai ta sauke idanunta kasa hawaye ya soma sauko mata, yanajin tana sheshekar kuka nan yabita da kallo da mamaki.
“Dan allah karka gujeni, idan duk kowa ya nuna baya sona karka qi ni, wallahi ina sonka uncle taj, inasonka sosai fiye da raina, ka taimakeni ka aureni,”
Ta karashe tana kallonshi, shima kallon nata yake sai yaji wani dan tausayinta ya ratsa shi, da ranshi harya soma baci sai kuma data fara kuka yaji bacin ran ya tafi, bayason ganin mace na kuka ko kadan, a sanyaye ya kauda idanunshi sannan yace “stop…crying, clean those”
Ya fada yana mata nuni da fuskanta, wani irin sanyi taji aranta, plan dinta is working,
“meke damunki? Who hate you?” Ya tambayeta a natse.
Daga yanda yake magana ta gane cewa ya danji wani abu game da kuka nata, so shes going to play a victim game, don ya tausaya mata.
Matsar kwalla ta sakeyi tare da sunkuyar da kanta, sannan tace
“Kowa, duk basa sona sunfi son wannan munafukar, ta rabani da kowa, sanadiyarta kowa baya sona”
Tunda ta soma maganar sabeeha yaji bacin ran nashi ya dawo sabo haryama wanda ya fara ji data shugo mashi daki babu sallama, babu gaisuwa kai tsaye.
Wato daga yanda take magana ya hango jealousy, da bakin ciki a cikin magan ganun nata, harma da rashin kunya a ciki, don harda anne ta sako a maganar tana fadi mashi yanda dama chan ba sonta take ba, banda rashin hankali irin nata bai kamata tace sabeeha ruined her life ba ta rabata da kowa hasalima sanadiyar chanzasu da akayi ne yasa sabeehar ta shiga rayuwa mai kunci, rayuwarta ta gaza inganta saboda rabata da akayi da asalin iyayenta ita kuma akayi replacing dinta a matsayin sabeehar.
Kwata kwata bata dago taga yanayin da yake ciki ba take ta zuba, trying to make him pity her, nanko ta tabo inda bai kamata taje wajen ba.
“Youre ungrateful” ya fada rai a bace sai a
Lokacin tayi saurin dagowa ta kalleshi saida gabanta ya fadi kuwa, ranshi a bace ya cigaba “are you trying to blame her for what your biological mother did? Did fatima hate you for being on her seat this whole time, did you even know what she had to go thru????” Ya sake jefo mata tambaya trying to add sense to her brain don yaga yarinta ma yana daya daga cikin abunda ke damunta bayan she’s being brutally selfish.
“Instead of you to be grateful?”
Bakinta ta soma motsawa tana hawaye, “yess because saboda ita na rasa komai, kowa fatima fatima fatimaa…i hate her, i wish ta dade da mutuwaaaa…”
nuni ya mata da kofa, baice komai ba tsabar bacin rai amma tasan abunda yake nufi, jikinta na rawa ta kalleshi tana tattara courage din yi mashi magana a wannan yanayin “whys everyone siding on her?? Meysa ka tsaneni Uncle taj?”
Bai sake kallonta ba ya nufi hanyar futa tayi saurin shan gabansa, without any second thought ta soma kokarin zare veil din dake kanta sannan ta soma kwance igiyar rigarta, a tsorace take dashi amma wani confidence takeji kawai nayin abunda yazo ranta.
“Wallahi zan iya baka komai, har kaina zan iya sallama maka,…” ta karashe tana kokarin sauke rigar tata kasa taji saukan mari tasss akan kuncinta ranshi a mugun mugun bace, babu abunda ya tsana kamar yaga loose mace, musamman wannan yarinya qanqanuwa.

