Author : Queenmerh Category : Complete Novels
rayuwar da kikayi ba a baya ba don ke kadai ce zaki fadi irin rayuwar da kikayi amma ina godiya ga allah dayayi mana protecting dinki, ya kuma kareki ya maido mana ke wajenmu, alhamdulillah alhamdulillah…duk muna kaunarki, muna sonki sosai, kuma kinada gata, kinji ko”
Sabeeha na hawayen farin ciki tace “nagode nanna… kukan da nakeyi kukan farin ciki ne, ban taba tsammanin inada gata haka ba, na kasa yarda da hakan, idan na tuna irin rayuwar danayi a baya..”
Sai kawai tayi breaking hawayen dake fuskanta, ya soma saukowa sosai, nanna ta rungume ta sosai tace
“Ki mance da komai kinji, karki saka komai aranki kinji ko? Duk abunda ya faru mukaddari ne daga allah dama chan allah ya rubuta hakan ne zata kasance bazamu san ke jininmu bace sai bayan wannnan shekarun masu tsayi,You have us all, kina cikin gata da soyayya, Ina fatan kuma zan ganki da mahaifiyarki..”
Saurin saukar dakai sabeeha tayi, jikinta yayi sanyi sosai wani sabon hawayen ya soma sauko mota.
Nanna ta lura da hakan tayi saurin jawota jikinta ta rungumeta, “tsakaninki da mahaufiyarki bahijja? Shin bakya farin ciki data kasance mahaifiyarki”
Nanna na gama magana kamar ta tsokalo mata wani abu kawai ta fashe da kuka, ta girgiza kanta, “meysa baza kije wajenta ba?”
“Bata sona!!!” Sabeeha ta fada kai tsaye.
“Karki taba tunanin haka, wallahi babu wanda yakaita sonki duk soyayyar da muke nuna maki, bansan meya shiga tsakaninki da ita ba da har yasa kikayi wannan tunanin amma inaso ki sani duk avubda ya faru cikin rashin sani ne,ki bude zuciyarki fatima, wannan dama ce allah ya bamu harda ke, ki dauki abun kamar an sake haifarki cikin wata ni’imatacciyar sabuwar duniya kinji ko?”
Magangnun nanna ba karamin dadi sukayi ma sabeeha ba kuma suka sake kwantar kata da hankali,
……..
After a week…
Cikin sati gudan nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa shine tabbatatuwar rayuwar sabeeha data chanza on a blink of an eye, tun bata amince da hakan ba tana ganin abun kamar wasa harta yarda, soyayya take samu da gata ta kowanne bangaren, har ta soma sakin jikinta baiwar Allah, ganin abun take kamar a mafarki tana jin kamar za a ta tashi, dukda ta san kowa a gidan tunda sun kusa shekara da zuwan su gidan ita da hadiza jinsu take kamar yau ta fara sanin su, mutanene masu daraja da son jininsu fadin irin farin cikin da take ciki bata lokaci ne, a da kullum cikin kwanakin saidai taita kuka tana tuna irin rayuwar datayi a baya, amma kasancewar nanna da anne da anty fadila a gefenta uwa uba kuma mahaifinta, wanda har zuwa lokacin ta kasa yarda da ita sabeeha wai tana da uba kuma tana da gata, soyayya suke nuna mata babu adadi, from left and right ta kowanne bangare, bangaren ya sameer ma da nashi iyalan suna farin ciki, musamman anty mubina, hamad ma ya samu damar yin magana da ita kuma yana mai farin cikin kasancewarta yar uwarsa ta jini, laila ko har zuwa lokacin ta kasa zuwa ta ga sabeehar saboda tunawa da irin abubuwan da suka mata ita da maya, yanxu ashe duk wannan lokutan maya ba asalin cousin dinsu bace yar matar da ta sauya masu cousin dinsu ce? Kai ba lailan kadai ba duk wanda ya tuna da wannan abun sai yaji gaba daya baya son ganin mayar.
Yan uwan majeed ko tattaki sukayi tun daga Lebanon suka zo, iyayensa daman sun rasu, sai sisters dinshi, yanda kowa ya shiga shock haka suma suka shiga saida suka zo sukaga sabeehar, it was an emotional moment for all of them abun dai ba a cewa komai.
