Author : Queenmerh Category : Complete Novels
kunna lights din tana mai dubanshi tace ‘’na fada maka you should save your energy don babu abunda zai hanani aywatar da kudiri na, ka daina wahalar da kanka ma’’
jamid najin haka jikinsa ya saki, hawaye na zarya akan fuskanshi, da kanta ta miqe ta karaso inda yake ta gyara mashi kwnciyarsa dukda yana kokarin tureta, tabashi da takeyi kamar tana saka mashi garwashi a jikinsa haka yake ji.
bangaren su sabeeha tana shiga bedroom din ta taddashi kwance, karasowa tayi bakin gadon bayan ta ajiye bowl din a gefen bedside table tace ‘’didi ga fruit din’’
shuru babu response ganin haka yasa ta dubi fuskanshi, lumshe idanu yakeyi kamar wani mai maye, ganin haka yasa ta janyo mashi duvet ta rufeshi kafin ta miqe ta dauki bowl din ta fuce dashi zuwa kitchen, tana shiga ta ajiye bowl din a fridge ta wuce dakin.
asuba nayi ta farka, bathroom ta shiga ta dauro alwala, tana idawa ta futo yanda ta barshi haka ta taddashi, tashinsa ta somayi, da kyar ya bude idanunshi da sukayi jaa sosai ya sake lumshe su,babu yanda batayi ba yaqi tashi haka ta hakura ta barshi yayi barcin ita kuma ta tada kabbarar sallah.
Bayan kwana biyu,
gaba daya tunanin hidaya ya koma wajen neman wannan mutalib din, abunda yasa ta asa ganoshi kuwa saboda bata san identity dinshi ba kuma duban duniya da connection din da take dashi babu wanda batayi usning ba wajen ganin ta ganoshi batayi sa a ba, da farko tayi tunanin abun mai sauqi ne sai yanxu ta tabbatar khaal has prepare for consequsnces din da zai biyo baya shiyasa ya boye identity din mtabblib din, ko mutanen dake tare da khaal din basu san mutalib dinba, gashi jamid ne kawai ya ganshi shi kuma babu yanda batayi threatning dinshi ba yaqi fada mata komai, wannan kwayar kuwa bata fasa banka ma taj ba kullum, tsabar rashin imani kwayar da ake bama masu hauka guda daya ita har uku takje afka mashi kullum, cikin kwana biyun nan lamarin taj ya soma sauyawa, sabeeha ce kawai ta lura da hakan tunda ita ke kwana kuma ta wuni tare dashi, gaba daya ta kasa gane dalilin sauyawar tasa, physically and mentally abunma harya soma bata tsoro, ya zama wani iri baya magana kwata kwata haka zai wuni bazaice mata tak ba, ga wata rama da yakeyi kamar ana zuqe ruwan jikinsa, abunci ma idan ta bashi baya ci kwata kwata sai ruwa da yakesha sosai, a rana saiyasha bottle wajen goma, haka zai zauna kamar wanda tunaninshi ya soma gushewa sometimes idan ta mashi magana saiya dunga kallonta kawai kamar bai santa ba wani sa’in kuma baya yin haka, ita tunda take dashi bai taba irin haka ba sai yanxu gashi batasan dalilin hakan ba, kwata kwata bata taba lura da magani hidaya ke bashi ba, bangaren hidaya ita datasan komai batayi kasa a gwiwa ba ta cigaba da dura mashi wannan maganin kullum tsabar rashin imani,
yau kwata kwata baiyi wanka ba yana zaune ya kurama bango idanu, bakinsa ya bushe idanunshi yayi jaa sosai, babu yanda sabeeha batayi ba ya tashi yaqi, ko gizau, abunci ma haka ta dunga kokarin ganin yaci yaqi, hankalinta bai fara tashi ba saidata ga kamarfa baida lafiya, gashi yaqi mata magana kwata kwata.
yanxu haka ma tana gabanshi, da tea, tana rokonshi akan yasha yaqi, ‘’didi meke damunka?, dan allah ka fada min, please talk to me ko hankalina zai kwanta dan allah’’
shuru bai amsa ta ba saima kafa ma bango idanu da yayi babu kiftawa, shugowar hidaya part din yasa sabeeha sauke nunfashi, karasowa hidaya tayi bakin gadon wannan ya bama sabeeha damar gaisheta, saidai kamar kullum yauma ko kallon inda take batayi ba, kallonshi hidaya tayi kafin ta maida dubanta ga tea din da sabeeha ta ajiye a gefe tace’’ meke damunshi?’’
