Advertisements
Chapter 5 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 107

12K to 15K   out of 320.4K words

shugowa ne yayi breaking silence din, daukar wayarta tayi ta bude message din, take hoton mutallib ya bayyana, a kasa an rubuta agent mutallib da bayanan shi duka harma da inda yake a yanxu, saurin waro idanu hidaya tayi ganin tabbas ta taba ganin fuskar saidai ta mance ko a ina ne.
Wani mesaage din ne ya sake shugowa,wayar na hannunta, sunan tareeq ne ya bayyana wajen mesaages din nata…..“


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 59

Wani mesaage din ne ya sake shugowa,wayar na hannunta, sunan tareeq ne ya bayyana wajen mesaages din nata…..“
Da mamaki take kallon sunanshi dayayi popping kan screen dinta da message din daya tura mata “i have to something very important for you”

“Ukty!!!!”
Fadwa ta kirata, “are you listening to me?“
Hankalinta yayi nisa sosai wajen kallon screen din wayarta,kwata kwata bata jin abunda fadwa ke fada saboda tayi nisa wajen nazari, karar landline din dake kan table dinta ne yasa ta dauke idanunta daga kan wayar, for the second time ya sake kara, dagawa tayi takai kunneta,“yes let him in” kawai ta iya fada kafin ta ajiye landline din ta zauna kan kujerarta.

Bayan yan seconds da ajiye wayar landline aka budo kofar, dagowa sukayi gaba dayansu suna kallonshi, da mamaki fadwa ke kallonsa surprisingly, shima baiyi expecting din ganinta a office din hidayar ba, kuma a daidai wannan lokacin, nan take ya soma contemplating anya wannan ba bad timing bane,don yasan idan suka koma gida definately saita tuhumeshi qila ma tayima zuwan nashi mumunan fassara.

Takowa ya somayi ya karaso seat din baki fuskanshi a washe, yace “ahlan wa sahlan ukty, babes ashe kina nan, what a concidence, i was passing by shine nace bari nazo mu gaisa da ukty”

“Save all this drama ka fadi abunda ke tafe dakai, What could be so important that you texted me just now,” hidaya ta fada babu wasa akan fuskanta tana mai fuskantarshi, wani irin mugun miyau ya hadiye ganin irin kallon da fadwa ke mashi, dan dole ya tattara courage dunshi ya saka hannunshi cikin aljihunsa ya zaro wayarshi ya danna kafin ya ajiye akan table din, muryar sabeeha ce ta bayyana da ta mutallib ashe yayi recording conversation dinsu gaba daya,confusely fadwa ke sauraron recording din hidaya data gane akan me suke magana tuni hankali ya soma tashi, recording din na karewa ya dauka wayar ya shiga wajen pictures wanda ya dauke su ba tare da saninsu ba ya ajiye mata a gabanta yace “I dont know what they have been talking about but i just feel like ya kamata ki sani,”
“Wannan yarinyar yar leken asiri ce, shi wannan shine ya kawota gidan, sannan naji sunata maganar wani file da yake hannun jamid, sau biyu ina ganin su tare a boye suna maganar ba tare da sunsan na gansu ba shine nace you might need to know about this, cause ina tunanin they have been cooking something up, ni daman tun farko ban yarda da yarinyar nan ba”

Tunda ya soma magana fadwa take cije lebe, idanunta yayi jaa sosai,bata taba expecting haka ba, her plan where going smoothly yanda ta tsara komai gashi yanxu ya ruguje mata shirinta.


Daukan wayar hidaya tayi ta kura ma picture din idanu, sai kawai ta runtse idanunta, she was so amazed by how wannan agent din yayi tricking dunta,for over a month now hes been hiding under her shelter, ba tare da saninta ba, gaba daya lokaci guda saita sauya kamar ba hidaya ba, miqewa tayi tsaye ta dauki wayarta, suna ganin haka suma suka miqe kota kansu batabi ba ta fuce daga office din.
Tana futa fadwa ta kalli tareeq, wani irin mugun kallo take aika mashi itama zari jakarta ta fuce daga office din, shima ya mara masu baya.
Kowa motarshi ya shiga suka fuce daga kamfanin a guje musamman hidaya dake bama motar tata wuta,


