Advertisements
Chapter 35 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   35 / 107

102K to 105K   out of 320.4K words

sosai jin maganganun da take,”im talking to you”
Ta daka tsawa don ranta ya baci.
Zama yayi akan kujera dake facing nata ya daura kafa daya kan daya kamar wani boss, wallahi ganinshi haka datayi gabanta saida ya fadi, kafin ya soma magana “I’m sorry first love for coming un announced, i wanted to talk to you in personal and check how the business is going..”

“Check what? Suddenly youre having interest on the family business? “
Saurin katseta yayi abunda bai taba yi ba “there’s nothing wrong with that first love isn’t it? “
Kai saida gabanta fa ya fadi,ta samu waje ta zauna trying to calm her self down.
Sai yaji wani irin rashin dadi don bata taba magana ya maida maga kai tsaye ba saboda yanda yake ganin girmanta da darajarta
“I’m sorry first love, i just came here to inform you inason na koma uk but idan har baki
Amince ba babu matsala i will…”

“Yaushe zaka koma din?” Ta amsa shi kai tsaye
“Anytime..from now”
“No problem idan chan yafi maka nan babu matsala” wani irin dadi yaji aranshi ya tashi yayi pecking kumatunta ya mata sallama.

Tunda ya futa ta kama haban tana wani iri. Nazari, zuwa kawai yayi office dayayi yasa ta shuga tashin hankali inaga ance ya karba kamfanin? No impossible bazata taba barin haka ta kasance ba dole ta nisantashi da nan gaba daya har abada….



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 81

Zuwanshi kamfani ba karamin tarzoma ya tado ba, washe gari gaba daya kafar yada labarai da media ta dauka, waenda basu sanshi bama suka fara sanin shi, mata da maza,ashe jiyan daya zo har an dauke shi hoto first thing first the next day ya zama topic of headline da safe, the return of the taheel heir bayan matsalar kwakwal daya samu, nanfa mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu kowa da nashi.
Mutanen kamfani kuwa nanma suka fara rade rade, ay jiya daga zuwanshi ya kawo masu solution din matsalar da suke ciki, workers are in support of him, shareholders kuwa daman kowa ya gaji da alamarin hidaya, ta kanaynnaye, bata neman shawarar su idan zatayi making decision for the kamfani, abu dai fa kamar wasa wasa ya fara zama rigima don har meeting aka shiga akan wannan zancen akan dole ta sauka ta bama taj yayi handling kamfani, shiko baimasan me ake ciki ba kwata kwata, he’s just prepping yabar kasar gaba daya don he can’t stay here anymore.

Yana cikin hada kayanshi call din mutallib ya shugo, bayan sun gaisa yake fada mashi yanxu yake ganin yana yawo a social media tun safe, yayi mamki sosai don shi saiyayi wata da watanni bai hau instagram ba, and shiba ma’abocin kallo ba.
Yana kashe wayar ya shiga links din da mutallib ya tura mashi ya fara dudubawa, babu abunda akeyi sai sukar hidaya ana maganar cewa tasan ya samu sauki amma taqi barinshi yayi taking over, maganganu dai iri iri daga wannan sai wannan lokaci guda hankalin shi ya tashi, shifa baya son crises din family business dinsu, he’s not interested in that at all.

Yana zaune bakin gado yayi shuru yana duban wayanshi call din hidaya ya shugo, saida yaji wani irin a jikinshi, yana dagawa ta soma magana “kazo nan office ka same rn”
Tana fadin haka ta kashe wayar, miqewa yayi ya zari key dinshi ya futa.

