Author : Queenmerh Category : Complete Novels
shigo, karki manta kice mata kanwar ubanta ce ta shugo okay?, now excuse us'' ay tunda ammu ta soma magana jikin maid din ya fara bari, ammu irin masifaffun nanne wanda basa shuru idan sukaga abu, cikin hanzari kuwa maid din ta fice ta basu waje, sai a lokacin ammu ta dago ta kallseshi ganin ya runtse idanunshi gam, kwata kwata yaqi yarda ya dago kanshi ya kalli ko''ina dake cikin part din, ammu najin yanda hannunshi keyin zufa sosai, tana mamkin meysa daga shugowarshi ya sauya haka?,ko ya tuna da wani abunne?, tambayoyin data dungama kanta kenan, ita gwarama ya tuna din ayita ta kare kawai.
jamid na daga kwance idanunshi a rufe, kwata kwata baisan me ake ciki ba saboda maganin daya sha mai nauyin ne sosai wanda yayi dosing dinshi off, tunda ammu ta fara shugowa dubashi hidaya tasa nurse dinshi tana bashi maganin da zai dunga dosing dinshi off saboda tsoron karya fada ma kowa wani abun dukda tasan aynxu he's useless, prevention is better thatn cure, shiyasa duk sanda ammu ta shigo yana barci.
yanxu ma barcin yake yi har suka shugo baisan suna dakin ba, ''taj are you okay?'' ammu ta tambayeshi, shuru baice komai ba saida ta sake cewa ''tajudeen?,'
sai a lokacin ya bude rinannun idanunshi ya sauke akanta, ta inda take tsaye wajen gaban gado ne wannan yasa yana bude idanunshi ya sauka kan katon frame din fattu, cikin hanzari ya runtse idanunshi ya budesu sannan yayi saurin kauda kanshi daga wajen ya maida kan jamid dake kwance akan gado, yana kallon fuskanshi wani memory din yazo mashi lokacin da suka futa zuwa asibitin, inda ake mashi therapy, sai ga memory din lokacin da akayi kidnapping dinsu shida sabeeha abun saiyazo ashi barkatai, cikin sauri ya dafe kanshi jijiyoyin kan nashi suka sake fito lokaci guda ya koma jaa, ammu na ganin yanayinshi tace ''subhanallah'' baima iya sauraronta ya juya zai futa daga dakin saboda nunfashinsa da yaji yana seezing, binshi da kallo ammu tayi tana fatan wani abun ya tuna, duk yanda akayi ma wani abun ya tuna don ta hango tsoro da fargabar dake cikin idanunshi with dissapointment.
taj ko tunda ya dawo daga london sau daya ya shigo wannan part din, daga nan bai sake shugowa, saboda da zarar ya shugo yake tuna traumatic moment din daya tsinci kanshi a ciki shekaru da suka wuce tun kafin ya mallaki hankalinsa, hoton daya gani kadai ya tuna mashi da duhun daya rufe kaf farin cikin rayuwarsa ya hanashi sukuni haryakai zuwa yanxu, ya hanashi barin kowa ya shugo cikin rayuwarsa, he can clearly recall ranar da fattu ta shigo dakin da yake kwana da wuqa a hannunta,lokacin yana karami, yanayin ta kadai ya furgitar dashi,maganganun data fadi mashi har yau suna yawo a kunenshi, tun yana karami, ya kasance shi mai riko ne sosai, idan disturbing abu ya tsaya mashi rai baya iya cireshi aranshi, idan yayi mafarkin wannan fuska baya iya barci kwata kwata, he had a traumatic childhood da yayi affecting dinshi phsychologically wanda bazai taba mantawa.
abuncin da bai ciba kenan, ya dade a zaune akan gado hannunshi dafe akanshi.
