Author : Queenmerh Category : Complete Novels
saida suka karaso dabb, ga bahijja tsaye ba lulubi a furgice ga sojojin guards dake kula da tsaron apartments sun zagaye sabeeha da bama a hangota, kokari kwasarta kawai suke kamar kayan wanki, sannan ga rabi daketa faman kuka a gefe tana bada hkuri sai maya itama a tsaye da riga duk jini.
Motar su ya sameer ce a gaba da suka fara shugowa wadda driver ke tukawa,daya dauko su shida hamad daga airport, isowar su kenan suka wuce asibiti, anne da nanna na bayan motar, sai anty fadila a bayan motar taj sai kuma hamad daya zauna a gaba sai kuma motar daddyn maya dake biye da tasu da shima ya dawo gidan a daidai lokacin, duk babu wanda yasan meke faruwa a wajen saidai ganin yanda sukayi chirko chirko kana gani kasan ba lafiya ba.
A tsanaki sukayi parking ta gaba gaba sannan suka fifito, banda taj daya tsaya cikin motar sa yana amsa wani important call, tundaga shugowar motocin nan gaban maya ya fadi, ba ita kadai ba hatta bahijja amma kuma har zuwa lokacin idnaunta a rufe suke,cikin sauri ta karaso jikin mummyn nata ta kankameta, tana wani rawar jiki, harda dafe kai, bahijja tayi saurin riketa a jikinta.
Kusan a tare duk suka firfito, hamad ya bude seat din baya, bayan ya fito da wheelcahir da za a saka anne, nanna ma ta futo duk suka maida hankalinsu ga inda su bahija suke, uncle sameer ne yayi gaggawar karasowa wajen yana duban guards din suka sara mashi, “whats going on here?”
Bai gama magana ba ya hango sabeeha da suka zagaye ta rakube “subhanallahi whats going on here, meke faruwa anan???”
Daddy daya biyo bayanshi yana karasowa shima take gabanshi ya fadi, yana duban bahijja da maya da duk jini ya bata jikinta yace “innalillahi wa inna ilaihi rajiun? Bahijja???meke faruwa anan,”
Duk kowa yayi shuru babu abunda kakeji sai sheshekar sabeeha ahankali abun tausayi, gashi babu wanda ya bada answer,
“Kunyi shuru whats going on here????”
“Wannan yarinyar…” bahijja tayi nuni ga sabeeha, har hannunta na karkarwa idanunta yayi jajawur tsabar bacin rai, ta cigaba “tayi kokarin ilatar da maya, badan ikon allah yasa na…”
bata karasa magana ba nanna ta karaso don ganin meke faruwa a wajen, tana isowa ta doka salati,wnda hakan yasa bahijja dakatawa bata karasa magana ba “innalillahi wa inna ilaihi rajiun,”
“Meya faru bahijja? jinin menene wannan?”
Abunda ta fada dai shi ta sake maimaitawa “Wannan makirar yarinyar ce tayi kokarin illatar da maya, badan ikon allah ba saidai a tsinci gawar maya,''
''wani irin magana ne wannan bahijja,ki mana bayanin meya faru, meya hadasu da har zai illatarwa,?'' nanna ta sake magana hankali a tashe.
'' na shugo main house naji maya na ihu daga sama, ina hawa sama naga wannan shiadaniyar yarinyar rike da wuka a hannunta ga maya jikinta duk jini unconciously, , she was trying to harm her tana kokarin kashemin yarinya?”
Duk gaba daya sai suka dago suna kallon mayar data langwabe hannunta na fidda jini, a rigarta ma duk ta baci da jini, daman da gangan ta shafa jinin don afi yarda da gaske sabeeha kokarin yankata tayi da wuka,sai faman hawayen munafurci take tana langwabewa.
“Innalillahi wa inna lailihi rashin….wuka? Ta yanka maya??? why??Meya hadasu? a ina ta yanketan”
Nanna ta sake jero jero mata tambaya, rabi dai tayi shuru har zuwa lokacin hawaye takeyi, nanna ko ta kasa gasgasta abundaa taji.
Daddy kam gaba daya lokaci guda ranshi yayi mugun mugun baci, zancen bahijjar gaba daya doesnt add up, idan ta samu maya unconciously bazasu ganta tsaye ba saidai a ganta ranga ranga sai asibiti, kallon maya kawai yayi ya gane kamar bata da gaskia, yanda take ta faman kauda idaanu tana qin hada ido dashi.
