Author : Queenmerh Category : Complete Novels
sameni inaso muyi magana”
Shiru ya danyi kafin ya amsa shi.
Yana aje wayar email ya shugo mashi kan cewa sai yayi presenting evidence dake nuni da akasin allegations din da akeyi akanshi, sannan in 2days idan baiyi presenting evidence ba, za ayi canceling maganar sauya leadership, baza a bashi kamfanin ba, dukda mahaifinshi ya shigar da sunanshi cikin ahalinsa.
He understands haka system din yake dole saiyayi providing duk wani abu da suka buqata saidai yasan babu wanda ke pressuring abun banda hidaya don shes not giving in kwata kwata kuma ita keda da hannu da wannan al’amarin ko ba a fada mashi ba.
miqewa yayi tare da kwasar takardun shi dake kan desk din ya fita, nan yaci karo da merk ya shaida mashi yayi informing dinshi duk yanda ake ciki anan office din kafin ya futa.
Tunda ya hau kan titi babu abunda yake sai tunani iri iri, different kinds if thoughts na yawo a kwakwalwarshi, wallahi sam baiga ana binshi ba, saida ya kusa karasawa hideout din kamar ance ya dago kawai idanunshi ya sauka a wata baqar mota dake binshi, baikawo binshi akeba saida ya sauya hanya yaga still motar na bibiyarshi nan ne ya karama motar mugun speed ba kadan ba, irin sosai dinnan fa ba kadan ba trying to escape tailing dinshi da akeyi, cikin ikon allah dake he’s smart ya kufce masu.
Girgizq kanshi kawai yayi ya shiga wata hanya daban harta kaishi ga hideout din.
Yana isowa yayi parking tare da dan jinkirtawa, gaba daya he feels so weak and tired.
Mutallib daya hango motarshi yayi saurin karasowa inda yake, tare da bude motar, tak din ya futo.
Kallo daya mutab yayi mashi yaga tsantaar damuwa a tattare dashi,sai yaji wani irin tausayinsa sosai wallahi ba kadan ba don harga allah shima saida yayi questioning maganar da akayi ta cewa shi din dan taintiwa ne dukda bai yarda da hakan ba saboda bai taba jin koda khaal ne yayi maganar magaifiyar taj din ba balle akaiga ya ganta.
Kallonshi taj yayi yace “i was tailed,inason ku chanza hideout kafin komai ya daidaita, bazai yiwu mu khaal ya bayyana ba yanxu don za a iya kamashi, sonake saina fidda gaskiar allegations din da akayi mashi, i need to prove bashida laifi akan komai kafin ya bayyana gaban duniya,”
“But taj we don’t have time, suna gab da cin mana, hidaya ta saka a nemoshi kuka ina gudun..”
“She can’t do nothing…”
Girgiza kai kawai mutab yayi suka shiga daga ciki.
Kai tsaye dakin khaal suka nufa yana zaune yayi shuru, tun dazu yake kallon abubuwan dake faruwa a yanar gizo, ranshi ya baci sosai ba kadan ba, and he has come to conclusions zai fayyace ma duniya komai, dukda yasan ba lallai a yarda dashi ba za a iya mashi wata fassara daban wata qila ma ace shi yayi fabricating mutuwarshi, komai dai zai iya zama complicated amma yanajin hakan ne zai iya dakatar da wannan long term qiyayyar data zama masifa, jini ba abun wasa bane, jinin dake yawo jikin taj shike yawo a jikinsu gaba dayansu.
Sallamarsu yasa ya dago ya kalli taj din ganin yanda idanunshi sukayi jaa sosai.
Zama yayi tare da kama hannun khaal ya sumbacesa.
Mutab ya fita don ya basu waje suyi magana.
Kallonshi sosai khaal keyi ba kiftawa saiya nemi kalaman dazaiyi amfani dashi wajen yima taj din maganar da yakeso ya mashi.
Harga allah ba ayi mashi adalci ba, kuma sai yanxu khaal ke ganin haka, tun tasowarshi babu wanda ya taba zama dashi ya mashi maganar mahaifiyarshi ba, yama cire batun mahaifiya a rayuwarshi gaba daya don bai taso ya ganta ba, baiji duminta ba, baisan dadinta ba.