Ay baisan futsararriya bace ta karashe sai yanxu, bai iya dukan mace ba ammada da akwai belt a jikinshi babu abunda zai hanashi zaneta, a very young girl like her har tana iya yin tunanin sakin jikinta to a man? For the fact yana matsayin uncle dinta, ranshi inyayi dubu ya baci sosai ba kadan ba hannunshi har karkarwa yake ya mata nuni da yatsa “before i count to 3, if i dare see any sights of you here, you’ll regret it”
Ay ko marin daya mata yasata gama shiga hayyacinta, tayi saurin maida rigar jikinta a furgice ta futa tana kuka.
He feel so disgusted, ranshi yayi mugun mugun baci, irin yara kamar wannnan abun tsoro ne musamman a cikin ahali babba kamar haka, she can go to any extent don ta samu abunda takeso, kuma ko kunyar idanunsa bataji ba, bayason yayi making abun as an issue but zai iya zaneta sosai akan wannan don ya ladab tata.
A furgice ta futo ta wuce part dinsu, tana shigowa as usual ta tadda basira na goge goge, tabi takan ruwan mopping din ya bare rai a bace ta wuce sama, basira ta kalleta ta bita da harara “mai baqin hali, mteww dama ance abunda ka shuka shi zaka girba, waye zai taba tunanin kece yar hadiza, kai allah ya wadai, itako sabeeha babu ruwanta halinsu daya da hajiya ashe shiyasa ma babu ruwanta saboda itace yarta ta asali bake ba yar masu da fadin rqi da izgilanci,mtewww”
Haka nan ta dingi kwashe ruwan don harya jiqa carpt din walkway din wajen.
Maya na shiga daki ta soma fashe fashen data saba tana hawaye, gana daya turartukanta dake kan dresser saida ta fashesu duka har hannunta na fidda jini, kamar wadda ta haukace haka ta miqe ta soma watso kayan wardrobe dinta hartayi nasarar daukan wani box irin na jewelry box haka dake boye a wajen, ta bude shi, take kwayoyintabda kayan mayenta suka bayyana a ciki, ba tare da wani tunani ba ta fiddosu ta aje bakin gado, ta fara ambulawa cikinta, kan kace me kawai tayi over dosing kanta sosai, muyagun kwayoyi ne da shansu keda hadari sosai don har mental asylum yana iya kai mutun idan ya zama addictive kuma ya fara taba kwakwal.
Tana layi ta zaro wata allura ta dura a cikin syringe sannan ta chaka ma kanta tana gamaqa ta soma sauke ajiyar zuciya ahankali hankali chan kuma ta bange dipp.

Acahn wajen taj kuwa bayan futarta haka ya futo ranshi a bace zuwa main house yana shiga ya wuce part din nanna, suka gaisa, ta tambayi jikinsa yace mata da sauki, ya futo ya wuce part din anne don achan zai karya, yana shiga ya zauna, fadila ma na part din annen suka gaisa dashi tasa laila karama tayi serving dinshi abunci yaci anan parlor.
Yanaci suna hira, shida anne sama sama,har ta tambayehsi jikinsa don nannna tace shima zazzabi ya hanashi zuwa yin breakfast yace mata da sauki, fadila tayi murmushi tace “abun naku kamar hadin baki kaida fatima, itama haka ta tashi da zazAbi saida aka hada mata allurai ma allah dai ya kra sauqi”
Yayi shiru baice komai ba, yana tuna abunda ya faru dasu jiya da daddare, ya gama deciding situation dinsu shida ita, daman shima bawai so yake asan da aure a taakaninau ba don idan nanna tasan irin rayuwar dayayi a baya she will be heart broken, bama ita kadai ba.
And har yanxu yana jin guilt din abunda yayi ma sabeehar da yanda ya qulaqantata a chan saudiyar aftwr all he has done for her.
Yana cikin wannan tunanin anne tace “ inka gama ga shiga ka dubata, nasan ta farka yanxu ko?”
Fadila ta dubi laila tace “yanxu kika fito daga dakinta ta farka kuwa?”
“Ah ah mami tana tare da mummy ma sanda na fito amma bari na sake dubawa”ta amsa sannan ta futa daga dakin.
Bayan ya gama cin abunci ya fito daga part din anne har zai sauka kasa kuma ya dakata, yana mai duban bangaren sabeehar, samun kanshi yayi da shiga part din da sallama, sabeeha da farkawanta kenan laila na zaune gefenta while bahijja ta koma part dinta don ta mata corn chicken soup da zata dan sha.
Tana jin sallamanshi gabanta ya wani irin fadi dam, saiga kamshinsa ya biyo baya wanda laila tunda ya shugo dazu taji kamar kamshin sa taji a dakin sabeeha,ba ita kadai bama hatta bahijjar saida taji wannan kamshin.
“Bismillah uncle taj” laila ta fada ahankali, sabewha kuma ta kauda kanta zuwa gefe,
Zama yayi wajen cute resting chair setting din da akayi a gefe yana fuskantarsu.
Gaba daya wajen saiya zama awkward, laila ta dubi sabeeha data hade ranta tayi kamar batasan da zuwanshi ba kasa kasa tace “madam yadai? Yazo dubaki”
Yi tayi kamar batajita ba wanda duk hakan akan idanunshi akayi, ya dubi laila da itama a lokacin ta dago karaf suka hada idanu, wani irin signaling yayi mata da ita kanta batasan yanda akayi ta gane me yake nufi ba wanda yasa ta tashi ta zura flats dinta sannan ta futa, sabeeha har zata mata magana sai kuma tayi shuru kawai wajen ya dauki silence.
Sun dauka wajen minti biyar a haka baice qala ba haka zalika bata dubeshi ba, ya kafeta da idanu, she looked so pale kamar wadda tayi jinyar kwanaki, ta wani hade rai sosai tama qi yarda ta kalleshi, saiya kara jin haushin kansa for what he did yesterday, urge dinshi zai kaishi ya baroshi,