''toh tsayuwar me kuke baku kaita asibiti ba?, how badly was she injured? sannan Su wannan securities dinfa? Me sukeyi anan?” majeed ya sake magana, “
“bakaji me nace bane?, na ganta tana kokarin illata maya, she injured her da makami, badan nazo ba kasan me zatayi ne??? Wallahil azeem yarinyar nan bazata sake kwana cikin gidan nan ba, kuma she must learned her lesson don saina kulleta ku fita da ita kafin na ilata ta”
“Bahijja, are you even listening to your self? Kin tsaya kinyi binciken abunda ya hadasu?”
“Bincike???? Majeed bincike fa kace wani irin bincike zanyi i saw her with my own eyes, bawai fada min akayi ba, rike da wuka tana kokarin harming maya, kuma nasan ba kowa ne ya sata ba sai makira annamimiyar uwarta, jinin hadiza ce fa? Menene bazatayi ba? Daman da sun samu waje babu abunda bazasuyi,, har kun iya manta abunda hadiza tayi, kuka barta da diyarta suna zaune cikin ahalinnan to wallahi ni ban mance ba, muna zaman lafiya mun gayyato ma kanmu bala’i da masifa, su fitar da ita tun kafin na illatata don wallahi zan iya nakasa ta…” Bahijja ta karashe rai a bace
Hamad na turo anne basu kaiga karasawa inda su bahijja ke tsaye ba suka juyo ga inda suke jin magana da karfi, kamar yanda kowa ya maida dubanshi ga jamila dake tsaye.
“Ai KUWA DA KINYI BABBAN KUSKUREN DA HAR KI KOMA GA ALLAH BAZAKI TABA YAFE MA KANKI BA'' tana fadin haka ta bisu daya bayan daya da kallo yanda suke kallonta itama, sai kawai ta sauke wani makirin murmushi, aranta tace lokaci yayi.
MATAR TAJ (destined with you)
Written by
Queenmarh
Book2
PAID
Chapter 107
Akan idanunta bahijja ta futo da sabeeha kuma taga komai daga farko har karshe, bata samu damar magana ba sai yanxu.
Hadiza dake daki bayan fitar jamila haka kawai jikinta ya bata ta biyo bayan jamilar taga kota futa, don makircin jamila ya wuce tunani, don kuwa zata iya komai koda kuwa tana kan gabar mutuwa ne, bata tashi biyota ba saida har suka iso, dake tsakanin backyard din zuwa compund din akwai nisa sosai wannan yasa bata hango abunda ke faruwa ba, kamar ance ta dago karaf idanunta ya sauka kan anne dake zaune kan wheel chair.
take gabanta ya fadi ganin jamila tsaye daga gefe ta kure su da ido, tuni hankalinta ya tashi.a tunaninta ta rigada ta futa don neman yanda zata tseratar da kanta,
hankalinta bai gama tashi ba saida taji maganar da jamila tayi don da karfi take magana, ay batasan sanda ta taho a guje ba kamar zakanya, daidai lokacin kuma allah ya bama jamila nasarar hangota daga nesa tayi wani makirin murmushi ta janye mayafin datake rike dashi a hannunta ta daure a kugunta dashi, ta fara taunar chewing gum, ji kake kass kass.
“Jamilaaaaa jamilaaaaa !!!!!” Hadiza ta kwalo mata kira tana gudu, harda tuntube ta fadi kasa, jamila ko me zatayi banda dariya kamar mahaukaciyar sabon kamu, ta sauke wani makirin murmushin mugunta tana taunar chewing sautin nan na futa ji kake qas qas ta tuge daurin ta zuwa gaba, Ta dubi hadiza dake kokarin tashi zata cigaba da gudun duk don ta dakatar da ita tace
“Da kin daina gudu kin taho ahankali, don babu abunda zai hana yau dinan na tona asirinki da kika kwashe shekaru ashirin da uku kina binnewa”
Gaba daya sai suka maida attention dinsu ga sabuwar dramar da suke gani, taj na daga zaune a mota, waya yake mai amfani dayasa ya kasa katsewa amma idanunshi nakan abunda ke faruwa a tsakar gidan.
