Advertisements
Chapter 29 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   29 / 107

84K to 87K   out of 320.4K words

gidan gaba daya lokacin wajen karfe hudu da yan mintina, cikin gaggawa ya shiga motar yayi horn aka bude ya fice daga gidan gaba daya hankali a tashe.



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 77
Washe gari da asubahin fari ta tashi da irin matsanancin ciwon ciki ta tashi, which result too wannan abortion pills da aka bata bata sani ba, allah yaso tana da jini mai karfi, har yasa side effects din ya tsaya kan ciwon ciki data dunga yi, shima tun wajen asuba data dunga fitarda wani irin stool mai ruwa ruwa ta samu sauki.
Sai ya zamana da safe garau ta tashi abunta, sonata kuwa kasa barci tayi jiya, tana jiran tsammani shuru, wayanta na hannunta tana jiran jin motsi ko ihun sabeeha shuru,
wato ashe ranar da sabeehar ke kitchen har ammu ta shugo suna magana a ranar ne sabeeha ta shugo dakin ta maqala wani traverser dake recording conversation, ranar taso shiga har cikin daki saidai allah bai bata iko ba don daidai lolacin ya fito daga daki wannan yasa tayi hanzarin futa daka part din ba tare da ta bari ya ganta ba.

Daman tun safe suka hauro sama ita da afiya,kamar daga sama kuwa sukayi karar bude kofar part din nasu, har guje guje suke wajen fitowa daga sitting room din, daidai nan sabeeha ta rufo kofar part din ta sanye da doguwar riga ta nufi kasa hankalinta kwance.
Ba karamin mamaki sukayi ba suna kallon juna, aka rasa wanda zaije ma dan uwan sa tak nazari da tunani harma da mamaki ya gama cinsu, sonata na kallon afiya tace, “kodai bata sha bane? Ko maganin baya aiki?”
Afiya ta karbe zancen, “ya zakice maganin baya aiki, guda biyu fa muka saka, wannan abortion pils din nasha yafi sau nawa kuma yana aiki sosai guda daya kawai idan nasha kamar zanyi hauka, kuma babu kowa a dakin, waye zai hada tea ya ajiya saidai idan…”
Kasa karaswa tayi tana mai duban sonata data zaro ido itama tunaninta bai tsaya ko ina ba saidai idan babu cikin kenan..”saidai idan babu cikin kennan a jikinta?” Sonata ta karashe.
“Yes..don babu yanda za ayi ace lpiyarta kalau indai tasha abunnnan, “
“Wow…lallai yarinyar nan she has the audacity to fool all of us..wallahi saina fadama taj..saina fada mashi…hahah i knew it”
“Ke kinga matsalarki kennan Lets reconfirm first..what if we were mistaken? Let’s say babu cikin kina tunanin kika tunkareshi da maganr zai yarda? Dole sai mun samu medical approval tukunna”
“To ya zamuyi kennan? How can we get the medical approval??”
Matsowa afiya tayi daidai kunnenta tayi mata magana kafin ta kalleta.


Bangaren taj dan dole ya kwana a garin saboda bai samu flight ba zuwa saudi, saboda weather din daya chanza lokaci guda dole ya hkura ya kwana da zummar dawowa washe gari, a ranar saida ya tabbatar ya bama matar khaal property dinsu, ba karamin dadi taji ba kuka kam tayi kuka harya gode allah haka zalika ta kasa ce mashi komi, duk yanda sukayi ko saida ta fada ma mutabblb nan ya shaida mata komai gameda yanda taj din ya karbo masu property ya saya da kudinshi, ranar dai kwana tayi tana goiiya ga allah sannan tayi taj din addua sosai.
Haka ya masu sha tara ta arziki sosai ita da mahaifinta da yaran ma.
Washe gari ya sake dawowa ya masu sallama, nan matar khaal ta fiddo da wani tsohon envelope ta bashi.
“Ga wannan….naka ne khaal na yawan cewa ko bayan ranshi yana son yaje hannunka don zai maka amfani nan gaba” Ta miqa mashi
Kallon envelop din yayi bayan ya karba, bai wani kawo komai cikin maganganunta ba ya saka cikin aljihunsa sannan ya masu sallama ya shiga cikin taksi ya wuce bayan sunyi sallama.


