Author : Queenmerh Category : Complete Novels
duk abunnan da maya keyi bata taba tanka mata ba, bawai don tana tsoronta ba no sai don albarkacin kakarta, sai kuma maman ta data jaa mata warnings akan yan gidan, ko zasu daketa karta sake ta tanka.
Amma badan wannan ba yanda takeji idan taga maya kamar ta mata dan banzan duka, wai har maya ke kushe hallitar sabeeha, harda ce mata bata da fasali, da sabeeha ta tuna wannan saitayi dariya kawai ita kadai, wai mai nannane hanci ce zata ce mata bata da kyan gani.
Idan suka shiga general class kuwa, harara ce kawai ke shiga tsakaninta da mayar, ita da makarrabanta wasu yan mata su biyu da basa ji sosai suma kamarta, laila kuwa babu ruwan yarinya mai saukin kai.
End of month anne na sawa akaisu shopping su saya girly abubuwan da zasu buqata kamar irinsu pads ne, mayukansu,da dai abubuwan da baza a rasa ba sannan suje gyaran gashi da menicure.
Unexpectedly maya batayi expecting abunda anne tasa ayi ba wannan karan, hamad tasa ya kaisu gaba dayansu this time around harda yar aiki wato sabeeha kenan, ran maya idan yayi dubu ya gama baci kamar ta hadiye zuciya ta mutu don bakin ciki, da suka fito ta bangaje sabeeha yafi a kirga, jinta take a wuya kodan taga bata kulata ne oho
Hamad yaga abunda mayan tayi ma sabeeha, saidai baice mata komai ba don bayason raini kwata kwata ko kadan, saidai kuka yana mamakin halin sabeehar, sauqin kanta yayi yawa sosai ba kadan ba wallahi.
Haka ya kaisu shopping mall hardashi suka shiga this time around not like the other times da yake kaisu yayi wucewarshi idan ya gama ya daukosu, maya dataga laila na jiran sabeeha ta fito rai a bace ta jaa hannunta suka wuce ciki, sabeeha dake komarin gyaran takalminta daya tsinke, batayi tsammanin zai jirata ba, ashe yanadaga tsaye ya hade hannayenshi yana kallonta daga tsaye.
Saida tayi managing takalmin ta tururashi don silipas ne kafin ta fito, harta kafarta kasa ta ganshi gabanta ya duqa ya aje mata wasu crocs masu kyau dayake ajewa a motar, dagowa tayi ta kalleshi ya sauke mata murmushi daya karama fuskarshi kyau sosai ba kadan ba “change to this,”
Saurin sauke kanta kasa tayi saiwani murmushi ya kubce mata, tsugunnawa yayi ya zame nata takalman ya kakkabesu ya aje cikin motar ba tareda ya kyamaceta ba, kai saukin kanshi is on another levels, kawai sai bashida yawan dariya ne da sakewa da mutane shima.
Saka crocs din tayi sai ya dan mata yawa a siraran kafafunta saidai kuma ya mata kyau.
Rufe motar yayi ya zagayo yayi gaba ta bishi a baya.
Ciki suka shiga ya tsaya ko zaiga su laila,wayarshi ya zaro ya kira laila ta shaida mashi inda suke, suka karasa har wajen.
Maya ta jidi abubuwa sosai a trolly dinta kamar ba gobe, laila ma ta dan deba abunda zata buqata don batada qale qale kamar maya.
Kallon sabeeha yayi data tsaya kamar wata yar rakiya yace “get that trolly”
Inda ya nuna mata ta nufa ta jawo trolly din har inda yake ya dubeta da kyau kafin ya kauda kanshi yace “ki dauka abunda kikeso kema”
Zaro idanu tayi ta rasa me zata ce mashi, me zata buqata ita kuwa? “Bana buqatan komai”
Saida tayi magana ya sake juyowa ya kalleta da kyau, kafin ya matsa zuwaga attendant mata dake wajen ya nemi attention dinsu wajensu, wata mata na zuwa ya nemi ta zagaya da sabeeha wajen toiletries da mayukan mata duk wani abu da mace zata buqata.
