Author : Queenmerh Category : Complete Novels
kasa plate din ya fashe.
Dukawa tayi ta soma kwashe plate din rabi ta karaso inda take kasa kasa da murya tace
“Garin yaya kika fasa? Kina menene?”
Amsanta sabeeha tayi itama yanda daga ita sai rabi ne zasuji tace.
“Wallahi anty rabi Itace ta fasa,”
“Barshi kije ki dauko tsintsiya karkiji ciwo a hannu”
Da toh ta amsata tare da nufar hanyar kitchen daidia nan ya karaso wajen dining din don tabbatar da muryar da yaji mai kama data sabeeha dayaji a kunneshi.
Saidai kashh yana isowa wajen ta shige kitchen sai dan glance din bacewarta a wajen daya gani.
Kallon rabi yayi dake tsaye sai maya tafayi saurin mikewa ganinshi ta sauke wani irij murmushi,
“Ina wuni yallabai” baijin hausa amma yanda rabi tayi magana ya gane gaishesa tayi, da mamakin kansa baima san ya iya kalmar ba yace “lafiya” ashe dai ya fara dan koya Kadan kadan.
Maya ta taho inda yake cikin kaudi kamar ba itace ta gama cin mutuncin sabeeha ba ta zauna tana harare harare itama rabi bata tsira ba don rashin kunya take mata
“Hey uncle taj….do you need anything?”
“No thanks” ya bata amsa ba tare da ya sake kallonta ba ya dauke kanshi ya juya, daidai nan sabeeha ta karaso”
Rabi ta girgiza kai tace “wannan yarinya akwai munafuka, ji yanda takeyi kamar ba yanxu ta gama sababi ba”
sabeeha data jita ta dago ta kalli inda rabin ke kallo, bayanshi kawai ta kurama idanu har suka bace kata daga gani, “ya kika tsaya? Tattare wajen” rabi ta mata magana.
Sama ya wuce maya ta bishi a baya tana karemashi kallo ta bayan, few steps ne tsakaninsu don yanajin takunta amma hankalinshi baya jikinsa yana ga muryar dayaji datake kama data sabeeha, toh kodai yawan tunaninta ne yasashi yakejin muryarta yanxu kuma?and he feels her presence a ko’in.
Daidai wajen shiga part din nanna ta dakata harya shige daga ciki kafin Ta koma daki tana murmushi.
Washe gari…
Tun wajejen karfe sha daya jamila ta kira hadiza ta tura mata adireshin gidan, sannan ta shaida mata tana nan tafe.
Hadiza fa bata kwana kalau ba don zuwan jamila da kiran da jamila ta mata dagaji ba na alkahiri bane.
Hadiza ta futo daga dakinsu ta rabi dake kitchen, “rabi dan Allah kiyi ma security magana yar uwata zata zo”
“Hajiya tasan da zuwan bakuwar taki?” Rabi ta tanbayeta
Rai a bace hadiza tace “yar uwatace zatazo kuma hajiya ta santa”
“Toh naji” rabi ta fada tare da cigaba da abunda take.
Hadiza kamar ta shaqeta dan baqin ciki.
Daga chan wajen security aka kira cikin gida, daman rabi ce sukeda access da ita suka tambayeta akwai mai expecting bakuwa tace eh, suka tambayi suna tace masu su barta ta shugo.
Jamila fa tundaga bakin gate idanu suka raina fata ta dunga wiki wiki dasu tana rarrabawa, aranta babu abunda take fadi sai lallai hadiza ta debo ruwa, kut…aljannar dubiya saimai rabo”
Futowar hadiza ta backyard ta hangota daga nesa cikin sauri ta karaso insa take, “jamilaaa…”
“Naam hadiza, anan kuke? , bura..ubanchan kaiii, lallai hadiza kinyi wuta, kunama mai zafin dafi”
“Muje daga ciki” hadiza ta fada tare da jan hannunta sukabi ta backyard.
Ta kitchen din suka wuce jamila suka gaisa da rabi kafin hadiza takaita dakinsu.
Suna shiga daga ciki hadiza ta karo kofa harda saka key jamila har an hau gadon zamani an zauna ga ac na buga dakin.
“Bamu gaisa ba ko? Hankalina yayi gaba naga duniyar arziki”
“Jamila ina magnar gaisuwa kin sani cikin tashin hankali? Ey?”
“Ay kya bari nasha ruwa ko? Ina yar taki?”
“Wacce daga ciki?” Hadiza tayi tambaya, jamila ta kyalkyale da dariya.