Fadwa..
Bata dawo gidan ba sai wajen around karfe 10 na safe, sai baza kamshi takeyi ta zubo da gashi ta kan gadon bayanta.
Kai tsaye cikin gidan ta nufa maids na ganinta suka fara gaisheta, tasan a daidai wannan lokacin sunata hidimar kaye kayen kwashe breakfast.
Part dinsu direct ta nufa bata yada zango ko’ina ba sai dakinta ta watsa jakarta ta wuce bathroom tayi wanka sannan ta fito da towel daure a kirjinta, zama tayi bakin gado ta dauka wayanta dake ruri takai kunne,
A shagwabe tace “Yes I’m back safely”
Ta amsa daga chan akayi magana nidai banji me akace ba sai chan kawai ta soma hamma tace “okay bye love you”
Miqewa tayi ta nufi hanyar closet, sai a lokacin ta lura da kamar an bubude wardrobs dinta, mamaki ne karara a fuskarta ta dan yi jim, chan ta daga idanunta zuwa ga secret hideout din, alamun budewa ta gani wanda yasa ta matsar da kofar wardrob din ta danna abunda ke bada access zuwa ciki, tun kafin ta karasa ciki taci karo da id card din tareeq wanda ya fadi lokacin da yake kokarin zaro wayarshi daga aljihu don ya haska, a fusace ta shiga ciki, dakin na nan yanda yake duhu dum saida ta danna wani switch daga gefe ya kunnu take ko’ina ya bade da haske, da board din taci karo sai kuma laptop din dake bude wadda a rufe take barinta indai ta gama mata amfani.
Taabar rudu data shiga har towel dinta na neman kwancewa tayi saurin tallabeshi ta karasa cikin dakin ta kunna laptop din, tana kawowa ta shiga cctv camera dake recording dakin, tundaga daren jiya zuwa yau tayi playing,daga shugowarshi zuwa fitarshi da duk abuda yayi ta gani gaba daya, ashe dakin zagaye yake da cctv cameras shi baima sani ba.


A fusace ta fito daga dakin ta nufi bedroom dinta tare da janyo waya tayi dialing wata number, gaba daya ta karade ta sauya kamar ba ita ba, ana daga wayar ta soma magana kamar haka.
“Akwai matsala…”

Mintuna talatin da suka wuce baya….

Anan dining gaba daya suna zaune, ammu, afiya, barad, sonata harda sabeeha wadda ammu ta sata saukowa tayi breakfast din itama, tunda suka zauna babu abunda suke sai kurama sabeeha idanu, ammu na ankare da su saidai bata kawo komai a ranta ba, bayan sun gama breakfast kowa ta kama gabanta, gaba daya sonata ta hana afiya sakat, ita a dole sai sun samu shaidar da zata nuna cewa sabeeha babu cikin a jikinta, yanxu haka suna cikin bedroom din afiya suna saqawa suna warwara wa, ammu data biyo afiya daki don ta bata wayarta data mance a dining tun kafin ta kaiga shiga bedroom din ta jiyo maganganunsu, cikin ikon allah a daidai lokacin taji maganganun da sukayi da maganin da suka sama sabeeha na abortion which duk plan din sonata ne, da kansu suke maganganun har suka yanke yanda zasuyi drugging dinta yau da daddare don su samu damar diban jininta, yanxu haka babu wanda suke jiran dawowa kamar hidaya don ita kadai ce zasu fadi ma wannan zancen ta yarda, don shi kam bazasu iya tunkarar shi da maganar ba.

Ammu ranta ya baci sosai da maganganunsu, tabbas idan har da gaske sun gano babu ciki jikin sabeeha akwai matsala, abunda yafi tsaya mata arai shine abortion pills da suka bata yanxu da akwai cikin shikennan, dole tasan yanda zatayi dasu cikin gaggawa tun kafin taj din ya dawo harma da hidayar.