Doguwar ajiyar zuciya khaal ya sauke sannan ya dubi taj din kafin ya soma magana “Tajudeen….kai dan sunna ne kamar kowa, kuma kanada mahaifiya kamar kowa, “
Cikin saurin ya dago da rinannaun idanunshi da suka cika da ruwa badai na hawaye ba.
“Kayi hakuri, kayi hakuri, babu abunda zance maka saidai nace kayi hkuri, approach din mahaifanka with how they end up yasa ka shiga wannan yanayin,da rayuwa mai kunshe da kunci”
Nunfasawa khaal ya sakeyi yace “it’s high time ka nemi mahaifiyarka, baka da kamarta ayanxu, koni bazan taba maye gurbin iyayenka ba, don alkawarin dana dauka na kasa saukeshi”
Ya dan dakata, siraran hawaye na saukowa akan kuncinsa yayi saurin gogesu.
“Karka zauna ka cuci kanka saboda ni da kuma sunan wannan ahali namu da yan uwanka suka watsar, suka dauki duniya,…i want justice for you and i want to protect you don nasan bazasu barka haka ba saisun ga ka wulaqanta”
Saurin kama hannunshi taj yayi zaiyi magana khaal ya dakatar dashi, “bana buqatar ka wanke ni da laifukan da ke kaina, lets put and end to this”
“No khaal no, idan ka bayyana yanxu komai zai iya faruwa, they can use you against me, they can do anything, zaka bayyana only when na fiddakai na wanke laifukanka”
“But tajideen tayay? How?, na tsufa, ko sun aikani gidan yari yanxu kan laifukan da banba ba komai bane, we can only go down together i want to end this, and this is the only way”
“I will not allow that khaal, bazan bar haka ta kasance ba, if anyone is to pay for everything sune, bakada laifin komai and i would not allow that, ka damu dani tun tasowata yiu have been there till the very end, kanada iyali ta dalilina allah kadai yasan halin da suka shiga, they need you more than i do amma you stand for me, you protected me and i will forever be grateful, now its time for me to pay back, i will bring an end to all of this i promise”
Shuru khaal yayi yana nazari, ya zaiyi yanxu? Tabbas yanxu idan ya bayyana bashida kwakwarar hujja akan komai za a iya kamashi, na biyu kuma hakan bazai bashi damar binciken da yakeso yayi akan wani abu da yake suspecting ba kuma ya kasa tantancewa, yayi tunanin sharing maganganun da taj amma yafiao saiya tabbatar da hakan.
Ko mutallib baiyi maganar dashi ba kwata kwata.
Yanxu dai ba wannan ne mataalar dake gabanshi ba.
“Batun mahaifiyarka…”
Shugowar doctor dake kula da khaal yasa suka dakata,
Miqewa tsaye taj yayi ya dubi khaal din tare da riqe hannunshi da kyau yace “inason kubar wajennan yau, nayi ma mutallib magana, please don’t ask why”
Girgiza kai kawai khaal yayi taj ya mashi sallama ya fita.
Lokacin daya futo wajen around 5 pm ne, saida ya tsaya sukayi wasu maganganu da mutab cikin sirri kafin ya bar wajen.
Tana daga zaune a wani hadadden parlor ta dora kafa daya kan daya tana shan wine aka budo kofar parlor, as usual yaranshi ne ke fara shigowa dika dika dasu sunci baqaqen suit fuska duk maiqo.
Suna hangota duk suka wani sunkuyar dakai alamun girgimamawa, ko kallon inda suke batayi ba saima scrolling wayarta datakeyi.
Shugowar basit yasa ta dago, “princesssss”
Kauda kanta tayi ita wani a lallai fushi take, fuskarta a hade babu fara’a kwata kwata.
Sallamar sauran yaranshi yayi ya kalleta da kyau yace “kina fushi da papi har yanxu?, toh inason ki saki ranki okay”
“Zanyi murmushi ne only if kace min an gano inda yake”
Wani abu ya danna daga gefe aka bude kofar shugowa parlorn ya kalli black sannan ya miqa mashi tab din hannunshi,
Karba tayi tana kallon screen din, khaal ne a kwance aka dauko shi a hoto, wani irin makirin murmushi ta sauke.
