Advertisements
Chapter 79 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   79 / 107

234K to 237K   out of 320.4K words

a yau nafi kowa farin ciki, kullum fatana allah yasa kina cikin koshin lafiya, ina mai baki hkurin komai fatima,kinsha wahala sosai kuma duk nine sanadi,tunda ni na kawo ki ta hanyar leken asiri,on behalf of duk abubuwan da suka faru dake kiyi hkuri ki yafe min.
Tana kuka tace “dama chan allah ya rubuta duk abunda zai faru, kuma haka ya kaddara,”
Sun dade suna waya kafin suyi sallama ta kashe wayar,Ba karamin dadi taji ba da khaal ke raye, kamar yanda yace daman duk abunda ya faru akwai karshensa”
Har zata aje wayar ta dakata da mamaki tana kallon screen din wayar nashi, wani tsohon hotantane data tabayi a saudi cikin wayar da khaal ya saya mata, tayi smiling braces dinta sun fito, ba karamin kyau tayi ba, fararen idanunta suka fito darr gashi tayi wani smiling mai kayatarwa, iya fuskanta ne kawai akan screen din,
Mamaki ta dunga yi yanda akayi ya samu hoton, meysa yasa shi kan screen wallpaper dinshi, bashida reasons nayi hakan, Dagowa tayi idanunta ya sauka ga bathroom din, take ta zaro ido ganinshi tsaye yana wankansa hankali kwance ruwan nan na sauka kan a gashinsa masu silki, sai faman shafa gashin yake, gashi ya juya mata baya don bata hango fuskanshi sai huge attractive bayanshi kwata kwata baisan ana kallonshi ba.
“Wannan wani irin bandaki ne haka…”
Ta furta ahankali tana kallon glass din, thankfully ba’a hango wasu guraren daya shafi jikin dan adam, amma indai itace ta shiga bathroom din dole za a ga jikinta, don kasan ne kawai a rufe banda saman.

Kasa dauke idanunta tayi daga gareshi ta kare mashi kallo sosai, shidai ya gama haduwa, namiji ne cikakke kuma ingarma don allah ya bashi komai da kowacce ya mace zata mace akanshi, probably shiyasa maya ke hauka akanshi, ga kyau ga aji, ga arziki ga class, kai komai ya hada shi kadai, such a charismatic man.
Ta shagala sosai tana kallonsa unexpectedly ya juyo charaf ya kamata, gaba daya hankalinta yayi nisa da wani tunani daban, ko me take qissawa aranta allah kadai ne ya sani, don kwata kwata batasan ya ganta ba.
Murmushi yayi kasa kasa ya basar kamar bai ganta ba shima ya juyo yana fuskantarta, har wani irin shafa kirjinshi yakeyi ruwan na sauka a jikinshi, hakan nan dayayi saida yasa ta hadiye wani irin saliva daya zo mata harda kifta idanu, hannayeshin ya aza ga wuyanshi tana hango yanda ruwan ke sauka kan damtsensa, ay batasan haka yake jibegege ba sai yanxu, kwanciyar hankali tasa ya kara wani irin habaka yayi kyau sosai.
Saida ya barta tayi kallonta ma’ishi kafin ya danna wannan button din, take glass din ya soma dishashe ya koma fari tarr kamar an cire tint din wajen, kuma a daudai lokacin ta gane ya kamata tana kallonshi, hankali tashe cikin sauri ta kauda kanta tana wani rarraba idanu, koda wasa bata bari ta sake juyowa ba harya futo daga bathroom din.
Kugunshi nade da towel sai kuma left hand dinshi rike da hand towel da yake share kanshi dashi.
Kallonta ya farayi yana dan murmushi kasa kasa itako sai faman kakkauda kai take kamar rakuma.
Shi ko ko a jikinsa namiji dai baisan wani abu waishi kunya ba kwata kwata ya samu waje gefwn gadon inda take zaune yayi zamansa.
Hannunshi yakai gabanta yace “my phone”
Ba tare data waiwayesa ba ta juyo da hannunta tana kokarin mika masa ya hado da hannayen nata gaba daya da wayar ya matsota jikin sa.
“Are done looking?”
Kame kame ta soma yi tana wani harhade rai tace “ga wayar nan”
Muryanshi kamar mai rada rada yace “I’m not talking’ of the phone, ina magana ne akan kallona da kikeyi? Are you done or should i go back? Naughty girl”
Zumburo dan cute bakinta tayi tace “da wani idon kasan ina kallonka? Please idan ka gama maganar dakace zakayi ka maidani school i have things that are important for me to do”

