Author : Queenmerh Category : Complete Novels
ni ce wallahi”
“Allah sarki, wani ikon allah kenan?”
Dariya sabeeha tayi ashe har hannunta ta kama tsabar excitement, don har yau batajin zata taba manta nanna, saboda matar lokaci guda ta shiga ranta,
“Wallahi Har kika yadda wani dan hotonki ina dashi ma na ajiye shi cikin kayana kafin na tafi saudi”
“Saudi? Meya kaiki saudi?”
Shuru sabeeha tayi ta dan dakata batason tuna abunda ya faru a baya kwata kwata,
“Aikatau naje yi achan”
For few seconds babu wanda ya sake magana, yanayin nanna ya sauya gaba daya, “allah sarki yanxu na kara yarda bazaki taba yima kowa sata ba saboda kinada amana, dare yayi yanxu jeki kwanta”
“Nagode sosai hajiya saida safe”
Sukayi sallama nanna ta bita da kallo.
Hilton….
Misalin karfe tara da rabi daidaiya shigo, dakin bayan sunyi sallama da salim daya saukeshi, workers din wajen suka biyoshi da shopping dayayi ma kanshi na abubuwan da zai buqata na zamn da zaiyi.
Fuskanshi na kalla, ya shanza hair cut kuma ya amshe sa sosai don yayi kyauba kadan ba, ga gashin bakinsa daketa fama kyalli yasha gyara.
Agogon hannunshi ya zame a je gefe sannan ya shiga ya watsa ruwa mai zafin gaske sannan yayi ordern brunch na dare aka kawo mashi yaci kadan saboda tashin zuciya dayakeji sama sama.
Nan yasa akazo aka kwashi abunci don bai wani ci na kirki ba.
Yana zaune laptop dinshi nakan cinyanshi yana aiki da yan dube dube call ya shugo mashi, kallon screen dinshi nayi to my surprise kawai naga wani hoton sabiha da fuskatan yayi zooming sosai, tayi murmushi, skin dinta kamar madara ga dan v lips dinta yayi wani irin jaa gashi idanunta sun fito zara zara, ya dade yana kallon wayar bawai mai kiran yake kallo ba sai fuskarta daya kasa dalilin saka hotonta da yayi akan screen dinshi, ya dade sosai har call din ya katse kafin wani ya shugo ya dauka yasa speaker.
“Hello sir!!”
“Yes saalem?”
“How are you feeling now sir? Ko nazo muje asibiti?”
“No its just minor headache, will feel much better by tomorrow”
“Okay sir please let me know idan kana buqatar wani abun at anytime”
“Thank saalem” taj ya amsa shi don haka yake kiranshi.
Yana kashe wayar ya shiga messages din da merk ya tura mashi, yana dubawa, reports ne ya turura mashi na avubuwan da suka faru tsakanin jiya da yau.
Dayaga labaran dake circulating akan hidaya sai yaji zuciyar na karaya, wallahi wholeheartedly ya dauketa a matsayin daya bata kafin tayi watsi dashi tayi disappointing dinshi, kuma yana tausayin barad da jamid, albarkacinsu ne kawai zaisa bazai saka hannunshi ba cikin almarin don idan yayi haka she will be behind bars forever, yanxu ana trail ne da da ita kuma taqi bada hadin kai.
On the other hand baiyi mamakin ganin live press release din fadwa ba, he never trusted her and he will never, yasan this will be the out omen yanda sukayi ma khaal suka cireshi daga family saboda laifinshi haka tayi ma hidaya ta nuna kwata kwata kamar ba yar uwarta ba,ta nunawa duniya basusan haka hidaya take ba ta juya mata ba, wannan shine tsantsar cin amana, kuma company will not be responsible for hidayas wrong doings.
Kashe laptop din yayi jin gaba daya wani zazzabi ya saukar mashi gaba daya.
5am..da kyar ya iya bude idanunshi, rabin daren nan ko barcin kirki baiba kwata kwata, he feels so weak, sai faman bayan gida yake shiga, yayi stooling akalla sau goma a daren, dakyar ya iya runtsawa bayan sallar asuba yayi barcin wahala.
Around 10am jikin dak sai faman zafi yake dole ya kira salem akan yazo ya kaishi asibiti.