Washe gari da safe da abun ya kwana, saidaga baya ya fara tunanin yaayin daya tadda jamid a ciki, he really wants to know what has happen cikin shekara dayannan data wuce, baiyi wani barcin kirki ba wannan yasa baima futa gym ba don sai wajen asuba ya kwanta barci mai nauyi ya daukeshi.
yau dai gaba daya hankalinta ba a kwance yake ba saboda bataji motsinshi ba, yanayinshi da ammu ta fada mata da suka shiga wajen jamid ya tsaya mata arai, tasan duk abunda zai tuna daya danganci watannin da suka wuce a baya bazai taba jin dadi ba, he will be heratbroken he will be shatterd, yayi rayuwa a matsayin wanda baya cikin hayyacinsa bayan wannan kuma ga qalubalan daya fuskanta, inta tuna wannan tana jin rashin dadi a ranta, yau da bai futa ba kwata kwata ma taji rashin dadi sosai.
Taheel company…
achan taheel kamfani kuwa, yau gaba daya kamfanin ya rikice, hidaya tazo da sabon abu, tunda ta soma magana kowa yayi shuru ana sauraronta, wannan magana datazo dashi ba karamar magana bace,ya za ayi tayi deciding janye tallafin daya daga cikin manyan investor din kamfanin?,janyewar nan ba karamar matsala zai kawo kawo masu musamman yanxu da take kokari producing sabon business gashi ta tattara duka kudaden kamfani wajen sabon product din nasu, daban kudaden da investor ke shigarwa ne kawai ke tafiyar da kamfanin ayanxu, wannan decision ba karamin abu bane, kuma wannan zai iya jawo masu babbar matsala, hankali a tashe daya daga cikin manyan shareholders ya soma mata magana ''gaskai ma'am bazai yuwu ba, babu kudi cikin kampani, finance department sunyi korafi, kudaden kamfani da muka saka cikin sabon product din da akeyi ayanxu idan har aka samu matsala bamuda backup,kafin ma akai ga cire investor ya zamuyi compensating dinsu?, what if suka buqaci share din kamfani?, madam a dai sake duba wannan''
dagowa hidaya tayi tana kallonsu daya bayan daya, ita ba maganganun da suke na risk din da kamfani zai shiga ne agabanta ba, dole ta fidda investors dinnan,dole ne, bazai taba yuwuwa tabarsu a cikin jerin masu tallafin kamfani ba saboda tasan ko wanene yake tallafin kuma idan har shareholders dinnan suka gano taj ne shikenan, she will lose everything that she has work for, ayanxu datakai matsayin nan bata jin zata taba barin haka ta faru, she has sacrifice alot, the last thing da zata taba bari ya faru shine kamfanin nan yabar hannunta ya koma wajen wanda tayi rantsuwa bazata taba barin ya samu koda digo daya ne daga cikin gadon kamfanin ba, balle har ya zama nashi, bataji bata gani kwata kwata.
a harziki ta tashi rai a bace tace
''ba wai shawarar ku nake nema ba, wannan order ne nake badawa, dole a cire waennnan investors''
''but madam dole ki bamu reasons din da zamu basu kuma kinsan zasu iya sueing dinmu akan wannan yarjejeniyace mukayi a tsakani, duk profit din da muka samu zamu basu nasu percentage din,''
''i dont care, kudin da sukayi investing na wannan shekarar za a maida masu, its a contract zamu iya ending duk sanda muka ga dama tunda partnership ne,''
''but ma'am idan muka basu kudi bamuda wanda zamu…''
''im done…..talking, not a single word from anyone'' ta daka masu tsawa, tuni kowa ya kama kanshi, ''do you want me to make you understand me better?'' ta karashe tana mai kallonsu daya bayan daya, tuni kowa ya soma sauke kai kasa saboda tsoron abunda zai biyo baya.
''we are canceling TNT investors,saboda proposal din da suka kawo mana is not authentic, saboda haka thats final''
tana kaiwa nan ta fuce daga hall din, secretary dinta na biye da ita ba baya, tunda ta fita ake ta cece kuce, chan na hango fadwa daga zaune, daman tare suka shugo office din, shine itama tayi joining meeting din.
hidaya na futa ta mike itama tabi bayanta zuwa office dinta, tana shiga ta tadda hidayar nata zarya tsakanin office din nata, ''yanxu what is your next move?''
