Advertisements
Chapter 40 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 107

117K to 120K   out of 320.4K words

ba ayanda ka sanni nake ba, ni yaron khaal ne kuma nine na hannun damanshi wanda ya yarda dashi ya amince dashi, banyi approaching dinka da wata manufa ba sai alkahiri taj, kuma sai dan ganin na rike alkawarin dana daukar ma khaal ”
Hannu taj ya daura a kanshi ya shafa sukan kanshi ya sauke kan kasa jijiyiyin kanshi sun fito rudu rudu, ya dubi mutallib din yace “you’re all
Insane, me kuka maidani ne? Kwallon wasa? Da wannan zai buga wannan ma ya buga, does making fool of me make yall happy?”
“Listen to me taj, abunda kake tunani ba haka baneba kuma duk avunda detective ya fada maka gaskia ne, sannan akwai boyayyen sirrin dake boye wanda kai kanka baka sani ba na bari sai…

Hannu ya daga mashi bai sake kallonshi ba azafafe rai a bace yabar wajen.
Da wanne zaiji, wannan batun wannan detective din ko kuma batun mutallib? The guy he trust’?
Menene boyayyan sirrin da yake magana akai, he needs air to claim duk maganganun da kunanahi suka jiyo mashi,
Mutallib ya miqe yabi bayanshi, ranshi a bace don ya kasa gane inda taj din ya dosa gaba daya, gaskiayr ce baya son ji ko kuwa.
Harya bude kofar mutallib ya maida kofar ji kake bam.
“Why are you running away from all of this bayan sanadinka ne duk hakan ke faruwa, you don’t want to listen to me at all”
“This is all my fault???? You’re saying this is all my faulttttttt!!!!”
“Yesss it’s all your fault mutallib ya daka mashi tsawa, tabbas khaal duk halin daya shiga ta dalilinka ne, wani irin mutun ne kai? why can’t you understand that, daga rayuwar ka achan uk har zuwa yanxu wallahi wallahi bazanyi kaffara ba saboda khaal kake cikin koshin lafiya har kakai yanxu harka zama abunda ka zama, kana tunanin waye yayi supporting din business dinka lokacin daka fara achan uk? Ba kowa bane face khaal, kana tunanin waye ya dunga saving spot dinka a lokacin da ake neman tauye maka hakkinka? Ba kowa bane face khaal, kana tunanin waye ya tsaya maka, yayi protecting dinka ya soka tsakani da Allah? Ba kowa bane face khaal din.., your life was in danger this whole time kuma bai iya runtsawa kona second daya ne, tunaninsui ya rayiwar ka zata inganta, ya zaka samu lafiya, ya zaka bude idanunka ka kalli gaskiayra dake gabanka,”

Bude kofar taj ya sake yi ya shige daga ciki ya kunna tare da yin reverse a zuciye yabar wajen.
Yakai awa yana tuku magnagnun mutallib na yawo kanshi, wa zaiyi trusting? Wa zai yarda dashi,? This is so much for him to handle.

Wato shifa ga gaskiayar a gabanshi amma ya kasa yayi accepting dinta, don bai taba tsammanin jin haka, kaii ya Allah.. tsantaar betrayal baiba, abunda kafi yarda dashi kaf rayuwarka lokaci guda kaga duk karyace ba hakan bane abun da zafi, its hard to believe and accept, he’s hurt, lies upon lie, tunda ya fara binciken nan baiji alkhairi ko daya ba.