“Kije”
Binta sabeeha tayi a baya suka dunga zage matar na tambayarta me take amfani dashi, amsar daya ce “babu,matar tayi mamaki sosai don kana ganin sabeehar kaga kalar hutu, da haka dai ta dunga mata recommending wasu abubuwan wasu ma sabeeha batace ta dauka ba take daukowa, duka duka ba wani abun arziki suka dauka ba don sabeehar taqi bata hadin kai, next round da suka zagayo sukayi clashing da maya dake fama daukan scrupa kala kala, dagowan da zatayi kuwa ta hango wannan attendant din da sabeeha a gefenta, “kambuu, yar masu wanke wanke an samu matsayi, har bunki ake a baya da trolly, mu yayan masu gida bamuyi yawo da attendant ba saike haihuwar wahala da asara? You are not even ashamed? Oh wow”
Kauda kai sabeeha tayi attendant dinnan kuwa saida taji wani irin rashin dadi wallahi, wannan ay cin fuska ne, da wulaqanci, wallahi da iata aka gayama wannan maganar saita ci uban yarinyar nan mai kama da aljanu, “malama idan baso kikeyi aikin ki ya tsaya daga yau ba let mw
Not see you near this thing” ta nuna sabeeha disgustingly, juyawa matar tayi rai a bace don a girme ta girmi yarinyar nan sosai da hauhuwar kauye tayi ma zata haifeta tass.
Matar na barin wajen sabeeha ta juya itama zata bar wajen, “ke har kin isa ki juya ba tare da izini na ba?”
Chak sabeeha ta tsaya tare da juyowa ta kalelta sama da kasa, wannan abun daya tokare mata a makoshi for over the days takeson amayarwa kuma wannan dama ce a wajenta tunda babu kowa a wajen.
“Malama zoko jaa wannan trolly din, amfaninki kenan”
“Idan nace bazanyi ba fa? Me zaki iya?”
Surprisingly maya ke kallonta, “ni yar wanke wanke ce fadi ki kara, saidai inaso ki sani baki fini da komai ba, yanda aka halicceki haka allah ya hallicni, banbancinmu daya ne, hankali da tunani don naga kina da karancin wannan”
Tana kaiwa nan ta wuce tabar maya speechless, yar aiki ce yau ke gaya mata magnagnau? Har tana ce mata batda hankali, lallai zata koyama yarinyar nan hankali sosai ma kuwa, she has the audacity to look into her eyes and say those kinda of words to her, karkuso kuga maya, rai a bace.
Sabeeha na futowa daga wajen ta doka tsaki, inda taga sun shigo tabi ta fuce daga wajen, cikin ikon allah ta iso inda motarsu take nan ta tsaya jiransu.
Bayan sun gama komai sun biya hamad dake wajen aski ya dawo cikin mall din, “ya hamad mun gama”
Kallonsu yayi ganin sabeeha bata tare dasu yace “ina fatima?”
Maya tace “wacece kuma fatima? Oh yar aikin nan?…”
Kauda idanunshi yayi akanta ya maidashi ga laila yace “kuje ina zuwa”
Futa sukayi shi kuma ya soma zagayen wajen, har allah ya hadashi da wannan attendant din, ya tambayeta sabeeha ta fada mashi kaf abunda ya faru dazun, yaji haushi sosai ba kadan ba saidai babu yanda ya uya da ita, halinta ne.
Nan yasa attendant din ta sake debo wasu abubuwan amfanin masu shegen kyau da tsada sake suke kula da harkokun kayayyakin da ake kawowa sunsan masu kyau sosai da tsada.
Komai fa attendant dinnan ta daukarma sabeeha, abubusan datasan zasu mata amfani sosai kuma zasu gyara ya, kama daga kan sabulan wanka, shower gell, set of makari products and more, pads ne, wipes ne, face cleanser, kai komai, tana gamawa yasa ta dauko mashi flat shoe masu kyau, taje ta dauko yayi payment sannan ya bata tip wajen 20k kyauta tayi mashi godiya sosai ya futo.
A cikin motar ya taddasu zaune, sabeeha na daga wajen bakin kofa ta tsaya tana kallon takalman daya bata dazu, tunda suka karaso uffan basuce mata ba, itama bata ce masu komai ba, maya kam sai faman cije yatsa takeyi.
Daga nan saloon ya kaisu bayan ya baka laila kashedin duk abunda akayi masu ayima sabeehar itama.
Hakan kuwa akayi, yanda aka gyara masu kai haka aka gyara nata, kai masha allah sabeeha badai gashi ba, irin blonde gashin nan ne da ita mai daukan ido, maya najin yanda ma’aikatan ke yaba gashinta da yanda yakeda curl sosao don sun kasa kitse mata shi, da an fara yake warwarewa, sai kitso daya da aka samu akayi mata irin weave dinnan sannan akayi masu manicure da pedicure.
