Advertisements
Chapter 7 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 107

18K to 21K   out of 320.4K words

bayanta,cikin natsuwa da muryarshi mai daukan hankali yace “how can i forget you my fav aunt,I’m sorry for making you worried “
Kallonshi ammu tayi hawayen farin ciki na sauka kan fuskanta tace “tell me meke damunka yanxu? What are feeling now? Are you okay?babu abunda ke damunka?”
“I’m fine ammu”

Fadwa datayi tsuru ta kasa motsawa saida tareeq ya tabo ta ta kalli taj din ta soma yaqe, tace “alhamdulillah! How are you feeling now? We were so worried about you,”
Dagowa yayi yanayin fuskanshi lokaci guda ya sauya ganinta da yayi kawai kamar baya son magana yace, “I’m okay now!”
Kauda idonta tayi ganin irin kallon daya mata,sai yanxu ta kara tabbatar da yayi recovering, idan zaima kowa magana ko zai amsa mutun haka yake banda hidaya, shiyasa suke mashi kallon mai ji dakai da nuna isa dukda qani ne a wajensu, kwarjini yakema kowa.

Tareeq ma baiyi shuru ba hardashi a masu nuna murnar samun lafiyar tashi a fili.

Shidai taj haka yabisu don harga allah baisan akan me suke magana ba kawai dai ya bisu a haka ne, kanshi fal yake da neman amsoshin tambayoyin da ke ranshi.

Ammu ce ta sake kallonshi har lokacin bata bar mamakin ganin ya samu sauqi ba compare to last time datazo lokacin mutuwar khaal, lokaci guda ya sauya kamar bashi ba, da yana daga tsaye sai ya dunga dariya yana wasu abubuwa kamar na yara, lokaci guda kuka ya dawo asalin taj din da suka sani shekara da shekru,sai kawia ta sake fashewa da hawaye tunaw ada yanda khaal ya damu dashi sosai, kusan kullum saiya kirata kafin ya rasu, bashida magana saita taj, ita ce shaidar aon da khaal kema taj, ya shiga damuwa sosai lokacin da taj din ya samu amnesia ya manta komai ya manta koshi waye ma gaba daya.
“How i wish khaal na tare damu, he will be so happy to see your recovery”
Tunda ta fara magana taj ke kallonta, bai gane inda maganar tata ta dosa ba, Hidaya kuwa na jin ammu na shirin baro mata aiki ba zato ba tsammani tayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa “mu barshi ya huta tukunna, daga baya sai muyi maganar”
“Kaje ka huta” hidaya ta umarceshi.

Hanyar stair ya nufa cikin natsuwa majestically suka bishi da kallo, har yakai sama ya jiyo muryar ammu na magana, “jeki taimaka mashi mana”
Ta kalli sabeeha dake tsaye , hidaya ce tayi saurin dakatar da ita tace “ammu, please mu barshi, he’s having a tough time now, yana buqatar time shi kadai, and beside doctor yace kar a dunga damunsa”

Kallon hidayar ammu tayi sai kawai ta kauda kanta gefe ta wuce part dinta da take sauka nan kasa kusa dana su afiya, haushinta takeji sosai tun lokacin mutuwar khaal na qin protecting iyalan khaal din datayi lokacin da aka kwace property dinshi da yanda tayi outcasting dinshi harda press conference dinnan datayi, wannan abun ya tsaya mata arai, wannan yana daya daga cikin abunda yasa ammu taji akwai matsala kuma akwai avunda ke faruwa a gidan wanda bata sani ba kuma khaal bai taba gaya mata ba.