10:30 saleem yazo suka wuce asibiti, sai daurewa yakeyi don inka ganshi bazakace bashida lafiya ba karfin hali.
Tuna isowa deda hospital saleem yayi parking sannan suka shiga shi ya zauna a reception salim kuma ya bude mashi file yayi duk wani payment da zaiyi, yana gama wa ya buqaci ganin one of the best doctor immediately,wata nurse ta mashi jagowara zuwa office din.
Asibitin irin asibitocin kasar wajene, standard dinshi da komai.
Lift suka shiga zuwa 3rd floor inda office din yake, ya shiga yaga doctor, sannan yasa a mashi test sannan ya mashi allurai don ya samu karfin jikinshi for now.
Kuma yaji dan dama dama sannan ya sauko kasa akayi test ya zauna don jiran result.
Vip Consultation room 3
Cikin dakin doctor ne zaune yana duban screen dinshi, ga patient dake zaune tana fuskantarshi.
Cire glasses dinshi yayi wannan yasa tace “dr barau akwai wani matsala ne?”
Sauke ajiyar zuciya yayi ya kalleta baima san ta yanda zai fara mata bayani ba, he has been her specialty for over the years kuma shike traking conditions dinta koda yaushe, yayi mamaki how he missed on this important issue.
“Karka cemin hawan jini ne fa? Don ga magunguna na nan na chanye su”
“Hajiya akwai matsala..”
“Wace matsala kenan?”
“You’re having a brain turmo hajiya ”
Dan murmushinsu na manya anne tayi tace “thats an expensive joke doctor barau, har lokaci na yayi kenan?”
Shuru ya danyi kafin yace “hajiya we’ve been turning blind eye on this, it has reach to a point that zai iya…”
“Zai iya zamowa ajalina?”
“Yes hajiya, we need to operate on you as soon as possible”
“Kanada assurance din zanyi surviving ne?”
“20%”
Tanajin haka kawai ta miqe, “hajiya listen to me,”
“Babu abunda zan tsaya naji fa barau, and ina baka umarin karka shaida ma kowa wannan, i want to keep it from everyone”
“Hajiya your family needs to know cause you will need them the most now”
“No barau, bazaka fadama kowa ba, i want to keep it confidential.”
Girgiza kai kawai yayi yace “hajiya please”
Batama tsaya sauraronsa ba ta fuce daga office din kirjinta na bugawa sosai, kafarta ya rike kyam sosai kamar ana rarraba kashushuwanta.
Hanyar lift ta nufa masu maintenance na daga tsaye suna aiki saboda lift din ta tsaya chak, dole mutane aka koma wajen private escalator, saida ta tsaya duk mutanen wajen suka hau tukunna kafin ta hau bata ganin gabanta haka ta hau escalator dinnan.
Zuciyanta ya karaya,it feels so heavy,kamar rock, ga wani jiri jiri da takeji, idan manyance yazo yana zuwa da kalubale iri iri wannan yasa ta fidda hope kawai idan ajalinta ne wannan babu wanda ya isa ya hana.
Baifi few steps ba ya rage ta sauko kasa kawai ta kasa daga kafarta taji ta wani sandare ta kasa daukanta.
Taj dake zaune reception tun daga sama ya hangota, kuma mistakenly ya dago idanunshi ya hangita saiya kasa daukewa kamar wanda ke karantar ta, kamar wanda keyi wani calculation ko ya karanci halun da take ciki yayi hanzari miqewa a guje kamar zai tashi sama aka bishi da kallo daidai inda ya kamata ta sauka kawai kafarta yayi trumbling jiri ya kwasheta tayo gaba cikin ikon allah ya taro saidai wani hanzari ba gudu ba dukda ya tarota hakan baisa mayafinta ya shige cikin lift dinba ya nemi shaqe mata wuya, fadin irin tashin hankalin da yake ciki bata lokaci ne,tuni security suka karaso aka kashe escalator din, kamar zai hauka haka ya soma warware wuyanta daya shaqe sosai don kanar zatayi passing out yana gama cirewa kawai ya kalli fuskanta, wani irin tsoro shock ya dabaibayeshi, baima san sanda ya furtaa..
“Ammi!!!!!!!!” Ba…..
Sama sama anne ke ganin mutanen dake wajen kafin ta sume akayi gaggawar wucewa da uta dakin gaggawa aka kwantar da ita aka bata taimakon gaggawa.