Wani irin dadi basit yaji ganin princess dinshi na murmushi, “thanks to wannan yaron we found him, yanxu haka doctor da sukayi hiring yana keeping eyes on him”
“Wow…what would i do without you papii”
Dariya yayi ta manya yace “yanxu duk abunda kikace haka za’ayi”
Miqewa tayi da tab din a hannunta ta tako inda black yake, ya wani tsaya kyaam, edge din tab din ta buga mashi a kanshi saida wajen kanshi ya fidda jini tab din ta fashe “the next time na baka aiki and you messed up i will forget how important you are to, i will crunch you into pieces understood?”
“Yess ma’am” ya amsata a ladabce
Matsawa tayi ta koma kusa da papinta tace “duk wannan matsiyacin ne ya wargaza min plans dina, I don’t even know how he gets into my scret room harya ya dauka hotunan nan, and kai kuma kaida useless yaranka kuka kasa yin abunda ya kamata har wannan stupid driver ya samu damar raina maku hankali,”
Ta karashe tana huci kamar ta shaqe shi,hannunta basit ya kama ganin she’s loosing it kuma zata iya yin komai don ranta a bace yake gashi shi black din suna buqatarshi har zuwa yanxu, “princess calm down, sun rigada sunyi dealing da wannan,”
Ajiyar zuciya ta sauke hartaji daj wani irin sauqi a ranta dataji sunyi maganin driver.
“Any update? Ko har yanxu baku gani dalilin dayasa ta ajeshi a dakin ba?” Basit ya tambayi black.
“Yes sir, har zuwa yanxu yana kulle, she only meets him privately ba tare da kowa ba, we couldn’t get conversation din da sukeyi”
“Why don’t you use your fucking head sometimes? Bunch of useless idiots, ka nemi spy recorder ka saka a dakin”
“Yes ma’am”
Kauda kai tayi tana doka tsaki, gaba daya she’s restless, she wants all her problems gone forever.
Tunda mutallib ya kawo ma khaal bayanin mutuwar driver daya taimakeshi ya kasa cin komai, yayi shuru yana girgiza kai kawai.
Babu abunda yake a zuciyarshi sai innalillahi wa inna ilaiahi rajiun, gashi bp dinshi na neman hawa sosai.
Babu makawa daga bayanan mutallib yanda ya shaida mashi cewa an tsinci gawar mutumin yayi raga raga dalilin accident yasan cewa sune, kuma saboda shi ne sukayi ma mutumin haka daga taimakonshi dayayi, wallahi hankalin khaal ya tashi sosai ba kadan ba da wannan zancen.
Bangaren taj tunda yabar wajensu khaal bai taaya ko’ina ba sai wajen detective dinnan, sun dade sosai suna zantawa, anan ne ma yakejin zancen akwai wani usb daya bama jamid dake kunshe da evidence akan incident din khaal kuma yana tunanin abubuwan dake ciki zasu taimaka sosai wajen fidda khaal, idan da zai samo masu usb din.
Shuru taj yayi don baisan ta inda zai fara ba, hidaya ta fidda shi kasar wajen tunda dadewa ba tare da sanin kowa ba acewarta kenan, saidaga baya ya sani.
Yanxu ya zaiyi ya samu wannan usb din? Ta ina zai fara neman jamid? Don baisan wace kasa ta kaishi ba.
“Barad” yaron ne kadai ya fado ranshi, definitely zaisan inda babanshi yake.
Da haka sukayi sallama lokacin wajen karfe goma na dare.
Baiso komawa gidan ba harga Allah don ko inuwa daya bayason sharing dasu amma dole ya koma kodan ya samu jin inda jamid yake wajen barad, daman school din da yake friday ake dawo dashi gida monday a maidashi kamar boarding haka take.