Duban bahijja jamila tayi sannan tace “kafin ki illatata inaso ki sani cewa yarki ta asali zaki illata saboda yar da ba taki ba, don wacchrr” tayi nuni ga maya “wachar ba yarki bace, yar hadiza ce”
Dammmmm, gaban bahijja ya fadi, bama ita kadai ba hatta daddy da fadila da nann, kai kowa ma dake tsaye a wajen.
Anne dai na daga gefe, basu kaiga karasawa ba tun maganar da jamila tayi ta farko ta dakatar da hamad ya tsaida wheel din ta dafe kanta, yau gaba daya tunda ta tashi bata iya magana da kowa ba, sunmayi tunanin ko ciwonta ne, har fadila na cewa kar ayi discharging dinsu don gaba daya yanayinta ya sauya gashi taqi fadama kowa komenene ke damunta, saima insisting datayi dole yau ayi discharging dinta haka kuwa akayi don yanxu dole a lallabata saboda yanayinta baason ta shiga wani state na damuwa.
“Wacece wannan mahaukaciyar??” Fadila tayi magana cikin bacin rai,
“Kinga da hankalina, ga uwarku nan tasan maganar da nake ay”
“Keeee!!!!! Kinsha kwaya ne? Who allowed this insolent woman in here????” sameer ya daka tsawa, jamila ko a jikinta, saima taunar chewing gums dinta data keyi hankali kwance, daidai nan hadiza ta karaso, tana yaqe kamar zautacciya, sai faman haki take, jikinta ko sai kyarma tsabar tashin hankali ''karku saurari abunda take fada, yar kwaya ce a buge take ma, makociyarmu ce achan anguwarmu, bashinta naci ban biyata ba, shine tazo na biyata, saboda ban cika mata sauran ba shine take kokarin bina da sharri don a koreni anan dan allah kusa a futar da ita''
''ai idan batasa an koreki ba yau dinnan zaku bar gidan nan keda wannan shedaniyar yar taki, mugaye wanda babu allah a ransu, a maku alkahiri ku sakawa mutun da sharri,har yarki nada guts din daukan wuka zata illata maya, idan har zata iya daukan wuka ta yanke ta to tabbas zata iya kisa''
hadiza najin an anbato maya hankalinta ya tashi, daidai lokacin idanunta ya sauka kan maya data rike hannunta daya baci da jini haka zalika rigarta, har zuwa lokacin hawaye takeyi fuskar nan yayi jaga jaga sai faman tabe fuska take tana washh,
da har ranta ya fara baci ganin wannan matar data gani a dakin hadiza daxu na kokarin bata mata shiri sai kuma yanxu da fadila ta dawo da maganar yankata da sabeeha tayi saitaji dadi, so take kawai a koresu daga gidan.
hadiza harda tuntube tsabar rudewa ta nufi inda maya ke tsaye hankalinta a tashe har tana bangaje bahijja dake gefen mayan tace ''innalillahi wa inna ialaihi rajiun, jinin menene wannan a jikinki? wa ya maki haka? ina kikaji ciwo?, jini ne wannan?, na shiga uku, da zafi?, waya maki haka? wallahi bazan bar koma waye ya maki haka ba''
gaba daya ta susuce tama manta da batun jamila gaba daya, saboda ganin mayan datayi da riga duk jini, kamar dai yanda hankalin kowa ya tashi saima nata yafi na su.
sai suka zama yan kallo, yanda ta rude ko bahijja batayi irin rudewar ba, sai faman tattaba maya take tana kokarin ganin inda taji ciwo, mayan kuma sai faman tureta take.
duk sai suka tsaya sororo suna kallon ikon allah, …Bahijja ko babu abunda take sai kallon hadiza da mayar, magnagnun da jamila tayi dazu na yawo a kwakwalwarta.
jamila na ganin haka kawai ta soma tafawa,''wato shifa sharrin jini ko, baya taba buya, sannan yau na kara tabbatar da hankali ke gani ba ido ba,koda yake bazanga laifinku ba tunda bata barku haka ba harda aikin asiri,''
chak hadiza ta tsaya tare da sakin maya, sai a lokacin hankalinta ya dawo jikinta, kwata kwata bata lura da abunda take shirin yi ba sai yanxu, ta fara kame kame.
fadila ce dai ta sake magana a karo na biyu ''wannan wani irin maganan banza ne wacece ke da har zaki shugo cikin gidan nan kina fadin magnagnun da basuda fasali? ku fitar da su daga gidan nan''… ta fada rai a bace tana instructing guards din
daman tana da zafi sosai don tafi bahijja zafi.