“This is more important than whatever you’re going to do at school,”
Yana fadin haka yayi kwanciyarsa tare da rufe idanunshi, da mamaki take kallonsa, wai me yake nufi ne? Ta tambayi kanta, saurin miqewa tayi daga gadon ta matsa gefe.
“Dan allah ka maidani school i have things to do,”
Idanunshi na rufe ya sanya hannunshi ga bakinsa yace “shiiiiiii…”
Kaga wani karfin hali, ta fada aranta, da tanada yanda zatayi wallahi guduwa zatayi, ta kai waien rabin awa a tsaye kamar soja bata motsa ba, ta cika tayi famm gashi tanajin wani irin futsari da tun da suka shugo ta soma jinshi.
Kallonshi tayi ganin barcin sa yake hankali kwance, kamar ta dora hannu aka som takaici, gashi ko da wasa bata tunanin yin gigin shiga wannan bandakin da sunan yin futsari, koda wasa.
Dataga go no go kawai ta samu waje bakin kujera ta zauna ta doka uban tagumi abun tausayi.
Barcinsa yake cikin kwnaciyar hankali, peaceful kamar wani jariri.
Ya dauka wajen 2hrs kafin ya bude idanunshi, wasu yan addu’oi yayi kafin ya tashi zaune, lokacin wajen karfe biyu.
Tashi zaune yayi ya ganta zaune jikin kujera tana bar inta hankali kwance, daga gani ka a takure tayi shi.
Mikewa yayi ya wuce bathroom ya danyi abunda zaiyi kafin ya futo, a gaggauce ya saka kayanshi sannan ya tunkari inda take, so yake ya tasheta amma ganin barcin ya mata dadi yasa ya kyaleta, ya nufi wajen da akayi providing for sallah.
Hawa kan sallayan yayi ya tada kabbara daidai nan ta Tashi firgigi, mararta ta cika pamm da futsari, batasan sanda tace “innalillahi wayyo allah na”
Ta wani irin miqe zubbur, sallama yayi ya juyo ya kalleta ganin yanda ta kama doguwar rigarta, ga zufa dake keto mata dukda ac dakin, wani irin mafarki tayi mai tada hankali, akanshi da ita, yana mata wasu abubuwa daya kulle mata kai har tana neman yin futsari, ashe dai futsarin a zahiri take jinshi kiris ya rage bata sakeshi ba a mafarkin don dadi.😂yarinya da kinyi abun kunya.
Karasowa yayi inda take yace “are you okay? What wrong?”
Girgiza mashi kai tayi ta kasa cewa komai sai kama gaban rigarta take, “hey!!!what wrong ya fada yana kai hannunsa ga inda inda nata hannun yake tayi wani baya, kadan ya rage bata saki futsarin ba, tace “i’m pressed”
Hannayenshi ya nade ga kirjinshi, idan futsari takeji batasan ind abathroom yake bane ta tsaya.
Nuni ya mata ga bathroom, cikin sauri tace “gaskia bazan shiga nan ba”
“Why????” Ya jefo mata tambaya ta kalli bandaki ta kalleshi, arabta tace “haka kawai na dage rigata na hau kan wc kana hangoni a wannan bandaki? Inaa bazai yuwu ba”
Girgiza kanta ta soma yi, “ana hango mutun daga waje fa”
“And so what?” Ya jefo mata tambaya.
“Gaskia bazan shiga ba..”
Hade rai yayi soaai yace “you’re not really pressed, idan har ya matseki sosai bazaki tsaya ba”
Zai juya kenan ta kamo hannun rigarsa tace “dan allah ka rufe min toilet din gaba daya saina shiga”
Kallonta yayi yana nazari, wato bazata iya shiga ba ya ganta kenan?.
“Okay!!” Yace tare da nufar toilet din tabi bayanshi.
Suna shiga ya danna wani abu take glass din ya koma baki,”there you go, “
Juyawa yayi zai futa ya dan dakata tare da cewa “ki gyara jikinki”
Yana fadin haka ya futa.
Yana futa ta leka don tabbatar da ko’ina a rufe yake kafin ta soma kokarin dage rigar jikinta, kafafunta har rawa sukeyi tsabar a matse take.
Saida ta rage mararta taji wani irin dadi kamar an cire mata komai, waige waige ta somayi na neman abunda zatayi tsarki dashi babu, kwata kwata batasan automatic smart wc ne ba wanda yake fidda ruwa daga jiki ya maka tsarki, gashi batasan ta yanda zatayi flusging ba don madannan sunada yawa sosai, “toh kodai ta futa ta kirashi? Ta tambayi kanta, wannan abun kunya haka ta wuce gaban faucet din shower ta kunna ruwa ya zubo ta tsugunna tayi tsarki, tana gamawa mistakenly ta dago garin danne dannen ta ta danno wajen shower ruwan ya zubi mata, cikin sauri tayi baya allah yaso bai jiqata sosai ba.
Sauke ajiyar zuciya tayi tana kallon bandakin yanda ya hadu ba karya, inda ya danna ya zuge glasa dinnan ta duba aranta tace “ko waye yayi inventing wannan bandakin oho? Kana wanka na waje na hangoka ay iskanci ne wannan”
Juyawa tayi ta futa daga bandakin, hangoshi tayi yana sujjada, ta dan tsaya harya sallame.
Daidai lokacin akayi knocking, miqewa yayi yaje bakin kofar ya danna wani abu kofar ta bude wata mata ta shugo da hanger jibge da kaya a jiki kala kala, rarraba idanu sabeeha ta somayi har matar ta shugo ta gaisheta sannan tace “this is all of our boutique collections sir”
Kallon hanger din yayi yace “thanks”
Matar ta futa ya juyo ya kalli sabeeha yace “ki shiga kiyi wanka kizo kiyi sallah”
Wanka? Ni zanje nayi wanka?” Ta fada aranta, “lallai ma, saboda me zatayi wanka don zatayi sallah?” Ta sake fada aranta