Abuja nigeria…
Yau satinsu guda, har sabeeha ta soma farfadowa, daman bataji hutu bane, suci mai kyau su sha mai kyau, ga kaya da anty fadila ta kawo na laila da suka dan kwana biyu aka bata, hadiza bata hanata sakawa ba kuma bata ce komai ba don itama an bata har kala biyar masu kyau.
Aiki kuwa suna yinshi, yawanci ma sabeeha ce keyi, zata tashi da asuba ta shiga cikin yanmatan gidan masu aiki suyi tare, yawanci ma dai ita wanke wanke ake barinta dashi sau kuma harkar yanke yanken veggies da gyaran tafkekwn kitchen din.
Duk inda ta zauna da mutun kafin ta tashi saita shiga ranshi, dukda batada magana bata da hayaniya kwata kwata, ahankali ahankali ta fara sakewa da yan aikin gidan dukda tana kaffa kaffa da kowa sbd warning din mamanta, hadiza ko ba laifi itama tana fitowa aikin, yawanci itama dai aikin cikin gidan nan takeyi, banda sama don akwai masuyi a sama, da farko ma dai bata shige ma mutanen gidan da yake kuma ansan juna haka fadila ke dan janta jiki.
Hamad ko tunda yasan sabeeha na gidan koda yaushe yana part din anne donma dai suna shiri sosai shida ita don tace shine fav dinta, duk shigowannan da yake bai taba haduwa da sabeehar ba kwata kwata ko sau daya kuma so yake ya ganta koda sau daya ne.
Laila da maya ko basu taba haduwa da ita ba basuma san da wasu sabbin mutane cikin gidan ba, don basa zaman gidan kullum suna makaranta weekends kuwa kowa tana part dinsu, maya na wajen anty laila, inta rayo mata ta tafi yawanta ta dawo, laila karama kuwa tana wajen mummynta.

Akwai ranar wata saturday da aka kawo provisions da yawa da za ayi restocking store, indo tasa yan matan zuwa inda akayi parking motar kaya ta gaba su kwaso a shugo dashi ta back yard, a cikin masu debowa harda sabeeha,suna cikin kwasowa hamad ya fito daga main entrance, tunda ya hango sabeeha ya kasa wucewa ya tsaya yana mai kallonta sosai irin kallon kurullan nan,harya wucewa ma ganinshi.
Part dinsu ya koma yana shiga yaga wannan mara kunyar, da kallon banza ta bishi, ya dauke kanshi yana mamakin yarinyar sosai.
Yanajinsu suna maganar shiga part din anne.

Atare suka fito suka nufi part din anne, saman suka fara zuwa suka gaisheta sannan suka wuce wajen nanna, dake tafi sakewa da kowa sosai ga faran faran wannan yasa suka dade sosai wajenta kafin su sauko, laila tace “bari na dauko mana cake din da nanna tace mu dauka”
Ta tashi ta wuce kitchen, tana shugowa babu kowa sai sabeeha data juya mata baya tana wanke few cups, “please akwai cake a fridge ki saka min a saucer guda biyu ina parlor”
Tana fadin haka ta juya zuwa parlor, sabeeha data tabbatar ita kadaice kitchen din babu yanda ta iya haka ta dauka saucer ta yanka cake din ta saka guda biyu sannan tasa fork ta aje kan tray ta fito,
Hanyar parlorn tabi tana tsoron karta bata, allah ya taimaka ta hango yanmata biyu zaune ga muryar dayar data mata magana na tashi alamun ma waya take.
Karasowa tayi har parlor maya na danna waya ita kuma laila na waya, har ta aje gabansu laila
Ta mata alamu da hannu ta miqo mata nata ta miqa mata tace “thanks tare da mata murmushi tana mamaki ko wacece wannan din don bata taba ganinta ba, harta juya maya da bata kalleta ba tace “ubanwa kika ajema wannan?”
Itafa maya batama yan aiki da sauki, shiyasa duk yan aikin suke cewa bata da mutunci laila ko babu ruwanta.
Takowa sabeeha tayi ta dauka nata ta karaso inda take ta miqa mata sai a lokacin maya ta dago ta kalleta, tashin farko ta gane ko wacece, saitayi kamar zata karba plate din bata karba ba ya fadi kasa ya fashe tass a kas, a zafafe ta miqe ta wanke ta da mari for the second time, batasan ko ita wacece ba.
“Ke wace iriyar donkey ke, illiterate stupid human, haka ake serving a kauyenku? Why are they bunch of useless people in this house huhhh get the fuck out of my way,”
Harta juya ta sake tsaidata, ran sabeeha ya baci sosai ta danne “go and get another one rubbish”
Juyawa sabeeha tayi laila dake waya ta dubi maya ta girgiza mata kai itako maya ko ajikinta.
Wani sabeeha ta sake kawowa har gaban maya, wallahi ko kallonta batayi balle tasa ran zata karba data “ko na aje maki a kasa?”
Wani irin banzan kallo ta mata tare da miqa hannu zata karba, sabeeha ta ankare da abunda tayi dazu take son ta sakeyi, kuma bazata bata dama ba wannan yasa itama ta miqa hannunta daidai jikin maya din tana aje mata plate din a hannu maya ta sakeshi unknowly zai zuba jikinta ya bata mata jikinta gaba daya, icing din.
Wani irin kara tayi ta miqe tsaye tana mai duban sabeehar harta daga hannu zata wanke ta da mari sabeeha tayi baya abun ya kara kular da maya, taji lokaci guda ta tsani sabeeha kamar ranta, laila tayi saurin kace wayarta, sabeeha bata ankara ba ta shiyo ihun hadiza, “keeeeeeeeee” wallahi saida ta tsorata,ashe ta dade a tsaye tana kallon abunda ke faruwa run dazu, idanun ta sunyi jaa sosai kamar wadda tayi kuka, nan har inda maya ke tsaye ta tako ta dubi sabeeha tace “dan ubanki sa’ar kice, kizo har cikin gidansu tana magana kina tsaye?kuma tasa kiyi mata abu kika zuba mata a jiki” ji kake tasssa marin da maya batayi mata ba hadiza ta sauke mata tace “tsugunna ki bata hakuri naceeee!!!!” Ta daka mata tsawa, hawaye na sauka idanun sabeeha ta duqa kafarta na karkarwa tace “kiyi hkuri bazan sake ba”
Murmyushi maya tayi, wannan matar ta burgeta sosai, dukda bata san ko ita wacece ba haka ake dealing da yan aiki waenda basuda kunya samm.
“Dan allah kiyi hkuri kinji, laifina ne da ban nuna mata banbancin na gida dana waje ba”
“Ohh so kece maman ta kenan, bunch of weird people every where, the next time kika kara ganina ki tabbatar kin chanza hanya, rubbish”
Tana fadin haka ta wuce kamar zata bangaje sabeehar da hadizar ma gaba daya, maya ta girgiza kai ta duqa ta kamo sabeeha tace “I’m very sorry dear”
Murmushin yaqe kawai sabeeha ta mata ta juya ta bi bayan maya, hadiza ta dubi sabeeha “tashiiiii”
Sabeeha da jikinta har na neman yin rawa ta miqe tabi bayan hadiza.