Suna isowa gida sabeeha ta dauka takalmanta ta cire wanda ya bata ta mashi godiya, har zata bude kofar ya dakatar da ita don su maya sun fita already.
“Meysa kika fita daga cikin mall din daxu?”
“Ba komai” ta bashi amsa
“Don’t lie, it doesn’t suits you fa..ti..ma”
Saurin kallonshi tayi cikin idanunshi shima yana kallonta, tayi saurin cire nata tana wasa da yatsunta tace “kaina kemin ciwo banson hayaniya shiyasa na fito”
Jinjina kai
Kawai yayi sannan ya bude motar ya fito, booth ya sake bude ya dauko bagss dinta leda uku sannan ya rufe motar ya zagayo inda take yace, “maida wanchan takalmin kafarki”
Babu musu ta maida takalmin a kafarta sannan ya miqa mata ledojin ya rufe motar, “naki ne”
Yana fadin haka yayi gaba ya barta speechless, bayanshi tabi da kallo, kyakyawa ne ajin farko, so nice and sweert yet calm, bashida hayaniya.
Hadiye mamakinta tayi ta wuce ciki da ledar hannunta zuwa dakinsu.
Hadizq na kwance tana barci, wannan ya bata damar ajiyesu gefw sannan ta futo ta wuce sama.
Tana kokarin knocking saiga indo ta futo, “har kun dawo”
“Eh ina wuni” sabeeha ta gaisheta don kullum saita gaisheta, “lapiya lau sabeeha, zakiga hajiya ne”
“Eh zan mata godiya ne”
“Toh shigo bari nayi maki sallama da ita”
Ciki suka shiga sabeeha ta zauna a kasa kan carpet indo ta shiga, bata dade ba ta futo tace “ki shiga ciki”
Tashi sabeeha tayi ta shiga dakin da sallama daga nan bakin kofa ta duqa ta gaisheta,sannan
Ta mata godiya sosai da hidima, anne tace mata karta sake yi mata godiya daga yau.
Shuru ne ya biyo baya anne tace “kina gane karatun kuwa”
“Eh”
“Toh a dunga dagewa bansa wasa, banason shiririta, kiyi abundaya kaiki banda kawayen banza da samarin banza”
“Insha Allah” sabeeha ta amsata
Kafin ta mata sallama ta futo.
Koda ta sauko hadiza harta tashi ta bubude ledojin tana duba kayan, sabeeha ta gaisheta sannan ta wuce bathroom, tana fitowa hadiza tace “ke kika kwaso waennan abubuwan kuma su suka biya kudin?”
“Eh”
Tabe baki hadiza tayi ta ture ledar ta fuce daga dakin tace “arzikin ne ya maku yawa”
Saudii…
Bude idanu khaal ya sake yi don tabbatar da ba mafarki yakeba, kokarin tashi yayi zaune mutallib da taj suka taimaka mashi, har zuwa lokacin kallon taj yake daga sama har kasa da mamaki kwance akan fuskanshi sai kawai sukaga yana hawaye, hawaywn farin ciki.
“Taju…deen?Ka samu lafiya? “
Girgiza mashi kai taj yayi har zuwa lokacin yaqi bari su hada idanu sai sunne kanshi yake, kamo hannunshi khaal din ya sakeyi for the second time yace “ina fatima? Ina fatima tajudeen?”
Kallon juna mutallib da taj sukayi, jin ya sake tambayar sabeeha for the second time, ganin sun kasa bashi amsa yasashi cewa “tana lafiya dai ko? Basuyi mata komai ba ko?”
Mutallib yayi saurin cewa “tana lafiya khaal”
“Tana ina?”
Nanma dai shuru sukayi, sukabar taj cikin zullumi, taj yaji sauqi ya dawo hayyacinshi to ina sabeeh? Take yaji ya rasa nutsuwarshi, fatandai ba cutar da ita akayi ba innalillahi wa inna ilaiahi rajiun, yarinya amanar daya daukarma kanshi akanta, idan har wani abu ya sameta bayajin zai iya yafema kanshi.
“Ina!!!! Fatima!!”
