Advertisements
Chapter 60 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   60 / 107

177K to 180K   out of 320.4K words

booth dinshi ya bude abal ya dauko mashi classy LV luggage dunshi, daidai nan hamad ya futo daga cikin gidan, yana hangosu ya karaso inda suke sannan ya jagoranci taj din zuwa masaukinsa.
apartment din dake gefe kusa dana anty bahijja hamad ya bude,yawanci irinshi ne ma aka bama sufyan da amaryarsa duk sanda sukazo hutu anan zasu dunga sauka.
Duk apartment din sun zagaye main house, saboda ahalain ya dunga expanding yasa akayi part part din, tunda gashi duk samarin tasowa sukeyi kuma zasuyi aure duk me so zai iya zuwa yayi zamanshi.
Suna shiga abal ya shiga da luggae dinshi har ciki, an suya komai na ciki apartment din, interior din part din black and white, so esthetic babu wani abun hayaniya, parlor ne a kasa dayasha english kujeru sai dining wajen kitchen sai kuma sama bedrooms guda biyu, daya master dayan kuma second bedroom, suma dai Masha allah.
Kafin su futa hamad ya shaida mashi nanna tace he should settle in and rest zuwa gobe saiya shugo main house sannan idan yana buqatar wani abu ya nemi hamad din, nan sukayi exchanging contacts, abal kam tuni ya karbi nashi number din tun a mota, Suna futa ya sauke wata ajiyar zuciya yabi ko’ina da kallo, komai goes to his taste dayake shi bamaisan hayaniya bane.
Sama ya wuce zuwaga bedroom din shima ko’ina fess fess a gyare babu kazanta ko kadan.
Setting in ya soma yi kafin ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito ya saka jallab, lokacin wajen karfe sha daya ya tada kabbarar sallah, tunda ya fara sallah abi zauna ba har wajen karfe uku babu abund ayake zai godiya ga Allah daya nuna mashi wannan raya, ta bangaren nanna ma bata iya barshi ba haka ta kwana tana godiya ga Allah, gaba daya a ranar babu wand atakema addua kamar taj.

Sai wajen karfe uku da rabi ya iya tashi ya kwanta kan kace me wani irin ni’imataccen barcin da ya mance rabon da yayi tun bayan tafiyar sabeeha yayi shi.
He sleeps peacefully kamar wani baby, gaba daya ji yake kamar an cire mashi 90% of damuwarshi.

Kiran sallar farko a kunneshi, koda ya bude idanunshi ya dauka mafarkin komai yayi sai yaga zahiri ne, this is the life he dream for him self,yanajinshi kamar he’ss complete, a take zuciyarshi ta raya mashi how he can’t be complete without her, tunaninta da yake hana kanshi saiya kasa gaba daya, memories dinsu ya dawo mashi kamar anyi rewinding, daman ance sai an samu kwnaciyar hankali ake wani tunani, don har steamy moments dinsu saida ya dunga zuwa mashi, ya mafi tsaya mashi arai don gaba daya yasa jikin shi yayi wani irin sanyi, akanta yasan he’s a man, very needy man infact theres a needy monster inside him that makes him crave for her presence, her scent, her breath and her boobs.
Shagalcewa fa yayi ya kasa tashi gaba daya yana tunanin sabeeha, watanni nawa kenan ya kasa cireta aranshi, kai dukyanda za ayi dole ya nemota.
Kiran sallah na biyu ne yasashi tashi dakyar ya wuce bathroom kamar wani mara lafiya, ya sakarma kanshi ruwan zafi sosai kafin ya danji dama dama sannan ya futo a gaggauce ya saka jallab da wani cute ovy black slippers ya sauko kasa lokacin har an fara tada kabbara.
Da suka shugo estate din gidan ya hango masallaci daga gefe wannan yasa yana futowa ya nufi wajen,yana dab da shuga ya sameer dasu abal da sufyan harma da hamad suma suka karaso gaba daya suka shiga masallacin sukabi sallah.
Suna idarwa bayan sun fitfito ya gaggaisa da kowa, ya sameer ya bashi hannu su abal da sufyan suka gaishesa hamad ma ya gaishesa a mutunce kafin ya koma part dinshi.
Barcin da bai koma ba kenan ya bude laptop dinshi ya fara aiki, da duban report din da merk ya tura mashi.

