Advertisements
Chapter 14 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 107

39K to 42K   out of 320.4K words

fada na aura mashi ita da khaal yayi ne, abubuwan dake ranshi yasa na kasa inda ya dosa,shi kanshi ya rasa a wani matsayi zai bar yarinyar,? Yana kallon abun kamar a film, sabeeha baiwar allah yanda kasan an dasa ta taqi motsawa kwata kwata, tana jin idnaunshi na yawo akanta, tana nan tsaye kawai aka budo kofar aka shugo, sonata na hangota tsaye taji gaba daya duniyar ta mata wani irin daci, kishi, haushi, tsana duk babu wanda bai darsu a zuciyarta ba. Cije lebe kawai tayi tana raya abubuwa aranta sai kawai ta suake wani murmushi ta wuce ta gaban sabeeha tana juya duwaiwuka, kamar kullum dai babu kayan arziki a jikinta, takowa tayi har inda yake ta zauna a gefensa tana kashe murya tace “hey zaddy”
Ko kallon ind atake baiba idanunshi na kan tv, tunda ya duake ido daga kan sabeeha ya maida tv bai sake kallonta ba, haka zalika baice mata ci kanki ba, baima damu da sanin meya kawota ba as far as he knows baisan da mutun a wajen ba tunda batayi sallama ba.
sonata dataga kamar yana neman dizgata gaban yarinyar nan kuma tana son ta kunsa mata saboda yanxu tasan ko kallon inda take bazaiyiba, ada ma don taga yana sa matsalar kai ne shiyasa take da iko dashi amma ayanxu yana da iko akan karan kansa,no one is responsible for him, kuma tasan wannan dai maid dinnan dai can never be on his league, yafi karfinta nesa ba kusa ba, ko kasa daya bata isa ta taka dashi ba.

Sabeeha kuwa tun shugowar sonata ta hade rai sosai, taoron nata ma ya kau, saima ta manta lafiyar taj din lau ganin sonata na tunkarar inda yake.

Sonata dataga sabeeha ta kafesu da idanu, wannan yasa ta dora hannunta kan lap dinshi ta sake kashe murya tace “babe, me maid dinnan keyi anan? Wani abu zata maka ne? Dont worry i can do it for you zaka iya sallamarta”
Sai a lokacin ya dauke idnaunshi daga kan tv ya maida kan hannun sonata dake kan lap dinshi tana yawo dashi kan fatarshi,”get your filthy hands of me” ya fada yanda dagashi sai ita ne zasu ji, tana jin harsh tone din da yayi magana dashi tayi saurin dauke hannunta ya miqe yabar parlor ma gaba daya, sonata ma ta bishi a baya tana murmushin yaqe duk dan ta kunsawa sabeeha, sabeeha kuwa taga duk abund aya wakana a wajen sai taji wani irin aranta, daman tayi expecting haka, bai tuba ta ba baima san ko ita wacece ba, gashi dai a gabanta amma tana ji ya mata nisa, kafarta har nauyi take mata, kamar sata juya ta tsaya tunawa da maganganun da sukayi da ammu,dole ta tsaya, dole ta dawo nan saboda ta hanyar nan ne kawai zata samu ya tunata har ya yarda da ita.
Tana nan tsaye sonata ta futo rai a bace, korarta yayi kiri kiri kamarma kyamarta yake da zarar ta tunkaroshi, plans dinta will not succeed idan har bata samu kanshi ba, dole ne ma tasan yanda zatayi don ta sameshi don wannan ce hanya kadai da zaisa ta sake shugowa rayiwarshi tun bayan lokacin daya gano tana cheating dinshi ta kasa samun wanda zai maye gurbinshi a zuciyarta, abunda yafi damunta kuma take dana sani shine rashin samun kanshi datayi a baya, duk yanda taso tayi seducing dinshi yaqi falling, yana da wata taurarriyar zuciya, tana mamakin yan uwansa da suke mashi wani gani gani, basu san koshi waye ba, bata taba haduwa da mutunminda ya iya takunshi ba kamar taj.