Bangaren sabeeha duk batasan wainar da ake tauyawa ba, gaba daya yau dinnan cikin walwala take sannan tana regreting abubuwa da dama musamman maganganun daya fada mata suka tsaya mata arai, tabbas babu maganar so tsakaninsu, zaman ma da take dashi ina amfaninshi? Ga karyar data mashi na cikin da babu shi ma a cikin lissafi, tunawa da wannan kadai yana dagula mata lissafi, badan ammu ba dake convincing dinta tana jin gwara kawai ta fada mashi gaskia, don karya babu inda zata kaisu.

Misalin wajen karfe hudu na yamma ya iso saudi, bai tsaya ko ina ba sai gida directly, dawowarshi yayi daidai da dawowar hidaya, after 2 long week of tafiyanta,saida ya jira tayi parking harta fito kafin ya dan nunfasa tare da sauke ajiyar zuciya, wannan ce tafiya ta farko da yayi tun bayan dawowarshi kasar kafin ya samu amnesia harya warke ba tare da ya sanar da ita which he feels like she doesn’t need to know, bawai dan yana boye mata ba kawai dai yanajin shes doesn’t have to know don baisan yanda zatayi reacting to abun ba shiyasa bai fadama kowa inda zaije ba ammu ma daya fada mata yayi hakan ne don yasan zata sa ido akan sabeeha da babyn shi dake cikinta, don kwata kwata hankalinshi ba a kwance yake da fadwa ba, yasan yanda she’s loose and obsessed akanshi, which he feels zata iya cutar da sabeeha, tun ranar ma dayaga juice dinnan da aka bata hankalinshi bai kwanta da kowa ba a gidan.

Hidaya na fitowa ta dubi inda moton shi ke parke harya futo daga motar ya kulle tare da tunkarar inda take.
Babu abunda yake sai kamshi mai sanyi, Yana karasowa inda take ya rungumeta, tare da pecking kumatunta yanda larabawa keyi, fuskanshi na nan yanda take babu yabo ba fallasa ya gaisheta, itama dai girman kanta baisa ta sauya fuska ba ganinshi, tadai amsa shi suka shiga cikin gidan tare.

Ammu dake zaune a sitting room tana ganin shugowarsu ta miqe har suka karaso inda take, shine ya fara pecking kumatunta kafin ya matsa hidaya ma tayi, aladace dake nuna respect ga elders saidai su basu fiye practicing dinta ba yanxu haka ba don taga yayi ne badan haka ba suna gaisa zata wucewar ta sama.

Hidaya ce ta fara wuce wa sama kafin ammu ta dube tare da tambayarsa how was his trip yace mata alhamdulillah.
Ganin yayi shuru yasa dabara tazo mata tace
“Ay jiya she couldn’t sleep, she’s nauseous amma na kaita asibiti and sun bata medication,”
Girgiza kai kawai yayi ba tare da yace komai ba ammu ta sake cewa “tajudeen”
Dago da lumshashun idanunshi yayi ya duveta “you have to be giving her more attention, she needs us now, kasan pregnancy hormones, yanxu da babu iyayenta a kusa she needs you the most”
Nan ma dai baice komai ba ya miqe tare da mata sallama.

Su afiya kwata kwata basu san ya dawo harma da sonata don a lokacin sun fita basa gidan.