“Jamila yanxu ba lokacin dariya bane, ki fada kin meke tafe dake? Wace matsala ce ke tunkaro mu”
Gyara zama jamila tayi ta yaye mayafin dake kanta tace “wannan yarinyar nemanta ake,”
“Wa kenan?”
“Kinsan wa nake nufi, jiya jamilu yazo gida ya shaidamin wai wasu mutane masu kudi sunzo har agency dinnan nemanta, kuma da alamu yanda suke kakkashe kudi don ganin sun ganota babu tantama kisan kai tayi ko kuma sata tayi ake nemanta”
Dafe kirji hadiza tayi tace “na shiga uku ni hadiza? Kisan kai?”
“Kwarai kuwa, kuma kinsan cewa jamilu shine ya kaita wajennan a matsayin marikinta, duk wani abu datayi shi za a fara kamawa saboda haka wallahi tallahi kisan nayi,“
“Na shiga uku ni hadiza, kin tabbar kisan kai yace maki tayi?”
“Ah ah fa, hasashen mu ne inba haka ba meysa masu kudi haka zasu dunga nemanta eyy?”
“Jamila wallahi wallahi bazan dauki asara ba, tun ban cimma buri na ba a duniyar nan”
“Toh ya zakiyi? Daman dalilin zuwana kenan,dan wallahi igiyar aurena na hannunki, jamilu yace zai iya sauwwake min wallahi, ki kwasheta ku koma lafiya kawai inyaso saiki dawo”
“Jamila bazan iyaba,nayi kokarin yin haka tun ba yanxu ba”
“Toh kina nufin idan akazo a kama mu kenan?”
“Ah ah jamila zanyi tunani akai”
“Gwara dai kiyi tun wuri, ki debo mi dan abun kamusawa mana naci arziki kafin muyi arzikin?”
….
Sama rabi ta hau sai gata da anne sun sauko har kasa, zuwa sitting room.
Wani mutumi ne a zaune don ya dan manyanta, an aje mashi bottle water da snacks a gefe yana daga zaune a kasa.
Daga ganinshi zakasan anji jiki don yana sanye da wata riga yar shara da wando blue fatau an kure adaka, sai wage baki yake da yayi jaja saboda cin goro.
Gefenshi bilki ce zaune tana sanye da hijabi sai kayanta dake cikin jaka mai kyau, ka ganta fess fess tayi bulbul abunta.
Anne na karasowa ya sake gyara zaman babbar rigarshi dake kan yar sharar, “sannu hajiya sannu hajiya”
“Sannu dai” anne tayi magana kafij ta zauna
“Ina wuni hajiya? Mun sameku lafiya?”
“Lafiya lau alhamdulillahi ya mutan gida?“
“Lafiya kalau kalau kalau hajiya”
Kana ganinshi zakace wani burkitaccen mutun ne amma da hankalinsa tsabar duniya ta bugi idanunsa ce.
“Kaine kawun nata?”
“Ee nine hajiya”
“Toh Masha Allah”
Matsowa rabi tayi da kudade aqalla zasukai wajen 500k ta aje gabanshi anne tace “ga wannan ayi mata duk wani hidiman biki, idan akwai abunda yayi saura ma saita bilkin ta kira”
Kamar zai taugunna mata haka yake ji, sai faman gadiya yake kmar bai taba rike kudi kamar irin wannan ba.
“An gode hajiya an gode sosai, bilki marainiya bazatayi kukan maraici ba kun mata komai hajiya an gode an gode”
“Ba komai Toh bilki saduwar alkhairi allah ya bada zaman lafiya ya sanya alkahiri”
“Ameen duk suka amsa a tare bilki harda kukanta suka futo daga gidan bayan tayi sallama da kowa, basira harda hawaye, rabi ma saida taji wani iri haka sukayi sallama suka futa.
Suna fita ya chusa kudin cikn babbar riga ya zaro goro ya fara tauna.
“Wallahi idan baki kirani ba zaki ga daaowata hadiza na fada maki,”
“Kai jamila kamar babu yarda tsakanin mu?”
“Ke hadiza ba abar yarda bace ni kadai nasan koke wacece.
Dahiru har zai wuce ya dakata ya kare masu kallo musamman jamila.
“Jamilan zango???”
Jamila najin sunanta da ake kiranta dashi lokacin da suna en mata ana shan duniya ta juyo da mamaki,”
Tana ganin dahiru gabanta ya bada dan daran dammm, dariya ya kyakyace dashi irin ta manya yace “jamilan zangoo, ashe rai kanga rai? Ah madallah”
“Kin sanshi ne?” Hadiza tayi magana tana kallonta ganin gaba daya bata cikin hayyacinta hankalinta ya tashi.