Kamar dai yanda majeed yaji lokacin daya fara ganin sabeeha har yaga kamanninta da kakarsa haka suma yan uwansa suka dunga fada, ranar dai sabeeha taga soyayya, haka suka dunga rungumeta suna sumbatarta a kumatu yanda suke a aladarsu suna murna harda masu hawaye itama dai hawayen farin cikin take.
Fadila kam ko maganar mayar ma bata son yi, akwai ranar da laila ta shiga part dinsu mayar donta dubota saboda hamad yace ta dunga zuwa tana dubata, yanda taga mayar hankalinta ya tashi sosai har kwalla saida ta mata saboda tsakani da allah tana sonta har cikin zuciyarta kuma ta kasa yarda da ba cousin dinta bace ta asali, shes a replacement of sabeeha, bayan wannan yanda taga mayar ta koma ma saida ta tsorata, ranar sunsha kuka sosai maya na tambayarta shikenan yanxu ita ko kowan kowa bace kuma ba yar mummy da daddy bace yar mai aiki ce? Kuma yanxu shikenan tunda batada alaqa dasu za a koreta ko? Kuma duk sun daina sonta ko? Laila dai nata tausasata tana nuna mata cewa bazasu tsaneta ba tunda itama yarsu ce kuma ba laifinta bane, itama haifarta akayi, batada laifi,
A haka dai suka rabu ta fito daga wajenta,
Tana koma part dinsu ta fada ma mami (fadila) yanayin data tadda maya tana hawaye fadila ta daka mata tsawa sannan tace mata karta sake kawo mata maganar wata maya, gaba daya saitaji tsanar mayar daman tun farko tana doubting yarinyar kamar ba yar bahijja ba,ashe hunch dinta gaskia ne,
Bahijja ko har zuwa yanxu ta kasa tattara courage din fuskantar yarta ta asali wato sabeeha, a cewarta bata chanchanci kasancewa mahaifiya a gareta ba saboda irin abunda tayi mata a baya, ta nuna tsana a gareta.
Nanna da fadila kullum nusar da ita suke illar kauracema sabeehar na qin fuskantarta da takeyi, kuma blaming din kanta da take bazai amfaneta da kkmai ba, ta kama yarta, ta jata jiki, abunda ya faru ya rigada ya faru bazqsu iya sauyawa ba, kuma rubutattacen al’amari ne, cuta dai hadiza ta cutar dasu cuta mafi tsanani wanda allah kadai ne zai saka masu kuma zai sakama sabeeha.
Su hadiza ko kamar an shafe babin su, babu any track of them, dss ake magana fa😂tunda suka tattara su ko alamun motsinsu ko tarihin su ba a ji, ana chan ana shan azabar da sun gwammaci a kashesu ma, musamman hadiza da basa sassauta mata.
Jamilu kuwa kwana daya biyu uku da baiji motsin jamila ba, ya kira wayoyinsu da hadiza shuru haka kawai jikin shi ya bashi akwai matsala wannan yasa ya tattara yayansa ya sayar da gidan da suke ciki ya tasa su sai kauye.
Maya ko, bana jin zan iya fayyace maku a wani yanayi take ciki, ta shiga wata ukubar rayuwa, taga go no go, ta tabbatar da tabbas ita ba yar gidan bace, sabeehan dai datake wulaqantawa takema kallon wulakantacciyar itace asalin yar gidan, ita kuma yar mai aiki ce, yar mai aikinda bama ta da asali ko tayi tunanin tana da uba, bata iya cin komai, bata iya chan komai, har wata yar natsuwa ce tazo mata, wato wargi ma waje ya samu, ko shaye shayen ma batabi ta kanshi ba, don ba kwaya ba ko roci ce batajin zata iya magance mata matsalar dake kanta, she cant bring her self to believing that ita yar hadiza ce kai ta cuceta data kawota duniya kuma mummy da daddy ba iyayenta bane na asali, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, cikin kwana biyu ta rame ta kanjame, tayi la’asar, kullum tana daki bata fitowa, ay bata gama yarda da gaskiayra dake gabanta ba saidata yi kwanakin nan bahijja bata shugo dakinta ba yanda ta saba, matarda bata iya barci bataji motsinta ba, shikenan tata ta kare, yanxu idan komai ya lafa tunda sun samu diyarsu korarta za ayi kenan? Kai tsanar datakema hadiza ko mutuwarta, tana jin inama za a tasheta ace mafarki take ko zataji sauqin abunda takeji.
