Advertisements
Chapter 28 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 107

81K to 84K   out of 320.4K words

daga dakin.
Hankalin gaba daya a tashe yake,he has come to conclusions so take ta rabu dashi kenan? Shiyasa take waennan abubuwan? She’s just going to wipe him? Bayan wannan ma da alamu so take ta kaudashi da babinsa a cikin rayuwarta?
Fadin irin tashin hankalin da tareeq ya shiga a wannan lokacin bata lokaci ne, fadwa butulu ce,”wato you want to play it dirty?”
Wata shekakkiyar dariya yayi, “lallai bakisan bariki ba, a cikinta na taso, youll regret this fadwa”
….
, “


✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 76

Tareeq Yana fita daga gidan bai tsaya ko ina ba sai wajen wani shakawata dayake haduwa da friends dinshi, yana zuwa ya samu abokin harkarsa, duk wani sirrin juna sun gama sani don tare ma suke yin abubuwansu.
Zaune suke cikin motar tareeq yayi shuru ya kasa cewa komai idanunshi sunyi jaa sosai jijiyoyin kanshi duk sun tashi hannunsa kuwa har bari yake, kallonshi abokin nasa yayi yana sauraronsa bayan ya kwashi kaf abunda ya gani daxu a dakin fadwa kafin ya fito.
“Bazan barta ba, bazai yuwu ba, she can’t just take me out just like that, babu abunda na samu,”
Sauke ajiyar zuciya abokin nasa yayi kafin ya soma magana shima “well idan na fahimci inda zancen ka ya dosa, she’s trying to get rid of you? Just like that? Baka tunanin akwai wata a kasa? Baka tunanin akwai wani abu daya sha mata gaba game dakai? Koma dai kaine ka sha mata gaba? Anyways muje ma dai tana son ku rabu? Meysa zatayi gathering wannan evidence din against you?”

“It’s obvious mana she doesn’t want anything that has to do with me, ni nasan tun da dadewa tasan duk abunda nake and i will not take that as the reason”
Kama haba abokin nasa yayi yana nazari kafin yace “this is bad, you need to find what shes up tun kafin tayi screwing dinka up, cause this is bad, you might end up in jail for this,“
Tareeq najin haka ya sheke da dariya, “she started it, and I promise it will not end well”

Sun dade suna tattaunawa allah kasan yasan abunda suke plotting.

Bangaren su sabeeha kuwa tun bayan abunda ya faru take wasan buya dashi, gaba daya yanxu bata yarda ta wuni a cikin dakin idan har yana nan, wani bi idan ta hada mashi coffee da safe bata yarda su hadu saidai ta ajiye mashi ta wuce kitchen tasha zamanta har saiya futa, bata yarda su sake hada ido kwata kwata, barci kawai ke kawota dakin, wani sa’in ma closet room take zuwa ta kwana abunta,
Ta bangarenshi ma dai gaba daya haushin kansa yake ji, saboda gani yake wannan abun daya faru tsakaninsu raini zai jawo masa, wannan yasa ya fita sha’anin ta, ko ganinta ba son yi yake ba don yana ganinta yake tunawa da moments din.

Bayan kwana biyu…
Cikin kwana biyun nan mutallib ya ka nemo mashi cikakken bayanan inda iyalan khaal suke, sannan ya shirya mashi takardun gidan aka maida shi karkashin iyalan khaal din, signature kawai ya rage.
Wani tunani ne yazo ma taj wanda hakan yasa ya buqaci taimakon mutallib din.
Har cikin zuciyarshi yanaji wani irin game da abunda zaiyi yanxu saidai wannan same zuciyarce ke ingizashi kuma take tantance mashi kan cewa abunda zai yi yanxu shine abunda ya dace.