Karfe takwas daidai wayanshi tayi ringing, number anne ya gani wannan yasashi saurin dauka ba tare da wani tunani ba yayi sallama ya gaisheta cikin natsuwa.
Ta tambayeshi ya kwanan sabon waje? Sannan yana buqatar wani abu ko wajen bai mashi ba ko yana san a sauya abubuwan da aka saka mashi, yace mata ah ah, babu komai, kuma hes so grateful for everything.
Nunfasawa tayi sanna tace mashi ya shugo main house yayi breakfast yanxu yace mata toh.
A gurguje ya shiga wanka ya fito ya kintsa cikin jallabiyanshi this time around black jallab ce ta amshi skin dinsa sosai kunsan ance black and white idan aka hadu bade kyau ba, gashi morning face dinshi is so breathtaking.
Wayanshi kawai ya dauka ya saka black slippers dinshi da suka fidda yatsun kafarshi doyage sannan ya futo ya tunkari main house, babu wani nisa baifi taku ashirin ba yakai aka bude kofa ya shiga daga ciki, rabi dake jera abunci a dining tana hangoshi ta kasa dauke idanunta,har chokalin hannunta da take jerawa a dining ya subuce, “allah gamu gareka,” ta furta a hankali hadiza ta bita da ido, kafin ta maida dubanta ga taj wanda rabi ke kallo, ay saita fi ma rabi rudewa, cha take “wannan waye kuma kamar balarabe a gidannan”
Rabi ta juyo tace “zaki zubarda coffee din, ta galla mata harara.
Maya dake zaune hadiza na zuba mata coffee tana jin abunda tace yasa tayi saurin miqewa da cup din coffee din a hannunta ta nufi inda suke tsaye ta hangoshi a taaye a wajen ya taaya ganin babu kowa a kasan.
Maya uwar kaudi tayi saurin karasowa inda yake kamar zata fadi har tana hardewa gab da inda yake nesa dashi kadan coffee din ya subce mata ya fadi kasa cup din ya fashe, daidai wajen yatsun kafafunshi dake bayyane tayi saurin cewa “oh my god im so sorry…”
Muryarta ce da yanda event din ya faru yasashi ganseta lokaci guda, the girl that split mocktail on him that very day”
Yi yayi kamar baisan da ita a wajen ba harta tsugunna daidai nan anne ta sauko ya karasa inda take ya kama hannunta ya sumbaceta, wannan alada taqi rabuwa dashi mufa nan bama haka a nigeria lol…
“Good morning Deen, how was your night?”
“Hamdullah!’” Ya bata amsa,
“Kaje sama kayi breakfast wajen oummin ka,”
Murmushi yayi mata shidai kamar bashida baki yace “okay an…ne”
Kiran rabi anne tayi tasata ta kaishi har part din nanna, ta jagoranshi bayan ta gaishesa har zuwa oart din sannan tayi sallama da
Nanna a bedroom dinta ta shaida mata da zuwanshi, yana daga zaune sitting room din
Tunda ya shigo gabansa ke faduwa dab dab dab ya rasa dalili amma yana alaqantashi da wani abu da yake jinshi mafi kusanci da zuciyarsa, futowa rabi tayi tace mashi ya shiga ciki, yana shiga daidai nan sabeeha ta fito daga dakin da take kwana tun lokacin da rabi ta nuna mata.
Rabi na ganin futowarta don tana gab da futa tace “baku tafi ba?”
“Eh yanxu zamu tafi ina kwana anty rabi”
“Lafiya ta amsa ta”
Ta dauka kasan zata sauko sai taga ta nufi bedroom din nanna har zatayi kncking rabi ta dakatar da ita tace “me zakiyi?”
“Daman zan ce mata na tafi ne?”
“tanada baqo a ciki, ki tafiyarki kawai”
Da toh sabeeha ta amsa mata sannan ta bi bayan rabi suka sauko kasa tana dafe kirjinta.
Tun jiya da daddare gabanta ke faduwa ta rasa dalili

,nanna na zaune kan carpet an jera breakfast hannunta rike da coffee sai news papers dake hannunta ta dago ta kalleshi ta sauke murmushi tace “come in bismillah” ta mashi nuni da gefenta wajen carpet din.