Taheel residence

Hankali a tashe ya miqe zaune daga kwnace da yake wayar dake hannunshi na wajen kunenshi yace “what!!!”
“Yes sir, i think you’re in danger, sun gano inda kake you have to leave now!” Daga cikin wayar aka amsa shi.
“Ya akayi suka gano? I thought you have handle that?”
“Sir thats not important now, you have to leave now”

Saurin sanya rigarshi yayi a jikinsa ya futo daga dakinsu na ma’aikatan gidan, da yake safiya ce, ma’aikantan gidan kowa ya futo yana aikin gabansa, gaba daya hankalinsa ya gama tashi, bazai yuwu yabar gidan ba, yanxu idan ya tafi bashi da wata hanyar dazai tseratar dasu, gaba daya yaka rasa wani tunani zaiyi? Tunawa da last call din da sukayi da khaal yasa shi karaya inda yake cewa “agent mutallib kai kadai zan iya trusting, ko bana nan promise me that you will protect tajudeen da fatima,saboda nasan rana irin ta yau zata iya zuwa yasa nayi shiri tun wuri,the only person that i want you to trust is
Fatima!!!Zaka samu komai wajen fatima”
Dakatawa yayi tare da yin nazari, tunawa da wannan, “fatima!!”
“Shit, how did i miss on this, that mean original file din na wajen fatima kenan? But meysa ta nuna bata san me nake magana akai ba?”

Bai gama wannan tunanin ba kawai ya jiyo ihu daga cikin gidan, sabeeha dake saukowa daga sama hankali a tashe tana bin digon jinin data gani tundaga gadonshi,har zuwa kasa,
Wani irin wahalallen nishi ta soma fitarwa tsabar furgici ta karaso daidai wajen entrance din shugowa gidan ta ganshi kwance, head maid na tsaye a kanshi da sauran maids sunata faman “sir sir”

ambaton sunan Allah ta soma yi ganinshi kwance kamar wani matacce, “innalillahi wa inna ialaihi rajiun, didi didi wake up, na shiga uku wannan wace iriyar masifa ce, someone should be call the ambulance”
Ganin dukta burkice yasa head maid tace “ma’am please calm down mun kira madam tace tana zuwa yanxu”
Rai a bace sabeeha ta dago tana kallonsu tace “sai an jira madam ta iso? Idan ya mutu kuma fa? Ku wane irin azzalumai ne”
Muryar sabeeha dayaji ne yasa ya tunkaro wajen, sauran ma’aikatan gidan maza da suke kula da waje wajen gidan kowa ya maida hankalinsa wajen aikisan kamar basu san abunda ke faruwa ba, saboda rules ne aka kafama masu babu wanda ya isa ya nufi cikin gidan,koda sukaga mutallib ya tunkari entrance din kowa mamaki ya dunga yi, yana karasowa cikin wajen entrance din ya tunkari inda taj din ke kwance, sabeeha na ganinshi ta soma shesheka, “dan allah ka taimaka mashi kada ya mutu, wallahi tun safe jini ke futa a hancinsa, dan allah ka ceceshi, mu kaishi asibiti dan allah, bana son ya mutu, wallahi idan ya mutu bazan iya rayuwa ba,”
Tunda ta soma magana mutalib ya rasa ya zaiyi, yama rasa wani decision zai yanke yanxu, abu daya ne bazaiyi ba adaidai wannan lokacin, shine bazai tafi ya barsu haka ba musamma dayaga taj a wannan yanayin,
,head maid na ganin mutallib har cikin gidan yasa tayi gaggawara cewa “kai bakasan rules din gidannan ba?Ba a yarda ma’aikata maza su shigo cikin gida ba, kana son rasa aikinka ne?”

