Advertisements
Chapter 63 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   63 / 107

186K to 189K   out of 320.4K words

fasa yinshi ba, dole ma ta nemoshi a duk inda yake saboda kar asirinta ya tonu.
Hidaya ko zatasan duk ya da tayi bata futo ba, batason kashe ta yanxu don saitaga ta zama miserable.
Wanda ya sauke barad ko ta gane mutallib,don ranar da tareeq yazo ya kawo masu hotunan sabeeha da mutallib da recordings din maganr su ta gane shine driver, shika tasa a nemoshi a duk inda yake.
Abdul basit da fadwa burinsu ya gama cika, sun tarwatsa wannan ahali, hidaya will rot in jail don an saka trial dinta, kotu zata yanke hukunci kawai base on buncike da akayi.
Kuma har zuwa lokacin babu wanda ya tsaya mata kuma batayi making any move ba.



Deeda hospital nigeria.
Yana tsaye a asibiti wayanshi yayi ringing har sau biyu baima sani ba, futowa yayi inda yasan babu hayaniya ya daga wayar.
Yana kaiwa kunnashi yayi sallama nanna ta amsa.
“Ina kaje ne taj? Hamad yace kun fita tare da anne”
Shuru yayi bayason yi mata karya kwata kwata saboda hankalinta zai iya tashi sosai idan taji zancen turmo din anne.
“Kayi shuru?”
“Munzo asibiti ne,?”
“Subhanallah waye babu lafiya? Anne ne?”
“No lafiya lau oummi, ki kwnatar da hankalinki,”
Sauke ajiyar zuciya tayi tace “yaushe zaku dawo”
“In an hour insha allah” ya bata amsa kafin suyi sallama.
Komawa yayi treatment room din da ake treating anne, traetment din na dauka awa biyu.
Ana gamawa suka wuce gida.

Shi da kanshi ya taimaka ma anne har zuwa bedrom dinta ta saka mashi albarka kafin ya sake futa.
Motanshi ya shiga tare da dialing number salim yana dagawa ya Shaida mashi ya tura masa lokacin din inda yake yana nan tafe? Yana turawa kuwa ya kunna motar ya futa.
Bai tsaya ko’ina ba sai agency din daya fada mashi, yana zuwa ya fada masu abunda yake buqata.

Da sallam laila ta shugo part din anne hannunta rike da tray na abunci, maya dake zaune tana latsa waya ta dira kafa daya kan daya tana mata kallo daya ta dauke idanunta itama ta kauda kanta.
Hanyar kitcwhn ta nufa tayi sallama tana ganin rabi tace “sannu da aiki”
“Yauwa laila, inq wuni ya karatu”
“Alhamdulillah, daman mami ce tace na kawo lunch din uncle taj, tun dazu aka gama”
Karba rabi tayi tace “toh bari akai bangaren nanna”
Bilki dake goge goge tayi saurin cewa “anty rabi kawo nakai saman”
Wani irin kallo rabi ta mata ba tun yanxu ba ta lura da shirman da sukeyi ita da basira dayar yar aikin, idan an turasu gyaran part dinshi har rige rigen zuwa sukeyi, “wazai maki aikin? Ko nace maki bazan iya kaiwa bane dakaina”
Kama kanta tayi ta cigaba da goge gogen basu lura da shugowar maya ba kwata data dade da tsayuwa a wajen.
Laila ta juya ta futa avunta, maya ta dauka zata mata magana sai taga akasin haka, itama juyawa tayi har zata futa ta dakata “abuncin waye ta kawo wannan?”
“Na kawunku ne,“
Smriking maya tayi tace “kawo”
Kallonta tayi da mamaki kafin ta bata tray din ta futa dashi.
A maimakon takai sama part din anne saita wuce part dinshi, ba tun yanxu ba take son zuwa amma bata samu dalili ba, kowacce smart door ta gidan anyi setting pin din shiga 1234 wannan yasa batasha wahalar budewa ba tasa kai ciki.
Tundaga sitting room take jin kamshinsa mai shegen dadi, ko’ina fess fess kamar babu wanda ke rayuwa a ciki, well organised.
Aje tray din tayi a dining kafin ta fara zagaye ko’ina na cikin apartment din har zuwa bedroom dinshi.
Batayi tunanin yana nan ko baya nan ba ta bude kofar kai tsaye.