Abun ya ahde masu biyu, ga situation dinta ga shock dayasa tayi passing out ga hawan jini datake dashi amma ta boya familyn gaba daya don ko sameer bai sani ba.
Da taj aka tafi da ita emergency ya kada zaune ya kasa tsaye, yama manta da tashi rashin lafiyar, wani irin fargaba da tsoro yakeji, yana tsaye doctors da nurse na shige da fice.
About 30mins later wata nurse ta ya futo daya kasa hkura saiya tareta yace “whats going on in there? Hows she? Mwke damunta?”
“Please what are you to the patient”
Daburcewa yayi ya rasa answer da zai bata “excuse me sir? Who are you to the patient?”
“I’m her son now tell me what is going on? Meke damunta?”
Yanda yake magana zaka san hankalinshi baya jikinshi.
“I’m sorry sir, she’s in shock rn, and jininta ya hau sosai probabbly saboda news din daya risketa”
“Wani news kenan? Meke damunta?”
“She has a stage 3 brain turmo”
“Nurse betty” wata ta kirata daga ciki ta wuce ta barshi a tsaye
Baya ya danyi, yanajin wani irin abu gaba daya ya kasa controlling kanshi, first of all akan idanunshi ta kusa faduwa kuma irin faduwa kamar wannan can lead to shanyewar jiki secondly, ya rasa dalilin dayasa yakejin wani irin tattare da ita.
Yana nan zaune doctors biyu suka fito doctor barau ya kalleshi ya miqa mashi hannu yace “thank you so much for saving my patients, you have really a saving grace, badan kaiba komai zai iya faruwa were really grateful”
Girgiza mashi kawai taj yayi tace “hows she? Is she going to survive this?”
Da mamaki doctor ke kallonshi yace “survive?”
“Brain tumor??”
“I guess you had from the nurses?”
“Yes im sorry, hankalina ya tashi ne i wanted to know wani condition take ciki”
“Well shes safe now, but i dont think she will be tomorrow?”
“Why???” Taj ya tambayeshi, “it’s confidential information”
Hannu suka kara gaisawa sannan doctor ya wuce shi kuma taj ya shiga dakin,
A zaune ya tadda anne ta fizge drip da aka saka mata yanxu, kokarin saukowa tayi yayi hanzarin karasowa inda take yace “ma’am please don’t”
Kallonshi anne tayi ta kasa duake idanunta akanshi sai kawai murmushi ya kubce mata ta koma ta zauna shima ya zauna a gefenta yace “how are you feeling? Did you get hurt in any way ma’am”
Hannunshi anne ta kama ta rike ganin kamar ba bahaushe ba don appearance dinshi ya nuna hakan kuma musulmi ne don yayi mata sallama yasa tace tace “whats your name?”
“Tajudeen!!!”
Saida ta nanata sunan aranta sannan tace “thank you so much tajudeen may allah bless you for me”
Jinjina kai kawai yayi sannan yace “karkisa damuwa aranki ma’am, you have your family, they will stay with you and stand by you i promise,”
“I don’t have….”
Bai bari yaji mai zatace ba don yaui tsammanin zatace mashi batada family itako so take tace mashi batada courage din fada masu.
“You have one now! I will stand with you,”
Da mamaki take kallonshi tana hango yanda jikinshi yayi sanyi, wannan shi ake kira da pure mutun, ya ceceta daga halaka a lokacin da kowa ne zai iya hakan ba, ta lura da gefen hannunshi daya kurje ma shi bai lura ba.
“Duk wadda ta haifeta tayi haihuwa mai amfani ga alumma, allah ya baka abunda kake nema duniya da lahira, ko na mutu yanxu i have achieved everything”
“No ma’am bazaki mutu ba.. i promise, sai lokacinki yayi”
“Toh ay lokacin ne yayi tajudeen, zan iya mutuwa koda yaushe”
Idanunshi sunyi jaa sosai jiniyoyin kanshi na futowa ridu ridu kamar shine yake sharing pains dinta yace “no ma’am, i promise you zaki samu lafiya, cuta ba mutuwa bace, kuma duk wata cuta nada magani, mutuwa kuma sai lokaci yayi”
Hannunshi ta rike gam sosai tace “okay okay I believe you okay???”
