Advertisements
Chapter 101 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   101 / 107

300K to 303K   out of 320.4K words

wuce taj kuma daya dade da zuwa yana jiranta yana kallon komai, idanuntavya taru da ruwa.
Laila dake zaune a baya tana kallon yanayin hamad saitaji wani irin aranta, ita kadai tasan yanda yayanta ke son sabeeha sosai.

Washe gari haka aka sake maimaitawa, shine ya kaita kuma ya daukota, kullum fadan yau daban na hibe daban, and he’s really trying and going along with abubuwan da takeyi saboda yanajin guilt din abunda ya mata.
Ta wani bangardn kuma wannan shegen magani da maya ta saka mashi a abunci ba karamar illa ya mashi ba, har saida yaje asibiti, don tundaga lokacin shikenan ya kasance mabuqaci, daman fa yasan deep down there’s a monster in him, karfin tsoron allah ne kawai baisashi ya fada zina ba.
Amma fa da zarar ya ganta kai hatta muryarta dayaji yakejin sako ya isar mashi, hes so hard for her.
Sannan ahankali ahankli abunda ke shiga tsakaninsu ke dawo mashi, dukda ga sakamakon yanda abun ya kasance hakan baisa yaji shi cikin wata ni’ima, he wondered how abun yake, ashe it’s beyond explainable, shiyasa he’s looking up to more amma fa da yardarta da amincewarta.
What he got for her as per al’adarsu achan saudi idan mace ta bama miji budurcinta yana nan, wannan campany daya bude anan nigeria under sunanta ne ma, bayan wannan other gift suna nan a ajiye, ya maida sunanta kan inheritance dinshi na komai, hatta credit card dinshi she’s eligible to use it adul sanda taga dama basically arzikinsa dai ya zama nata, yana raye ko yana mace she has right over it kuma zata iya yanda taga dama dashi.

tun bayan abun nan baiyi gigin tabata ba ko yi mata komai, but fa duk motsinta akan idanunshi, duk wani abu da takeyi.
Ba anne kadai ta lura da how affectionate he is to fatima ba har ma nanna,saidai bata taba kawo komai aranta ba tadai yi fatan dama ace zasu so junansu?? She will be the happiest.

Ta bangaren anne kuwa ita tasan abunda take kullawa, babban shiri takeyi sosai wanda lokaci guda zata yanke hukunci kuma dole kowa ya amsa.
Bangaren maya tunda taga plan A by yuwu ba saita koma plan b, kokari take sosai wajen manipulating bahijja into making her believe idan har bata auri taj ba yanda take sonshi zata iya mutuwa, abun har tsoro yake bama bahijja don har tana cew zata kashe kanta idan har bata samesa ba.

Bahjiia tayi shirin samun anne da maganar anne ta dakatar da ita kai tsaye, bata ma tsaya sauraronta ba tace karta sake kawo maganar har abada don indai tana raye tana nunfashi taj bazai taba auren maya ba.
Bahijja a tunaninta kodan saboda yanxu an gano maya ba yarsu bace shiyasa gashi ta mata alkawari, harga allah a ganinta taj is the best for maya, zai kula da ita zai tausaya mata at least zataji a jikinta har yanxu she’s part of the family. Ta samu majeed da maganar ta fahumtar dashi shidai baice komai ba kawai yace suyi addua.

After 2weeks..
Ranar wata very weekend kowa na gida.
Anne ta shirya family dinner gaba daya kowa yazo, bangaren sameer da bangaren fadila da iyalanta kowa tace duk tanaso suzo ayi family dinner.
Misalin karfe bakwai duk kowa ya hallara a cilantro wani exotic restaurant, anci ansha Masha allah, anata hira sosai har gideo call siada akayi da yayan ya sameer dake kasar waje.
Bayan an gama duk wani ciye ciye anne tayi gyaran murya.
“Allahdullah alhamdulillah..im so blessed to present here ban mutu ba da yar uwata jinina sannan da iyalaina gaba daya, ina rokon allah ya dauwanar damu cikin farun ciki gaba daya.”
Suka amsa da ameen.
“Ina mai farin cikin shaida maku wani decision dana yanke kuma ina fatan zai zamo mana alkairi kuma zai kara danqon zumuncin mu”