‘’yaqi cin komai tunda safe’’ sabeeha ta amsa ta kai tsaye.
shuru hidaya tayi chan kuma tace get me some water, futa sabeeha tayi don ta dauko mashi ruwa tana fita hidaya ta kalleshi tare da shafa fuskanshi tace ‘’kana jiran wannan ne ko?,’’
yana jin haka kuwa ya kalleta tare da duban hannunta, kamar wani maye cikin hanzari ya fucike kwayoyin dake hannunta ya jefa a bakinsa ya hadiye kamar wani mayen zaki daya kwana goma baici komi ba, yana hadiyewa yayi wani sighn of relieve, take gaba daya jikinsa ya soma magnifying sai yajishi kamar a saman, haka ya jingene ya kafa mata idanu, gaba daya jikinsa ya saki, tana ganin haka ta miqe tsaye ‘’//saura kadan tajudeen, ‘’
budo kofar dakin sabeeha tayi da ruwa a hannunta, daga nesa tana hango hidayar nayima taj din magana saidai bata jin abunda take fada, haka ta soma takowa har zuwa inda suke, ‘’gashi’’
kallonta hidaya tayi kafin ta tabe baki ta fuce daga dakin.
da mamaki sabeeha ke kallonta harta fuce daga dakin, jiki a mace tamaida dubanta ga taj da tea din, tama dauka ko tea din ta tilastashi yasha saitaga akasin haka, ganin yana hamma yasa ta taimaka mashi ya kwata.
****
karfe 8 barad ya futo daga cikin gida da school bag dinshi a baya, yana karasowa wajen parking space sabon driver sa ya bude mashi ya shige baya yana zama driver yaja motar sukabar wajen.
ta jikin mirror yake kallon barad din da hankalinshi yayi nisa wajen kallon glass, ganin hankalinshi na kan notepad din dake hannunshi, wannan ya bashi damar cewa ‘’barad!! meysa kake kuka kullum idan zan kaika school’’
dagowa barad din yana kallon driver nashi, chan kuma yace ‘’ya akayi kasan ina kuka kullum?’’
‘’ina ganinka mana’’ ya bashi amsa,
‘’shuru yaron yayi baice mashi komai ba chan dai driver ya sake magana don neman kusanci da yaron yace ‘’ka daina kuka kaji, youre a big boy now, big boys basa kuka, duk da bansan dalilin dayasa kake kukan ba but if you keep praying komai zaizo karshe kaji ko?’’
jinjina mashi kai barad yayi chan kuma kawai sai ya fara hawaye, ganin haka yasa driver ya dago ya kalleshi suna hada idanu barad din ya soma magana ‘’how can i stop crying bansan inayi ba’’
ganin dama ta zo mashi cikin sauqi yasa driver saurin tambayarshi, ‘’me ke saka ka kukan?tell me kaji, when you share your burden zaka ji saukin kukan naka’’
‘’daddy na ne, i missed daddy, ammu ta hanani na ganshi, ‘’
‘’mey ya samu dadyn naka?’’ ya sake jefo mashi tambaya
‘’hes paralyse’’…..
dammm gaban mutalib ya bada, badan akwai facing cap a fuskanshi ba babu yanda za ayi baza a ga tsagwaran tashin hankali ba a tattare dashi, ‘’tun yaushe?how? daman bashida lafiya ne’’ mutabblib ya sake tambayarsa,
‘’wannan tambayoyin yasa yaron ya sake fashewa da kuka saida mutalib ya bashi hakuri tukunna ya daina kukan har suka iso school ya suakeshi shi kuma ya juya da motar.