Tana fadin haka ta moqe tsaye ya taimaka mata, yanajin kamar sunyi sharing relations haka itama takeji game dashi, doctor ya shugo daidai lokacin ya bata magangun dayayi prescribing sannan ya roki next ganin da zaiyi its for her acceptance don ayi mata aiki.
Tadai girgiza mashi kai kawai sannan ta fita.
Taj na rike da magungunanta suka karaso wajen lift zata shiga yyi hanzarin kama hannunta ganin zata dafe, suka shiga lift din.
Duk sukayi shuru anne ita tasan tunanin da take akanshi, don irinsu ne one in a million.
Har waje suka fita saleem na zaune cikin mota yanajin kida baisan sun fito ba.
Har bakin motarta ya rakata sannan driver ya bude baya “ma’am”
“Call me anne”
Dan sunkuyar da kanshi yayi sannan ya dago ya kalleta yace “An..ne, please promise me youll be fine,?”
“I will insha allah tajudeen”
Yanason ya karba contact dinta amma bayason zaqewa wannan yasa ya juya ta dakatar dashi ya dawo da sauri ta miqa mashi wayarta tace, “samun number ka anan”
Wani irin farin ciki ne ya bayyana akan fuskanshi ya rubuta yayi dialing number ya shigo wayarshi sannan ya mata sallama anne na yaba halayyanshi, very nice and gentle man.
Yana nan tsaye sukabar wajen ya koma mota ya zauna saleem ya karbo mashi magungunan da aka bashi da result dinshi, its just food poisoning, cimar da yake bata amshi cikinsa ba tukunna.
Jiki a mace anne ta koma gida tana tuna tajudeen, yanayin yanda yake very soft kanar hamad favorite jikanta sai takejinshi kamar jikanta shima.
Gaskia duk wadda ta haifesa ta iya haihuwar alkahiri, well mannered and respected young man, baisanta ba bata sanshi ba amma lokaci guda ya shiga ranta.
The next morning..
Su sabeeha suka koma school, ita da maya saidai harara, laila kuwa wani irin kunyanta takeji sai take ganin kamar sun hada bakine da maya, sabeeha kuwa batada riko, bata kawo komai aranta ba kwata kwata.
Nanna ta bata wani irin confidence, datakejin she can stand for her self a ko wanne lokaci.
Suna shiga first class awa daya da rabi suka fito suka shiga next one.
Ana gamawa ta tattara littafanta as usual saida kowa ya futa ta tashi.
“Hiii” taji daga bayanta.
Dakatawa tayi ta juyo karaf idanunta ya sauka kan wanda ta taimaketa jiya.
Excitedly sabeeha ta karaso inda take tace “hey…ya kike? Inata nemanki”
Dariya haya tayi tace “toh gani”
“Thank you so much for yesterday”
“Don’t thank me okay nasan bake kika dauka ba ay, nasan wacece ta aje maki ba tare da saninki ba”
Da mamaki sabeeha ke kallonta, hannu haya ta miqa mata tace “Haya”
Sabeeha itama ta miqa mata hannu tace “sabeeha”
“Nice,can we be friends?”
“Yes sure we can”
Haya kyakyawace sosai masha Allah, kuma farace saidai siririyace don batada qiba.
Gata yar gaye don dressing dinta kadai abun kallo ne masha allah, decently.
Aranar dai kawance ya kullu kamar an dade da sanin juna,haya ta jasu cafe ta saya masu abubuwa sosai sabeeha ta rasa bakin godiya, sukaci suka sha suka koma class, lokacin tashi nayi Haya ta wuce motarta maya ta tsaya jiran ya hamad, yana isowa su maya ma suka fito.
Tana komawa gida nanna tasa a kirata, lokacin hadiza batanan tana baya tana wankin kaya da maya ta bata.
Wato shakuwa wani abu ne da baka sanin lokacin dake shiga taakanin mutun da mutun, lokaci guda ta shiga tsakanin nanna da sabeeha, sabeehar da bata da sakewa saita sake sosai da nanna harda taya ninke kaya, ta gyara mata gadonta.
Abun yayi ma nanna dadi sosai don yarinyar tun lokacin nan ta gama shiga ranta.