Yanda yayi tambayar saida yasa gaban taj faduwa, ya dago ya kalli khaal “ta koma kasarsu”
Kallonshi sosai khaal keyi don yanason jin karin bayani, suda suke neman bayanai a wajen khaal sai ya zamani shike da answers da zai baka khaal din tukunna.
Kuma yayi mamaki tunda khaal ya farka ya kira sunanshi d next thing daya tambaya shine yarinyar nan.
“Ya akayi ta tafi kasarsu? Korarta sukayi? Basuyi mata komai ba dai? Ku fada min gaskia, yarinyar nan amana ce a wajena,nina kawota gidan nan na jefa rayuwarta cikin hadari kuka na kasa protecting dinta dakai”
Taj daya kasa rikewa yace “ni na koreta…”
Tunda ya fara magana khaal ke kallonshi, yana jawabin yanda ya kasa yarda da ita saboda ance mashi yar leken asiri ce, saida yakai full top khaal ya dubeshi idanunshi sunyi jaa sosai ranshi ya baci sosai yace “ka koreta? Baka saurareta ba? Kasan wacece ita kuwa a rayuwarka? Kasan irin sacrifice din datayi akanka? Kasan wahalar datasha akanka? Ta kusanceka lokacin da ake kyamatarka ? Ta kula dakai kamar yanda uwa zata kula da danta? Bata kyamaceka ba? Ta kula dakai dukda tasan rayuwarta zata shiga hadari at a young age ita ka kora? Saboda yan uwanka? Waenda basu taba kaunarka ba kuka bazasu taba kaunarka ba saboda suna ganin kaine silar mutuwar mahaifiyarsu? Ka koreta saboda su??”
Wani abu mai daci khaal ya hadiye ya runtse idanunshi kafin ya budesu, “kayi kuskure, a matsayinka na namiji har mata zasu juye maka tunaninka? Amma Banga laifinka ba, saidai banyi tsammanin zaka yarda da karyayayyakim da suka maka ba ba tare da kayi buncike ba”
Khaal na fadin haka ya saki hannun taj din don he’s so disappointed with him.
Wallahi taj ji yayi duniyar ta mashi nauyi, ya kasa cewa komai, sai miqewa kawai yayi ya futa daga wajen, tabbas yayi dana sani sosai da actiona dinshi, kauna da yardar dayayi ma hidaya ta rufe mashi ido sosai ba kadan ba, har ta sanya shi manta abubuwa da dama sai yanxu yake tunasu, lokacin da aka kawoshi gidan yana karamin hidaya bata taba treating dinshi right ba,hasalima itace wadda yafi tsoro cikinsu gaba daya, don da akwai lokacin data turashi a bene ya fado daga sama, saida ya kwana biyu baya cikin hayyacinsa, he one’s draw ta dalilinta, tace mashi abunta ya fadi a cikin pool ya shiga ya dauko, tana kallo ya shiga yana neman draining bata taimaka mashi ba har saida nunfashinsa ya tsaya chak, dakyar aka samu ya dawo hayyacinsa wannan dalilin yasa aka cire pool a gidan, bayan wannan ma, lokacin dayafi peanut ita kadaice tasan cewa he’s allergic to it kuma ranar da sukayi breakfast ta bashi yaci yayi affecting dinshi sosai, irin waennan wahalhalun ya shasu ba kadan ba, saidai dan rashin wayo da hankali yasa bai gani ba.
Wallahi saboda hidaya ya kusa lalacewa, achan london, saidai kuma allah da baya barin a zalunci bawansa baibarga taci galaba akanshi ba ya tsareshi ya kareshi kuma ya nutsardashi bai lalace ba.
Da mugun speed ya fuce daga hideout din, ya dade yana tukinda baima san inda yake nufa ba, da mugun speed yake tafiya kamar zai tashi sama, with a blink of eye yaga wata katuwar mota fara ta taho highway ta inda bai kamata ta biyo ba, wallahi saura kiris su gabsa ya ankare yayi saurin kaucewa da hanzari, harya buge wata bishiya dake gefe allah ya taimaka baiji ciwo ba saidai ya dan bige kanshi da dashboard, “ya subhanallah!” Ya furta ahankali yana mai dafe kanshi, dumm yaji kanshi nayin wata kara take memories din lokacin accident dinnan ya mashi flashing, yanda ya fito daga motarshi yana cikin driving har message din fadwa ya shugo wayarshi, harya bude yaji voice recording din data tura mashi, bai kaiga gama jin karshe ba kawai wata truck tayo kan motarshi, sauda motar tayi sama ta wuluwa sannan ta fado kasa,harta fara kamawa da wuta.