tana karasowa inda sabeeha take ta kalleta, har ta fidda bacin ranta a fili ta tuna wani avu saita boye ta soma magana kamar haka, “ wow wow wow…i thought kince ke matarshi ce, ya akayi bai tuna dake ba? Hahaha Listen bari nayi maki clearing kanki ke matarshi ce a lokacin da hankalinshi baya jikinshi sannan kwakwalrshi ta yara, Yanxu kuwa yafi karfin ki, inbanda karfun hali irin na talaka, ungrateful people how can you even think of your self as his wife, you’re nothing but his maid Just a maid, and as you can see now I’m his first love, your title as his wife is just a name, he will never accept you bitch”
Tana kaiwa nan ta kyalkyale da dariya tabar wajen, sabeeha kuwa tunda ta fara magana harta gama jikinta yayi sanyi sosai.
Ta dade a tsaye har kafarta ya soma mata zafi kafin ta wuce sitting room ta zauna a kasa.

Chan bangaren taj yana shiga daki sonata ta biyoshi a baya, gaba daya ganinta ma baya sonyi don gazanta yake gani da zarar ya kalleta,
Kallota daya tsaya yi yasa ta fara tunanin ko tayi attrating dinshi ne wannan yasa ta fara kokarin shafa shi, rai a bace ya kora mata ta fito daga bedroom din rai a bace bayan ta bashi hakuri, cike lebe kawai ta dunga yi abunda take so kamar zai mata wuyar samu….

Tana futa ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya saka kayan barci sannan yabi lafiyar gado abunshi..

Asuba nayi ya farka, daman time nayi yake bude idanunshi, tashi yayi zaune kafin ya miqe ya shige bathroom ya dauro alwala, dayake baya son yawan haske dakin nashi is very dim sai hasken bedside lamp,daman wuraren wajen karfe 5:50 ne,yana fitowa ya shiga closet ya saka jallabiya sannan ya futo ya hau kan carpwt din sallah, saida yayi raka’a tainul fijir kafin ya tada kabbarar sallar fajir, bayja yabsallame ya dade sosai a zaune kar ya soma kulle idanunshi, karar bude kofa da yaji yasa ya maida idanunshi direct zuwa wajen, ahankali ta sako kanta cikin dakin tana duban wajen gadonshi tana fatan allah yasa bai tashi ba, da yake tasan baya tashi a daidai wannan loakcin lokacin da bashi da lafiya sai tayi tunanin habit dinshi ne, kwata kwata batasan cewa ya tashi ba harta wuce ta gefen ind ayake zaune ta shige bathroom ta rufo, alwala ta dauro bayan tayi easing kanta sannan ta futo ta shiga closet wajen inda kayanta yake ta zaro hijab ta saka, sannan ta futo, sai a lokacin ya gane ashe kayanta nw a cikin closet room dinshi kenan harma da towel da panties din da ya gani wanda yasa aka zubar dasu daga bathroom dinshi, yana kallonta ta bude kofa ta fuce saga bedroom din sannan ta karo kofar, sai a lokacin ya tabbatr da anan part din tayi barci kenan.

Sabeeha na fitowa ta fuskanshi qibla ta tada sallah tana idarwa ta hade jikinta waje guda tana tunanin rayuwar datayi a gidan bataji karar futowarsgi daga bedroom dinba harya karaso inda take, inuwarsa ta fara gani kafin ta dago idanunta, suna hada ido hudu tayi saurin gyara zama tana zazzare idanu, kirjinta na dukan uku uku haka ta dake,kanta a kasa tace “good morning”
Ba wannan ne ya kawoshi wajenta ba don haka ya samu waje ya zauna yana fuskantarta, “whats your name” yanda ya furta calmly yas ata dago da sauri suka hada ido, tana kallon yanda idanunshi ke kyalli, saurib dauke nata tayi muryanta kasa kasa tace “fatima!” Kallon bakinta yayi, sai a lokacin ya lura da yanayin hakoranta datayi magana, kauda kanshi yayi ya sake jefo mata wata tambayar, “so ke yar aiki ce?”
Tana jin haka gabanta ya bada wani dammm,