Washe gari ta kama friday, its a short day, bayan first class da suka fito second one din lecturer din yayi delaying dole suka tsaya jiranshi wasu suka fito bakin auditorium suka tsayatsaya.
Sabeeha da Haya na tsaye suna hira some ither student ma na tsaye, click dinsu maya sukazo wucewa, kamar bataga sabeeha ba haka tazo ta gefen wajen other end din stairs din wajen ta watso mata books dinta akai, duk akan idanun haya kuma wasu daga ciki student sun gansu
“Oppsss sorrieee”
Kauda kai kawai sabeeha tayi maya ta miqo mata hannu alamun ta dauko mata books dinta, kamar bata ganta ba haka sabeeha tayi ta kauda ido maya ta kufulu soaai kamar zata tashi sama kuma ta kudiri niyar kunsasa mata, rai a bace ta duqa ta dauki littafan daidai lokacin haya ta gama cin bananas data dauko daga jakarta, ta wulla wajen hanyar stairs din ta kauda ido kamar batayi ba har wani counting takeyi don tason dole maya ta taka bananas din.
“One two three four..”
Tun kafin tace five ji kake timmmmm a kasa tayo baya kan duwawunta ta dunga sauka daga benenen a haka, me za ayi banda dariya, so embarrassing, maya kamar ta nitse harma masu video, kamar tayi kuka kawayenta sukazo suka taimaka mata ta mike ta bar wajen a guje tana kiran wayar saleem.
Sabeeha dake dariya kasa kasa tana dagowa taga haya na daga mata hannu suka tafa.
Haya tace “serves her right..no one dares to mess up with my friends”
Anatse sabeeha tace “thank you haya”
“Fadamim meysa take treating dinki haka? Meysa baki ramawa? Ki koya mata hankali mana”
“I çant haya”
“Meysa?”
“Saboda ni yar aiki ce a gidansu, ni ba kowan kowa bace banida gata banida kowa”
“Kinada gata sabeeha, and i promise to stand by u okay”
“Thank you haya.”
“Zanyi maganin ta ne idan naga dama bazata kara tako kafa school dinnan ba”
Da mamaki saveeha ke kallonta haya ta ja hannunta tace “bakisan koni wacece ba ko? Bana fada ne, nice first and only daughter na founder din makarantar nan, Haya baba Datti”
Baki sabeeha ta kama tsabar shock yanxu wannan yar me makarantar ce? Ba girman kai babu dagawa? Ikon allah.
“Aje wannan shock din naki ga lecturer yazo muje class”
Transcorp hiltons hotels…
Kallon wayar yake da mamaki, yanxu nan ya gama tunanin ta saiga call dinta ya shugo unexpectedly.
Jiya sun dade sosai a waya, kuma duk tsawon wayar nan encouraging dinta yakeyi yana nuna mata cewa she’s not alone,he understands her fear saboda tsufanta and he wants to help her through the journey, yanajinta kamar uwa, kuma wallahi duk a tunaninshi batada kowa.
Sannan daga baya ta tambayeshi about himself ya fada mata komai bai boye mata ba, kasar mahaifarshi da inda ya taso da abu daya ne bai fada mata ba rayuwar da yayi a baya da dalilinshi na zuwa nigeria kawai dai yace mata wasu ayyuka ne suka kawoshi nan, dake macece wadda tasan harkar business sosai and she has interests in the field tunda hannunta yayi aiki a ciki over the years, taji dadin iin yanda yakeda nashi experience din.
Abunka da wayyayu sai suka zama very close lokaci guda, ita kanta tana mamakin yanda ya shiga ranta lokaci guda.
Dagawa yayi cikin hanzari bakinsa dauke da sallama.
“Walaikum salam tajudeen, how are you my dear”
“Hamdullah, how are you feeling? Kinasha medication? Akwai avunda ke damunki?”
“I’m fine tajudeen, thank you for your concern, i will like to invite you for dinner this evening”
Murmushi yayi ya dubi agogon hannunshi, hopefully zai gama abunda yake kafin lokacin.
“Tajudeen are you there?”
“Yes anne i am…”
“Please inason kazo, I will like to treat you dinner with my family to thank you enough for helping me”
“Insha Allah zanzo..zan aje duk wani plans dina for the day”
Wani irin dadi anne keji ganin yanda yake answer ta with