Ammu na wucewa su fadwa ma suka bar parlorn ya rage daga sabeeha sai hidaya, kallon sabeeha hidaya tayi yanayin fuskanta ya sauya sosai tace “as for you, as you can see baisan koke wacece ba, he doesn’t remember who you are cause you’re not important, koda wasa let me not see you around him not a single word from you”
Takowa tayi inda sabeehar ke tsaye hidaya tayi kafin ta kure ta da idanu fuskar nan babu digon imani akai tace “its not like he will be happy to have you as a wife, you are nothing but his caregiver, sannan karkiyi tuannin bansan yanda kika shugo gidannan ba a matsayin yar leken asiri, korar daga gidannan shine avu mafi sauqi, idan kinason na barki ki zauna a gidan nan you have to do what ever i said to you, inba haka ba i will make your life miserable, let me give you a sounding warning,not a single word from you, koda wasa naga kin rabe shi, I’m going to do my worst”
Shuru sabeeha tayi saida ta gama sauraronta tass, gabanta na mugun bugu, haka ta dake ta bude bakinta tana kallon hidayar cikin idanu babu tsoro ko fargabarta ko digo tace “kina tsoron karna fada mashi rayuwar da yayi a gidan nan lokacin da baya cikin hayyacinshi? ki kwantar da hankalinki, bazan fada mashi komai ba, saidai inason ki sani allah baya barci yana kallon duk abunda ke faruwa, yanda ya dawo hayyacinshi lokaci guda alokacin da babu wanda yayi tsammanin haka, a sannu a hankali zai tuna komai, its just a matter of time duk karyar da zaki fada mashi bazatayi tasiri ba saboda karya fure take bata yaya,i dont care if ya karbeni a matsayin matarsa, all i know is that I’m his wife and no one can change that”
Tana kaiwa nan tabar inda hidayar ke tsaye ta nufi part din data taba zama a ciki, lokacin sa jamid ya kaita, daman ba tun yanxu ba take shanye duk rashin mutuncin da hidaya keyi, haka kawai taji lokaci guda wani confidence yazo mata, daman tana threatening dinta da taj dinne, tsoron kartayi mashi wani abu yasa take yin shuru bata cewa komai kuma bata iya tunkararta, tundaga ranar da mutallib ya fada mata cewa hidaya ce sanadin accident din taj da abubuwan data dunga yi donta cutar dashi da kwayar data dunga dura mashi wadda ta kusa illatashi tundaga ranar ta daina jin tsoranta gaba daya kuma tayi allawarin saitayi protecting dinshi, tsoron hidayar babu abunda zai haifar mata saidai yayi ta bata damar yin abunda taga dama, yanxu kuwa data tabbatar ya samu lafiya batajin hidayar zata iya yin wani abun,ada datayi ma don taga bashi cikin hayyacinshi ne yanxu kuwa abunda take mai hankali bazai dauka ba, ko kusa ma bazata iya kokarin citar dashi ba ayanxu.

Tunda ta fara magana har yakai aya har tabar wajen hidaya bata gama dawowa daidai ba mamaki ya gama cikata, Ai kamar ta bugama hidaya guduma akai Haka taji, Saqe tayi tama kasa yin komai, bata taba expecting haka daga wajen sabeehar ba…


***
Bangaren taj jiki a mace ya shugo part dinshi yabi ko’ina da kallo, komai na part din nashi ya sauya, kamar anyi refurnishing komai, komai looks weird to him, ga kanshi sai wani tsannain ciwo yake mashi sosai, bayason tunanin komai don da zarar ya fara tunanin yakeji kanshi na sarawa.

Abund aya lura dashi shine, duk yanda akayi wani abu ya faru dashi, ko yayi loosing memory dinshi ko kuma he was in coma, definitely akwai abund aya sameshi, don babu yanda za ayi ace rana daya kawai ya bude idanunshi ya ganshi a 2023, how is that possible, he can recall is bayan ya dawo daga london, ko sati gida baiyi ba koma menene ya faru dashi.
Da kyar ya lalaba kanshi ya wuce bedroom dinsa yanajin wani irin zafia ranshi ya rasa dalilin, dakin ya shige nan ma an sauya komai, duk wasu abubuwan shi na amfani babu.
Idnaunshi ne ya sauka kan gadonshi, kamar mai son tuna wani chan kuma ya kauda idanunshi ya sauke Sigh of relief gaba daya jikinshi ciwo yake mashi babu abunda yake nema sai shower, kai tsaye ya nufi kofar bathroom dinshi ya bude, kallon bathroom din yayi har idnaunshi ya sauka kan towels din dake rataye guda biyu, yellow da white, juyawan da zaiyi idanunshi ya sauka kan panties dake hange akan hangers, yayi mamaki sosai ganin panties din saiya fara tunanin kodai wani yayi mashi amfani da part dinshi? To ko hes mistaken ba nan ne part dinshi ba? Ko anyi re-arranging gidan ne?” Tambayoyin daya dunga ma kanshi kenan.
Basar da zancen yayi ya soma rage kayan jikinshi, farar fatarshi ta bayyana sosai, kallon kanshi ya dunga yi ta mirror, ya rame sosai, he feels so light, sai yake ganin kanshi kamar bashi ba.
Ya dade sosai a bathroom yayi wanka kafin ya fito daure da towel a kugunshi, kasa dauke idanuna nayi akanshi, gaba daya ya sauya kamar bashi ba, lallai hankali ke gani badai idanu ba, yanxu da hankalishi ya dawo jikinshi ya koma mutum completely.