Basira kullum saita kawo mata abunci, amma yanda ta kawoshi dakin nan haka zata daukeshi don bata tabawa, kuma duk maganar da zata mata bazatace uppan ba, kullum tana daki futila a kashe,tana kuka.
Nanna ce kawai ke yawan dubata, sai kuma hamad da daddy (daddyn sabeeha🥹 lol)dadyn nema yasa basira na kula da cinta bayan shiga dakin dayayi sau daya don ya dubata, yaga yanda ta koma, da ya tuna abunda hadiza ta masu na sauya yarta datayi da tasu saiyaji gaba daya zuciyarsa ta tsinke, he cant help it, yanajin zafin abun sosai saidai kuma ya kasa yaji tsanar maya saboda ya rike ta a matsayin yarsa kuma har zuwa lokacin yanajinta yarsa ce itama, kuma ba karamın tausayi take bashi ba don itama bata da laifi, laifin mahaifiyarta bazai shafeta ba.
Babban tashin hankalin da suka shiga a satin kuwa shine heart attack din da bahijja ta shiga, saboda damuwar data sama ranta, ranar gaba daya kowa ya shiga tashin hankali mara misaltuwa musamman majeed, da nanna da suka san abunda take ciki.
Saida likitoci wajen uku suka hadu akanta kafin a samu kanta da daidaituwar nunfashinta.
Idan ka ganta dole ta baka tausayi, lokacin da gaba daya ahalin sukaji cewa zuciyarta na cikin barazar bugawa sun shiga wani maquyacin hali.
Sabeeha ko tafi kowa shiga tashin hankali, duk kwanakin da suka dunga yi a asibitin tana gefen bahijja bata matsa ba, kuma basu hanata ba suka barta, anne cema tace su barta kusa da bahijjar saboda bahijjar tafi buqatarta a irin wannan lokacin.
Haka zata kwana tana salloli tana rokon ma mahaifiyarta lafiya, ko barcin kirki bata iya yi sosai, majeed ma yawanci a asibitin yake wuni, da daddare yake komawa gida.
Duk sanda yazo yaga sabeehar kusa da bahijjar tana rike da hannunta sai yaji wani irin dadi a cikin zuciyarsa farin ciki mara misaltuwa ya lulubesa.
Kwanansu wajen uku a asibiti kafin bahijja ta farfardo, ranar data farfado wajen karfe shida na safe tana bude idanunta taji hannunta cikin na mutun, kwata kwata batayi tsammanin sabeeha ce a gefenta ba don tana bude idanunta komai ya dawo mata, ta fara kokarin tashi zaune har zuwa lokacin hannunta na jikin na sabeeha da barawon barci ya dan tafi da ita tayi saurin farkawa.
Ashe tana kwance gefen ta ta dora kanta bisa gadon da bahijjar ke kwance, kafin barcin nan ya dauketa sallar asuba tayi ta dawo kusa da bahijjar ta zauna tana kuka tana kallon fuskarta, tana ayyana ma ranta cewa wannan mahaifiyarta ce ta asali kuma itace ta tsugunna ta haifeta, tana jin yanda she’s blessed, don ba tun yanxu ba takejin tana son bahijhar sosai musamman yanda taga tana son maya sosai, tasha rokon allah dama ace itama tana samun irin wannan so da gatan
Tana cikin wannan emotional state din barci ya fusgeta, sai yanxu data soma jin motsi ta farka.
Bahijja na tabbatar da sabeehar ce a gefenta kawai saita fashe da kuka, tana hawaye sosai gwanin ban tausayi dayasa sabeehar itama ta soma kukan har zuwa lokacin hannunta na cikin na bahijja idanunta yayi jaa sosai, samun kanta tayi da rungume bahijjar sosai kamar zata shige jikinta, hannunta na karkarwa, itama kanta bahijjar jikinta karkarwa yake ta kankame sabeehar sosai, suka rasa wa zai lallashi kowa.