Wani irin janyota hadiza tayi ta kusa gwarata da bango tace “so kike ki hawo min bala’i? So kike a koremu daga gidan? Ke zaki ciyar damu? Wannan talaucin da muka baroshi kikeso mu koma? To wallahi zan jaa maki warning, daga yau hanyar da sukabi kikabi sai ranki yayi mugun baci, ko cikin idanunta kika sake kalla ban yafe maki ba, babu ruwanki da harkarsu, ke ba kowa bace face yar aikin gidansu,yauwa”
Tana fadi haka ta futa a fusace sabeeha ta zauna zaman dirshen sai hawaye.

Anne data fito tun ihun maya na farko tundadaga sama take kallon duk abunda ya wakana a kasan.

Dakinta ta koma tayi dialing pa dinta yana dagawa ta soma magana “inason ka nema min final year entry admission a baze university as soon as possible”
“Yes ma’am” ya amsata.

Saudi…
Taj na barin wajen mutallib yabi motar shi da kallo, jiki a mace ya juya wajen tashi motar yana kokarin shiga wata baqar mota van ta tsaya, wasu mutane su biyu suka fito suna sanye da baqaqen kaya da facing cap, daya ya tsaya ta bayan mutallib yace “don’t move” chak mutallib ya tsaya jin bindiga a bayanshi, “turn around”
Nan ya jiyo a hankali suka sashi cikin motar suka taci dashi, innalillahi wa inna ilaihi rajiu’un
Ko su waye waennan suka dauke mutallib allah kadai masanin gaibu ya Allah….



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 84

Saudi…
Taj na barin wajen mutallib yabi motar shi da kallo, jiki a mace ya juya wajen tashi motar yana kokarin shiga wata baqar mota van ta tsaya, wasu mutane su biyu suka fito suna sanye da baqaqen kaya da facing cap, daya ya tsaya ta bayan mutallib yace “don’t move” chak mutallib ya tsaya jin bindiga a bayanshi, “turn around”
Nan ya jiyo a hankali suka sashi cikin motar suka tafi dashi, innalillahi wa inna ilaihi rajiu’un
Ko su waye waennan suka dauke mutallib allah kadai masanin gaibu ya Allah….