Maya aka wani gyara zama ana smiling, sabeeha ko hankalinta nakan waya tana message da haya.
“Na yanke hukunci hada dana Tajudeen da jiqata Fatima sabeeha aure Insha allah..”
Take wayar sabeeha ta subuce mata, hamad ya saki spoon din hannunshi da yakeshan desserts dashi maya kuma nunfashinta ya tafi na wucin gadi, bahijja ta dubi anne, nanna ma ta dubi anne, dadyn sabeeha ko me zaiyi banda murmushin farin ciki, samwwd ya juya ya dubi dadyn sabeeha ya miqa mashi hannu yace “alhamdulillahi..kai Masha Allah allah ya tabbatar da alkairi”
Fadila me zatayi banda guda yiriyiri, anne ta murmusa tace “kuma bana son aja komai nanda Sati biyu zasu fara exams ko? Toh suna gamawa insha allahu za a daura auren fatima da tajudeen”
Sabeeha data sandare dagowan da zatayi kawai idanunta ya sauka kan nashi, take taji wani irin amai ya tokarota, abuncin ma ya nemi dawowa gaba daya ta tashi a guje ta tunkari rest room suka bita da kallo.






MATAR TAJ (destined with you)
   Written by 
          Queenmarh

Book2 
PAID
Chapter 115




Bahijja tayi shuru jikinta yayi sanyi tana duban maya tana ganin yanda take hawaye tana kuda idanu, nanna me zatayi banda murmushi ta rungume anne tace “allah ya tabbatar da alkairi” anne ta amsa da ameen tana kallon bahijja da gaba daya yanayinta ya sauya.
Sabeeha na dawowa kana ganin fuskanta kasan hawaye tayi, anne ta kalleta kawai saitayi murmushi.
Har aka koma gida sabeeha bata cikin natsuwarta, gaba daya jikinta rawa yakeyi, kanta ya fara wani irin ciwo sai zazzabi.
Kwananta biyu zuwa uku tana zazAbi ta kasa kwantar da hankalinta, kullum kuka hawaye kamar rabta zai futa, vata sonahi bata kaunarshi amma bazata taba iya bijirema na gaba da ita ba, amma fa saidai akai gawarta gidansa don wallahi bazata taba zaman aure dashi ba.
Haka ta karacii ciwonta dukta rame ta fada sosaiabun duniya ya isheta amma bata fasa maida hankalinta ga karatunta ba.
Gaba daya bahijja kuwa hankalinta ya koma ga maya, tausayinta take ji sosai, idan sabeeha yarta ce maya ma har yanxu matsayin yarta take kuma tana bala’in sonta sosai ba kadan ba.