Yana isowa ma’aikata kamar zasu kwanta mashi, wani irin kwarjini yake dashi da haiba yake dashi, he’s walking majestically classy and handsome, duk inda ya gifta suna gaishesa yana daga masu hannu, kana ganinshi kasan girma da arziki ya bi jikinsa, fadwa dake taaye daga office din hidaya tun daga 10th floor take kallonsa, zuwanta babu abunda tayi banda balbala ma abunda ke cin hidaya wuta, saida ta gama zugeta tsaff ta yanda hidaya bataji bata gani.
Babu abunda take sai smirking, its about time for her to step up on them, he’s her next target yanxu.
Kai tsaye ya shugo babu wanda ya tare shi har office din hidaya yana cin karo da fuskar fadwa ya wani hade girar sama da kasa kamar bai taba dariya ba kap rayuwarshi, tun kafin ya karaso hidaya ta miqe tsaye idanunta sunyi jaa sosai, ta nunashi da yatsa, “you are going to fix this? Okay? Bazan taba barin kamfanin nan ya salwanta ba, not now not ever.. now let’s go”
Kallonta kawai taj yake da mamaki kwance akan fuskanshi, mey first love ke tunani ne? Cause ya kasa gane maganganunta daga jiya zuwa yau, yanda take magana kamar tana magana ne da wani makiyinta ko kuma someone that she’s scared of

Futa sukayi gaba dayansu zuwa wajen press conference dake cikin kamfanin, suna shugowa aka fara kyaskyasta masu hotuna, yan labarai sun cika wajen, charaf ta k kama hannunshi ta rike cikin nata tana wani irin makirin murmushi kamar ba ita ya gani ba yanxu a office dinta, haka ta dunga janshi har suka zo wajen zamansu suna facing reporters dake ta faman daukansu hotuna.
Suna zama tayi gyaran murya ta soma magana gwanin ban tausayi.
“We are here to clear the air and the rumors going around, kamar dai yanda kuka sani wannan qanina ne kuma jinina abun alfahari na banida kamarshi” ta karashe tana sumbatar hannunshi harda hawayenta, “some few months ago ya samu amnesia which cause alot of problem and emotional damage to all if us…his relative,”
Ta dan dakata tana matsar kwalla, abunfa kamar drama taj yayi saqe.
Wani reporter ne ya jefi mata tambaya “shin ya samu sauki ne? Kuma zaki bashi makaminshi na shugabancin wannan kamfanin”
Da sauri ta dago idanunta harda kwalla ta daga hannu secretary dinta ya shugo da wasu takkardu harda wani professional likita da aka sanshi sosai a kasar suka shugo tare suka tsaya daga bayanta doc din ya gabatar da kanshi kafin ta bama mutumin answer.
“Wannan shine dr james, shine ke handling case din tajudeen, kuma har yanxu shike kula da lafiyarsa har muna fatan allah yasa ya dawo hayyacinshi, my brother is not just mentally ill, he’s also suffering from brain tumor, he only needs you prayers rn”
Tunda ta soma magana yake kallonta da mamaki? Hidaya ke karya agaban idanunshi kuma akan lafiyarshi saboda kamfani, duk girmanta da yake gani saida ya runtse idanu ayau don tayi mugun bashi mamaki? Daman dukiya da power zaisa mutun yayi haka?”meysa zatayi haka? Why lie?

“But madam ayanda muke ganinshi a haka he doesn’t look like someone that…”
Saurin katseshi doctor yayi yana mashi bayanin ay haka yake, za a ganshi kamar lafiyayye saidai kuma baya cikin hayyacinsa baisan me yake ba kuma yana da cutar mantuwa, kai wata karyar da aka lafto kan rashin lafiyar nan ba karamin mamaki ya bama wasu reporters dinba saidai basuda jaa da maganar doctor din tunda official statement ne.