Shugowanshi cikin gidan kenan bai tsaya ko ina ba sai part din ammu.
Yau ne rana ta farko daya shiko bangaren nata a daidai wannan lokacin misalin karfe 9 daidai na dare.
A zaune ya taddata sitting room din part din da take, tana ganin shi kuwa ta sauke mashi murmushi.
A ladabce ya karaso inda take ya kama hannunta ya sumbaceta yanda su larabawa keyi kafin ya zauna.
Da fara a ammu ta kalleshi kafin ta soma magana “ina fata dai lafiya? Wani abu ya samu fatiman?”
Dan nunfasawa yayi kafin ya soka magana, “zanyi tafiya ne gobe da safe”
Yana fadin haka yayi shuru ya kasa cewa komai kuma, ammu dai zuba mashi ido kawai tayi tanason jin abunda zaice,ganin bashida niyyar fadin abunda ya kawoshi yasa tace “toh allah ya kaimu Allah ya kiyaye”
“Ameen “ kawai yace ya miqe ya nufi wajen fita bayan ya mata saida safe.
Sama ya wuce direct, as always yana shigowa sitting room ya hangota kwance kan sitters barci ya debeta a wajen,har zai kauda kanshi chan kuma ya tako har zuwa inda take kamar yanda yayi suspecting kuwa kiris ya rage ta fadi wannan yasa yayi sauri tareta da hannunshi faya yanda bazata tashi ba ya maida ta ta gyara kwanciyan nata da kyau.
Dakin ya wuce ba tare da ya sake mata kallo na biyu ba.

Washe gari da safe tun wajen karfe tara ya gama shiryawa cikin kandura,ya aza rawanin ya futo sak balaraben shi asalin arab guys,yayi masifar kyau sosai, daman shigar itace shiga da mutunci da kamala sosai.
Ataikaice dai wajen karfe 10 ya gama komai ya dauka wajen shi da wata mini bag ya fito,bai tsaya ko ina ba sai hanyar kitchen daya nufa jin karar mutun a wajen, ya dade yana contemplating ya shiga ciki ko karya shiga daga karshe dai hade fuska yayi sama da kasa yasa kanshi ciki.
Lokacin daya shugo vata ma san da mutun a wajen ba, ko second biyu ba a yi ta juyo karaf idanunshi ya sauka cikin nata.
Da hanzari ta cire nata daga nashi gabanta na faduwa sosai har tana nema ta rikice tayi saurin gaishe dashi, shima dai ta bangarensa tunda ya mata kallon daya ya kauda nashi idanun ba tare da ya amsa gaisuwan nata ba.
Duk sai sukayi shuru, shi baice mata qala ba ita kuma tsoron dagowa ma take su hada idanu, don gaba daya cikin kwana biyu ya sauya mata hakan yasa ta danyi baya baya dashi.
Futowa yayi daga kitchen din tana ganin haka tabiyo bayanshi itama daidai tsakiyan parlor ya dakata ba tare da ya jiyo ya kalleta ba yace
“I will be out of the town,“
..fuskar shi na nan yanda take yayi magana a hade yace “take care of your self” kamar am mashi dole haka yake magana.
saurin dagowa tayi ta kalleshi da mamaki, tunda ya dawo hayyacinshi bata taba jin yace zaiyi tafiya ba, saita samu kanta da son jin karin bayani inda zai je don harga allah ta damu dashi sosai, ganin tayi shuru ta zuba mashi wannan idanun nata yasashi juyawa zai futa “didi…”
Chak ya tsaya bai juyo ba haka zalika bai tafi ba, dalilin kamo hannunshi datayi,he can feel yanda hannunta ke rawa sosai kamar wadda ke cikin furgici, chan kuma data lura da abunda tayi tayi saurin zame hannun nashi tace “sorry…”
Kame kame ta fara, ganin tana wasting mashi time yasashi cewa “anything else?”
Yanda ya fada babu wasa a fuskanshi,kamar zatayi kwalla tace
“Yaushe zaka dawo? Dan allah ina zakaje?meysa zaka tafi?” Harga Allah tayi wannan tambaoyinyin ne sbd tana taoron kar wani abu ya sameshi idan ya tafi badan wani abu ba.
Shiko dake a wuya yake da ita juyowa yayi ya mata wani irin kallo yace “bakida ikon sanin inda zance? Just because na baki attention kina tunanin you have d audacity to pretend like a wife to me?” Ya karashe yana kallon cikin idanunta as he’s talking.
“Stay on your limit lady…and don’t ever ask me that kind of a question I’m i clear?”
Tunda ya fara magana ta soma jin wani hawaye na gangaro mata a fuska, harya fuce batama san ya futa ba.
Tabbas tasan batada wani daraja a idanunshi, kuma baiyi considering dinta as his wife ba, ta yarda da hakan don tasan yafi karfinta amma bata taba tunanin wannan daga gareshi ba.