“Basai nayi wanka ba, bana buqatar yin haka” ta fada tana kauda kanta

“Yes you have too, ga kaya nan, saiki dauka wanda kikeso ki sauya”
“Bana buqata, na jikina ma ya isheni”…
Ya lura batasan cewa ta soma bata jikinta ba kuma bazai yuwu tayi sallah a haka ba.
Take ya sauya kamar bashi ba yace “don’t make me repeat my self, go…in there…and take a bath…indai baso kike ki kwana anan ba, this is a command”
Lallai ma, meysa yake wasu abubuwa kamar ya ajiyeta? Ta tambayi zuciyarta, ay ya ajiye kin ne tunda da alamu ya karbi aurenki dashi, wata zuciyar ta bata amsa
badai yana tunanin zai karbi auren dayake maganar akwai shi ba? Ay maganar aure ita dashi babu, dama chan yafi karfinta, bazama ta taba hada kanta dashi ba, menene amfanin auren? Daman dalilin tun a saudi ne abubuwan da suka faru a baya, yanxu ko daya gano komai ya dawo hayyacinsa ay babu wannan maganar.

Kallonshi tayi bayan ta gama wannan tunane tunanen nata, da maganar da sukayi da khaal kafin tace “i am here only because kace min zamuyi wata magana, kuma mun gama yinta, maganar aurenmu dakake cewa baka sakeni ba babu shi, tunda tun farko daman kasan dalilin auren badan komai baneba saboda halin da kake ciki, kuma i stand by you, i protected you daga yan uwanka kafin ka koreni, koda ka dawo hayyacinka dama chan baka karbi wannan auren ba, yama za ayi ace kamar kai ka auri yar aiki,mara galihu sannan wadda bata da gata kamar ni kaskantacciya? Hanyar jirgi daban ta mota daban, idan auren namu yana nan then what next?? Are we going to be real couples or what?….”
Ta tambayeshi tana kallon cikin idanunsa, “lets end it here,divorce me, yanda baka buqatata a rayuwarka haka zalika nima bana buqatarka, ni ba kowa bace face yarinyar data taba kula dakai a baya sanadiyar hakan kuma aure ya shiga tsakanina dakai,yanxu tunda bashida wani amfani sai a rabu”,
Tunda ta soma magana ya kafeta da idanu, bai taba shiga bacin rai kamar yau ba, ya rasa ta inda maganganunta ke dosa ita ko tayi hakan ne don ta gane inda ya nufa, mey yake nufi da ita?
Saurin controlling kanshi yayi, he’s not ready to open up, yadai san fatima is already part of him which he can never let go of, but he’s not sure of his true feelings, what he has for her.