Zama yayi cikin biyayya ya gaisheta irin gaisuwarsu, nanna ta tambayeshi how was his night yace mata alhamdulillah sannan da kanta ta mashi serving abunci tace bismillah.
Yanajin abun kamar a mafarki ba gaskia ba, yau gashi ga mahaifiyarsa, bini bini nanna ke dagowa tana kallonshi tana murmushi, harya cinye tass baima san ya cinye ba tunda yazo baici abunda ya mashi dadi ba kamar wannan.



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
QueenmarhBook2
PAID
Chapter 96
Suna zazzaune a kan dining anty bahijja, maya, anne sai hamad da shugowanshi kenan,suna karin kumallo cikin kwanciyar hankali, tunda suka zauna bahijja ta lura da yanayin maya daya sauya gaba daya, hankali kamar baya jikinta ta tafi wani tunanin daban, kallonta bahijja tayi tace “baby eat mana..ko bai maki ba? You want something else?”
Daga hamad har anne babu wanda ya dago ya kallesu, sai wani lallabata take kamar wata karamar yarinya, hamad ya miqe ganin time dinsu na neman kurewa.
“Go and call fatima time yana kurewa” ya fada yana kallon maya, “bazanie ba yau”
“Are you not prepping for exams?Ba test zaku fara ba next week?”
“Mummy please i want to be with you the whole day”
Murmushi bahijja tayi ta dubi hamad tace “ku tafi kawai hamad”
Anne da bata tanka su ba tun daxu ta dago ta kalli mayar tace “tashi ku tafi”
Kwalla ce ta soma zuboma maya, harga allah yau batayi niyar zuwa school dinan ba kwata kwata, ganin tana son yin hawaye yasa bahijja cewa “anne a barta monday zaita je tunda yau friday and its a short day”
“Bakiji me hamad yace bane?“
Ganin yanayin anne ya sauya yasa bahijja yin shuru dole maya ta miqe ta wuce sama don shiryawa harda hawayenta.
Har bahijja ta miqe anne ta dakatar da ita, “binta zakiyi? Saboda me?”
Komawa bahijja tayi ta zauna hamad kuma ya fita.
Yana fita ya sameer ya shugo main house din don gaisheda anne, duk safiya yake zuwa gaisheta kafin ya tafi office.
Hamad na karasowa wajen moto ya tadda sabeeha tsaye, sai laila ya bude masu kofa suka shiga kafin maya ta futo daga baya rai a bace.

Ya sameer na zuwa yaga yanayin anne ya gane cewa ranta a bace yake, bahijja ko taqi yarda ta hada ido da ita don anne nada zafi sosai.
Yana gama gaisawa dasu ya fita anne ta wuce sama bayan ta buqaci bahijjar tabiyo bayanta.
Suna hawa saman anne ta hau kanta da fada sosai, “wannan wani irin shashanci ne bahijja? Daman ku kuka lalata yarinyar nan? Zatayi abunda taga dama bazaku mata fada? Zaman kasar waje hauka ne eh?”
Shuru bahijja tayi ta kasa cewa komai jiki a mace sai bata hkuri kawai tayi ganin yanda ranta ya baci.
Koda tabar part din anne ta nufi inda ta sauka anan saman wayarta kawai ta zaro ta soma dilaing number majeed.

Bangaren taj bayan yabar wajen nanna part dinshi ya koma abal yazo suka dunga hira sosai yana nuna mashi abubuwan daya danganci kamfanin sa a laptop, lokacin lunch nayi kuwa anne tasa rabi ta aika akai mashi part dinshi.
Anty fadila ma ta aiko masa da tuwo da miyan egusi mai dadin gaske.

After 2 dayss
Cikin kwana biyun nan taj ya sake sosai da mutanen gida, abal is one if his favorite don suna tare dashi, a cikin kwana biyu anne tasa ya sameer ya kaishi kamfaninsu ya gani, haka ya zaga dashi ko’ina yaga yanda suke tafiyar da kasuwancinsu.
Tsakanin shida mahaifiyarshi kuwa sai godiyar Allah, minti kadan zata kira taji ya yake me yake, haka zalika shima zaije wajenta sau nawa, haka take janshi sosai a jiki don sanin komai game dashi.
Kwata kwata batayi kokarin tambayarshi rayuwar da yayi a saudi ba bayan tafiyarta, da abunda ya shafi mahaifinsa harma da yan uwansa, she’s trying so had ta mance da komai.