“Ma’am akwai hirar da kikayi watannin baya da suka wuce and kin shaida mana baida wani amfani don kwakwalwarshi ta tabu gaba daya, shin akwai wani hope din samun lafiyarshi,?”
Kamar jira take ya kai karshe tayi saurin cewa “babu wani hope..babu he will forever stay like this,”
“Ma’am bakya fatan ya samu sauqin ne?”
Sai a lokacin ta lura da tabarar data so yi nan danan ta sauya fuska kamar ba itava abun tausayi ta sumbashi kumatun taj ta shafa kanshi kamar wani dan yaro tace “sai nafi kowa farin ciki idan naga qanina ya dawo hayyacinshi ya samu lafiya, he’s my life, my everything he only has me in this world cause ni kadai ce gatansa kuma farin cikin sa”
Chapp wannan Kalamai nata na karshe sun kara rikita mashi lissafi, ashe irin wannan words din dake futowa daga bakinta are something that are easily comprehended? Sai ya fara contemplating shin daman duk soyayyar da take nuna mashi throughout his life are just like a comprehensive words?
Wallahi gaba daya he’s lost in his thoughts, baima san har ta jawo hannunshi sun futo daga wajen ba, sai binta yake kamar raqumi da akala, suna isowa office dinta ta dubi fadwa tace “take him home”
“Kai kuma babu inda zakaje, you will stay back, and i forbid you from any activity da zaisa ka shiga public, gym da kake zuwa, malls da duk wani encounter din da kake,”

“Why????” Shine kalma ta farko data futo daga bakinshi, har gabanshi ta iso tana mai kallon cikin idanunshi yana kallon nata tace “because i said so, i will never allow you ka ruguza min duk wani tanadi danayi shekara da shekaru, you’re nothing and you can never be anything da zaisa…”
Sai kuma tayi shuru kawai ta dubi fadwa tace “take him home, and makesure that babu any reporter da yayi noticing da motarshi yazo, zansa amaida motonshi gida.”
Taj fa is speechless, ya rasa tunanin da zaiyi, he’s so disappointed, wallahi inya cigaba da kallonta sauran respect din da yake mata zai iya zubewa kasa, baya kaunar karya, balle yayi participacing a cikinta, ta sashi cikin wani state daya kasa gane what is right and wrong, she manipulated him into thinking duk yanda akayi she has her reason for what she did amma he’s giving her benefit of doubt wannan yasa bai musa ba yabi bayan fadwa, saidai abubuwa da dama na mashi yawo a kwakwalwa musamman maganar sabeeha, inda take ce mashi meysa bazai bude idanunshi ba? Waenda ke sanshi su yake nisantarwa waenda basa qaunar ganin shi sune yake saka wa as his top priority.
Yana cikin wannan tunanin fadwa ta bude motarta ya shiga itama ta zaga wajen driver ta shiga, tasaka belt, sannan ta fara kokarin saka mashi ya kalleta tace “akwai reporters anan you need to behave”
Tana fadin haka ta fara janyo belt din kamar tana shafa kirjinshi harta saka mashi ta sauke wani makirin murmushi, tana hango yanda he’s lost in his thought gaba daya, badan hidaya ba bazai taba shiga motarta ba lallai dole ta nemi amincewarshi da yardasa, ta haka ne kawai zata maidoshi tafin hannunta.

Suna cikin tafiya ta soma magana da siyaya.
“Why are you so shocked kamar bakasan how obsessed she is akan power ba da kamfanin nan? She wants it all to her self, there no way zata bari komai yayi slipping a hannunta ba so easily, abubuwan da tayi akan kamfanin nan yafi karfin tunanin ka so i will advice kayi stooping so low karka sa ta fusata ka koma gidan jiya tunda gashi nan ka dawo normal ”
Yana jinta yayi banza da ita saidai gaba daya maganganunta yayi breaking dinsu into his head, trying to understand inda maganrta ta nufa.
Chan gefe ta gangara da motarta tayi parking ta dubeshi, “you need to trust me taj, nasan we are not in a good terms amma inason ka sani bazan taba cutar dakai ba, ina sonka ina qaunarka”
Wani irin banzan kallo ya mata ranshi a mugun bace har zai bude bayan motar tace “kanaso ka kira ma kanka masifa kenan? Bakaji me tace bane? Karka sake kayi abunda zaisa ayi tunanin lafiyarla kalau, kalla!!”
Ta nuna mashi mirror, waenchan da kake gani reporters ne, kuma kana futa zasuyi capturing and i promise me you will be shattered”
“What do you mean?” Ya tambayeta a zafafe, “when the time comes you’ll understand, hidaya bata kaunar bata son ganinka..youre a threat to
her”
Wata irin tsawa ya daka mata dayasa ta zuba mashi ido a furgice, “don’t you dare..dont ever say that to my face, kina tunanin zan taba yarda da maganar ki?karya kike i will never, now step on this car kafin”
“Calm dowm mr T ford”
Surprisingly yake kallonta jin kiranshi da tayi da sunan, mumushi kawai tayi ta kunna motar suka bar wajen.