Parking yayi bai kashe motar ba karar ac na tashi, bude wayanshi yayi ya shiga pictures din sabeeha yana scrolling, duk bunciken da yakeyi ya kasa gano inda take, baisan nigeria komai namu sai a hankali ba yanxu haka qila illegally aka shigar da ita kamfanin da suka dauketa suka kaita kasar waje aiki, duk wani reasonable waje yaje manya manyan agencies daban daban amma babu record dinta ko mai kama da ita ma.
Jiki a mace ya kashe motar tare da futowa, a gajiye yake gaba daya yau ko lunch bai yiba, suna dawowa daga asibiti ya futa.
Part dinshi ya wuce direct yana bude kofar yasa kai ciki, bai tsaya ko’ina ba sai sama ya sanya hannunshi kan door knob yaji kofar a bude.
Da mamaki ya karasa bude kofar,ya shiga daga ciki sannan yabi ko’ina da kallo.
Wayanshi da key din motarshi ya aje kan bedside kafin ya nufi walk-in closet.
“Excuse me!!”
Cikin sauri ta juyo da turaren shi a hannunta saura qiris ma ya fadi, yanda yake kallonta haka take kallonsa, murmushi ta kirkiro tare da aje turaren nashi tace “good afternoon uncle taj, I’m sorry for encroaching without your consent, daman na kawo maka lunch ne”
Hade ranshi yayi lokaci guda, bayason ana invading privacy dinshi, ba kowa yakeson yana taba mashi abunda ya shafesa ba.

Ko gyaran part dinshi da ake zuwa yi yana daurewa ne kawai amma ba kowa yakeson yana ta’ammali dashi ba.

“Anything else? Idan babu Zaki iya futa” ya fada kai tsaye, yanda yayı magana kamar yana cikin bacin rai,
Juyawa tayi zata futa jiki a mace kafin ta bude kofar ya dakatar da ita “i don’t appreciate invading of my privacy okay?”
“Girgiza kai tayi cikin ladabi kamar ba maya ba ta futa.

Tana futa ya sauke ajiyar zuciya tare da furzar da iska, ya rasa me ya bata mashi rai lokaci guda.




✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 98
After 2 weeks..
Cikin sati biyun nan taj bai samu sukuni ba, duk wani registered agencies da ake kai yan aiki saida salim ya nemo masa sukaje neman ta, amma kwata kwata babu mai kamaninta a record dinsu, dukda haka baiyi giving up ba.
Shidai salim baisan dalilinsa na neman wadda yake nema ba don bai fada mashi ba amma ganin yanda ya dage sosai yasan cewa yarinyar is very important to him.
Amma me zaisa mai kudi kamarshi yana neman yar aiki? Anan nigeria? Ya tuna da lokacij daya taba tambayarshi meya kawoshi Nigeria ya shaida mashi its something personally important.
Fada mashi da babanshi yayi cewa taj din is someone that is very important to their business yasashi dagewa don neman yarinyar.


Yau ne last day of the semester, wanda ya kasance ranar da zasu gama last paper na exams dinsu.
Sabeeha tunda suka fara exams ta kebanci kanta da komai, da duk wani abu da zai jawo mata fitina da maya.
Tunda taga kiri kiri mayar ta tsaneta don tundaga lokacin datayi mata sharrin sata ta gane binta take da sharrin.
abun da sabeeha bata taba expecting ba shine anne data yarda cewa ba itace tayi satan ba, dukda bata fadi cewa maya ce tayi mata sharrin ba, da farko dataga reaction din maman maya da yanda ta yarda lokaci guda kan cewa itace tayi sata saiyata jin kowa ma yarda da hakan zaiyi, saitaga akasin haka
Wannan yasa ta kudurci duk avubda zai faru bazata taba bari tayi abun da zaisa anne ta zama disappointed da ita ba.