“Koba jamila bace wannan?”
Ya sake tambaya ganin tana kakkauda kai, “ay ko barci nake na tashi dole in ganeki jamila ta”
Jin haka yasa jamila cije lebe ta juyo ta kalleshi tana yaqe tace “dahiru kenan, kana nan dai yanda kake an buga duniya an barta”
“Kwarai kuwa, yaushe gamo? Rabona dake shekara wajen ashirin da yan kai, har kinyi aure ko ay hikenan kin barni”
“Kaifa ka fiye hauka, an girma ba a san an girma ba mteww”
Kallon hadiza yayi har yana motse idanu kafin yace “wannan ba kawarki bace? Har yanxu kuna tare? Lallai amincinku mai karfi ne ba itace Wacce kika…”
“Dahiru.. me kazo yi nan ne?”
Tayi saurin dakatar dashi hankali tashe, “yar dan uwana ce take aiki anan zan aurar da ita kinga mun kwana biyu ko?” Ya fada yana yage baki.
“Kwarai na gani kuwa”
“Ke yama sunan masu gidan?” Ya tambayi bilki tace “gidan alhaji santuraki”
“Ku meya kawoku nan anguwar?”
“Bani lambarka zan kiraka anjima” jamila tayi cutting conversation din, ya zari wata yar nokia ya bata number.
Zasu wuce bilki tace “sai anjima hadiza na tafi”
“Toh bilki” ta amsa ta.
Suna barin wajen hadiza ta dubi jamila tace
“? Ina kika san wannan jemamman kamar wani dan wiwi”
“hadiza mun shiga uku dahiru ne,”
“Wani dahirin?”
“Ke amma jakace, shekaru ashirin da uku da suka wuce….”
Ay bata karasa ba hadiza ta kama haba tace “ke da shi?….”
“Shine, hadiza dahiru bashida kai wallahi, inata yi maki signal mubar wajen kika kasa ganewa, dan wiwi ne wallahi bashida kan gado, tunda har ya ganmu akwai matsala”
Haka suka tsaya kana ganinsu zakasan basuda gaskia kwata kwata.
Dahirun da bilki na barin wajen ya dubeta yace “ina kikasan wadda naji kik kurata da hadiza”
“A gidan da nake ayki suke ita da yarta”
“Yarta?”
“Eh kawu”
“Tun yaushe suke gidan?”
“Zasu kai wata shida a gidan” ta bashi amsa
“Ta manyanta da batada aure dana jarraba sa’a ta”
Dariya bilki tayi sanin yanda kawun nata yanda yake da son mata ga auri saki inya auri hadiza ay bala’i zasuyi, matar nan datake jin kanta kamar masu gidan harma ta fisi kafafa.
“Ay kuwa dai kawu, gashi batada miji don kamar ya mutu,”
“Toh ko yar zan nema ne? Tunda da kwari na zatayi kamarki?”
“Kawu na girmeta bazata wuce irin shekaru ashirin da uku ba haka”
Kyakyacewa yayi da dariya, sosai ba kadan ba “madallah..” ya fada yana tabo kudaden da anne ta basu daga aljihunsa.
Suna tafiya anne ta dubi rabi tace, “toh yanxu gashi yan matan wuya samu suke,“
“Va danuwa hajiya, tunda ga sabeeha ga basira sai a raba masu aikin kafin sabeehar ta koma makaranta nasan za a samu wata”
“Toh hakan yayi, naga fatimar nada tsafta ta dunga zuwa bangaren deeni tana gyarawa safe da yamma, duk abunda ya danganci bangarensa”
“Toh hajiya” rabi ta amsa ta.
Rabi na rabuwa da anne ta kira basira da sabeeha ta shaida masu kowa da aikinta, basira kamar ta kwada ihu, tanata murnar aikin bilki zai dawo hannunta, gyaran part din nanna da bangaren taj.
“Daga yau ke fatima zaki fara, bilki tayi na safe yamma nayi zakije ki gyara bangaren, shara mopping gyaran bandaki gyaran gado, komai, idan da lundry ma zaki dunga yi da goge.”
“Toh anty rabi”
“Dan allah banda kazanta, baya son kazanta ko kadan, yanayin rayuwarshi da tamu ba daya bace, kazanta kadan saita sashi amai abunka da ba dan nigeria ba”
Jinjina kai kawai sabeeha tayi, kwata kwata bata taba bada attention dinta gareshi ba sai yanxu, tadaiji ance dan anne kuma ba a kasar ya taso ba, amma bata taba sama ranta gani ko sanin wayeshi ba.