''kafin kisa a futar dani inason ki sani….''
hadiza na jin haka batayi wata wata ba kawai tayo kan jamila iya karfinta, duk ta burkice gaba daya, har dan kwalinta na neman faduwa kasa, kamar wadda zatayi hauka, jamila tayi wani irin kukan kura ta turata ta fadi kasa kamar kayan wanki, ta dubeta tace;
''duk fa abunda zakiyi bazaisa na fasa tona maki asiri ba, a tunanin ki wai guba kika bani daxu ko? toh bari kiji, a shirye nazo gidan nan yau dinan, ni bana rufa rufa, daman na fada maki indai har kika ci amanata saina wulaqantaki hadiza, kuma nice zan zama ta farko da zan kwance maki zani a baynar nasi, wannan annamimiyar da kuke gani idan har kukaji abunda tayi maku to wallahi bazaku kara barinta tayi yawo a doran kasa ba don…..
a daidai lokacin wani karfi ya sake zuwanma hadiza ta fara kokarin tashi kamar zautacciya ganin dai da gaske jamila tona asirin ta zatayi, inda da akwai wuqa a kusa da hadiza babu abunda zai hana ta daba mata adai dai wannan lokacin duk don kar asirinta ya tonu, ga idanun kowa a wajen, da asirinta ya tonu gwara ta kasheta inyaso itama a kasheta, don bazata taba bari asan cewa maya ce yarta ba sabeeha kuma itace yarsu, tunda har ta kawo e yanxu bazata bari komai ya wargaje ba, bazata taba bari yarta ta dandan talaucin rayuwa ba, sannan yar bahijja kuwa saidai ta kare rayuwarta a wulaqance wannan alkawari ne ta daukarma kanta.
daidai nan idanunta ya sauka kan irin manya manyan grass sweeper machine da ake gyaran grass dasu, kamar mahaukaciya haka ta dauko sandar karfen abun ta taho da gudu, ko tsoron manya manyan guards dinnan bataji ba, bataji bata gani, “jamilaaaaaaaa,…saina kasheki, saina kashekiiiiiii!!!”
kafin kace komai sai kawai suka biqe da bugun juna, basuyi aune ba sai ganin waennan guard din sukayi akansu, hankali tashe hadiza tace ''wallahi mahaukaciya ce, mahaukaciya ce karku saurari maganganunta''
Ya sameer ne ya dubi securities din ya bada umarnin a fidda jamila daga gidan, ganin haka yasa hadiza ta soma washe baki.
“ku saketa''!!!!!” Anne tayi magana wanda yasa duk kowa ya maida hankalinshi gareta.
tuni dariyar kan fuskar hadiza ta koma da furgici…“Hajiya hajiya wallahi mahaukaciya ce, cutar haukace da ita karku tsaya bata lokacin ku wajen sauraron maganganunta na banza, yama wannan zancen zai zama na hankali???” Hadiza ta fada tana ihu duk bakinta ya fafashe saboda bugun juna da suka dungayi ita da jamilar.
jamila ko me zatayi banda dariyar yan bariki, ta sake maida daurinta gaba, kafin tace
“A karamar kwakwalwarki kina tunanin zanzo da magana ta baki ne kawai? Da shedu na nake tafe…, nii jamila da kaina na chanza yar bahijja da yar hadiza, ranar 24th ga watan October shekarar dubu 2001 a ranar da aka haifesu..”
Wani irin dummm bahijja taji akanta kamar an buga mata guduma, fadin irin shock din da kowa ya shiga a daidai wannan lokacin bata lokaci ne, daddyn maya ko idanunshi bai kaiga ko'ina ba sai kan sabeeha dake tsugunne, sabeeha ko in banda kuka babu abunda take, tsabar rikicewar datayi tunda taga wannan guards din sun zagayeta, tsabar rudewar datayi batama san maganar me akeyi ba.
Maya ko da ba maida hankali tayi ba wajen magnagnun da sukeyi akai, burinta kawai so take a futar da sabeeha.