Maya ko tana tare da mummy ta kullum, qin yarda ma tayi ta koma bedroom dinta, inda mummynta ta sauka nan ta dawo for the mean time.
Sabeeha tun ranar da suka hadu da rabi a sama ta shaida mata ta daina kwana wajen nanna din tunda ta smau sauqi wannan yasa shugowarta main house da part din nanna ya ragu ba kamar da ba.
Kullum tana bangarensu, babu abund ake fiddata sai aikin da zatayi na gida, data zauna a daki ko karatu takeyi na shirin test da zasu fara, gaba daya ta maida hankalinta wajen karatun yanda ya kamata.
Duk sanda ta shugo kitchen ko sai taji yan matan gidan nan na maganar baqon daya zo wanda suke alaqantashi da dan nanna da sukaji ana fada da yanda suke zuzuta siffarshi kamar ba bahaushe ba, ba yawan shigowa cikin gida take ba, balle zagaye cikin sauran apartment din don bata da alaqa da wajen, aikinta na nan kirchen tana gamawa daki kawai take komawa, gashi ita ba ma’abociyar shishigi ba wannan yasa bata famu da sanin mutanen gidan ba banda ya hamad.

Yau ta kasance monday morning…
Tun wajen asuba data tashi bata koma ba take karatu, gudun kar mamanta ta tashi yasa ta wuce backyard ta zauna wajen kujerun dake wajen, dake ko’ina na gidan akwai haske kamar rana.
Bata tashi daga wajen ba har saida gari ya soma haske, ta koma daki ta aje littafanta lokacin yan aikin gidan kowa ya rigada ya futo duk sun fara aiki, kallon inda hadiza ke kwance tayi, mayafin da take lulluba dashi sabeeha ta jawo mata ta rufa mata ganin ya yaye kafin ta futa.
Daga shugowarta hadiza taji motsinta ta farka, tabi kofar data futa da ido, Sai a lokacin tayi ta tashi tayi sallah.

Sabeeha na shugowa kitcwhn ta gaisheda rabi da sauran waenda ta tadda a wajen sannan ta basu helping hand.
Ana gama breakfast suka soma fifitowa da avubuwan karin kumallo.
Su bilki na gaba da warmers while sabeeha na biye da suka aje kafin su juya don sake kwaso sauran warmers din.
Adaidai lokacin nanna ta sauko kasan cikin shiri, bahijja ma ta sauko kasan, suka nufi dining.
Bilki dake kokarin komawa kitchen ce tace “sabeeha dan allah jera plates din bari na dauko flask”
Da toh kawai ta amsa ta tana kokarin jera plates din su nanna suka karaso.
Tana ganin isowarsu tayi saurin rissinawa tace “ina kwana nanna”
Murmushi nanna tayi tana mai dubanta tace “lafiya kalau fatima, daga tayani kwana kika gudu kuma,”
Dan dagowa sabeeha tayi tana dan murmusa tace “anty rabi ce tace na dawo kasa”
“Toh ay shiknan, kwana biyu da ba’ayi min tausa ba sai naji kafar na min zugi kuwa”
Sunkuyar dakai saveeha tayi tace “in muka dawo daga school zanzo nayi maki”
“Toh allah ya kaimu, allah ya bada sa’a”
Nanna na rufe baki bahijja data zuba ma sabeeha ido ta kasa daukewa tace
“Ina muka samu yarinya haka”
Dan kallonta sabeeha tayi kafin tayi saurin rissinawa har kasa cikin ladabi tace “ina kwana hajiya”
“Lpy kalau”
“Yar hadiza ce ay,fatima sunanta” nanna ta bata amsa.
“Wata hadiza kenan nanna?”
Sabeeha najin sun fara magana bayan sun nufu mazauni tayi saurin juyawa ta wuce kitchen.
“Hadizar dai wadda kuka taso tare tar wajen inna mai aiki”
Zaro ido bahijja tayi da mamaki tace “hadiza dai?”
“Itafa rayuwa dai sai godiyar allah, innar ma ta rasu, ashe anan bayan gari suke zauna cikin ikon allah kawai sukazo bikin sufyan,“
Girgiza kai tayi da mamaki bayan ta gama sauraron.
Sallamar taj tasa suka juyo gaba dayansu, nanna ta sauke murmushin su na manya, anty bahijja tace “oh rabona dakai tun ranar birthday nanna,” da turanci tayi magana wannan yasa ya danyi murmushi har hakoransa na futowa yace “good morning a natse, “morning how are you”
“Hamdullah!!” Ya bata amsa tare da karasawa wajen nannna suka gaisa ta tambayeshi how was his night.
Yauma nanna ce tayi serving dinshi bahijja na kallon abun gwanin ban sha’awa, sai suka burgeta sosai.