Sun dade a cikin wannan yanayin basu san ma majeed ya shigo ba yana tsaye daga gefe tare da taj suna kallonsu.
Saida sukayi mai isarsu kafin bahijja ta iya bude bakinta ahankali dukda tana cikin wani yanayi na rashin kuzarin jiki tace “bansan da wani irin kalamai zan nemi yafiyarki ba, I’m sorry my daughter I’m sorry for all that you have gone through I’m sorry for not being by your side when you grow up, my heart felt so so heavy a duk lokacin dana tuna ko rikeki ban samu nayi ba bayan na haifeki, i just had a glimpse of you lokacin da aka ciroki daga jikina, when i was unconscious, i am so devastated for not recognizing you? How can i live with this kind of pain???? A tunanina inata rayuwar kwanciyar hankali kuma ban rasa komai ba, allah ya azurtani da komai ashe kina chan cikin wata rayuwar da bata kunshi komai ba sai kunci, hadiza ta cuce ni hadiza ta cuci, allah ne kawai zai min sakayya, ta cuceni….I’m very sorryyyyy my daughter.. ki yafeni, ki yafemin abunda na maki a baya, wace uwace zatayi ma diyarta abunda na maki…da wani ido zan kalleki, ki yafeni yata”
Ta karashe tana kuka mai karya zuciya, wallahi majeed dake tsaye saida kwalla ta zubo mashi, taj ko kasa tsayawa yayi ya futa daga dakin ya koma mota ya zauna.
Sabeeha na kuka harda majina tayi saurin tashi daga jikin bahijja ta tsugunna a gabanta kanta. Kasa tana hawaye ta soma magana “dan allah karki nemi yafiya a wajena, saukar hawayenki masifa ne a gareni, ni ce zan nemi yafi ya a wajenki…ma..ma!!!”
Wannan kalmar mama da sabeeha ta fada ba karamin shigar bahijja yayi ba, sai kawai taji wani sabon kuzari ya zo mata tama manta da canula dake hannunta ta sauko daga kan gadon ta tsugunna gaban sabeehar itama ta rungume sabeeha sosai, sai a lokacin majeed ya karaso cikin dakin yana murmushi bahijja na hangosa ta dago sabeeha ya hadesu gaba dayansu ya rungumesu, sai ya kasance sabeeha na tsakiyansu sun rungumeta, a daidai wannan lokacin me zatayi banda godiya ga Allah, wani irin ni’ima ce ta lullubeta taji ko allah ya dauki ranta yanxu to zata kasance wadda tafi kowa farin ciki a duniya, yau taji kuma tayi experiencing abunda ake kira soyayyar iyaye ga yayansu.
It was so genuine an emotional moment 🥺ya allah.
Gyaran muryar da akayi ne yasa suka daqo daidai, fadila ce ta shugo gefenta laila da hamad sunzo dubiyar bahijjar.
Fadila na dariya ta dubesu tace “what a happy family.. kodai mu koma ne mu barku ku cigaba da moment dinku”
Dariya duka sukayi gaba dayansu, kowa yana kallonsu, bakin sabeeha ya kasa rufuwa, data kalli bahijja saita kalli majeed.
Gaggaisawa sukayi gaba dayansu, aka sha hira bahijja tace itafa a sallameta su koma gida taji sauqi, fadila nata mata tsiya, hardasu cewa wai ay sabeeha tafi kama da dangin ubanta, saboda launin fatarta.
Laila ko tana samun dama ta kamo sabeeha ta rungumeta sannan tace “welcome to the family fatima, im so glad we’re cousins”
Murmushi sabeeha ta mata suka dan taba hira, hamad ma ya shiga cikinsu aka sha hira.
Bahijja dai yau tasan tayi breakfast na kirki rabonta da abunci tun ranar da taji cewa sabeeha yarta ce ta asali wadda hadiza ta mata replacing da diyarta wato maya…sai a yanxu ta tuna da maya.
Sallamar taj ce tasa duk suka maida hankalinsu zuwa ga kofar, yana shugowa idanunshi ya shiga cikin na sabeeha, samun kanta tayi itama da kallonshi.