“Ban rabu dake ba achan baya i will not do so now, cause you’re part of me,idan kina tunanin bana buqatarki, toh ayanxu ne nake kan buqatarki the most, i will never let go of you”

“Why??? Why?? Zakayi forcing dina ne? Why are you selfish, duk abunda na maka a baya? Ko danshi bazaka rabu dani ba? I have endured so much saboda kai, why cant we just part-ways kamar bamu san juna ba? Meysa”

Ta karashe tana hawaye, harga allah tunda yace mata akwai aurensu bai saketa ba take cikin tashin hankali, idan hadiza ta gano ta gama yawo, duk yanda zatayi saitasan yanda tayi suka rabu tun kafin a gano ma.

Daga yanda take magana ya gane a tsorace take da almarinsu shida ita kamar tana tsoron kar a gano cewa akwai aure tsakaninsu.

Aranshi yanaji wani irin zafi sosai, bazai iya abunda take so, batada kowa yanxu daya wuce shi, yasama ranshi wannan tun lokacin daya gano bata tare da asalin iyayenta kuma bata sani ba.
“Idan har bakiyi abunda nace ba ko abunda nakeso, you will leave me with no other option but to tell everyone cewa we are married…,“
Yana karashewa ya zauna tare da jawo wayanshi yana dannawa.
Tunda ya gano he can threaten her da haka yasan zatayi duk abunda yace, daman abu na farko dayasan zaisha wahala daga wajenta shine yanda zata karbesa bayan abunda ya mata a baya, kuma yasan cewa dama chan ga dalilin auren su.
Tanajin abunda ya fada ta tabbatar he just wants to use her, yanda yake tabata da yanda yake mata wasu abubuwa yasa tayi concluding hakan ne ma, daman waye gatanta da zai tsaya mata, haka rayuwarta ta taso sai yanda akayi da ita batada ta cewa, batada mai tsaya mata, gashi ta tabbatar bawai zai taba sonta bane, yama za ayi tayi tunanin haka?.
Jiki a mace ta juya bathroom din tana share hawayenta abubuwa da dama na yawo akanta, Allah kadai yasan irin tunanin da takeyi a wannan lokacin, ta soma rage kayan jikinta.

Yana ankare da ita har ta shuga bathroom din tana hawaye, kai itama dai kamar wata yarinya koda yake yarinyar ce mara wayo.
Gaba daya shiko ya damu da ita sosai, Yanda take kafiyar nan baiyi tunanin zatayi wankan dayace tayi ba wannan yasa ya dauoa smart remote din suite din wanda har labule yana kullewa kana daga kwance zaka iya operating komai na dakin.
So yake yaga mai takeyi, ko kuka takeyi?
Without second thoughts ya danna glass din bathroom din.
Take ya soma dishewa ahankali, qiqam ya tsaya yana kallonta, idanunsa kamar zasu zazzago har wani ruwa ruwa yakeyi.
Chan kasan maqoshinsa ya furta “damn…..”

Tana gama wanka ta daura towel a jikinta ta juyo bakin kofar ta kasa futowa, knocking din kofar da akayi yasa ta dago daga waje yace “i will out for a minute”
Ya fadi hakan ne don ya bata damar shiryawa duk wani tunani da take ya fita ranta.
Bude kofar tayi ta leko ganin baya nan yasa ta futo gaba daya ta wuce gaban hanger dinnan hannunta rike da sauran kayanta data cire, bin hanger din tayi da kallo ganin hadaddun abaya’s masu shegen kyau, guda daya ta zaro ta aje gefen gado sannan ta soma shiryawa a gurguje, tana gamawa ta zauna ta doka uban tagumi.
Cikin abunda bai wuce minti biyu da zamanta ba sai gashi ya dawo, kiri kiri taki yarda ta hada ido dashi shima sai kakkaucewa kallonta yake saboda abunda idanunshi suka gane masa, he cant stop imagining the way he saw her earlier naked, he felt so erouse kuma yasan idanda bai fita ba daxu anything can happen, the way he imagine her shes above beyond that, yana mata kallon yarinya karama, ashe tafi haka ba kadan ba, she’s a grown ass woman in full physically.
“lets go” ya fada yana hana kanshi kallonta.