Saukowa ta soma yi daga bene hannunta rike da wayanta sai jakarta, gaba daya hankalinta na kan waya wannan yasa bata lura da waenda ke dining ba.
“Baby kin sauko” bahijja tayi magana.
“Yes mummy, good morning!!”
“Morning dear,”
Dagowa tayi karaf idanunta ya sauka kanshi, yana gefen nanna, yauma yana sanye da jallabiya, gashin kanta ya kwanta lub kamar na jariri, ta kasa dauke idanunta.
“Maya..come have a sit”
Nanna tayi magana, tayi firgigi ta kalleta “good morning nanna”
“Morning” ta amsa ta
Jan kujera tayi daidai da inda yake, tunda ta jaraso bai dagoba balle tasa ran ya kalleta, yanada wani irin kwarjini, haka nan tana ganinshi komai ke kulle mata.
“Baki gaida uncle taj ba” bahijja tayi magana tana kallonta ganin irin kallon da take mashi.
Muryanta ba karyewa tace “good morning uncle taj”
Kallo daya ya mata ya kauda idanunshi tare da dauka glass of orange juice dake gabanshi kamar baison magana yace “morning..” kai tsaye.
Wallagi jintayi kamar an tsundumata a aljanna, muryanshi akwai dadin gaske.

Yauma dai ba wani cin kirki tayi ba don gaba daya hankalinta ta tattara zuwa gareshi kamar mayya, shiko baima san da ruwanta ba a wajen kamar she doesn’t exist gaba daya.
Wayanshi daketa faman vibration a gefen table daya aje ne ya kalla ganin sunan dake kiransa, tunda yaga kiran merk babu qaqqautawa yasan akwai matsala wannan yasa yayi excusing kanshi ya miqe nanna ta bishi da kallo, yana tashi ko minti biyu batayi ba itama ta miqe, “mummy byee”
Ta futa, “allah ya tsare ta amsa ta.
Gaba daya daga main sitting room ya futa zuwaga harabar wajen shugowa cikin gidan don a tsayen nan yana hango motocin gidan dake surrounding din wajen shugowa, da alamu ma fita za ayi da motar.
Wayar ya daga tare da kaiwa kunnenshi, maya dake sauri sauri ta karaso inda yake tanajin yanda yake zuba turanci tabi bayanshi da kallo, hes so huge, kai yana burgeta, wani irin kamshi yake mai dadi gaske, ya wani irin saka hannunshi daya cikin aljihun jallabiyan, daya kuma ya kai wajen kunneshi, ga slippers din kafafunshi sun karbeshi sosai saboda hasken fatarsa.
Kai dole ma tasan yanda zqtayi ta zama so close to uncle taj, he doesn’t seem friendly amma duk yanda zatayi saitasan yanda tayi ta zama close to him.
Ta gefenshi ta raba kamar zata wuce saita juyo fuskanta dauke da murmushi tace “bye uncle”
Shi bai kalleta ba shi bai amsa wayar da ake mashi ba saima kurama waje daya idanu dayayi.
Daga chan nesa kuwa sabeeha data biyo ta bayan backyard, direct ta wuce wajen mota, ta bama inda yake tsaye da maya baya, a daidai lokacin data juya allah ya bashi ikon kallon direction din wajen saidai kuma side viewdinta kawai ya gani kafin ta juya baya tana sanye da abaya baqa tayi rolling kanta da mayafin.

Gaba daya tunda ya zuba ma wajen idanu ya kasa daukewa kamar wani wanda ke nazari yana calculating abu, height dunta exactly irin na sabeeha harda jikin ma.

Maya na ganin inda yake kallo kamarma baisan tana magana ba taji wani irin maqoqon abu a zuciyar ta.
“Are

60 / 107