Tsugunnawa mutalib yayi ya cicibi taj din da kyar a bayanshi kafin ya kalli inda sabeeha ke zaune yace, “lets go”
“No ma’am i can’t let you, madam tace gata nan zuwa”
Kota kanta basubi ba suka fuce daga gidan, motar da aka bashi yake tuqa barad da ita ya bude ya saka taj din a ciki kafin ya zagayo ya bude mata ta shige ciki shi kuma ya shige mazaunin driver ya tada motar, yana kunna motar yayi reverse ya nufi hanyar futa daga gidan, da yake akwai tazara sosai tsakanin entrance din gidan zuwa ga gate wannan yasa securities basu san mw ake ciki ba har suka bude gate din ya fuce daga gidan,

Suna barin wajen ko minti biyar ba ayi ba motar hidaya ta danno kai cikin residence din, tana parking motor asibitin mahaukata data kira ta iso, ita bama rashin lafiyar taj din da aka fada mata ne ba a gabanta, wannan agent din takeson ta gani a zahiri kafin tasan yanda zatayi dashi, head maid dake tsaye jiki na bari tsabar tsoro tana hango hidayar ta tunkari inda take, daidai nan hidaya ta futo daga cikin motarta, suma nurses din suka fito kattin maza har guda hudu.
“Ma’am …ma’am i’m sorry, sun tafi dashi, i try to stop them madam fatima tace baza a jira ki karaso”

Da mamaki hidaya ke kallonta tace “sun tafi dashi? Su waye suka tafi dashi,”
“madam fatima Da Sabon driver da aka kawo”
“What!!!!!!!!” Hidaya ta daka mata tsawa kamar zata fasa gidan, tuni head maid tayi baya jiki na bari tace “I’m sorry ma’am nayi kokarij hanasu tafiya dash sai….,”
Tasa ta wanke fuskarta da mari, tuni hankalin hidaya ya tashi Gaba daya ta gama rikidewa fuskarta tayi jaa sosai idanun nan sun fito wiki wiki, she didn’t see this coming kwata kwata,
Wato this is his plan all along? Lallai tayi underestimating wannan agent din, yanxu bama wannan ba,tashin hankalinta daya idan aka kaishi asibiti za a gano kwayar da ake bashi,hakan kuma zai iya zame mata babar matsala duba ga yanda ta samu kwayar, dole ta dakatar dasu kota halin qaqa.

Kota kanta hidaya bata bi ba ta koma cikin motar daidai nan call ya shugo wayarta, tana dagawa daga chan aka soma magana “we got him ma’am, he’s heading to the expressway ..”
Tana jin haka tace, “ follow him and don’t loose track of him”
“Yes ma’am”
Wurgar da wayar tayi sai kawai ta fara dukan steering din gabanta kamar zautacciya, bata tsaya wani dogon tunani ba ta kunna motar tare dayin reverse ta juya fice daga gidan,batama lura da shugowarsu fadwa ba.
Fadwa na ganin fucewarta ta maida dubanta ga motar ambulance din asibitin mahaukata dake wajen, “whats going on here?”
Shine tambayar da fadwa tayi, head maid ce ta mata bayanin komai, saida ta gama sauraronta tass kafin ta shige cikin motarta tabi bayan hidayar bayan tasa an sallami masu ambulance din, tareeq ko tunda ya fito daga taheel company hankalinshi a tashe babu abunda yake sai tunanin irin kallon da fadwa take jifanshi dashi.

Chan bangaren su sabeeha tunda suka hau babban titi mutalib ke gudu,kwata kwatabai lura da ana binsu a baya ba, saida ya nufi hanyar dazai sadasu da asibiti ya lura, bayason ya tayar mata sa hankali don haka yayi shuru baice komai ba kawai ya cigaba da gudu akan highway din,

Hanyar expressway din hidaya tabi itama, wani irin gudu take kamar zata tashi sama, wayar ta ne ya sake kara tayi saurin dagawa, da yake wayar is connected to her car so tanajin komai a bayyane, “kana ina?”
“Ina bunshi a baya ma’am”
“Where’s he heading to?
“he’s heading to jedda international hospital”
Hidaya na jin haka ta kara rudewa, tare da kara speed din motarta tace, “karka sake ka bari yakai asibitin nan, just do what ever to stop him, you have to stop him right now!!!!”
Ta daka mashi uban tsawa, “yes ma’am”