Misalin wajen karfe biyar na yamma hamad yazo ya daukesu daga school, gaba dayansu daga yanda suka fito zaka gane wxams din ta jijiga su, hamad ya tambayesu how was the exam laila ce kawia ta iya amsa shi.
Yana tuki ya juyo ya kalli sabeeha ganin yanda ta rakube tayi shuru, ba tun yanxu ba ya lura gaba daya ta chanza, yanda take ada yanxu dukta daina, abunda ke hadashi da ita gaisuwa ne kawai daga haka bata sake cewa komai, she’s trying to be invisible a gaban su gaba dayansu, daman don hamad na tsaya mata ne yasa maya ke jin haushi ita da ba kowan kowa ba.
Wannan abu na damunshi sosai ta dawo yanda ya fara saninta, babu walwala babu fara’a.
“Fatima how was your exam?”
Ya jefo mata tambaya,shuru bahu response saida ya sake cewa “fatimaa!”
Firgigi ta dawo daga dogon tunanin data fada, “naam”
“How was your exams?”
“Alhamdulillah” tana fadin haka ta maida kanta ga glass window din mota ta cigaba da tunanin datakeyi.


…….
Da daddare rabi ta shigo part din anne da sallama ta gaida anne kafin ta soma mata bayani.
“Hajiya daman bilki ce tace kawunta ya kira zata koma kauyensu don an saka ranar bikinta nanda sati biyu”
“Toh Masha Allah shine basu fada da wuri ba”
“Eh wai itama batasan an badata bane, kisan auran kauye basa neman shawraar yayan tun suna kananu suke bada auren su” rabi ta bata amsa cikin ladabi.
“Toh kice mata ta nace ta kira kawun nata yazo cikin satin nan kafin ta koma, karsu mata komai na kayan daki na dauki nauyin wannan”
Cikin murna rabi tace “toh allah ya saka da alkahiri hajiya allah ya buda”
Ta amsa da ameen.

Rabi na barin wajen anne ta sami bilki ta fada mata komai, a take ko ta kira kawunta ta shaida mashi komai.

Washe gari da safe kowa ya hallara kan dining, anne, nanna, maya sai laila data kwana a part din nasu don sun shirya yanxu ita da mutuniyar tata sai kuma hamad da shugowanshi kenan.

Karasowar taj yasa duk suka maida hankalinsu gareshi, maya da laila suka gaishesa, hamad ma haka shi kuma ya gaisheda nanna da anne kafin su fara karyawa.
Hira sukey jefi jefi kowa ya maida hankalinsa ga abuncin da yakeci banda maya data kureshi da ido, laila tana ankare da ita don ba tun yanxu ba ta lura da hakan.
Shine ma ya fara tashi ya futa bayan ya gama saboda kiranda salim ke mashi.
Nanna ga tambayeshi harya gana yace mata eh zai dan futa ne, bata tambayeshi ina ba saboda yanxu kam ay ya san gari kuma yanada nashi privacy din avubuwa shiyasa bata tambayehsi ba ya futa.
Yana barin wajen maya ta sauke ajiyar zuciya, lailanta kalleta da mamaki.


Bayan sun gama dinner laila da maya na zaune dakin maya laila ta kaleta tace “wai kallon nan da kikema uncle taj na menene?”
Kallonta maya tayi tace “is there a problem inna kalleshi?”
Dariya laila tayi tace “maya are you crushing on uncle taj? If you are kima ajeshi a gefe, he definitely has someone”
Rai a bace maya ta kalleta laila na ganin haka tasan cewa maya has feelings for him.
“Shi yace maki he has someone??”
“Ke yanxu kina ganin yanda ya hadu ya gaji da haduwa, gashi mai kudi sosai kuma daga saudi yake saiki yarda idan akace maki bashida wadda yakeso, balarabiya yar kasarsu?infact banajin akwai yar nigeria da zata iya zama on his league”
Cije lebe maya tayi har yana fashewa kadan jini ya futo lokaci guda yanayinta ya sauya, tace “karya ne wallahi, karya kikeyi banza dallah zoki futa karki bata min rai”

Yanda take magana kamar zata hau kan laila, laila tayi saurin cewa “it looks like ba crushing kadai kike ba maya, badai son uncle taj kike ba? Don’t start dreaming what’s impossible don wallahi yafi karfinki”
Wannan magana da laila tayi mata kamar ta chaka mata wuqa a wuya haka takeji, rai a bace ta kalleta tace “you wanna bet on him?”
Laila najin haka tace “uncle taj din? Bafa yaro bane”
“You wanna bet on him or not? Don ni zan nuna maki cewa idan har inason abu saina sameshi no matter what, karkiga wai yana da kudi kuma halfcast ne wallahi i will make him fall for me, you wanna bet??”