Kamar jira take ta miqe da sauri tasa takalminta suka futo a tare.
Lift din da suka shiga kowannensu yayi tsit babu wanda yace da dan uwansa qala shi danna waya ma yakeyi har suka fito suka shiga mota.

Ta juya fuskanta ga window, tafiya sukayi mai dan tsayi kadan har suka iso shopping mall, suna isowa ya bude kofar expecting her to be out, baice komai ba kuwa ta futo yayi gaba ta bishi a baya.
Ciki suka shiga suna zagaye har suka iso floor din clothings da sauran accessories, sai a lokacin ya kalleta yace “pick abunda kike buqata”
“Bana buqatar komai” ta bashi amsa kai tsaye, baibi ta kanta ba ya shiga zarah cikin abunda bai wuce 10mins ba ya fito ya taddata tsaye hannunshi rike da paper bags sannan suka sauka kasa suka tsaya ga apple store, nanma dai qin shiga tayi sai shine ya shiga, abunka da masu hannu da shuri, babu lokacin yin wani negotiation ko minti goma baiba, ya fito da paper bag din apple da macbook laptop, other accessories da dai sauransu.
Inda take ya nufa ta wani hade rai sosai, kanar bata taba dariya ba, ya danyi smirking yace “lets go..”
Binshi tayi kamar jela har suka shiga motarsa, yaja motar suka futa daga harabar wajen, lokacin wajen karfe hudu harta wuce, time din duakansu ya shiga, kai tsaye gida ya wuce, suna karyo kwana gabanta ya soma faduwa, ta dubeshi tace “idan aka gane fa?..ka maidani school dan allah ya hamad zaizo daukanmu”
Banza yayi da ita har aka bude gate din entrance, ya shiga da motar ciki, sabeeha kamar tayi kuma tsabar tashin hankali, shiko ko ajikinsa.
Yana parking ya dubeta “talking of hamad, bana son na sake ganinki dashi a zaune kuna magana, ba magana kadai ba he’s not your muharram so be careful..”
Yana gama fadin haka ya miko mata jakkunan daya saya mata abubuwa ya aje akan cinyanta, sai faman rarraba idanu take, kamar baisan me take ciki ba, gaba daya hankalinta a tashe yake, bata sani bana ko an dauko su maya, ko basu dawo ba, idan sun dawo me zata ce idan an tambayeta? Sannan idan basu dawo ba waye zatace ya dawo da ita.
Ita bama ta abubuwan daya saya mata take ba ta dubeshi tace “ka ajesu a wajenka, bansan me zance ma mama ba idan ta ganni da abubuwan nan”
Tana fadin haka ta maidasu inda ya daukosu bayan kujerar sannan ta bude kofar hannunta na karkarwa.
Yana kallonta harta shige cikin gida ta kofar baya.
Babu kowa a kitchen din wannan yasa ta lallaba ta shige ciki da sauri.
Dakinsu ta bude daidai nan hadiza ta futo daga daki.
Jiki na rawa sabeeha ta duka kasa tace “ina wuni mama…”
Wani irin kallo hadiza ta mata, ji take kamar ta kashe yarinyar nan ta huta, yarinyar ta zame mata babbar barazana, yanxu taka hakura da batun barinta ta gama makaranta daman kwadayin dan abunda zata samu ne yasa ta dakatar da ita amma yanxu so take kawai ta rabata da gidan nan gaba daya bama nan kadai ba abujar gaba daya.
Gashi shegen dahirun nan yaqi daukan wayarsu ita da jamila, don hartayi planning kawaj ta dauketa ta tafi da

79 / 107