“Ah ah ashe kana tafe kaima” fadila tayi magana,
Dan murmusawa yayi, majeed yace “ay tun dazu yazo, kusan ma a tare muka iso asibitin”
“Good morning..ya mai jiki” taj yayi magana
Bahijja ta amsa, fadila ma ta amsa, laila ta gaishesa haka zalika hamad, sabeeha ma ta dago ta mashi kallo daya tace “good morning..”
Jiki a mace ya amsa har yana tambayar how shes doing, ta amsa da shes fine..sannan ya samu waje ya zauna yana facing dinta, tana daga zaunen nan tana jin idanunshi akanta.
Bahijja ma ta kasa duake idanunta kan sabewhar, data kalleta saita yi murmushi, shea the happiest mother on earth, wani irin so take ma sabeeha mara misaltuwa, yanda takeji game da ita daban ne, she will do anything to protect her and love her unconditionally……
After a month!!!!
Alhamdulillah alhamudulillah…
Sallamar da akayi ne yasa ta juyo wa da sauri tare da aje duvet din dake hannunta, nima dana rako hamad da paper bags bansan sanda na sakesu ba tsabar mamakin dana shiga, shi kanshi kasa duake idanunshi yayi akanta, tayi wani azababban kyau, wato kwanciyar hankali ma wani abu ne mai mahimmaci ga rayuwar dan adam, wallahi in kunga sabeeha bazku taba cewa itace ba duk kyan datayi a saudi bai kai kyan datayi ba yanxu cikin wata guda, don wannan ya qunshi kwanciyar hankali, farin ciki da kuma natsuwa, ga uwa uba gata ta ko’ina, tayi bul bul abunta fuskanta sai annuri take, sutura ko yanxu saidai sabeeha ta bama sutura baya, mayukan da take amfani dasu so hmm ba a magana, dady ya saya mata dankareriyar wayar da ake yayi, fadila ko ranar daya ta kashe ta shiga shopping mall tayi mata sayyayyar budurwa, lokaci guda suka chanzata, bahijja ko cewa take arzikinta bashida amfani idan har sabeeha bata amfanu dashi ba, duk wani properties dinta ya koma karkashin sunan sabeeha.
Dakinta ko da aka ware mata abubuwan da aka saka mata a ciki ba a cewa komai, anan main house ma aka fidda mata part dinta don anne da nannan sunce wajensu zata zauna hakan fa baisa bahijja taqi organizing mata part dinta ba anan bangaren su kusa dana maya.
Dakin nan an zuba dukiya kamar me, ko quarter shi maya bata samu ba, duk gatan da sukayi ma maya bai kai ko 10% na wanda akema sabeeha ba don komai suna yinshi ne extra yanda bazatayi lacking komai ba a rayuwa, zasu maye mata gurbin abunda data rasa a baya.
Talking of maya, bayan dawowar bahijja daga asibiti aka zauna akayi magana, tsakanin majeed da bahijja dasu anne, manya dai kawai suka zauna sukayi magana akanta.
Da aka zauna maganar mayar fadila na maganar a nemi chan dangin maya na chan kauyensu a miqata wajensu,suma su san da zamanta tunda bata da uba kuma shegiyar uwar tata tana chan a kulle, sai kuma bahijja tace bazata taba yarda a rabata da mayar ba tunda itama yarta ce, koda kuwa bata haifeta ba koda kuwa sanadiyarta suka rasa yarsu suka reneta a matsayin tasu she’s still their child, kuma zasu riketa kamar tasu itama.
Fadila dai bataji dadin wannan zance ba don gudun abunda zaije ya biyo baya, jinin hadiza ce fa? Barinta cikinsu abu ne mafi hadari,kuma she expect duk abunda hadiza ta masu bazasu yarda su rike yarta ba a matsayin tasu.
Duk wani abu daya danganceta ma abun kyama ne kuma abun gudu ne, saidai kawai allah ya rufa asiri.
Amma kuma duba ga yanda mayar tayi sanyi, ta koma wata saliha saliha sai duk kowa ya soma jin tausayinta anne ma tace a bunne maganar kawai yanda take tunda babu wanda yasan da cewa ba yarsu bace in banda hadizar da mutanen gidan gaba daya, duniya bata san da zancen ba don haka ya tsaya a haka kawai saidai abun gudu shine idan har aka tashi aurar da mayar, idan