Dariya sosai laila ta tunda yi tana kallonta tace “okay..lets see”
….
Bayan futarshi bai tsaya ko’ina ba sai inda zasu hadu da salim, daga nan suka wuce inda zasuje.
Tun a mota salim ya soma mashi bayanin kananun agency din da yanda suke operating wajen, kuma a gaskia illegally suke shigar da mutane kasar waje don gaskia gomnati batasan da zamansu ba.
A tare suka shiga wajen, irin local agency ne haka duk wani hanya da akeyi ta cuku cuku sunayinta, duk kasar da kake son zuwa don har visa sunayi ma.
Yara ko kauye kauye suke zuwa daukansu ana masu training akaisu wata kasar don aikatau.

Da farko masu kula da wajen kin basu hadin kai sukayi saida salim ya basu maqudan kudade tukunna kafin su kaisu wajen ogansu.
Suna zuwa ba tare da wani bata lokaci ba suka mashi bayanı, kudi babu abunda baya saka mutun yi, koda suka bada sunanta da hotonta da kuma inda tayi aikatau da shekarar, a take mutumin yasa yaranshi suka fara bunciken yaran da suka tura saudiyya shekara biyu da suka wuce.
An samu fatima’s da yawa saidai kwata kwata babu mai kama da ita daga ciki, su da sukaga hoton sabeehar ma daya bayar sun dauka ko batan hanya yayi, suda suke kwaso yan qauye, kowacce yarinya idan zasu turata saisun dauki hotonta, information din iyayenta, gudun samun matsala.
Har zasu bar wajen wani tunani yazo mashi, tunda yake nemanta da fatima yake amfani bai taba kawowa ko ba sunan take amfani dashi ba sai yanxu da abun yayi clicking a mind dinshi, ya dubi salim yace su nemi idan akwi mai suna sabeeha.
Take salim ya fada masu suka fara dubawa, suna daga zaune yaron dake buncikowa ya shugo da file din mutun daya da aka samu da irin sunan, baisha wahalar samu ba saboda sunan is unique.
Da aka kawo file din saida gaban taj ya fadi, har sauri yake ya bude don ya tabbatar da ita dince, yana tabbatar da ita dince ya sauke wata ajiyar zuciya, duk yanda kamanninta ya banbanta da hoton daya nuna masu bai hana shi ganeta ba, lokacin gaba dayanta babu cimar kirki a tattare da ita tayi wani irin baqi sosai, gashi dukda ta rufe bakinta saida gatson nan ya futo.
“She’s the one” ya fada beneath his breath, ya dubi salim yace su fada mashi inda zasu sameta yanxu yanxun nan, zai basu ko nawa ne yanason su fada mashi komai game da ita.
Salim ya fada masu tare da ajiye masu kudade dayawa a gabansu.

Ogan dayaga kudade take yasa cikin yaronsa su nemo mashi yar wani gari ce, kuma ta dalilin waye aka kawota aikatau, masu daukosu sunada yawa don kowanne gari akwai agent dinsu.
“Wannan yarinyar oga jamilu ne ya kawota”
“Wani jamilun?” Ogan ya tambaya.
“Jamilun dake dutsen habuja, yar dan uwansa ce”
Salim ne ya fasaara masa abunda sukace, sannan ya buqaci sanin inda zasuga jamilu, ogan yace ay agent dinsu ne bari ma
Ya kira sa.
Yana kiran jamilu wajen saunuku bai dauka ba, taj ya buqaci address din jamilun ogan give su dawo zaisa jamilu yazo har office dunshi.


Taj baiso haka ba dan ya matsu sosai, yanajin kamar bazai iya jura har zuwa gobe ba.

Suna barin wajen daya daga cikin agent din yayi saurin kiran jamilu, aiko yayi saurin dauka, daman jiran kiransa yake tundaya kirashi yace mashi karya amsa kiran oga, akwai matsala.

yana dauka ya fada mashi komai sannan ya shaida mashi yanda suka sakarma oga maqudan kudi don neman yarinyar dakyar inba matsala aka samu ba.
Daman gaba dayansu baki daya agent din harma da ogannin shiyasa suke tsaka tsantsan don business dinsu illegal ne.