“Karyaaa ne karya ne wallHi karya ne karya ne, karku saurari wannan mahaukaciyar, yar kwaya ce, ba tun yanxu take kwaya ba har taohon mijinta ta kashe, yar kwaya ce yar tasha ce ku fitar da ita daga nan” hadiza sai kawai ta fara soshe soshe ta dora hannu aka tana neman guduwa, kamar jamila tasan me take shirin yi wannan yasa tayi saurin damqo hannunta, ta kalleta cikin ido tace
''karma ki fara soshe soshen munafurci, wallahi taki ta kare yau hadiza,''
duk yanda hadiza taso ta kwace ma jamila kasawa tayi don riko ta mata na mu mutu tare, kowa ma ya rasa.
''baiwar allah wannan wani irin magana ne?kinsan abunda kike fada kuwa?'' nanna ta fada tana dafe kirjinta, don dakyar ne idan jininta bai hau ba.
''idan baku yarda da maganganun danayi ba zaku iya tambayar hajiya'' jamila tayi nuni da anne.
gaba daya sai suka maida dubansu ga anne, da mamaki sukaga tana zubda hawaye, tuni hankali sameer ya tashi, bama shi kadai ba harda fadila.
''allah ya tsine maki jamila, allah ya tsinema ubanda ya kawoki duniya, wallahi karya takey..''
ay gaba daya hankalinsu baya ga hadizar ma gaba daya, sun maidashi ga anne data kasa hada ido da kowa, kuma ta kasa cewa komai.
Bahijja data sandare, lokaci guda nunfashinta ya nemi daukewa, ta kafama anne idanu,ANNEN ma kallonta take, tuni taji gaba daya kafafunta na neman qin daukanta tayi baya zata fadi maya ta tarota.
bahijja na cikin wannan state din na furgici ta dubi hannunta inda aka deba jininta jiya da anne tasata zuwa asibiti da gaggawa, tuni ta soma jujuya kanta, ganin abun take kamar a mafarki, ay har gwara ace mafarki takeyi wata qila inta farka zataji sauqin abunda takeji.
kasa kallon inda sabeeha ke tsugunne anne tayi, don zuciyarta ta karaya, yau akwai babban tashin hankali a cikin gidan innalillahi wa inna ilaihi rajiun.
''anne? kodai jikinta ne? mu koma asibiti'' sameer yayi magana cikin tashin hankali, ko sauraron abunda yake fada batayi ba tace
“rabi dagata ku shigo ciki''
tana fadin haka ta dubi sameer, ''ku shigo min dasu suma” tana gama fadin haka hamad ya tura wheel dinta zuwa ciki, rabi tayi gaggawar taimakawa sabeeha ta tashi tsaye, gaba daya ta galabaita, ba karamin duka bahijja ta mata ba da wannan wire, tuni hankalin maya ya tashi ganin ana kokarin komawa da sabeeha cikin gida, sai a yanxu ta fara fuskantar abunda ke faruwa, daxu dai bawai ta maida hankali bane kan magnganun da akeyi.
hadiza na tirjewa haka jamila ta kankame hannunta guards dinan suka tasa su a gaba, hadiza babu damar guduwa, tayi tsuru tsuru, bata taba tsammanin asirinta zai tonu cikin sauqi haka ba, tayi dana sanin sanin haduwarta da jamila, zagi kuwa babu irin wanda batayi ma jamila ba, gaba daya ta susuce, bata sanin me take fada ita kanta.
Bahijja dai bata san yanda akayi ta shugo parlorn ba don ta shiga wani yanayi mai tafe da furgici da tashin hankali da fargaba, bin kowa kawai take da idanu gabanta na faduwa, har idanunta ya sauka kan sabeeha da tun shugowarsu ta sulale kasa sai faman kuka take kasa kasa tana shesheqa.
duk sun zazzauna kan kujera kamar waenda aka kawowa saqon mutuwa, duk sun zubama anne idanu, nanna na gefenta ta dafe kirjinta saboda yanda yake mata nauyi. daddyn maya ko gaba daya idanunshi sunyi jaa sosai.
ga su jamila da hadiza a zaune, har zuwa lokacin jamila fa bata saki hannun hadiza ba da har lokacin zage zage take, gaba daya ta zama kamar burkitattciya,sameer ya doka mata tsawa wanda