“Waya kawo ki? Who are you exactly? What was your agenda for coming into my life?”Yanxu da ya sake magana sai taji yanayin muryarshi ya sauya, “khaal?”ya sake jefo mata tambaya,

Tana jin haka tayi saurin dagowa ta kalleshi, wani irin kallo yake mata mai kama dana tsana, don haka kawai zata iya fasaara kallon,bai tsaya ma ya amsa tambayoyin da yayi mata ba shurun da tayi ya bashi amsa don haka ya miqe har zaibar parlor ya dan dakata,“you’re just a maid, my maid, keep that in mind and don’t have any stupid thoughts on your head, da zarar na gano abunda nakeson na gane zan sallameki,”

Yana barin wajen ta bishi da kallo, maganganunshi na karshe sun mata zafi sosai kamar zatayi hawaye, tama rasa wani irin tunani zatayi, he was calm at first then kuma lokaci guda ya sauya, tambayoyin da ya mata ne suka dawo kanta, waya kawota? What was her agenda? Duk yanda akayi hidaya ta fada mashi wani abun kenan? Daman ammu ta fada haka zata faru, gashi kuwata ta tabbata, innalillahi, yanxu wani irin kallo yake mata? Bazata iya tantancewa hakan ba, kuka bazatayi kasa a gwiwa ba,bai nuna mata alamun ya ganeta ba kwata kwata.
Ta dade tana nazari har barci barawo ya saceta a zaune ba tare sa saninta ba.

Shi ko baima koma barcin ba yanata fama da waya yana aiki ya dade sosai har wajen karfe bakwai ya fito, ko kallon inda take baiyi ba ya fuce daga part din.

Bata farka ba sai wuraren karfe tara haka,yar wayar da jamid ya taba bata na gefenta, daman yawanci wayar amfanin da take mata duba time ne kawai, ba wani abun take da wayar ba, tana ganin lokaci tayi saurin miqewa zaune, tana nazarin me zatayi da zaisa ya tuna ta, na farko dai routine dinta data saba shi zata fara yi, maganganun ammu na kara karfafa mata gwiwa ta miqe ta wuce bedroom din, tasan a daidai wannan lokacin ya futa don haka ta fara kokarin gyaran bedroom din nashi.

Hidaya dasu fadwa basu san cewa sabeeha tana dakin taj dinba, sonata kuwa data ganta a part din nashi batayi tunanin anan ta kwana ba,sannan kudirinta har zuwa yanxu bata chanza shi ba.

***
Wajen karfe goma na safe ya shugo gidan, da fadwa yaci karo a kasa tana kokarin fitowa daga part dinta cikin shiri da alamu fita zatayi, tubda ya shigo take binshi da idanu, yana sanye da kayan gym yau ko sauyawa baiyiba, don yana gama workout ta nufi gida, daga sama har kasa take binshi da idanu tana hango gumin da ya danyi daga workout din kwance a jikinshi dukda daga ac ya fito,
he’s so attractive yet so calm and hard at the same time,kammaninshi gaba daya ya fita daban daga nasu, donshi kanar ruwa biyu yayo, the arab side of him a fuska ne the physique side of him kuma irin na manyan maza, yawanci fararen mazan saudi zaka gansu kamar solobiyo shidai ya fita daban, tama rasa yanda zatayi describing dinshi, the inner him is like a black American every womans dream,

Ta shagala sosai wajen kallonshi harya wuce ta gabanta yayi kamar dutse ya gani a wajen, “hey baby brother”
Ay kamar da iska take magana, ya wuce sama ba tareda yace mata ci kanki ba, murmushi kawai ta danyi tana tuna wasu abubuwa,da yanda hidaya ke underestimating dinshi, akaha dai zata bisu da ido dashi da hidayar taga wazai cimma wani,haka ta fuce tana murmushi ita kadai.
Tana shiga motarta tayi dialing wata number ana dagawa ta soma magana “any update!”
“Yes boss,”
“Doctor fah? Have you handle him? You need to be meticulous bana son any kinds of problem,”

“Yes boss”
Ana fadin haka ta kashe wayar tana murmushi kawai,dadin yanda take taimaka wa hidaya takeji ba kadan ba.