Parking yayi ya kashe motarshi bayan ya kwashi duk wani abun da zai buqata, ya nufi cikin gidan, bell ya danna shuru ba a budeba, sake danna wa yayi nanma ba a bude ba, a takaice yakai wajen 20mins a tsaye, ya hade hannayenshi a kirjinshi, yana kokarin juyawa aka budo kofar, hidaya ce tsaye cikin kayan barci ta sauko da gashinta kasa tana kallonshi yana kallonta cikin ido.
Kauda idanunshi yayi zai raba gefenta ta damqo hannunshi tace “you have d audacity ka shugo cikin gidan nan? As who?”
“I have no time for this mrs hidaya” ya bata amsa kai tsaye.
“What?? Securityyyy!!! Security!!!!”
Ta doka masu kira da ihu kamar zata tsaga gidan, “how dare you, kai harka isa ka shugo gidnan nan? Zaka iya taka kafarka cikin gidan nan only idan ya kaidin jinin ahalin gidan nan ne, as for now? I will never allow a bastard to…”
Jikinshi ne ya soma suma Idanunshi sunyi jaa tsabar bacin rai yace “enough!!!! Enough! Hidaya, you are trying my patience”
“Wow…ni kake kira sunana kai tsaye? Banga lifinka ba, and yanxu na kara tabbatar da kai din ba dan halal bane, probably tsintarka akayi aka kawoka gidan nan, na raineka a banza”
Yatsanahi babba yayi mata nuni dashi hannunshi na karkarwa ga securities kusan goma sun tunkaro inda suke yace “i am warning you hidaya…don’t make me loose my patience”
“What will you do? Kanada abunda zaka iyayi ne?”
“Yes inadashi, zan tona duk sirrikanki ba komai bane a wajena, kina tunanin bansan you are behind my accident ba? You think i’m dumb? You planned it shiyasa kikayi insisting aranar saina fita? Don ki aywatar da abunda kikeso? I know all of that and i have all the evidence i need, boye wayana da kikayi bazai maki amafnain komai ba don i have all i need, so don’t push me if you do…..ya girgiza kai
Har zuwa lokacin yana kallon cikin idanunta yace i promise you….you will miserable hidaya”
Yana kaiwa nan ya shige ciki.
Yanda kasan ya cire kaf ma’aunin dake rike da gangar jikinta,taj just threatened her, and dayaga yanda yake magana ta tabbatar yanada evidwnce din da yake ikirari, what is she waiting for? Meysa take jinkirin kawar dashi kamar yanda fadwa ta fada, she can’t allow him to step on her, these has to come to an end.
Yana shiga daki ya watsar da komai kan gado, ya soma buttoning gaban rigarshi ya fisgeta kamar wani zautacce haka ya wuce closet room yana shiga ya sauke wata ajiyar zuciya, kamshinta na shiga hancinsa ya jingina da bangon dakin, wani irin nutsuwa yakeji na shigarshi, ya dade tsaye a wajen don nan ne confort zone dinshi, yana imaginging gatanan tazo inda yake ta rungumoshi, perishing him and showing him how much she cares, ya ilahi wallahi he missed yarinyar nan ba kadan ba, she’s his comfort zone, ita din wani bangare ne a jikinshi.
Daman ance Baka sanin darajar abu da amfaninsa saika rasashi gaba daya.
Takowa yayi wajen kayanta ya bude wardrop din yana kallonsu daya bayan daya,komai neat neat, har zai rufe wardrop din idanunshi ya sauka kan laptop dinta da wayarta da khaal ya taba bata, kwata kwata bai taba lura dasu ba sai yanxu, dauka yayi ya fito daga closet din ya wuce daki ya aje kan gado sannan ya wuce bathroom.
Wanka yayi da ruwan zafi sosai kafin ya nado jikinshi da towel.
Sallah ya farayi sannan ya sake komawa closet room dinshi ya saka kayan barci ya fito.
Bakin gadon ya zauna tare da jawo wayar nata da laptop din ya kunna su.
Wayar ya fara latsawa tana kawowa, yayi tsammanin zaiga pins saiyaga akasin haka, wannan ya bashi damar budewa kai tsaye ya dan dakata, to me zai duba ma acikin wayar nata?