jin abunda ya samu jamid ba karamin tashin hankali mutablib ya shiga ba, saida ya samu ya gangara gefe yayi parking motar kafin ya soma nazari,hankalinshi gaba daya ya koma ga file din daya bama jamid din, ina file din?, shiyasa ya kasa samun jamid din kenan? babu abunda yake sai innalillahi a ranshi don baisan hannun wa file din ya shiga ba fatanshi daya allah yasa jamid ya killace file din, don shi kadai ne file din dake dauke da evidence akan abubuwan da hidayar tayi a wajensa kuma baiyi coping wani ba sai na wajen khaal original copy din, daman wannan dinma khaal baisan shi yana dashi ba,gashi khaal ya mutu, yanxu wannan dinma allah kadai yasan inda yake fatanshi daya allah yasa bai fada hannun hidayar ba, kuma ya tabbatar yanxu nemansa take ruwa a jallo shiyasa ya nemi aiki a cikin gidan don ya cike alkawarin da yayi ma khaal na ganin yayi protecting sabeeha da taj.
tunanin yanda zai ga jamid ya somayi, gaba daya kanshi ya gama kullewa yama rasa ya zaiyi, tunawa da sabeeha yasa shi gyara zama, ita kadaice wadda zata iya connecting dinshi to jamid, toh amma tayaya zai ganta?, yau wata guda kenan yana aiki a gidan as driver bai taba ganinta ta sauko kasan ba ko ta futo gashi ma aikatan gidan maza basa shiga cikin gidan, bayan wannan ma ko ya ganta ya zaiyi ya samu ta yarda dashi kenan?, ita kadaice option dinshi don haka ya kudirci samun duk hanyar dazaibi don ta yarda dashi.
yau sati guda cip, duban duniya hidaya tayi ta kasa gano wanene wannan agent din khaal din wanda tunawa da yanada eveidence din da zai iya kawo mata matsala yasa ta kasa sukuni.,
yanxu haka ma tana cikin jirgin ruwanta inda ya doshi island dinta, tafiyar awa guda ta kawosu private iland dinta, kamar kullum driver dake shiga da ita wajen yana tsaye yana jiranta, tana karasowa ya bude mata baya ta zauna, daman kurma ne bayajin komai.
ciki suka shige tana hakimce zaune a bayan motarta har suka karaso yayi parking ita kuma ta futo, sanye take da abaya baqa wadda ta sauko mata har kasa tayi mata kyau sosai.
bakin hanyar shiga building din wasu qatti ne su kusan goma sun zagaye building din gaba dayan sa, sunci suit da bakin glass, kowannensu na ganinta yake sara mata, wajen ya chanza sosai ciyayin dake zagaye da bulding din duk an yayyanke su, takawa ta soma yi majestically wajen bulding din waenda ke gadin kofar ne suka bude mata ta shiga ta nufi inda take zuwa as usal, black na hangota daga nosa ya karaso inda yake tare da sauke kanshi yanda k=yake gaishe ta koda yaushe, daga mashi hannu kawai tayi tana mai kallon dakin daya fito daga ciki,
‘’any information about agent din?’’
‘’no madam’’ ya amsa ta kanshi a kasa
wani irin kallo tayi mashi rai a bace tace ‘’useless people, mutun daya kun kasa nemowa for over a week’’
‘’i apologies madam, zanyi kokari’’
dakatar dashi tayi rai a bace, ‘’i dont want words of promising just act, ya za ayi ace neman mutun daya ya gagare ka?,kanaso ka cemin ka kasa ne?’
‘’im sorry madam!!! ki bani yan kwanaki kadan’’
‘’you better take action, don wallahi idan wannan sanadiyar…..’’
bata karasa ba daidai nan aka budo kofar dake gabansu, likita ne da uniform dinshi complete, yana ganinta ya tunkaro inda take tare da rissinawa ya gaisheta,
bata ma amsa ba ta jefo mashi tambaya, ‘’menene matsalar’’
‘’high blood pressure ne madam’’ ya bata amsa, saida ta gama sauraransa kafin ta sallameshi ya tafi, ita kuma ta nufi cikin dakin, black ne ma ya bude mata kofar ta shige shi kuma yana biye da ita a baya……
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
BOOK 2 paid book
chapter 57
Update!