Abu daya ne ya tsaya mashi chakkkk abunda yaji cikin voice record din he vividly remembers maganar dake ciki.
“Yanxu ya zakiyi ki dashi tunda khaal ya sashi dawowa” fadwa ta tambayeta.
“He insited on dole saiya dawo ko? To he will regret dawowan shi”
“Hmm ukty..I’m sensing something terrible happening soon”
Dariya hidayar tayi saiga call ya shugo ta amsa tasa a speaker duk batasan fadwa tayi recording dinnan ba “madam everything is ready, target is approaching”
“Okay…, make-sure that bakuyi mistake ba, don’t leave a traces of evidence, inason ya zamana kamar accident ne kawai”
“Yes ma’am”
Wannan ne recording din da fadwa ta tura mashi, yana kokarin sake sauraron recording din don bai gane komai ba accident din ya afku.
Innalillahi wa inna ialaihi rajiun kawai yake furta, its a planned event not an accident? Daman anyi ne don a kasheshi? Why why meysa? Mey ya masu? Hidaya shi take son kashewa? Saboda me ??saboda dukiya? Saboda suna tunanin shine dalilin mutuwar mahaifiyarsu? Saboda mahaifinsu ya auri mahaifiyasa? Wadda baisan dadinta ba? Wadda bayajin zai iya tuna ya kamanninta yake? Wanda baiji dumin ta ba?baisan dadinta ba? Ina laifin iyayanshi ya zama nashi? Shi ya hada iyayenshi har aka haifeshi cikin wannan rayuwar? How is it his fault? Haifarshi akayi shima, Idan an bashi zabi bazaiso ya shigo ahalin gidan ba, bazaiso yayi rayuwa cikin kunci ba, bazaiso yayi rayuwa babu wani abu waishi kusanci da so da kauna ba, ya dade sosai yana innalillahi, he’s devastated.
Matar daya yarda da ita gaba daya rayuwarshi,matarda yake mata kallon kamar uwa, his mentor, matarda ya amince sa ita yayi respecting dinta fiye da kowa, wanda ya maida top priority dinshi? Itace ke kokarin ganin bayanshi? Ganin baya nunfashi a doran kasa? Dukdan saboda tsana? Hatred? Why? Baiyi deserving haka ba don bai tsaya mata a gabanta ba, baida kwadayin business dinsu, baida burin baqanta mata kwata kwata.
Yakai har wajen magrib a wajen yana tunani kala kala, gashi babu kowa a wajen don high way ne, dakyar ya tattara kuzarinshi ya fuddo da wayarshi ya kira mark sannan yayi instructing dinshi akan yanason yayi retrieving tsohon icloud dinshi, kuma yanason shi as soon as possible.
Yana gama wayar ya kira mutallib ya tambayeshi khaal, nan ya shaida mashi yanda khaal yaji zafi sosai gameda fatima,sai a lokacin mutallib ke shaida yanda how special fatima is, da yanda khaal ya kawota gidan a matsayin yar leken asiri, sannan ya shaida mashi yanda khaal din ya aura mashi ita, da wahalhalun datasha wajensu hidaya, wallahi maganganun nan ba karamin karya mashi zuciya yake ba, musamman idan ya tuna yanda ya dunga treating dinta.
“Tun bayan tafiyarka yaqi ya fada maka komai taj, mun tambayeshi ya bamu details akan komai yaki taj”
“Ba komai, ku barshi for now, i felt sorry for everything mutallib and im grateful for having you in my life, kana cikin mutanenda bazan taba mantawa daku ba har abada kuma bazan iya biyanku ba, you stood for me, nagode sosai”
Dariya mutallib yayi yace “karka godemin, ka godema khaal, shine mafi soyuwa a gareka kuma shine gatanta,”
Da haka sukayi sallama ya kashe wayar ya sauke ajiyar zuciya, this is a big battle for him, and he need to dive into it and make them pay ta hanyar dayasan itace suke tunanin bazai iya samu ba cikin ruwan sanyi babu wani tada wuya.
A nan yayi waya da few shareholders din kamfanin, ya shauda masu hidden identity dinshi wanda suka sani da huge investor dinsu, ba tare da wani bata