Sabeeha na kwance a couch barci ma yayi gaba da ita ba tare da saninta ba don tana ta faman aikin tunanin tun bayan datayi sallar isha’i.
Tundaga nesa ya hangota, tana nan yanda take babu abunda ya sauya a tattare da,fuskanta so innocent babu wani hayaniya.
Takowa yayi daidai wajen kujeran da take kwance ya tsaya a tsaye hannunshi biyu cikin aljihu ya zuba mata idanu, tambayar kanshi ya soma yi, maisa iyaye zasu zabarma yayansu rayuwar wahala rayuwar aikatau? Komi wahalar rayuwa wannan ba hujja bace da zaisa su bar yayansu suna wahala suna kawo masu abunda ba responsibilities dinsu ba na iyayen, yanxu ga wannan baisan daga wata uwa duniya take ba, tunda ya tambayeta dalilinta zuwan nan data fada mashi mamanta ta kawota abun ya tsaya mashi arai kuma bai tambayi ina mahaifinta ba, shes so young and beauti….
Saurin kauda kanshi yayi gefe ya nufi hanyar bedroom.
Gab da sallahr magrib ta farka bakinda dauke da salatin annabi, abu na farko daya fara kai mata ziyara shine kamshinsa da yake bin sahu, kwata kwata bata kawo cewa ya dawo bane,miqewa tayi ta nufi bedroom din kai tsaye ba tare da wani tunani ba, tana shiga ta nufi hanyar bathroom, tana kokarin budewa kawai ya budo daga ciki, a razane tayi baya don ta taorata sosai batayi tsammanin shine ba kwata kwata, saida ta tabbatar shi dinne ta gyara tsayuwar wani irin shimfidedden murmuahi ya sauka akan fuskanta ba tare da sanin ta,tambayar kanta ta soma yi ko yaushe ya dawo? Kai abun ya bata mamaki.
Ganin ta zuba mashi manya manyan idanun nan nata yasa ya dage gira daya fuskanshi bai sauya ba ya mata alamun yadai?
Saurin sauke kanta kasa tayi a natse tace “sannu da dawowa”
“Thanks” ya amsa fa a gajerance yabar wajen.
Wani irin sanyin dadi taji aranta kafin kuka ta kauda duk abunda ke ranta ta shiga ta dauro alwala a gurguje ta fito.
Harya tada kabbarar sallah tayi hanzarin bin bayanshi har suka sallame.
Bata son shishige mashi da yawa don har yanxu maganganunshi na ranta wannan yasa tayi hanzarin tashi ta nufi hanyar futa daga dakin
“I need coffee” tsayawa tayi tare da juyowa ta kalleshi,gabanshi kawai yake kallo bai kalleta ba,
“Tohm” tana kaiwa nan ta wuce kitchen direct ta hada mashi coffee mai kauri da zafi sosai tasa a tray mai kyau, tana futowa saiga ammu ta shugo dakin da kyakyawan plate a hannunta guda biyu, sabeeha na ganinta da murmushi akan fuskanta ta gaidata.
Kallon cup din ammu tayi tace
“Coffee zakisha ne fatima”
“No didi ne yace na hada mashi”
“Shikenan ma, daman daxu nayi kunafa snacks dinmu na larabawa, ki hada ki kai mashi, kema ga naki”
“Wow thank you ammu”
Dora mata dayan plate din ammu tayi akan tray dayan kuma ta ajiye mata akan center table sannan ta mata sallama fuskanta dauke da murmushi.

Dakin ta shige tare da sallama, ya amsa ciki ciki, yana zaune kan resting chairs din dake dakin, takowa tayi har ind ayake ta ajiye a kan karamin stool dake wajen sannan tace “bismillah..”
Kallon kunafa yayi don yasan bai buqaci a kawo mashi ba, ay ko tana ganin kamar zai tambaya akai tayi saurin cewa “ammu ce ta kawo yanxu”

Coffee din ya fara tana ganin haka ta juya salam salam ta fuce daga dakin zuwa parlor don allah allah tace taci kunafa din don abun burgeta yasha syrup glaze sai daukan ido yake.

Zama tayi ta fara gutsura tana kaiwa baki, yayi mata dadi sosai ba kadan ba saidai dan syrup din da aka sa da yawa, daman tana son zagi sosai wannan yasa ita sai abun ya birgeta sosai.
Ta bangarenshi shika yaci sosai don daman da yar sauran yinwa a cikinshi don tunda yayi tafiyan bai wani ci avuncin kirki ba saboda bai saba da cin abuncin wani wajen ba.

Shidai ba ma’abociin zaqi ba saboda haka bai ci sosai chan ba amma yaci wajen rabi don yanason kunafa dessert tun yana karamin.