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 85
Suna shiga cikin motar dashi wasu mutane biyu dake zaune a baya sukayi wrapping din kanshi da wani kyalle baki, har suka bar wajen bai iya ganin fuskokinsu ba.
“Suwaye ku? Me kuke nema dani? Me na maku?”
Wanda ke zaune mazaunin gaba ne ya jiyo yana taunar cingum, kunenshi daya kamar an taune shi sai gefen idanunshi da yayi baqi sosai, “hahaha, dakayi shuru da bakinka qwaro, daya fi maka, at long last dai mun kamo ka”
“Ku fada min ku suwaye, me kuke nema dani”
Da sukaga ya ishesu da tambaya sai kawai suka toshe mar baki.
Hayakin vape da taba duk ya cika motar gaba daya.


Abuja nigeria…

Share hawayen dake fuskarta tayi sannan ta guara zaman wayan a kunenta “malam ko ke fa, yanxu tunanin yanda zaki samarwa kanki matsuguni zakiyi a cikin gidan nan, inace akwai babban yayansu a gidan, na rantse da allah in nice ke saina aure shi, tuni da taimakon malam zan hauqe mashi”
“Hmm jamila kenan, mutanen da suka wulaqantani, suka cimin mutunci, suka min abunda bazan taba mantawa kike cewa na shiga cikinsu?, ay wallahi saina tarwatsa farin cikin gidan”
“Na nawa kuma kawata, hahah.. ke dai har yanxu wallahi hadiza kanki baya jaa, an an toshe maki basira gaba daya, yanxu idan kika auri wannan sameer din menene bazakiyi ba, ka kudi a arziki, sannan kuma ta bayan fage ki ci dunduniyar su ki balbala masu wutar masifa gidan ya tashi gaba daya kawai”
“Hmm kina tunanin zan iya hakan ne? Wannan, matar nan a tsaye take akan iyalanta,”
“Toh ay shikenan, shawara nake baki, kuma saikinfi kowa amfana da shawara, kinsan abunda nake nufi ay”
Wani irin murmushi hadiza ta sauke, nidai ban taba ganin hadiza tayi irin wannan murmushin ba sai yau”
Suna sallama da jamila ta wanke fuskarta tass sannan ta fito daga bathroom, yanxu lokacin yin dinner ne wannan yasa ta futa kitchen don ayi da ita, tunda suka dawo gidan ba wani aikin kirki hadizar keyi ba, yawanci duk sabeeha keyi, saidai kaga ta fito jefi jefi, zuwa kitchen, ko ta shigo dinna. Saidai kaji tana bada order yi wancen ajje wanchan dauko wanchan, har kusan fada saida sukayi da indo dake itama idanunta a bude yake, ta nuna mata fa kartaga wai dakinsu ya banbanta dana yan aiki, yanda suke aiki ana biyansu itama haka zatayi ita da diyarta.
“Ke asma’u fita da wannan warmers din, zuwa dining”
“Anty indo”
“Kawo na taimaka maki” hadiza ta fada tana mai karban warmers din.
Sabeeha na daga bakin sink ko juyowa batayi ba, saima aikin gabanta da takeyi kawai.

Nanna ce kawai da hamad zaune kan dining banda anne, yawanci ita a sama take saboda ciwon kafa.
Kallon hadiza nanna tayi, murmushi kwance kan fuskarta as always tace
“Sannun ku da kokari hadiza”
“Yauwa hajiya barka da dare”
Sallamar laila ce tasa duk suka juyo suna kallonta musamman hadiza, har wani irin murmushi tayi ganinta, “yau anan zakiyi dinner ne kishiyallare”
Dariya laila tayi tace “nanna yau tuwo mami tayi, ni kuma gaskia banson cin tuwo harga allah”
Ta karashe tana mai janyo kujera ta zauna, hadiza ta kalleta tace “bari a kawo maki plate”
“Tohm nagode”
Ciki hadiza ta shiga ta futo ta aje mata plate din laila tace “ina…uhm bansan sunanta ba, dan allah kuyi hkuri da abunda maya tayi mata dazu”
Kallon mamaki nanna tayi mata tace “me mayan tayi masu”
“Wallahi nanna ni kaina bansan me tamata ba, dazu da kikace mu dauka cake a fridge shine..”
Saurin katseta hadiza tayi “haba ba komai, itama sabeehar ay laifinta ne”