Wunin ranar haka tayi shi shuru kamar wata baiwa, chan wajen yamma ammu ta shugo suka gaisa nan amra ke shaida mata ay yayi tafiya tho bai fada mata inda zaije ba, ammu taga damuwa karara a fuskanta wannan yasa tayi consoling dunta.

Chan bangaren taj awa uku yayi a jirgi sai gashi a egypt..address din da mutabblib ya bashi yayi amfani dashi zuwa inda yake so yaje..bai wani sha wahala ba ya iso gidan, gida ne dan matsakaici, saida ya karaso gaban gate din yama rasa me zaiyi, gashi bai da contact din ta balle ya kira, sai yanxu ya tabbatar ta ya watsar da zumunci kuma hakan ba daidai ba, ko min lalacewar naka naka ne.
Yana cikin wannan nazarin aka budo kofar gate din gidan, wani babban mutun ne ya futo daga gida, furfuran fuskanshi duk ya gama cika gashin dake fuskanshi.
Da mamaki yake kallon taj shima yana kallonshi kafin ya fan sauke kanshi kasa.
“Sannu bawan Allah..akwai wanda kake nema ne?”
Mutun min ya jefo mashi tambaya, dukda taj bai san ko wanene ba ganin yanda ya manyanta yasa shi saurin gaishesa sannnan ya masa bayanin abunda ke tafe dashi da kuma koshi waye.
Wani irin dadi ne ya lullube tsohon nan ya mashi jagora zuwa cikin gidan.
Basu tsaya ko’ina ba sai wani babban parlor da aka shimfideshi da carpet da tuntun zama.

A gaggauce babban mutumin ya shiga cikin gidan bai wani jima ba sai gashi da matar khaal sun fito gaba dayansu harda yaranshi guda biyu.
Tunda ta shugo daya mata kallo daya ya sauke idanunshi, idanunta sunyi jaa sosai saboda kukan datayi jin wanda yazo gidan, abunda bata taba tsammani ba kwata kwata dukda mutallib ya kirata ya shiada mata tana da bako.

Yaran na ganinshi sanin koshi waye yasa suka tafi wajenshi da gudu don suyi wasa, suna rungumeshi kuwa yaji gaba daya ya sare, wani irin nauyi yaji a kirjinshi.

Bayan sun gaggaisa tsohon ya futa don ya basu waje tare da yaran, sai a lokacin taj ya samu damar gaisheta kanshi a kasa ya kasa hada idanu da ita don wani irin kunya yaji ganin yanda suka koma.
Ganin ya kasa cewa komai yasa ta soma magana, “allah mai yanda yaso, ashe inada rabon ganinka tajudeen..ayau dukda khaal baya raye burinshi na duniya ya gama cika”
Tunda ta soma magana ya dago ya kalleta chan kuma ya sauke kanshi kasa, tambayar data kefo masa yasa ya dago don ya amsa ta.
“Ya wajen yan uwan naka?”
“Suna lpy..” ya amsa ta a taqaice.


Taheels resident…
Kallon sonata afiya ta soma yin jin abubuwan da ta fada..”ke ya akayi kikasan baya kasar?”
Wayar ta zaro tare da danna recording sannan ta miqa mata don taji da kyau, maganganun su ne radau ke fitowa sosai daga cikin wayar inda yake cema sabeeha zaiyi tafiya sai magnganunahi na karshe wanda suka sa sonata jin wani irin dadi aranta, ashe duk abunda sukeyi a gabansu duk karya ce, baiyi accepting din sabeehar ba a matsayin matarshi, yana zaune da ita ne kawai saboda cikin shi dake jikinta wanda tayi alkawarin a yau yau dinnan saita aan yanda tayi ta zubar da cikin.
Wani irin makirin murmushi afiya tayi kafin ta zaune gefen gado ta daura kafa daya kan daya sannan ta jefo mata tambaya..” how did you get this? kina spying dinsu ne?”
“Obviously..kina tunanin zan hkura ne..dole na samoma kaina waje a gidan nnan kafin wannan old rag din taku ta koreni, cause it’s obvious bason zamana take ba..infact babu wani dalilin zama na a gidan nan indai bazqn samu big T ba”
“Toh yanxu me zakiyi kennan?” Afiya ta jefo mata tambaya.
“Zaki taimaka min?” Sonata ta jefo mata tambaya da turanci.
“Yea count me in…last plan dinki baiyi ba hope this time around zaki chanza wani?”