Bangaren sabeeha tana gama saida ta dauka irin wajen 30mins haka ta tabbatar ya gama tukunna kafin ta shiga dakin, lokacin yana zaune akan couch din ya rufe idanunshi kamar mai tunani, koda tayi sallama cikiciki ya amsa wannan yasa bata ji ba.
“Zan iya packing dinsu?”
Shuru babu response, ganin haka yasa ta juya don a tunaninta ko bai gama ba, “yezz” ya amsata kamar ana fuzganshi
Tana jin haka ta kwashe ta futa dashi, tana futa ya bude shanyayyyun idanunshi da suke kokarin rufewa ahankali ahankali, miqewa ya somayi a hankali yana dafe da kanshi, tun bayan ya gama cin abunda ta kawoa mashi da coffee cikin abunda bai wuce minti biyar zuwa goma ba ya soma jin sauyi a jikinshi, wata iriyar kasala ce ta soma saukar masa wadda ya dangantata da stress din tafiya da ya danyi, ciwon kai kam yanxu ya zame mashi kamar jiki so daga ya fara jin ciwon kai jijiyoyin kanshi ke tashi, miqewa yayi ya nufi hanyar bathroom dan dauro alwala cause lokacin sallar isha yayi, yana shiga bathroom din ya soma jin wani irin azababbaen zafi, sai kuma wani irin jiri jiri dayake ji, yanajin haka yayi tunanin ko fever ne ke neman kamashi, dafe wash hand basin yayi kafin ya dago da kanshi yana mai duban mirror dake maqale a gabanshi, kallonshi fuskanshi yayi datayi wani irin jaaa sosai kamar an toya shi, jijiyoyin kanshi sun firfito rudu rudu, kunna tapp yayi ya tara da hannunshi sannan ya watsa a fuskanshi, ay ruwan sanyin nan daya sa kamar ya karama kanshi wani azama ne don ya ratsa shi.

Sabeeha na shugowa dakin ta dubi inda ta barshi zaune ganin baya nan yaza ta gane ko ya shiga bathroom, dole ta jira saiya futo kafin ta shiga, adaidai lokacin wayarshi ta soma ruri, harta tsinke wani call din ya sake shugowa, harzatayi ignoring sai kuma ta karasa inda wayan yake ta dauka, duban screen din tayi tana sunnan first love a jiki wannan yasa ta gane wake kiranshi, har zata ajiye wayar chan kuma kawai nufi hanyar bathroom din ta danyi knocking, “di..di your phone is ringing..”
Shuru babu response, wanda tasan indai yana ciki to ya jita, juyawa tayi zata bar wajen taji karar faduwar abu kasa kamar kwalba, sai kuma ta soma jin futar nishi ahankali ahankali kamar zaki..
A gaskia ta dan tsorata don bata san meke faruwa ciki ba kuma ta tabbatar yana ciki, “arhhhhhhhhhhhhhh” taj ya fidda wani irin sound mai rikitarwa, abunka da namiji babba ba yaro ba murya ta fashe, batasan sanda tayi saurin sanya hannunta kan handle din kofar ba ta bude kawai, a tsaye ta taddashi jikin wash hand basin din ya dafe da both hannayenshi kanshi a sunkuye, cikin sauri ta karasa inda yake ta tsaya daga gefenshi hankali a tashe tace “didi…meke damunka are you okay?”
Kallon brush holders din daya watsar a kasa tayi da sauran mayikanshi na kai dayake gyara duk sun fadi kasa allah yaso basu fashe ba,
Saurin kama damtsen hannunshi tayi,take taji hannun nashi ya wani murde, tana kamawa ya fara karkarwa,dan jijigashi tayi ganin bai motsa ba kuma baice mata qala ba gashi ya rufe idanunshi ya sunkuyar dakai, “didi…menene?baka da lafiya ne?”


Wani irin warmth breath ya furzar tare da dagowa ya kalleta da jajayen idanunshi wallahi saida ta razana, ya koma jaaa ga jijiyoyin kanshi duk sun bayyana.
“Let go of my hand” da wata iriyar murya yayi mata magana mai hade da sanyi da zafi.
Wallahi taka manta da bafa taj din baya bane ba wannan wani ne daban, when it comes to him da lafiyarshi gaba daya tunaninta kaucewa yakeyi.
“Wallahi saika fada min meke damunka..meysa kake min haka? Meysa baka son nasan damuwarka? Why are you pushing me away..nasan baka daukeni matsayin matarka don nasan kafi karfina amma ka duba darajar lokacin da mukeda kusanci, banida kowa saikai,kuma na damu dakai bazan hana zuciyata yin…”
Saurin turata baya yayi don maganarta tana mashi wani irin waiwaiyi don sunyi kusa kusa da juna kuma kamar rada

29 / 107