Bangaren taj yana haura wa sama ya wuce daki, gaba daya yama manta da wata sabeeha, ajiye jakarshi yayi kafin ya soma cire rigar jikinshi, yana cirewa ya ajiyeta a wajen ya rage daga shi sai short tight, kai tsaye ya wuce bathroom yana bude kofar yasa kai cikin bathroom din cikin saurin ta juyo hankali a tashe, suna ido hudu jikinta ya soma rawa shi kuwa ganinta daga ita sai towel take memory din lokacin da suke cikin bathroom yazo kanshi,

burkicewar da tayi yasa juya mashi baya ta fara
Kokarin zura hijab dinta allah yaso ta shugo dashi, taba kokarin sakawa ma ya shugo, innalillahi wa inna ialihi rajiun kawai take aranta,

Allah ya taimaka ma ta daura towel a jikinta da yake akwai towels da yawa a bathroom din ta
allah ya taimaka saida ta saka ya shugo bathroom din, shi baiyi expecting din kowa ba don haka ya shigo kai tsaye, tunda ya kafeta da kallo harta saka hijab dinnan bai cire idanunshi a kanta ba , take kawai fuskanshi ta koma jaa sosai,sabon memory na mashi flashing, ranar da ya shigo bathroom zaiyi futsari ya kasa cire zagiyar wando, sai kuma memoryn ya sake confusing dinshi gata nan ta tsungunna gabanshi zata zare mashi zariyar wandon shi sai lokacin daya shugo bathroom lokacin ta gama wanka harya fara kokarin taba kirjinta a bathroom din sai abun ya mashi kamar itace take kokarin sakashin yin haka, gashi ga ta a bathroom din a lokacin, mekenan hakan ke nufi? Kusancinsu har yakaiga shigansu bathroom a tare ko me? Wannan yar yarinyar? A maid? Har tana zare mashi zaryar wando? Yama kasa tuna what next happens after that, “What the f**k!!!”

Ya fada yana mata wani mugun kallo, jijiyoyinshi sun fito rado rado, tana jin saukar muryarshi tayi hanzarin juyowa ta nufi hanyar futa daga bathroom din, kamar zatayi tuntube haka ta karaso tsakiyar dakin tana haki,shiko ya kasa wrapping mind dinshi, yama rasa dalilin bacin ranshi, me sukayi da yarinyarnan? Abunda hidaya ta fada gaskia ne? Yana ganin ta kamar karamar yarinya,did she take advantage of him da lalurar daya tsinci kanshi Koko yaya? Don ya kasa gane dalilin da yasa ya nemi taba wannan yarinyar.

Sabeeha kuwa kasa tsayuwa tayi a dakin ta fuce bedroom din ta nufi hanyar kofa daidai nan sonata ta shugo, ko kallon inda take sabeeha batayi ba ta fuce daga dakin.
Sonata kuwa suman tsaye tayi don jarabar mamaki, cikin abund abai wuce second biyar ba ta kalli sabeehar harta gano cewa daga bathroom take donga digon ruwa nan akan fusknta, hankali a tashe sonata ta shige cikin bedroom dinshi, tana jin saukar ruwa cikin ta ya duri ruwa itama, ta dauka wajen 20mins tana zarya tsakanin dakin yanda kasan ta dauka 2hrs haka takeji, allah allah kawai take ya fito taji meya kawo sabewha da sassafe dakinsa, badai kwana tayi anan ba?“Haa it can’t be possible” tana gama fadin haka saigashi ya fito daga bathroom, yana ganin sonata ya sake hade rai, daman ranshi a bace yake, wankan ma cikin bacin rai yayi yana kallon gabanshi, dake shedan shugaban yan zuga ne haka ya dunga raya mashi banzan abubuwa akanshi, yanxu haka yarinyar nan taga jikinshi? She take advantage of lalurarshi, sai yaji gaba daya ya tsaneta, ko kallonta baya son yi.