“Yes of course”
Tafawa sukayi tare da sakarma juna wani irin makirin murmushi.

Around 8 na dare suka hauro sama, nan sitting room dake saman, daman tun dazu sonata ke zarya tana neman chance din hawa saman saboda ammu dqta kwasar mata kashedin hawa.
Kamar munafukai haka suka dunga labe har suka isa bangaren taj da sabeeha.
Babu kowa sitting room din sai tv dake kunne babu sound gefe kuma irin dan karamin couch blanket dinnan ne sai tea akan center, wani irin sanyi sonata da afiya sukaji aransu don hakan na tabbatar masu da itace ta ajiye.
A gaggauce ba tare da wani bata lokaci ba sonata ta bude wani bottle ta miqa ma afiya dake gaban cup din ta zazzaga wasu kwayoyi kananu a cikin sannan ta juya tea nan kafin su fice daga part din.
Suna fitowa sukayi tafi tare da dariya mugunta sannan suka sauka kasa.
Baiwar Allah sabeeha data shiga bathroom tana fitowa ta dawo parlor ta zauna ta sake doka wani sabon tagumi, ta jima sosai tana tunani kala kala,yau har tunanin mahaifiyarta saida tayi ita allah ya cire mata tunanin gaba daya kamar daukewar ruwa.
“Ko me yakeyi yanxu? Shin yaci abunci kuwa? Yana cikin koshin lpy?” Tambayoyin datake ma
Kanta kennan tunda ta zauna, ko abuncin kirki kasa ci tayi gaba daya tunda ya tafi, tana cikin zulummi sosai, yanxu haka ma takura ma kanta tayi dole ta nemi tea tasha.
Ba tare da tunanin wani abu ba kawai ta dauka cup din ta kafa a baki saida ta kwankwade duka sannan ta sauke ajiyar zuciya sannan ta aje cup din gefe ta lullube da blanket dinnan ta kwanta hawaye na zarya akan fuskanta tunawa da maganganunshi.