Kwanaki sun dan ja har sun fara exam, sabeeha haka nan ta dage da karatu sosai amma ranta na cike fall da damuwa, ta gama yanke shawarar zata fada ma mamanta kawai wata qila zata saurareta.
Yanxu hamad ne ke zuwa kaisu kuma ya dukosu
Saboda exam,
Specially yasa laila ta dunga dawoqa gaba tana zama ita kuma sabeeha ta koma baya, yanda yakeyi da ita ya ragu sosai ya danne abund ake ranshi.
Zaman bayan nan fa babu alkairi a ciki, son in banda harara babu abunda ke hadata da maya, maya data ganta ji take kamar ta kasheta, ayfa bawai ta hkura bane ba akan batun taj, sun nuna mata ita bare ce ay kiwa zata nuna masu tabbas ita bare ce don zata iyayin komai ganin wannan ayren bai yuwu ba koda kuwa kashe sabeehan zatayi.
On the last day of papers dinsu sabeeha ta fara wani irin rashin lafiya, exam din da bata samu tayi ba kenan aka maidota gida,da school bus, tana dawowa anne ta kira doctor tazo ta dubata.
Doctor tazo ta dubata ta shaida lafiyanta kalau ta bata multi vitamins da dan pain killer kawai da zaisa ta danji dama dama.
Ay kuwa tana fara sha taji dama dama ta koma school akayi mata remaking exam specially tayi.
Wani abun mamaki makarantar da kayi mising paper daya shikenan saidai ka sake semester sai gashi oga na zuwa me yayi me yayi allahu akbar, tashin farko akayi engaging dinta specially tayi.
Suka koma gida sai preparation na report da zasuyi defense.
Ilimin dai babu wuya, idan har akwai kudi, yau sabewha ce ke rike da takardunta, report din da tana yin defense shikenan sai graduation ta zama a degree holder kai alhamdulillah, irin farin cikin da take ciki da godiya ga allah da takeyi daya sauya mata rayuwarta ya inganta mata ita babu abunda zatace sai hamdullah.
Allah baya barci kuma baya bari a zalinci bawansa allahu akbar.
Yau Ranar friday, juma’atu babbar rana mai girma mai daraja, ayau allah ya basu ikon kammala karatunsu cikin sauqi ita da laila, murna ba a cewa komai daka gansu, su hajiya kaya kuwa ashe semester biyu na jiranta saboda yanda ta tara carry over, tsabar bakin ciki ko zuwa makarantar batayi ba ranar, daman an gama exams anyi hutu, dan dalili ne ke fiddata which is yawan banza da takeyi.
Su sabeeha na dawowa gida aka shirya masu congratulatory liyafa mai kayatarwa,anan compound din gidan, kowa murna yake da farin ciki sosai, what a happy family, maya kiri kiri taki futowa ta hau ta hau famm fam sosai, kowa da yaji cgp din sabeeha saisu bude baki waaa, what a wonderful result, laila ma tayi kokari don itama nata 2:1 ne.
Ana cikin cin abunci sabeeha ta dubi laila tace “pass me the noodles”
Anne tace “ki tura nata duka gabanta mana tadaina wahala wajen diba tunda rabta naso”
Laila najin haka ta tura mata, anne tayi murmushi tana kallon sabeehar.
Oga kwata kwata ya kasa daina kallonta, tayi wani irin fresh, kumatunta ya futo bulbul, gashi da zarar ya kalleta sai yaga tana wani lumshe ido sexily, which turns him on, ita batasam ma tanayi ba, haka kawai data zauna take yawan jin barci just like that, saida taci noodles din sosai ba kadan ba sannan ta jawo snacks zataci kenan tana gutsiran wani pie da akayi da tuna kawai taji amai yazo mata gadan gadan, tayi saurin ajewa ta miqe tsaye zata bar wajen tayi yuuu zata fadi yayi saurin tarota, bahijja tayi gyaran murya anne ta kallesu tayi murmushi fadila tace “oh babu kunya yayan zamani..meke damunta ne i noticed tun dazu she looks pale”
Duk suka maida dubansu ga mayar, sai ayanxu suka lura da changes a jikinta annw tayi saurin breaking silence din tace “propapbly tayi karatu mai tsayi sosai dayasa tayi exhausting kanta,
Daidai nan maya tazo kamar ana wullota, fadila ta kalleta tace “ke kuma baki iya sallama ba”
Tayi banza da fadila, laila tace “ba magana mami ke maki ba”
“Dallah ance maki banji bane”
“Kinga karki fadamin maganar banza…ke ko boye bakin cikin ki bakyayi..”
“Uwar…”
“Maya!!!!!!!!” Bahijja ta daka mata tsawa ganin tana neman yin rashin kunya, yanda tazo tana surutai kamar a buge take