Jamila na tafiya hadiza ta koma gida gaba daya kamar ta burkice sabeeha na shigowa dakinsu ta taddata zaune
“Ke zo nan”
Karasowa sabeeha tayi cikin ladabi ta zauna kasa, “da kikace chan saudiyyar meya dawo dake? Meysa aka koroki? Karki sake kimin karya? Kisan kai kikayi ko sata? Wanne daga ciki”
Idanun sabeeha ya ciciko da hawaye ta kalli maman nata tace “mama wallahi…”
“Karki fara min rantse rantse munafuka, kisa kikayi ko sata wanne daga ciki? Don shi kadai zaisa azo ana nemanki”
Mamaki gaba daya da confusion ya cika sabeeha, hadiza ta zaro wuya tace “ko ki fada min kona kasheki anan na huta,iskanci kikaje kikayi ko wani kika kashe?”
“Mama wallahi banyi ko daya ba,”
“Meysa ake neman ki???? Ehhh????”
“Bansan wake nemana ba mama, wallahi ban sani ba”
“Wace iriyar rayuwa kikayi achan???”
Damm gabanta ya bada ta rasa ya zatayi, wace amsa zata bama mamanta? Ko karan hauka ke cinta bazata taba cewa aure tayi ba.
hadiza duk yanda taso ta tsorata da wuqa bata samu komai ba kwakwara dazai nuna cewa kisa tayi.
Wunin ranar cikin zulumi da kunci sabeeha tayi shi, tasha kukanta ta gaji ta hakura sannan ta fara tunanin maganganun mamanta, wake nemanta? Wazai nemeta? Babu mai bata amsa.
Yamma nayi wajen 4 ta shuga part din da zata dunga gyarawa, da sallama ta bude kofar kamshin diffusers ya bade ko’ina, bin ko’ina tayi da kallo wajen ya burgeta sosai ba kadan ba, har wani natsuwa takeji, haka ta fara gyaran parlor da babu datti kwata kwata ta share dakin shima ta sauya bedings ta wanke bathroom kal kal kamar ba a taba shiga ba sannan ta futo ta rufo kofar.
Tana futawa ta samu dakali daga chan wajen compound din ta bama wajen baya tana tunani da nazari.
Tunda ta zauna babu tunanin wanda yake circulating a ranta saina taj,duk iya kokari da take na ganin ta yakice shi ta kasa data fara ma take hana kanta ta hanyar tunawa da abunda ya mata yau ko ta kasa hana kanta.
Misalin wajen karfe shida da rabi ya shugo compund din wajen parking spot yayi parking motarshi kafin ya nufi hanyar part dinshi, kamar ance ya juyo ya kalli wajen da take zaune kuwa ya juyo ya ganta tana kokarin miqewa, take gabanshi ya soma bugawa fat fat fat, ya kasa daga idanunshi allah allah yake kawai ta juyo yaga ko wacece a wajen da zuciyarshi ta dakatar dashi babu dalili, tana miqewa kamar zata juyo kuma saita tsaya tare da daukan slippers dinta daya tainke ta dauka adaidai lokacin ya dawo hayyacinshi ya wuce cikin part dinshi ita kuma ta juyo.
Sallah ta shiga tayi taci abunci sannan suka fara prepping shirin aje dinner.
Yana shiga part dinshi yabi ko’ina da kallo, duk guaran da ake mashi sai yaga na yau is times 10 of it, sai yaji dadi aranshi soaai, komai anyi organinzing to his taste.
A tare sukayi aikin kitchen ana gama cin abunci suka tattara, harda sabeehar suka wanke ita da basira rabi kuma ta wuce don hidimar anne.
Wayar landline dake kitchen aka kira basira ta dauka kafin tace “gata”
“Tohm hajiya”
Kallon sabeeha tayi tace “hajiya nanna na kiranki, tace a yanka fruit”
Murmushi sabeeha tayi tace toh, ta fidda komai ta yayyanka yanda ya kamata ta zuba zuma a bowl ta jera kan tray sannan ta wuce sama.
Babu hijab a jikinta tana sanye da doguwar riga kuma ta mata kyau sosai daidai jikinta, ta dan rame saboda damuwa saidai kuma dirin na nan yanda yake gata yar gajeruwa.
Da sallama ta bude kofar part din bayan an bata izini ta shiga, nanna na zaune sitting room ta dubeta tace “sannu yar albarka,”
“Nanna ina wuni?”