Yana kashe wayar dannama yaranshi kira, “inason ku kashe duk wani cctv camera dake kan expressway to jedda international hospital right now!”
Yana kaiwa nan ya karama motarshi wuta, daman kan titin express ne babu yawan motoci a wajen,mutabblin dake hango bakar motar dake bunshi yana ganin yanda motar ke tunkarosu ya karama motar wuta, sabeeha dake zaune gefen taj din da is unconscious sai a laokacin tunanin ta ya dawo ga mutallib ganin yanda yake gudu yana kaucema hanya,bugun motarsu da akayi ta baya yasa ta furta innalillahi wa inna ilaiahi rajiun” a gigice, juyawa da zatayi aka sake bugo motarsu, “stay still, ana bibiyarmu a baya”
Tana jin haka gabanta ya fadi daramm, maida dubanta tayi ga taj daya farfado saboda bugun motar da akayi, hannunshi ta kama gam dukda gabanta na mugun faduwa haka ta tattara courage dinta ta kalleshi, tare da kamo hannunshi ta riqe gam,hawaye na zarya kan fuskanta.
Gaba daya ya galabaita bayama jin abunda take fada, yana jingine a jikinta da kyar yake iya bude idanunsa.
Babu zato ba tsammani wata katuwar trailer tayo kansu wajen hanyar lane din da suke, gashi a bayansu ba a bar bugun motar tasu ba wannan yasa mutalib ya kasa taka burki, karshe ma burkin ballewa yayi, gadan gadan wannan trailer tayo kansu,
budewar ido da taj zaiyi idanunshi ya sauka kan trailer dake kokarin yowa kansu take kawai komai ya soma mashi flashing, memeory din lokacin da mota ta hau kashi yazo kanshi visibly sai wani dummm dayaji a kunneshi, baisan lokacin daya kama hannun sabeeha ba ya kwala kara yace “allahumma ajirnin fee museebati”

Sabeeha na ganin motar itama tayi saurin rungumeshi donta saddakar mutuwa zasuyi kawai, mutalib daya tabbatar da wannan motar kansu zatayo gashi ya kasa controlling steering motar yanaji yana gani, har motar tazo gab dasu, wani ikon allah, allah ya bashi iko juya steering din gefen titi, saboda speed din daya taka gashi babu burki dole motar ta bugi wani katon factory house dake gefen titin, ta fasa ginin kafin ta tsaya, gaba dayansu ba karamin buguwa sukayi ba musamman shi mutalib din dake gaba, sabeeha ma dake bangaren mazauninshi ba karamin bugu tayi ba saboda yanda ta juyo ta kare taj din wannan yasa ta buge sosai.
Da yake babban factory ne kuma da mutane a cikin sa tuni aka fara fiffitowa daga ciki aka zagaye motar, babu abunda motar keyi sai hayaqi, black na ganin haka ya juya akalar motarshi,ya gangara chan gefe.

Mutanen da suka firfito suna ganin accident din aka kira ambulance, sannan suka fara kokarin ganin sun fidda waenda ke cikin motar saboda hayakin da takeyi.
Gaba daya wajen lokaci guda ya karade da mutane,sabeeh dake rungume da taj gaba daya ta gama jigata tana dagowa ta kalleshi ganin baiji ciwo ba, ta sauke wata ijiyar zuciya sai kawai ta sume warr a wajen,
Shiko har zuwa lokacin bai dawo daidai ba, kunenshi ya gama toshe wa gaba daya memory dinshi ya dawo mashi yana flashing akanshi,ya runtse idanunshi hannunshi na kan kunnenshi ya toshe, baima son lokacin da aka fito dashi daga cikin motar ba, yana bude idanunshi hasken rana ya buge shi sai kawai ya sume daidai nan motar ambulance din da ka akira suka karaso tare da motar policey,cikin hanzari aka sakasu cikin motar, abun mamaki an fidda taj da sabeeha sai aka rasa matuqin motar kuma, haka aka dungumesu sai asibiti……

***
Tunda ta fara sharara gudu kan titi babu abunda ke yawo a zuciyarta sai tsoro da fargaba, idan har bata dakatar dasu daga zuwa asibiti ba wannan zai iya jawo mata babbar matsala, bama ita kadai ba saboda kowa yasan hadatin kwayar nan sannan ana neman masu ta’ammali da ita, kuma tasan definitely za ayi kwakwaran buncike, gashi ta yanda ta samu kwayar ma illegally tanan za a fara gano wa.
Bayan wannan ma plans dinta zai ruguje, dalilin bashi maganin badan komai bane sai don ta kaishi gidan mahaukata, ya kare rayuwarshi achan.