Sai kaqi ta fashe da kuka, daman ba a sona a gidan nan, baku taba sona ba kwata kwata.
“Keee!!!!” Anne ta daka mata tsawa sannan ta matsa dakuwa, “bahijja ja yarki ku wuce, futsarar tata har ta kaiga tazo har cikin manya tana maganar nan?? What sort if disrespect is that?”
“Anne kiyi hkuri…a bita a hankali..”
Tana fadin haka taja maya suka bar wajen tana kuka.
Fadila tace “chap akwai aiki,”
Nanna tayi shuru batace komai ba jikinta ya sake sosai, tasan matsalar maya da bahijja.
“Taj rakata ciki ta huta” anne tayi magana
Ya kamo sabeeha auka shige ciki, tun kafin su kaiga shiga ta fuzge hannunta taashi kaskantaccen kallo, “na fada maka karka sake tabani”
Ya fara matsowa kusa da ita har suka kai bango yace “why?, meysa karna tabaki? Ko kuma just hannunki ne karna taba?”
“Saboda baka da qima da darajar yin haka,”
“Niko nake dashi, kuma inada right din taba ko’ina a jikinki yanda na taba every angle if your whole body..”
Take ta soma hawaye ta runtsw idanunta ta bude kafin tace “wallahi wallahi idan kaga na aureka kaddara gawata aka kai, bana sonka bana kaunar, wallahi mai irin sunanka banson ji balle gani…kayimin abunda har abada banajin zan taba yafe maka” tana kaiwa nan tayi wucewarta, rabi dake taaye taji abunda sukace tayi gyaran murya ta wycw sadaf sadaf, tana shuga dakin sabeehar ta taddata tana kuka, rabi ta kamo hannunta cikin lallashi tace “menene???”
“Anty rabi bansan ya zanyi ba na tsane sa bana kaunarsa, yamin abunda bazan iya mantawa dashi ba kullum bana iya barcin kirki, yayi traumatzing dina”
Share mata hawaye rabi tayi tace, “indai har yana matsayin mijinki toh tabbas daman akwai hakkinsa na aure akanki kuma dole ki basa,shi iyayenmu sukayi har suka haife mu, ki saka ma ranki ruwan sanyi kinji ko?”
Sabeeha tayi shuru tana matsar kwalla, rabi ta cugaba da cewa “karki sama kanki damuwa dan allah, karya shafi abunda ke jikinki?”
Dagowa sabeeha tayi ta kalleta bata gane dai me maganar tata ke nufi ba amma ta basar kawai ta tashi tayo wanka.
Mutun daya take tunawa kawai takejin tsanaraa na raguwa wato nannan mahaifiyarsa, tana baka in son nannan har cikin ranta, itace mace ta farko da bata kyamaceta ba a lokacin da take cikin wulaqantacciyar rayuwar, saita tuna sanda take sayarda kwai, ranar sata fara haduwa da nanna.
Macece mai mutunci, mai zuciya mai kyau, mai hkuri, bata kyamar kowa, yanxu taya za ayi ace taki jininta? Ay bazata taba bari nanna taga hakan ba.
Tana wanka tana mutsika jikinta tana turo baki tace “baiyi halinta ba mace ce mai mutunci, mtewww dama nasan tun da shi dan iska ne, na tuna sanda baya cikin hayyacinsa lokacin da akayi kidnapping dinmu ya dunga taba min kirji, no wonder mteww”
Ta fada tana shafa kirjinta da suka wani irin chuchuko, tun sanda ya tattabatan nan nippy dinta har yanxu suna nan a tsaye.
Rabi na barin dakin sabeeha ta wuce part din anne tana murmushi, tace “kai fatima ba hankalin babu shekaru”
Sallamarta yaza anne dagowa tace “barka da hutawa hajiya”
“Barka dai rabi ya take?”
“Lafiya lau hajiya”
“Har yanxu tana jin haushinsa ko?”
“Eh wallahi hajiya amma komai mai wucewa ne, wallahi ina tayata murna,harma dashi, kuma duk basu san cewa allah ya albarkace su ba da gudan jini,”
“Saidai a masu fatan allah ya raba lafiya kawai rabi sannan ya basu zuriya mai albarka”
“Ashe daman mijinta ne tuntuni.. ikon allah” rabi ta fada
“Au bata taba fada maki ba kema ko?” Anne ta tambaya
“Wallahi bata taba ba kuma ban taba lura ba nadai san tunda ta fara zuwa aiki bangarensa ya hana kowa zuwa sai ita kadai hatta abuncinsa ita ke kaiwa”
Anne tayi murmushi kawai.
Dam damm gaban maya ya bada ta saki handle din kofar don harta bude, tazo dakin anne ne donta shaida mata abunda mummy ta kasa fada ma, itafa tana son taj kuma hartayi planning tace ay yayi taki ga advantage dinta ya kwanta da ita kuma tana da ciki, sai kawai taji wannan mumunan alamari, taj da sabeeha sunada aure, sannan sabewha na dauke da cikinsa?? Innalillahi wa inna ialaihi rajiun, lokaci guda ta burkice ta haukace ta futa a guje bata rufo kofarba, tafiya take amma bata ganin gabanta harta sauko kasa ta nufi part dinsu.