''ke kinsan dole ne na fitar dashi, i cant take that risk, idan har aka gano ya samu sauki kuma shine investing a cikin kamfanin nan komai zai wargaje, zasu kwace kamfanin daga hannumu,''
''kai ya allah, ya akayi ma kika bari har kuka partnership dasu bakiyi dogon buncike ba?''
''how will i fucking know hes behind all of this?, yaronda ban taba tunanin yana da wayo ba har ya iya zama mutun, kina tunanin turashi karatu da nayi kuma na hanashi dawowa nayi shi ne saboda ya daukaka ya zama wani abun?''
sauke ajiyar zuciya fadwa tayi sannan ta ce ''toh ay gashinan yanxu kinga plan dinki bai yuwu ba, dman kema ukty ay ba haka ya kamata kiyi ba tun farko, keep your enemies close to you so that you can see their progress and have control over them amma me? da kika tashi sai kika turashi chan inda baya kan idanunki balle kisan me yake ciki,duk hanashi zuwan da kikeyi bai hanashi ya daukaka ba, kuma ya boye maki hakan, me kike tunani kenan?, kinga wallahi i never trust yaron nan wallahi, abun tambaya ma anan da zaki fara yima kanki shine, duk yanda yake maki why did he lie about his identity?, why did he lie about koshi waye?, why didnt he tell you shike investing a kamfanin nan?, definately kudirinsa don ya karbe kamfanin ne daga hannun mu, you need to open your eyes, akwai wata a kasa ukty''..
ay tunda fadwa ta soma magana hartakai aya hidaya bata taba jin tashin hankali ba sai na yau, tabbas maganganun fadwa gaskia ne, duk yanda yake mata why did he lie?,ko dama tun farko ya gane kudirinta na hanashi dawowa?.
''yanxu ya kike so nayi?, '' hidaya ta kureta da idanu tana kallonta don jin amsar da zata bata,
''yanda yayi mana wasa da hankali haka zamuyi da nashi, first of all duk yanda zamuyi karmu bari ya gano munsan koshi waye, mu bishi a haka muma, na biyu duk wani abu da kikasan zaisa ya gano abunda ya faru cikin shekara dayan nan dole mu kauda shi,……
***
zaune yake a office, yaronshi na gabansa da wasu takaddu masu mahimmanci, tunda ya kafama takardun idanu ya kasa daukesu, a daidai lokacin incoming call ya shugo wayar secretary din, yana dagawa ya miqama ogan nashi, miqewa tsaye abdul basit yana sanye da suit yakai wayar kunneshi tun kafin ayi magana daga chan ya soma cewa .
''any update!!''
''yes sir, madam ta cire TNT Investors''
yana jin haka ya dago yana kallon yaronshi shima kallonsa yake da mamaki don anajin abunda ake fada daga cikin wayar, ''you mean ta yanke parnership dasu?, ''
''yes sir,''
''whats the reason,'' ya sake jefa mashi tambaya
''no reasons sir, the company is at risk, kudin kamfanin bazai iya daukar production din da ake ba''
''which means?'' abdul basit din ya sake jefo masa tambaya.
''kamfanin zai mutu sir its the end game'' abdul basit najin haka ya kyakyace da dariya, ya dade sosai yaan dariya sosai kafin ya maida dubansa ga yaronsa da yayi shuru, ''wannan dama ce a garemu, inason kayi preparing partnership da Tnt, wannan is an opportunity''
''yes sir'' yaron ya amsa shi,
yaron na fita ya yakyacewa da dariya yana kallon papers din dake gabanshi,
wannan information din daya samu daga daya daga cikin mutanenshi ne da suke taheel company, wanda ya kiranshi ma babba ne a kamfanin don shi abdul basit dinne ma ya bashi kudaden daya saya shares a kamfani, mutumin dai kmar shine eyes dinshi a cikin kamfani, duk wani sirrin kamfanin na hannunshi kuma yasan da komai, yana jiran lokaci ne kawai da zai kawo karshen kamfanin, bawai yanason ya fisu bane ah ah so yake kawai ya kawo karshen kamfanin taheel din.