a sanyaye ya soma magana kamar bashi ba” “Fatima!!…” ya kira sunanta datajishi har tsakiyar kanta, amma bata juyo ba balle ta kalleshi, saima runtse idanunta datayi sannan ta fara kokarin tashi, “i’m sorry….bibi” ya fada yana kallonta, ganin tana kokarin barin wajen ya sashi cewa “are you upset with me???” Ya sake jefo mata tambaya, bata tsaya sauraronsa ba ta tunkari bathroom, maganar dayyai yasa ta tsaya chak.
“Inada nawa dalilin dayasa ban rabu dake ba,kuma naqi rabuwa dake tun bayan tafiyarki,”
Ya dan dakata bai cigaba ba, ita kuma abubuwa da dama na yawo aranta at the same time gabanta na faduwa, what could be the reason? Tunda tasan basuyi rabuwar arziki ba, sannan kuma bayan ya dawo nan allah yayi haduwarsu cikin inuwa daya maisa bai rabu da itan ba? What could be the reason?” Ta tambayi kanta kafin ta bama kanta answer “Propably beacuse yanajin guilt din abunda yayi min bayan yamin korar wulaqanci, daga baya kuma ya gano cewa nice mai gaskiya amaimakon yan uwansa” ta karashe tana jin wani abu na tokare mata a maqoshi, ko da wasa bata kawo tunanin wai ko maybe he has something for her ne ba.
Rai a bace ta juyo, “idan har kanada naka dalilin naqin rabuwa dani a lokacin yanxu babu wani dalili, let’s just ends this”
“Sure!!!” Ya fada kai tsaye, yana takowa har inda take tsaye amma nesa da ita, take gabanta ya fadi,ta kafeshi da idanu shima ita yake kallo.
Hannunshi ya daga ahankali ya dora kan gashinta yana dabbing din kan nata kamar wata yar pet yace “bansamu damar yin haka ba a lokacin daya kamata amma yau zanyi…FATİMA thank you for being part of my life, thank you for standing with me, thank you for protecting Tajudeen that was blinded by evils, thank you for caring for the tajudeen that was helpless, kin haskaka rayuwata a lokacin da komai ya zamto min duhu ne”
Take jikinta ya soma rawa hawaye ya soma sauka akan fuskarta tana kallon cikin idanunshi kamar yanda yake kallon nata, it was a tough moment for him but tougher for her don wani abu takeji a cikin zuciyarta da ta kasa fasaarashi, fargaba ko tsoro? Ta kasa tantance menene
Hannunshi har zuwa lokacin na kan gashinta yana caressing kan nata kamar yar kankanuwar yarinya.
Saitaga sak didin ta, didin data bari achan saudiyya, didin daya kasance shine pillar kuma source of comfort dinta.
Hawayenta daya gani shi kansa yayi confusing dinsa, yana tuna mashi da rayuwar da sukayi da ita achan saudiyyan.
Har zai bude baki yayi magana kenan kawai sukaji motsin kofa za a bude, laila data fara hango su tayi saurin daga murya tace “mummy let me help da wannan”
Cikin hanzari ya dan matsa gefe sabeeha tayi saurin juyowa taga laila na kokarin karban tray din hannunta, cikin sauri ta soma goge hawayen fuskanta.
“Au tajudeen ashe kana nan, kazo dubiya ne kaima”
Gyaran murya yayi ya dubeta sannan ya gaisheta, yanayin shi gaba daya ya sauya, badan shugowarsu ba da yayi abunda he will regret for the rest of his mind.
Kallonta bahijja tayi sannan tace, “oh no…, mun barki ke kadai ko dear”
Tana kokarin boye yanayin da take ciki muryanta ciki ciki tace “No mummy ba komi, daman zan shiga bathroom ne”
“Muje na taimaka maki” bahijja ta fada tana kama hannunta with so much care.
Suna wucewa taj ya sauke ajiyar zuciya sannan ya futa daga dakin laila ta bishi da kallo.
Yana futa ya fuce daga gidan gaba daya, dan ko dinner bai samu anyi dashi ba a gidan.
Sabeeha ko tun bayan zuwan da yayi harya fits gaba daya kamar ya tafi da tunaninta ne, haka kawai ta kasa natsuwa maganganunsa na yawo a kwakwalwarta.
Bahijja taso su koma chan part dinta amma tace mata ah ah tafison nan, nan fadila tace ma laila tazo ta tayata kwana anan, daddy ma yazo ya sake dubata kuma suka sha hira shida ita kamar koda yaushe, kai kamar ma shakuwaraa da sabeeha yafi wadda ke tsakaninta da bahijja, he’s her total comfort zone, shima kanshi yanda yakeji game da sabeeha bai taba jin hakan da maya ba, wani irin connection ne tsakaninsu da yakeji da ita sosai, murnarsu da farin cikinsu daya shine yanda suka lura allah ya tsarkake masu diyarsu bai barta ta wulakanta ba ko ta kaucewa hanya, sabeeha akwai hankali, ladabi, biyayya, natsuwa, a yanda ta taso cikin rashin kulawa da muzgunawa da hadiza ta mata badan ikon allah babu abunda zai hanata lalacewa ta shiga duniya ko ta kasance futsararriya mara kunya da sanin ya kamata sai allah ya nuna karfin iyawarsa na qin barin hakkin wani ya hau kan wani.