3am..
Misalin wajen karfe uku na dare ya shugo gidan kamar wani barawo, tun ranar daya ga wannan takardun da fadwa ta ajiye bai sake dawowa gidan ba sai yau, yau dinma curiosity din dake cinshi ne ya hanashi sakat ya sashi shugowa bayan wannan ma hunch dinshi na bashi akwai abunda fada ke boyewa.
First thing first wajen motocinta idanunshi suka sauka a wajen, ganin babu sabuwar motarta a wajen parling lots din ya tabbatar mashi da bata nan, daman ya kira daya daga cikin securities din gidan sanin koshi waye a wajenta ya shaida masa ta fita bata dawo ba.
Wannan ya bashi damar shiga ciki a gaggauce, part dinsu ya wuce yabi ko’ina da kallo yana nan yanda yake yana wani nazari, futowa yayi daga dakin ya shiga nata dake daga chan sako ya bude kofar ahankali kamar wani barawo, kofar na bude lights din dakin ma babu wani haske sosai, dube dube ya soma yi har wajen bathroom don ya tabbatar babu ko kafin ya fara binciken daya kawo shi, daga kan closet dinta, bedside drawers..ko’ina babu inda bai bubbude ba, cikin rashin sa’a bai samu komai ba, tsabar bacin rai yasashi buga bangon closet dinta “shitt…wallahi nasan kina boye wani abu..kuma dole saina nemoshi, i will take you down wit me”
Ay bai gama magana ba kawai yaji motsi, cikin hanzari yayi magana tare da zaro ido ganin closet din na juyawa saiga wata kofa ta bude, mamaki tsoro babu wanda bai durar mashi ba sai kawai ta sauke wani makirin murmushi tun bai shiga daga ciki ba yaga menene “bingoo”
Ya furta kafin ya karasa tura kofar da kyau ya shige daga ciki, mamki Ne kwance cikin ranshi, bai taba tunanin akwai secret room kaf gidan, wato yayi underestimating dinsu gaba daya.
Cikin secret room din ya shiga, ko’ina duhu babu wani haske ko daya tal saida ya zari wayar ya kunna haske, take hasken ya bade ko’ina, bin dakin yayi da haske babu komi a wajen, shi yama yi tunanin ko kudade ne a ciki sai yaga akasin haka wayam babu komai, har zai juya idanunshi da hasken ya sauka kan table da wani board a gaban table din, ba tare da second thought ba ya taka har wajen yana haska kan table din, laptop ne a ajiye a rufe sai wasu wayoyi kamar guda goma a ajiye gefe kuma tray ne da wata powder akai, sai irin ticking watch dinnan yana tiktik tik a wajen,
Kujerar dake wajen ya jawo ya zauna tare da ajie wayanshi gefe ya kunna laptop din, sai fama jijijga kafa yake yana allah allah laptop din ta gama loading harta gama cikin ikon allah babu pin babu komi ya bude laptop din ya fara buncike, duk binciken duniya nan babu wanda baiyi ba harda backend server din baiga komai ba da zai mashi amfani, saima cctv cam recorder daya gani, koda ya shiga ma babu abunda ake gani sai blank black screen, rai a bace ya buga table..”shitttttt…damn it”
Rai a bace ya miqe ya nufi wajen board din ya juyo da katon board din yana facing dinshi, take ya zaro idanu yana kallon hotunan da aka manna sunfi guda dari a board din, wasu anyi canceling hotunan da irin jan marker dinnan ko fuskr ma ba a gani, abu daya ne ya gama daure mashi kai ganin hotunan taj hauka a wajen,gashi tayi rubutu akan pictures din da mine…minee kai abunda ba a cewa komai wasu hotunan ma babu tsari, harda wani hoto daya fito daga bathroom, kadan ne babu tsiraicinshi a wajen,tareeq dai yaga karamin tashin hankali a wajen, ga wasu irin details zane da akayi akan board din daya kasa gane na menene kamar irin plan structure dinnan, wayarshi yayi saurin zarowa yayi snapping duk abubuwan dake jikin board din..yana cikin yi ya tsaya Chak yana zare zaren ido gabanshi na faduwa jin tari mai sauti, tabbas yasan shi kadai ne a cikin wannan secret room amma daga ina sautin tari ke fitowa? Kodai ta dawo ne? Abunda yazo mashi mind kennan yana kokarin daukan hotunan abubuwan daya gama gani kawai ya juya harzai futa idanunshi ya sauka kan screen din laptop dinnan, chak ya tsaya ya kura ma screen din idanu, har baisan sanda ya tako ya zo wajen ba,jikin har rawa yake sosai barbar bar yayi saurin yin baya sosai, idanunshi sunyi jaa sosai, babu abunda ke kwance kan fuskanshi sai tsagwaran fargaba da tsoro, yakai wajen minti biyu bai kifta idanunshi ba har ya samu ya janyo nunfashinsa da kyar, bai gama processing tashin hankalin daya gani ba idanunshi suka hango mashi wani tashin hankalin, hotonshi ne a gefen laptop din kwata kwata bai lura dashi ba anyi irin marking zanen daya gani dazu a jikin board da alamu dai koma dai menene shine next target,wallahi sai tsintar kanshi yayi a bedroom din baima san sanda ya fito ba tsabar tashin hankali,dakinsu ya koma ya kwashi duk abunda zai kwasa daya san zai amfaneshi daga kan rolex data saya mashi, gold bars daya dan tara gaba daya kaf saida ya kwasa harda kayanshi sannan ya fito daga

28 / 107