Taheel residence…
misalin wajen karfe sha biyu ya futo daga bedroom dinshi ya shige kitchen, yaune ya fara shiga kitchen din tun bayan ya dawo hayyacinsa, bai wani tsaya dube dube ba ya bude fridge ya zaro ruwa yana rufe fridge din idnunshi ya sauka kan timetable din dake wajen, bai kawo kona menene ba ya fuce daga kitchen din ya koma daki.
wannan chocolate din daya sayo ya zauna ya dunga ci ya kora da ruwa, tunda ya dawo daga asibiti kwata kwata yake jin qin cin abuncin gidan ya rasa dalili, hatta breakfast dinnan yanaci ne kawai amma bada kwanciyar hankali ba cikin fargaba yakeyi, shiyasa baya yawan cin abunci,kuma batun yanxu yake jin haka ba tun usulin zamanshi a gidan.
yana zaune yana latsa waya yana cin chocolate yana aiki a wayarshi sabon email ya shugo, inda managers dinshi suka tura mashi rejection din da taheel sukayi na investment din da suke duk shekara, da mamaki yake kallon wayar bayan ya karanta report din, yau shekara wajen biyar kenan yana investing a kamfanin ba ayi rejecting ba maisa sai yanxu?,yanajin somthing is wrong don haka ya fara kokarin neman tnt group din da yayi enganging, message ya fara tura ma mr benjamin cikin mintina qalilan saiga call dinshi ta facetime video call
''good morning sir'' mr benjamin ya gaishe
''its afternoon here mr benjamin'' ya amsa shi da mavelous accent dinshi mai dadi, ''sir munata kokarin reaching on you we…''
''there was a certain issue over here that abrupted my absence''
''sorry bout that sir''
jinjina mashi kai kawai yayi sannan ya soma tambayarshi dalilin da yasa taheel kafani suka rufe karbar investment, nan ya mashi bayanin komai da yanda dakardatr ta futo, karshe ya karashe mashi da report din yazo ne directly daga chairwoman din taheel wato hidaya, a yanda take kamfanin batayi approving partnership dinsu ba na wannan shekara, tunda ya soma mashi bayani yake sauraronsa haryakai aya baice qala ba, yana gamawa sukayi sallah ya kashe wayar.
''what is she up to?kodai ta gano shike investing?,no it can be possible, toh amma idan ta gane ay zata tambayeshi?,'' they has to be something wrong, somewhere tunanin daya wuni yanayi kenan.
the next day…
misalin karfe takwas daidai sabeeha ta hauro saman,kwata kwata batayi tunanin bai fita yau ba don kwana biyu tasan yana futa da sassafiya wannan ke bata damar haurowa sama ta dan gyara mashi bedroom din, lokacin data shugo dakin is very dim babu wani hasken kirki don haka ta kunna fitilar, take hasken dakin ya bade ko'ina, sabon kamshinsa na mata sallama, takowa tayi wajen gadon nashi ta soma cire beddings din daya kwanta akai tana cirewa ta shige closet dashi ta ajiye ta dauko sabo sannan ta fito ta sanya mashi.
dagowar da zatayi ta soma jin saukan ruwa, shuru tayi tana nazari kodai yabar ruwa ne a kunne harta tunkari hanyar dazai kaita bathroom karar ringing tone ya dakatar da ita, tuni tayi turus ta tsaya, wajen inda wayar yake ta nufa ''innalillahi bai fita ba kenan''
ko gama rufe bakinta batayi ba taji alamun bude kofa, da yake akwai tazara tsakanin bedroom din da bathroom harma da closet wannan yasa cikin hanzari ta nufi hanyar futa, daidai tana rufo kofar shi kuma yana karasowa tsakiyar dakin yana goge gashin kansa da mini towel sai wani kuma a qugunsa, kamar ance ya dago ya daga kanshi idanunshi ya sauka kan kofar,dan jim yayi yana kallon kofar chan kuma ya kauda kanshi kawai ya maida hankalinshi ga abunda yake.
sabeeha na futowa ta dafe kirjinta, gudunshi take yanxu saboda wani irin kwarjini da yake mata, bata tsaya ko'ina ba sai bedroom dinta.
da yamma misalin karfe biyar ya futa daga gidan, bashine ya dawo ba sai wajen karfe takwas, motar hidaya ya fara gani a coupound din wannan ya tabbatar mashi ta dawo, don haka ya shige daga ciki, koda shigo babu kowa a kasan wannan ya bashi damar nufar hanyar dazai kaishi sama, bai karasa ba ya hango ammu da sabeeha a wajen dining, da alamu girki ma sukayi shine suke shiryasa ga maids na shigowa da warmers masu kyau, ''kin gaji ko fatima?''