Wani ikon allah ne kawai ya kaita dakinta tasa key ta rufe tana duban hannunta data rike prenancy testing strip dake nuna positive, anata shirman idan taje ta nunama anne sannan tace nashi ne babu yanda suka iya dole suyi accepting ayi aure koda kuwa sunce za ayi DNA test dole saita haife dan, inma akwai wasu abubuwan medical check up da zatayi salim will cover up don yace shi bazaiyi taking responsibility din cikin ba ta zubar ita kuma tace she needs it.
Tana zuwa kuwa daidai nan kunenta ya jiyo mata wannan bala’i.
Ta sulale kasa sai hawaye ta hautsina dakin, ta fasa wannan ta wulla wannan, bahijja dataji tazo dokin taji a rufe, bugun duniya tayi ma maya maya taqi budewa hankalinta ya tshi soaai ta wuce main house, harda hawayenta.
Tana shiga ta nufi dakin anne, ta soma magana anne ta dakatar da ita.
“Wallahi baki isa ba bahijja ki tsallake maganata ko kimin iyaka da abunda na kayyade, idan kinga taj bai auri sabeeha ba saidai dayan biyu, kodai bana nunfashi, ko kuma daya daga cikinsu ya nuna baya so”
“Anne maya ma yata ce, i cant stand seeing her suffering”
“Ita kuma sabeeha ba yarki bace, ke bari kiji, maya ba yarki bace, yar hadiza ce wadda ta wulqanta rayuwar yarki ta asali, ta musan yata da tata, son ta inganta tata rayuwar,stick that to your brain, ki dawo hayyacinki tun wuri bahijja”
Tana fadin haka ta umarci ta data futa.
Bahijja ta futa jiki a mace, ta quce dakin sabeeha, tana shiga ta taddata ta shirya kwanciya, bahijja ta shugo ta rungumeta sabeeha tace “mummy…yanaga fuskanki kamar da damuwa”
Bahijja tayi shuru tana mai kaunar yar tata tace “ya akayi kike gane aduk lokacin da nake cikin wani hali”
“Saboda ina jinki har cikin zuciyata mummy”
Bahijja tace “inason tambayar abu”
Sabeeha ta tattara mata natauwarta bahijja ta cigaba “kinason wannan hadin? Kinason taj? Ki fada min gaskia karki boye min”
Sabeeha tayi shuru yanayinta ya sauya idanunta ya kawo ruwa itadai batace komai ba bahijja ta kura nata idanu tace “bakya sonshi kenan?”
Sabeeha ta sakeyin shuru, bahijja ta share mata hawaye tace shikenan, ki kwanta saida safe, sukayi sallama.
Bahijja na futa daga part din ta wuce bangarensu lokacin wajen karfe goma, ta sake komawa wajen maya shuru hankalinta ya sake tashi ta kwaso extra keys ta bude kofa, gabanta ya fadi ganin dakin upside down, ga maya a kwance tana hawaye, da gudu ta karaso wajenta alluran data gani gaban maya yasa gabanta faduwa ta soma patting fuskarta “maya maya” maya ta dago, bahijja ta kalleta tace “menene wannan kinyi ma kanki allurar ne?? Karkimin haka maya ki rufim asiri, zai lalata maki rayuwa tell me kinyi?”
Maya na kuka ta girgiza mata kai, “ki barni na kashe kaina, idan har bazan samesa ba saidai na kashe kaina”
“Noo maya bazaki kashe kanki ba, indai ina raye saikin aureshi bi’izinillah” ta karashe sannan ta rungumeta maya tayi wani makirin murmushi aranta tace “na gama yarda da maganarki, baki taba sona ba kuma akan yarki bazaki taba bari kema na aure sa ba, at the end you will still choose her over me so i will do it my own way”

After few days..
Monday morning.
Kofar main entrance aKa bude gaba daya kowa ya juyo yana kallon futowarta, sabeeha ce ta futo sanye da wani irin designer riga mai dan karan kyau sosai, tabi shape dinta ta zauna mata dap, ta saka wani hills baqi da pink color kayan jikinta , kanta ta nade shi da wani dauri mai kyau, fuskanta walwL tasha diamond rings, haka zalika hannunta dake nan fari tarr kamar ruwan madara yasha gold, ya ilahi ta yabbi samawato, ta hadu ta gaji da haduwa masha allah.
Ta saka wani irin kohl dayabi shape din idanunta hannunta rike da wata designer bag sai graduation gown da wayarta a dayan hannu, hamad yana mata kallo daya ya daukw idanunshi ya shiga mota oga kuwa kasa daina kallonta yayi, yana admiring dinta, bai

101 / 107