Wayarta ce ta katse mata tunani tana ganin wanda ke kira tayi saurin dagawa takai kunneta, abunda ya fada mata ne yasa ta rikide fara masifa

“You are fucking stupid, how can you loose him how?”
Hidaya ta daka mashi tsawa a cikin wayar, “i’m sorry ma’am, it happens lokaci guda, bayan na dakatar da motarsu he manage to escape”

“Su kuma fa?” Ta sakw jefo masa tambaya
“I’m sorry ma’am”
Kamar zata zauce tace “what do you mean by that?”
“An wuce dasu asibiti…..”
Wani irin cursing word ta rarumo ta afka mashi, “im going to kill you idan ka bari wannan ya ruguza min plans dina, idan nasan bazaka yimin aiki yanda ya kamata ba dana bari an kasheka a banza, didn’t you hear me correctly dazu? Nace maka duk yanda za ayi karka bari suje asibiti now what!!!!! Now whattttt answer me you bloody fool”

“And you better make sure that you come clean on this, don wallahi idan ka jawomin matsala i will Be the one to finish you my self, sannan na baka nan da yan awanni duk inda yake ka nemoshi, you had me right?”
“Yes maam” ya amsa ta da gaggawa
Gudun motarta ta kara kamar zata tashi sama,fadwa da kyar ta cin mata, har suka karaso asibiti, already an shigarda su sabeeha emergency room.
A chan gida kuwa tareeq na karasowa gida ya tadda zuwan ammu, “kanwar babansu hidaya”
Wadda ke aure a kasar waje, tun bayan zuwan datayi bayan mutuwar khaal hankalinta ya kasa kwanciya da lamarin gidan bayan tabar gidan, daman saboda mijinta ne ta koma, rana daya kuma allah ya dauki ransa, gashi batada yaya dashi zamanta a kasarshi babu amfani don haka ta dawo kawai ko sati ba ayi da mutuwarsa ba.

Acahn asibiti kuwa ba karamin shick sabeeha ta shiga ba dakyar aka samu ta farfado, koda ta farka babu sunan data dunga kira sai didi didi, akaita wajenshi,tana son ganinsa, tamaqi yarda ayi dressing hannunta da karfen motar ya buga wanda yayi sanadiyar dislocating da yayi harya kumbura, ganin hankalinta yaqi kwanciya yasa likitocin suka kaita inda taj din yake.
Room 2, ana kaita ta ganshi lokacin yana kwance an mashi allura ana jiran ya farfado saida ta tabbatar hes fine kafin ta bisu aka gyara mata hannun nata aka mata sedation daya sa barci ya dauke ta saboda radadij da hannunta keyi.

Hidaya na shugowa asibitin fadwa ma ta karaso, kusan a tare suka shiga wajen emergency ward, Hidayan dake gaba ce ta nemi ganin doctorn da yayi treating mutane biyun da aka kawo emergency for accident yanxu, nurses din dake wajen ne suka jagorancesu inda yake, gabatar da kanta ta farayi kafin ta nemi sanin condition din da yake ciki, ganin hankalinta a tashe yake yasa doctor ya soma mata bayanin, “he’s in shock for now, bai samu wani ciwo ba sannan mun bashi sedation zuwa anjima zai farfardo, idan ya farfado zamuyi mashi general test da scan don mu tabbatar idan akwai wani condition din.”
Tana jin haka ta sauke nauyayyi ajiyar zuciya sannan ta nemi akaita inda yake aranta ta kudirci bazama ta bari ya farfado ba zata nemi a mashi transfer ko kuma tasa suyi discharging dinshi.
Sai a lokacin fadwa ta fuskanci avunda ke faruwa, bayan an kaisu dakin da taj din

5 / 107