Ya tambayi kanshi, chan kuma ya shiga messages dinta, babu komai a wajen sai irin sms dinnan da ake turowa daily, futa yayi ya shiga contacts, nanma daga number da akayi saving da khaal sai number jamid sai wata number,
Samun kanshi yayi da daukar wayarshi yayi dialing number a wayanshi don yasan kona wanenw number, aiko yana dialing yaga saunan mutallib ya baiyyana har call din ya shiga.
Shuru ya danyi chan kuma ya katse wayar ya shiga ya maida hankalinshi ga nata ya shiga gallery, da kyakyawar fuskarta yaci karo yayi hanzarin shiga folder din yaga hotuna biyar ne kawai a ciki.
Baima tsaya ya kalla sauran ba wanda tayi dinnan ita kadai ya fara maida hankali ga wajen, tayi masifar kyau sosai ta sanya abaya baqa tayi rolling kanta.
Ranar ta dauka ne lokacin da zasu fita da ammu tayi kyau sosai kamar ba itaba she’s photogenic.
Ya dade yana mata kallon kurillah sosai,don yakai wajen minti goma a haka kafin ya kifta idanunshi.
Baika lura da hannunshi dake zooming fuskanta ba yana shafawa.
Tana da kananun round hazel eyes, kwayar idanunta kamar irin greenish brown dinnan ne da ba kowa keda irinshi ba kuma sai an kureta da kallo ake gani, tanada cikar gira masha allah har tana neman hadewa, ga gashin sumanta daya taho gar fuskata a kwance da gashi.
Ga hanci masha allah kamar an tsaga kara, ga ido ga dan bakinta komai nata kifkif Masha allah.
“Masha….Allah!!!!” Ya furta harzardly beneath his breath ya sauke ajiyar zuciya.
Wuce picture din yayi ya shiga wani takw gabanshi ya fadi sosai, gashi bai iya tuna sanda akayi hoton ba, donshi ya daukesu, ya kamata irin sosai fuskansu na kallon juna ya daukesu hoton a lokacin baima sani ba.
Next one daya shiga shi ta dauka yana daga zaune yana yin puzzle game dinshi, next one ma shine yana dariya, the other onw kuma its like a video, yayi saurin playing video din.
“Bibi zanyi wiwi”
Da suari ta karaso batama san wayar na hanunshi ba shi kuma baisan yana video ba ta ja hannunshi suka shiga bathroom
“Bibi, wiwi zai futo, help me”
“Haba didi, kullum saina cire maka buttons? Ka dunga yi da kanka please”
Bubuga kafafunshi yayi kamar zai mata kuka tayi saurin duqawa gabanshi ta soma jan button din wandonshi,
Daidai wajen nan saida ya runtse idanunshi yanajin wani yanayi na shiganshi sosai, muryarta daya ji yasa ya bude ido, “toh ka tsaya na fita saika cire sauran kayi”
Bai saurareta ba yasa hannu daya yana kokarin zake boxers din ta arce a guje shi kuma ya aje wayar a gefe.
Daidai wajen yanda tayi gudun nan saida yasa taj dariya, kai masha allah zan iya cewa this is the first time na ganshi yaui dariya bayan ya samu sauqi, ashe idan yayi dariya wani irin kyau yake sosai ba kadan ba ya ilahi…”
Harda wani dan cute dimple guda daya yake dashi, bawan allah ba is gone, baisan yana murmushi ba, yayi replaying video din yafi sau goma a lokaci guda, har wayar ta dauko saboda ba charge ya ajeta gefe.
Laptop din ya bude hoping zaiga wani abun a ciki nan ma, allah yaso itama ba password, yana budewa babu abunda yaci karo dashi sai files dinta na karatu da sauran abubuwan online school essentials.
Budesu yayi kamar mara aikin yi daya bayan daya, ya duduba yana ganin abubuwan ta da progress dinta, he can say she’s so smart gaskia.
Wani file yaci karo dashi da akayi saving da TJ, shi kadaine bai shiga ba wannan yasa ba tare da tunanin komai ba ya shiga kawai, yana shiga laptop din ta buqaci face id don file din ya bude ga mamakinshi kawai yaga face dinshi ya dauka file din ya bude.
He was so surprised and shocked of how is that possible,
Kallon files uku dake ciki daya img ne sauran kuma