Har wajen karfe daya tana daga zaune ta kasa barci, laila na daga gefenta tana barcinta hankali kwance.
Ganin ta kasa samun natsuwa a zuciyarta yasa ta tashi ta dauro alwala ta fito ta tada sallah.

Bangaren maya tana chan a mangare kamar matacciya, abun har ya kaita ga yin miyagun allurai da tasan zai lalata mata rayuwarta allah ya shirya mana zuri’a.

After 2 days, yau ta kasance sunday, su sabeeha na shirin komawa school, alhamdulillah taji sauqin jikinta sosai ba kadan ba, rabonta da taj tun ranar nan, har fargabar haduwa take dashi, don ranar badan mummy ta shigo daki ba maganar su bazata tsaya daga nan ba, har zuwa lokacin tanajin wani irin yanayi game dashi, daya kasa fasaarawa, duk wannan haushinsa da takaicinsa da takejin tun bayan abunda ya mata a saudiya lokaci guda taji ya wanye tun da sukayi maganar nan, idan ta zauna saitayi shuru tana tunani, amma fa bata yarda kowa yasan tana cikin damuwa ba musamman bahijja data tare a part din annen, don anan take wuni sai dare take komawa main house.
Alamarin bahijja da anne kuwa Sanadiyar diyarsu ita da majeed yasa anne ta aje komai a gefe dama chan bawai ta tsanesa bane kawai dai tana jin zafin abunda ya faru ne a baya sanadiyar aurensu.
Bangaren maya ko tundaga ranar nan datayi allurar nan wadda cikin kawayenta wata tayi mata introducing allurar, tundaga lokacin ta aje syrups da take sha wasu kwayoyi ta koma durama kanta allurarnan, ta gama isolating kanta gaba daya, wanda bahijja ta kasa controlling dinta akai,tsakani da allah har zuwa lokacin bata fasa nuna kulawa ga maya ba, kuma tana sonta har cikin zuciyarta amma allah bai nuna mata wannan sabuwar hanyar da maya ta nufa ba.
Misalin karfe sha biyu duk suka futo, domin zuwa shopping, babu yanda bahijja batayi akan maya ta shirya ta bisu amma ta shiada mata bazata iya zwa ba kanta na ciwo,wannan yasa ta barta kawai, sai laila ne ta futo suka wuce da sabeehar hamad zai kaisu.
Tunda suka fito sabeeha taji wata ni’ima ta ratsata kamar yanda suka saba itace a gaba tana daga zaune laila nata zuba masu surutu, hamad kuma jefi jefi yake kallon sabeehar datayi shuru.
Sun dade wajen shopping, laila ta jidar masu abubuwa kamar babu gobe hanad ya biya suka fito suka wuce saloon aka gyara masu kai akayi ma sabeeha kalba, silky jajan gashi ya sauko har kwankwasonta masha allah, laila sai faman sha’awar gashin take tana rokon dama itama tanada gashi haka kamar na sabeeha, totally yarinyar halfcast ce, yanxu dataji gyara asalin ta yake bayyana sosai.
Ana gama masu akayi masu pedi and medicure, kai spa dinma badai haduwa ba waishi blushup_beauty, nan ceo din hajiya rukky tayi masu introducing sabon installment da sukayi na gyaran jiki, kuma da suka kasance vips akwai discount da za a basu specially for them, laila data kasance itama yar gwalli take tacema sabeeha suyi, kudi ba matsala bane ba kawai dai suna tsoron batama hamad lokaci wannan yasa laila ta kirashi a waya sabeeha ta rokesa ya amince sannan aka fara masu gyaran jiki, body polish ne, waxing ne, dukhoon steam duka babu wanda ba ayi masu ba Masha allah, kowaccensu ta

95 / 107