Yana dawowa gida sama ya wuce rai a bace,sai yanxu yake ganin all his life he’s being controlled, zama yayi yana kara kallon press din da sukayi daxu, daya kalla ranshi ke kara baci, magnagnunta sun bashi mamaki sosai, harya fara tunanin anya hidaya ce wannan? The hidaya that he knows will Never do this, koshi banza ne wannan kadai daya gani bawai an fada mashi ba ya zashi kokonto akan rayuwarsgi gaba daya, wallahi bai taba son shiga cikin family business dinsu ba he’s never interested kwata kwata, why are people around him like this? Haka khaal shima yyi kuma yayi mamakin labarin dayaji yanxu kuma hidaya? Noo noo? Thats impossible, dole she has her reasons maybe kamfanin yana cikin matsala, shiyasa take kokarin ganin ta rike kamfanin a wajen, deep down wata zuciyar tashi na ce mashi are you blinded? Open your eyes and face the reality of your life, saidai kuma tsabar how manipulated he is yasa yaqi bude zuciyarshi da zancen, saidai tambayr kanshi daya soma yi? what’s going on in his life? What has he missed?

Hidaya ko takanshi batabi ba, cause batajin he needs any explanation from her, lokaci guda maganar taj ta rufe ruff kamar ba a taba yinshi ba, kuma shawarar fadwa ce data kawo mata last minutes lokacin da ta rasa yanda zata shawo kan matsalar da take ciki.

Da daddare daidai lokacin da take yawan shiga study room dinta yaje don ya sameta kuma ya shaida mata cewa bashida interest alan family business din, koda ya karasa yana gabda yin kncking ya soma jin magnaganu daga ciki, maganganun are not very clear kuma bawai yayi eavesdropping bane kawai yaji last sentence din nata ne a kunnenshi kamar wake up call, “i was silent and low for a reason not because na barshi ne donya ruguza min plans dina,…i have come this far babu wanda ya isa yayi crashing dina, nor him not even khaal daya shiga gonata ban barshi ba.. kina tunanin turashi da nayi karatu chan england is not for a reason? No!!!“

Magana fadwa ta maida mata saidai ita ba ajin muryarta kwata kwata, dan dakatawa yayi yana nazari maganar me suke? Mey ya kawo khaal a zancen nasu har take cewa shima bata barshi ba? What is the beginning of the discussion,sannan turashi karatu England datayi is for a reason? What was the reason?”
Gaba daya ya kasa puzzling maganganun nata, shigan da baiyi ba kenan ya juya yana nanata magnganun nata akanshi,fadwa ta fito daga ciki, tana ganinshi ta tabbatar yazo wajen hidaya ne, hiw she wish he came earlier dayaji magnagnun dasukayi da hidaya.

Saidai hakan ma bata baci ba its a chance to her wannan yasa tayi wani murmushi, cikin sauri sauri tazo wucewa ta gefenshi tayi saurin watsa papers din data fito dasu a gabanshi intentionally, karaf idanunshi suka sauka kan headline din kan paper don da harufa manya aka rubuta, transfer of inheritance da shares ne
A kasan baiga sunan waye a jiki ba don rubutun sunyi kananu.

Kauda kanshi kawai yayi ya wuce ba tare da ya waiwayeta ba, yanata saqe saqe maganganunsu aranshi.

Fadwa ko tana tattare papers din ta miqe tabishi da kallo harya shige daki tayi smirking ita kadai tasan abund ake ranta.