Black ne ma ya bude mata kofar ta shige shi kuma yana biye da ita a baya har suka shiga dakin, daki ne babba ko'ina a rufe babu wani hasken kirki sai na kwan fitila guda daya dake daukewa yana kawowa, shuru babu sautin komai dake tashi sai na nunfashi ahankali ahankali, rufo kofar black yayi yana biye da ita a baya har zuwa tsakiyar dakin.
saida ta karaso wajen katifar na fara hangen mutun daga zaune ya basu baya, saboda yanayin rashin haske na cikin dakin yasa na kasa tantance macece ko namiji.
hidaya na daga tsayen nan ta sauke ajiyar zuciya tace ''how long has he been like this?''
''tun last few months ma'am, yaqi responding'' black ya amsa ta,
''you need to make him speed, i dont have patience of waiting anymore
''yes ma'am'' black ya amsa ta, tabe baki kawai tayi ta futo daga wajen
***
Samari ne su uku suka fito daga cikin wani A class tower hotel dake nan cikin sharja, tareeq ne shida wasu abokanshi goggagu,kowannensu na ji da kudi sosai don yayan manya ne sosai, kusan shi ne ma za ace bai kaisu kudi ba saboda su iyayensu ke da kudin shi kuma auren fadwa ne kawai yasa ya samu fame.
cikin jerin motocinsu dake parke a compound din vips sabbi classic ferrari da lambor kowa ya nufa, shima dai daya daga cikin motocin fadwa ya dauko ya fito da ita don yayi bragging saboda kar a rainashi, ba karamin kudade suka kashe ba kamar basu san zafinsu ba a wajen,
daga ma junansu hannaye sukayi inda kowa ya shige tashi motar sukayi sallama.
Daya bayan daya suka soma fidda motocin su daga wajen daidai nan wasu hadaddun motaci latest lunched suka shugo compound din, har akayi parking aka soma fitowa, harya juya akalar motarshi ya dakata ganin mace ke kokarin futowa daga cikin motar, daman gashi zalamamme da son harkar mata wannan yasa ya dan dakata, yayi kuri da idanu yana kallon macen data futo daga cikin motar yana tunanin ina yasan fuskar, saboda gilas din dake kan fuskarta baqi yasa ya kasa gano ina ya santa but she looks familiar, maybe ma qila tana cikin babes din dayake muamala dasu ne shiyasa yakejin kamar ya santa, saida ta juyo da kyau sosai ya waro idanu to the surpise of his life yaga fadwa ce, da akwai tazara a tsakanin su don haka ya contemplating anya ita dince ko kuwa, saida aka fito gaba daya daga cikin motar ya tabbatar fadwa ce tabbas, badan zamansu tare na tsawon shekaru biyar ba zai iya rantse ba ita bace ba, saboda ta sauya sosai kamar ba ita ba, taci wani glass baqi wuluk akan fuskanta, ga wata luxury abaya dake shimfide a jikinta, tana taku daidai, motocin dake biye da ita ma mutanen dake ciki suka fito suna taka mata baya, har suka shige cikin hotel din,
gyara zama yayi ya kasa wrapping kanshi, na farko bai santa da wannan motar ba na biyu kuma bai taba tunanin zata tako daga jedda tazo har sharja ba, sannan su waye suke binta a baya da alamu ma kamar bodyguards dinta ne, da dai afiya ya gani bazaiyi wani dogon nazari ba saboda ita yar ayi ce, tanason harkar manya kuma tana kaunar bragging life style dinsu, kuma kowa yasan wacece ita saboda background dinsu, but fadwa?, fadwa is like a peace maker a tsakaninsu,ta fita daban a cikin su shi a ganinsa shiyasa yake samun abubuwa sosai a wajenta da zarar ya samu chance shiyasa yake ganin ta kamar bata wayo kwata kwata.