Da farko jamilu shi harya mance da wata sabeeha daya kawo agency din saidaga baya ya tunata yar hadiza kawar jamila matarshi, shifa gaba daya ya tsorata sosai jin ance masu kudi ne suka zo nemanta kuma harda balarabe saiyayi tunanin ko kisan kai tayi achan kasar ne ba a gano gaskia ba saida aka maidota nigeria,sai yanxu ake nemanta gashi ya shugarda sunansa a matsayin mariqinta.

Yana tsaka da buga bugarsa ya koma gida ya hau kan jamila da bala’i, “mun shiga uku jamila, yarinyar nan kisan kai tayi ake nemanta, ki kira uwarta wallahi tallahi babu ruwanmu, ke kikace mu taimaka masu a turata aikatau, yanxu danace ni marikinta ne idan ba a ganta ba aka kamani fa?”
Kokarin kwantar mashi da hankali jamila tayi harda kwada mata mari, “me gida dan allah ka kwantar da hankalinka”


“Ina zan iya kwnatar da hankalina shin kinma san inda suke? Wallahi jamila idan kika sani matsala igiyar aurenki ce zata tsinke, haka kikasani muka aurar da ba tare da sanin uwar tata ba, muka cinye kudin da aka bamu yanxu idan wani tsoho ne fa aka aura mata gidan aikin nata ta kasheshi ta gudo ba a sani ba sai yanxu? Shin kinma san inda uwar tata take kuwa? Idan hadiza ta gudu fa?”
Jamila na hawaye ta kalli mijin nata tace “wallahi mai gida zan nemota bazanma fada mata me ake ciki ba sainaje naga inda take”
“Toh wallahi tallahi kiyi hanzarin zuwgobe goben nan ki shaida mata yauwa ehe”
Tana fadin haka ya fuce.
Jamila jiki na bari ta soma dialing layin hadiza tana dauka ta soma magana “hadiza akwai matsala..”
“Wace iriyar matsala jamila”
“Ki tura min adireshin ki gobe zanzo muyi magana”
Hankali tashe hadiza tace “ki bari ni zanzo goben”
“Ah ah tunda nace maki ki bari zanzo kawai”
Da haka sukayi sallama.

Tunda taj ya koma gida gaba daya yaji ya kasa sukuni, ya rasa mai zaiji aranshi dadi ko rashinsa, zai iya fuskantarta kuwa? Da wani ido zai iya ganinta? Gaba daya abun ya addabeshi ya kasa cin komai.
Misalin wajen karfe tara na dare nanna ta kirashi ganin ko dinner baizo yayi ba tunda ya fita da safe, daga yanda yake amsata ta gane kamar yana cikin damuwa, ta tambayeshi ko baya jin dadi ya shiada mata yayi loosing appetite ne kawai and yayi dinner tare da abokinsa kafin ya dawo gida.
Hankalinta bai kwanta ba ta sashi yazo part dinta.
Dole ya shirya ya wuce main part, tunda ya shugo yakejin sautin kwanuka daga wajen dining da Alamu kamar tattara wajen akeyi, sai maganganu dake fitowa daga wajen,bai kalli wajenba ya tunkari hanyar stairs yana dora kafanshi kan stairs din farko ya tsaya chak

“Subhanallahi Ya akayi ya fashe?” Rabi data tunkaro wajen dining din tayi interrupting dinsu ,

maya data matsa gefe ta kalli rabi tace “ya kike kallona, ga wadda ta fasa nan saboda tana baqin cikin masu gida, tana bakin cikin ganin munaci da luxury plates bata taba ci akan irin plate dinba bari ta fasa dan mugun hali”
Sabeeha da ranta ya gama baci ga baqaqen maganganun data gama gaya mata ta watsa mata juice a jiki da gangan dukdan saboda ta buqaci a dafo mata indomie ta dafo sau uku tana cewa baiyi dadi ba sai an sake shine sabeehar tace taje ta dafo yanda zai mata tana shirin barin inda take ta watso mata plate din da indomie din a

63 / 107