“Sabeeha” ya maimaita sunan a ranshi, yana jinsu saidai baice qala ba saima cin abuncin dake gabanshi da yakeyi, “me ya hada ta da wannan mara kunyar? Koma menene yasa maya ce batada gaskia”

Wayar laila ce tayi kara, har hadiza ta juya zata koma tajiyo muryar maya doj a handsfree tasaka, “kina ina ne”
“Ina part din anne, kizo yau anyi dambu”
Kashe wayar kawai maya tayi,
Cikin abunda baifi minti biyu ba sai gata, babu ko sallama, daidai nan hadiza ta shugo parlor da wani plate din a hannunta,
“Amaryar dady babu sallama”nanna ta fada tana mai duban mayar data ja kujera ta zauna, hamad kuwa wata iriyar zagbgegiyar harara ya watsa mata ko ta kanshi batabi ba.
“Salam!”
“Wa alaiki salam!” Nanna ta amsa ta,
Aje mata plate a gabanta hadiza tayi sannan tace “me zaki ci a zuba maki”
Wani irin kallo maya ta mata irin banganeba, ganin nanna na wajen yasa ta waske “zan zuba dakaina”
“Toh akawo maki lemo?”
“Barshi bana buqata”
Binsu da ido nanna da hamad sukayi, shifa bayason a raina babba ko kadan, ji dai yanda take ma wannan da zata haifeta magana babu respect ba komai,
“Jeki kawai hadiza, in tana buqata zata dauko da kanta” nanna ta fada
Jiki a mace hadiza ta juya.

Bayan sun gama dinner anan parlor suka yada zango hamad ya wuce sama sukayi hira da masoyiyarshi anne, sai wajen tara saura ya sauko kasan, anan ya taddasu sun bace, laila na waya maya kuma ta kurama wayanta ido, “keee”
Ya kira maya don a daidai saitin ta ya tsaya, “are you deaf?”
A harzuqe ta juya ta kalleshi , “bakasan sunana bane, ko ke aka rada min?”
Cije lebenshi yayi kafin yace “kije anne na kiranki”
Ay saida gabanta ya bada wani irin daram, baima tsaya ya sake kallonta ba ya wucewarshi, ta miqe ta wuce sama.
Da sallama tayi knocking kofar bayan an bata izini ta shugo, anne na zaunw kan babban carpt din parlornta gabanta shaqe da warmers na abinci data gama ci, sai cup din tea da take sipping.
Zama maya tayi a kasa kusa da ita tace “barka da dare anne na, you called for me”
“Yes i did”
“Inaso ki tattaro kayanki gaba daya daga part din sameer ki dawo nan,”
Hankali a tashe ta kalleta, harga allah batason dawowa nan wallahi, part din anty laila tafi sakewa sosai achan, babu takura babu tsangwama, idan zata futa sau dari babu wanda zai tsaya questioning dinta, shes just living her best lif.
“Anne, I’m comfortable achan, and ina taya anty laila yan gyare gyare”
“Wani gyare gyren zaki tayata tanada helpers har guda uku?”
“Anne….”
“That’s final…and secondly karki sake treating helpers din gidan nan yanda kikayi treating yarinyar nan daxu, suma mutane ne kamar kowa and sunada gata, treat each and everyone one of them with respect understood?”
“Yes anne”
“As from today Hamad zai dunga kaiku school and shi zai dauko ku, jeki saida safe”
Miqewa maya tayi, ko iya amsa mata saida safe batayi ba ta futa rai a bace kamar ta kumbura ta face.
Tana saukowa ta soma dialing number mummy ta.
Cikin shesheka ta soma magana “Mummy na gaji, na gaji, I don’t want to stay here anymore please its been 2yrs now mummy”
“Meya faru baby? Whats wrong talk to me?”
Aka amsata

40 / 107