da farko yayi tunanin ya shiga ya sameta sai kuma yayi tunanin qila tazo ne tayi attenting abunda ya shafi comapny, maganar comapny dayayi crossing mind dinshi yasa ya dan dakata yana nazari, kwana biyu yaga tana yawan waya, kuma yawanci idan zatayi wayarnan da zarar ta ganshi take excusing kanta, sannan kwanaki yaga wasu file na kamfani a hannunta, baiyi tunanin komai ba don haka koda ya fara karantawa ta karbe daga hannunshi sannan ta yanka mashi warning akan karya sake taba abubuwan ta idan har bata umarceshi da yin haka ba,shidai yasan fadwa da afiya basu da wnai interest akan kamfanin taheel shiyasa hidaya ke controlling komai, toh kodai yanxu fadwa is trying to go into the business itama?shidai koma dai menen ba damuwar shi bane indai he will benefit from it don haka kawai ya basar ya juya akalar motarshi.
har ya dawo gida ganin fadwa da yayi a hotel dinnan yana maid dinshi jira kawai yake ta dawo ya bugi cikin ta.
wajen karfe saigata ta dawo, lokacin data dawo yayi daidai da futowar daga bathroom, kallonta yayi daga sama har kasa, kayan nan daya ganta dasu dazu sune a jikinta nata wannan ya kara tabbatar mashi da ita din ya gani, ita batama lura dashi ba sai jinshi tayi ya rungumeta ta baya yana sansanar bayanta ''i wasnt mistaken ashe, na ganki daxu a A class tower hotel''
chak ta tsaya ba tare da ta motsa ba haka zalika bata juyo ba ta fuskance shi saida ya sake magana ''babe yaushe kika chanza mota?''
''do i have to tell you duk abunda nayi?,ko kudinka ya saya min motar?''
ta karashe tana mai zame jikinta daga nashi ta fuskance shi da kyau, ''me ya kaika hotel din?'' ta jefo mashi tambaya tana mai kure shi da manya manyan idanunta,
ganin yanda ta hade rai ya sashi cewa ''i went for lunch with my guys''
wani irin mugun kallo ta mashi disgustingly tace ''guys???i doubt that''
jin abunda ta fada ya sashi hade rai sosai yace ''what do you mean?, kina tunanin i will cheat on you ne?''
ko kallon inda yake batayi ba ta wurya wayarta kan gadonsu da jakarta tace ''who knows''
yana jin haka ya cije lebe tare da furzar da iska yace ''ke me kikaje yi hotel din?,should i think other wise''
''an gaya maka kowa irin ka ne?, unclassy, tacky ungrateful? look tareeq, duk abunda kakeyi karkayi tunanin zaka raina min hankali, you dont know what i'm capable of, you better shut your mouth an behave your self, bloody womanizer''
ay yana jin kalamanta na karshe gabanshi ya bada wani dammmm,harta fuce daga ganinshi bai kasa daina mamakin jin abunda ta fada ba, daga tambayarta ina taje sai abun ya juye akanshi? bai gama tunanin abunda ta fada mashi ba yaji karar notification a wayarta har sau biyu, without a second thought ya daukan wayar, alert din kudi na ya shigo masu shegenn yawan gaske har yayi loosing count din numbers sai kuma notification din sama hoto ne aka turo with a heart emoji an rubuta other half a jikin number, tuni hankalinshi ya tashi, ya kasa wrapping kanshi da ganin abunda idanunshi suka gane mashi, at that point babu abunda ke crossing mind dinshi sai tambayar kanshi da yake waye other half? ya tabbatar koma waye shi taje ta gani a hotel which means… akwai wata a kasa kenan?, bai gama wannan tunanin ba wani message din ya sake popping, 'ont forget to get those papers no matter what''
dai dai nan ta bude kofar closet room ta futo, ganin wayarta hannun tareeq ya kafa ma message din idanu yasa tayi hanzari karasowa ta karbe wayar daga hannunshi tana mai duban screen din, batayi wata wata ba tana dagowa ta wankeshi da mari,rai a bace ta soma magana ''karka sake taba min wayana or anything daya shafeni''
tana kaiwa nan ta bar wajen ta barshi tsaye saroro kamar wanda aka zarema laqa
***
washe gari da safe bangaren su sabeeha, yau kwana sukayi yana wani irin zazzabin data