Sonata na ganinshi gaba daya abunda ke kanta ya warware tama mance da haushin da takeji,nufoshi tayi ganin yana neman karasawa wajen walk in closet, “babe good morning”
Ko kallon inda take baiyi ba yace “excuse me” yana fadin haka ya wuce bathroom, tasan me hakan da ya fada yake nufi, ta futa zai shirya kenan, harta juya jiki a mace zata futa ganin yanda ya mata magana ta dakata, wani irin smirking flirty murmushi tayi kafin ta tunkari walk in closet din, tana shiga ta karo kofar wajen yana kokarin shafa body sprays dinshi,
“Are you deaf” ya fada in a harsh to, ay ko sauraron sa batayi ba ta tunkari inda yake tun kafin ta karaso ta dakatar da ita, “dont you dare take a single step” tana jin haka ta tsaya kyam,
Take ranta ya baci ta soma magana , “why are you pushing me away babe? Why? Don’t tell me it because of that maid?”
Da mamaki ya dago yake kallonta, kishi ya rufe mata idanu sosai, “yes, is it because of that ugly maid? Did you sleep with her? Huh?”
Yanda take magana kamar zata tashi sama, ranshi idan yayi dubu ya baci sosai, comparing dinshi da wannan yarinyar kadai da takeyi ba karamin bata mashi rai yake ba, take ya daka mata tsawa
“Get d hell out!!!!, this should be the first and d last time da zaki kara shugo min part dina, idan na kwana da ita whats your problem with that? Isn’t She my wife!!!!!!”
Ay kamar ya buga mata guduma aka, kuma yaga hakan a fuskanta, daman ya fadi hakan ne donya baqanta mata rai sosai,batayi wata wata ba ta fuce daga dakin rai a bace kamar zata amayar da kayan hanjinta don masifa.

Afiya na kwance a daki tana barcin asara sonata ta shugo, tana karasowa inda afiya take ta soma tashinta “babe babe”
Sama sama afiya ta soma jinta, harta bude idnaunta ahankali, ganin sonata na kuka yasa afiya ta zauna tana kallonta tace “yadai?, kuka fa kikeyi? Ko haryanxu kin kasa samunshi? Wai whats so special about him, that thing da kike nema a jikinshi akwai thounsands da suke dashi kuma kina samu, what so special about him”

Sonata najin abunda ta fada ta soma dunqule hannunta tana furzar da huci takaici tace “If i can’t have him then no one should,”
Da mamii afiya ta kalleta don bata gane inda ta dosa ba, “what do you mean”
“Babe i need your help,yarinyar nan jiya a part dinshi ta kwana, qila ma tare suka kwana ,what if he slept with her? What if she got pregnant bfr i do? Plan dina will be ruined i need your help”
Shuru afiya tayi tana sauraronta itafa wannan batada hankali, kallonta kawai afiya keyi, batasan cewa addinin mu bai amince da cikin da babu aure ba, duk plan dinta was ta knock him off and have him sannan ta samu ciki dashi wannan zaisa bazai barta ba, batasan cewa intimacy bfr marriage is prohibited kuma shi zaiza ma bazai taba auren nata ba bayan wannan ma auren baturiya? kafira kuma yar bariki ma? That’s impossible.
“Babe are you even listening to me” sonata ta tamabyi afiya
“Yes come again?”
“Yarinyar nan a dakinshi ta kwana, lets do something bfr its too late”
Afiya najin haka tace “trust me ans just calm down okay”


5pm…
Kusan a tare duk sukayi parking motocinsu, motar hidaya ce ta fara shugowa kafin ta fadwa, gaba dayansu kana ganinsu kasan da bala’i suka dawo gidan, tunda sukaji batun kwanan sabeeha a dakin taj, afiya ce ta kirasu ta shaida masu hakan conference call ma sukayi. kowannensu da abunda ke cikin zuciyarsa.

Suna shugowa cikin gidan hidaya tasa head maid ta kira mata

14 / 107