''ah ah ban gaji ba ammu,''
chak ya tsaya bai daga sake daga kafarshi ba, yana jiyo sautin maganganunsu, maganra sabeeha ne tafi tsaya mashi a rai, tabbas yasan muryar nan saidai ya rasa a ina, ''zokiyi maza ki kai mashi sama naga kamar daxu ya fita bai dawo ba,''
''tohm…'' sabeeha ta amsa ta,
saukowar fadwa daga stairs yayi daidai da tsayawar da yayi, kallonshi ta soma yi daga sama har kasa, shi baima lura da ita ba har saida ta zo gabanshi, gyaran murya fadwa tayi ya juyo ya mata kallo daya ya dauke kanshi, take yanayin fuskanshi ya sauya ya hade rai sosai ko kallon inda take bai sake ba ya nufi sama, cikin hanzari ta kama hannunshi, tunda ta rike hannunshi yabi hannun da kallo kafin ya maida dubanshi gareta, ''wai gaba kake dani saboda abunda ya faru ko saboda abunda na fada maka wanne daga ciki?, i thouth yanxu komai ya wuce, you still hold grudges?''
tana kaiwa nan yayi saurin runtse idanunshi kafin ya budesu akanta babu wasa ko kadan yace ''take your filthy hands off me''
yanda yayi magana yasa tayi saurin sakin hannunsa, sannan ta hade nata a kirjinta tace ''don't think i will be among those that you sill decieve,nasan ka tuna komai, MR T-FORD''
tana fadin haka ya dago yana mai kallonta, kwata kwata bai nuna yama san maganar da take ba ko ya nuna yayi mamakin sunan data kirashi dashi, tana ganin ta sauke murmushi ta tako inda yake har gabanshi tana mai jin saukar nunfashinsa tace ''we have unfinished business remember?, ''
tana fadin haka ya dago ya wurga mata wani irin kallo mai wuyar fassara, mai dauke tsana, da dacin rai,bai tsaya ya cigaba da sauraronta ba ya juya ya barta a wajen tana mai kallonshi kawai saita sauke murmushi.
yana hawa saman ya wuce bedroom tare da banko kofar, ranshi a mugun bace yake sosai, jijiyoyin kanshi sun fito rudu rudu tsabar baci rai, she's underestimating him, bai taba tunanin zata sake kawo mashi maganar data faru a baya ba, she has the audacity, har wani irin huci yake fitarwa tsabar baci rai.
karar kofa dayaji a parlor yasa ya miqe tsaye don ya dauka itace ta biyoshi har saman, yana bude kofar parlor idanunshi ya suaka a bayan sabeeha dake kokarin futa daga dakin, da yake bata da tsayi sosai yana dagowa ya hango bayanta, daman abunci ta kawo mashi ganin baya ci a kasa, wanan yasa ammu tace ta dunga kai masa saman, duk kawowan da zatayi haka zata dawo ta dauke ba a taba ba kwatakwata, kuma bata taba bari ya gane itake kawo mashi ba, toh idanma ya gane ba ganeta zaiyi ba, tana ajiyewa ta dago ta nufi hanyar futa daga dakin, bata kaiga kofa ba kawai light din part din dauke gaba daya,shi kuma a lokacin ya rufo kofar bedroom din garaf, tuni jikinta ya soma kyarma ta fara innalillahi a zuciyarta, takowa ya dungayi kamar wani kamar ana ingiza shi har zuwa lokacin yana nishi sosai, something is eating him up, abubuwa da yawa suna yawo akanshi,''who should i trust, who should i trust'' abunda ke raya mashi kenan a zuciya, da zarar ya shiga irin wannan yanayin,
bangaren sabeeha tashin hankalinta ya hadu biyu, na farko