Tunda ya dawo dakin babu abunda yake sai safa sa marwa,tunanin maganganunsu ya gama addabarshi.

Yana cikin wannan tunanin call ya shugo mashi, unknow number ne wannan yasa yaqi dagawa, tana katsewa wani call din ya shugo rai a bace ya daga wayar yakai kunneshi, to his fullest surprise muryar fadwa yaji, har zai katse wayar ta dakatar dashi da sauri tace “zan fada maka abu daya ko ka yarda ko karka yar wannan choice dinka ne,”
Kitt ya kashe wayar yaqi sauraron abunda ta fada sannan ya danna mata blocking.

Fadwa tunda ta tashi take nazarin yanda zatayi ta shiga tsakanin taj da hidaya, duk wani trick tayi amfani dashi amma alamun sun nuna basa tasiri akanshi, kwata kwata, tsakanin jiya da yau ta kira wayanshi sau ashiri da different numbers baya shiga saboda yayi restricting wayan.
Wata dabara ce tazo mata wadda take tunanin zata iya amfani da wannan don ganin ta cimma burinta.

Achan nigeria yau kwanan sabeeha bakwai cirr, kuma tayi shi ne cikin kunshi da rashin walwala, wallahi harta soma baki, sauro ya gama cicinye ta gashi ta saba da hutu, chan saudi babu sauro sai ac nanko sai azababben zafi, ko arzikin fanka bata samu ba a parlor iya daki ne kawai akwai fanka, skin dinta yayi rudu rudu yayi jaa sosai abun tausayi, tsakaninta da Hadiza kuwa tsangwama ne da masifa, ko gaisheta tayi saita balbale ta da masifa, wallahi ko qaunar ganinta batayi, yanxu haka suna tare da jamila datazo gidan suna kuskus.

“Kinga wannan yarinyar ko wallahi wallahi kadara ce a wajen ki hadiza, ki jata aiki gidan abuncin nan da kike zuwa, ko allah zaisa wani tsoho ya ganta anan wajen ki aura mashi ita.”

Shuru hadiza tayi tana nazari kafin tace, “jamila kinsan abunda kike fada kuwa? In fiddata duniya fa kike cewa?“
“Toh ajiyeta zakiyi? Dole wata rana zaki aurar da ita, bayan wannan ma yanda rayuwar nan ta sauya mai kudi ma yana jin jiki balle talaka? Na rantse da allay idan rusau dinnan da akeyi yayo kanku shikennan kun shiga uku”
Hadiza ta mata mugun kallo tace “dole kice na shiga uku ay tunda kunyi nakanku ke bakida damuwa”
Jamila tace “to ay na baki shawara kinqi dauka, ana takai wake ta kaya? ki sata gaba kawai ko wanke wanke ke tanayi a wajen mene amfaninta in bata nemo ba? Ke zaki nemo mata taci ko kuwa?”


Sun dade suna tattaunawa don da safe ne kafin jamila ta wuce gida, hadiza na shirin fita sabeeha ta shugo, har kasa ta duka ta gaisheta ko arzikin amsawa bata samu ba, wannan kudin da mutallib ya bata su ta zaro ta ajema hadiza a gefe, kafin ta soma magana a natse cikin kamewa, “mama, ga wannan ko za a saya abuncin gida dashi”
Kallon kudin hadiza tayi kafin ta dubeta tace “fita ki jira ni waje”
Tana futa hadiza ta kwashe kudin ta saka a jakarta sannan ta saka hijab dinta ta futo.
Anan parlor taga sabeehar na ninke kayan ta data wanke, mamakin girman yarinyar take sosai ba kadanba, ta ciciko babu alamun rama a tattare da ita, saita fara wondering wani irin gida aka kaita ne haka? Kodai iskanci tace tanayi achan, yanxu dai ba wannan ne gabanta ba wannan yasa tace “tashi muje”
Miqewa sabeeha tayi ta nada mayafin abayar kanta sannan tabi bayan hadiza suka kama hanyar bakin titi

35 / 107