“Lafiya lau my dear, how are you? Ya exams dinku an gama ko? Ina fata anyi abun arziki”
Dariya tayi tace “eh nanna”
“Aje fruit din akan dining, tajudeen zaizo yasha yanxu”
Dammmm gabanta ya bada badan ta rike tray din da kyau ba zai iya subuce mata.
“Tajudeennnn” kai ina zata iya mantawa da wannan suna a rayuwar nan.
Aje wa tayi tace “akwai wani abun da ake buqata?” Babu yarinyar kirki, nagode, rabi tace kin karbi aikin bilki ko? Gyaran part din tajudeen ya dawo hannunki”
“Eh, dazu ma naje part din na gyara”
“Toh Masha allah,”
“Saida safe nanna”
“Toh allah ya kaimu”
Sabeeha ta futa, koda ta futo ta wuce sama.
Washe gari wajen karfe goma ta shiga part din nashi, already harya futa wannan ya bata damar kimtsa ko’ina, yanda ya kamata, kayan data gani a closet a ajiye a kasa kamar cikin gaggawa aka ciresu ba a tattare ba ta kwaso ta sakasu laudry, ta taaftace wajen sannan ta nufi hanyar futa, har zata futa ta dakata idanunta ya sauka kan wani wrist watch, komawa tayi tana kallon watch din da mamaki, runtse idanunta tayi tana tunanin maisa komai yake reminding dinta da taj, kauda tunanin tayi ta duta daga part din.
Bangaren taj ya da sassafe ya futa ya koma agency,tun ana neman jamilu har aka kasa daina nemansa, salim ya gane wala wala suke masu, wata dabara tazo kashi cikin yaran wajen ya samu daya ya shaqe shi da kudi sosai ya fada mashi inda jamilu yake ayko bai tsaya wasa ba ya nemo mashi address dun jamilu.
A ranar suka dauki hanyar wajen gari habuja sai dutsen habuja, suna zuwa basusha wahala ba sukayi lokacin gidan jamilu, taj yayi mamaki sosai ganin anguwar, zuciyarshi kawia saita fara breaking sosai.
Akayi sallama da jamilu, jamila ta fito don jin ko waye, tana ganin jibgegeiyar kota gabanta ya soma faduwa, salim ya futo taj ma haka, ay sumewa ne kawai jamila batayi ba gar zata kulle gidanta salil ya mata sallama yace “dan allah hajiya ki dan saurare mu, muna neman jamilu ne”
“Mei sa kuke neman mijina me zai maku? Kamashi zakuyi?”
“Ah ah hajiya, babu ko daya cikin abunda kika fada, bai mana komai ba, wannan ogana ne, muna neman wata yarinya mai suna sabeeha, kuma an Shaida mana shine marikinta.
“Babu wata sabeeha a gidan nan, bamu santa ba, wata qila kunyi mistake ne, nice matar jamilu kuma bamuda ya mace yayanmu duk maza ne, dan allah ku daina neman mijina,”
“Amma Hajiya dakin saurare mi”
“Dallah nace maka babu wata sabeeha gidan nan” tana fadin haka ta banko kofar gidan gabanta na faduwa, jamilu dake zaune a daki yana ganin ta yace sune ko? Kamani zasuyi? Ke jamila wallahi tallahi taki ta kare na rantse da Allah”
*…
Tana rufe kofar salim ya fada ma taj komai, da yanda tayi dening, gaba daya everything doesn’t seems right, shi kanshi salim din ya gane basuda gaskia kwata kwata daga jamilun har wannan dake ikirarin matarsa ce.
Taj fa bai hakura ba yasa salim ya tambayi mutanen dake wucewa, wajen mutane hudu suka tambaya kowa sai yace bai santa ba.
Wani dan yaro daya taso daga islamiyya yana wasanshi dayaga an zagaye wayar da salim ke nunawa shima ya karasa wajen don ganin me ake gani, yana ganin sabeeha yace “kai wannan na santa”
Salim yayi saurin cewa “ina ka santa?”
“Ga gidan su chan kasan gangare, kudi salim ya bashi gar 5k yace zoka rakamu, aiko ya rakasu a kafa, gaba daya anguwar so disgusting, ko ina duk wari, taj dai bai taba zuwa iri waje haka ba baima san it exist ba sai yau, daudai gidan hayansu sabeeha ya tsaya yace “nan ne”
Tuni landlord dake ciki ya futo tare da yaron, irin igbo man dinnan ne sai bala’i yake yazo karban kudin wata yana ganin balarabe kawai ya soma washe baki.
“Oga please do you know this girl? We heard that she live here?”
“Ah yessoo, this girl and her mother, they never pay my rent they ran away, useless and wicked people”
“Mind your words please” taj ya fada