closet room ya nufa yana shiga ya bude closet din,gaba daya babu kayanshi ko digo daya, sai set of kaya ne farare a jere a ciki sai kuma kayan mata daya gani daga gefe a Jere fess fess sai kamshi suke mai dadin gaske.
Mamaki ya dunga yi har zuwa lokacin, tsuka kawai yayi ya rufe closet din kawai ya futo ya wuce bedroom din ya kwanta….




✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 61

UPDATE!!!
Jiki a mace sabeeha ta shiga dakin ta na qasa, yana nan yanda yake babu abunda ya sauya fes fess, bin ko'ina ta soma yi da kallon ta tuna tarin abubuwa da dama, kamar yau akayi, ranar da suka tuhumeta da sata ne ya fado mata arai, badan jamid ba da tuni sun wulaqantata, allah kdai yasan abunda hidaya zatayi mata badan jamid ya taimaketa ba a wajen, take tausayinsa ya mamaye zuciyarta, bawan allah, yanxu da zaiji labarin taj ya samu sauqi tasan ba karamin dadi zaiji ba, musamman khaal,
''ya allah ka gafartawa wannan bawa naka, allah sarki, nasan da zaiga rana irin ta yau sai yafi kowa farin ciki, harya mutu bashida burin daya wuce yaga didi ya samu sauqi'' tana karashewa ta fashe da kuka, kuka sosai sabeeha ta dunga yi, harga allah deep down taji dadi sosai ganin taj din ya warke, tashin hankalinta daya yanxu data lura dukda ya dawo hayyacinci bai tuna abubuwan da suka faru ba lokacin da yake rashin lafiyar kamarma baisan meya faru dashi ba watannin da suka wuce, wannan yasa ta daura damarar duk yanda zatayi saitayi don ta taimaka mashi harya gano gaskia, threat din hidaya bazaisa tayi qasa a gwiwa ba, indai tana matsayin matarshi protecting dinshi yanxu ta fara ma.
kwana tayi tana salloli tare da godiya ga allah sai wuraren bayan sallar asuba ta samu ta kwanta.

shima taj din sai wuraren karfe biyu ya farka na dare da matsanancin ciwon kai,gaba daya sai yaji dakin ya mashi fadi sosai, a jikinshi yanajin kamar something is missing wanda ya kasa gano ko menene, kwata kwata baima san time din lokacin ba saboda babu waya a kusa dashi, har zuwa lokacin towel ne a kugunshi, miqewa kawai yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala bayan ya idar ya kafama fuskarshi idanu, yana tambayar kanshi how did he loose so much weight haka, wani irin rashin lafiya yayi haka?, rashin amsar tambayoyinshi yasa yabar zancen a zuciyarshi kawai ya fito ya wuce closet room, cikin riga da wandunan daya gani fararen nan ya dauka daya daga ciki ya saka sannan ya futo ya wuce bedroom din ya hau kan carpet ya tada kabbara.
tunda ya tada kabbbar na natsu ina sauraron qira'arshi, lafazinsa akwai dadin sauraron cikin kamala da natsuwa, ya dade sosai yana sallolin yana rokon allah.
Yana idarwa kamar da wasa yarinyar nan daya fara gani dazu ta fado mashi arai, yanda take mashi magana da yanda take kamo fuskarshi kamar wani sa'anta, shi mai irin yanayinta ma bai taba gani ba gaba daya rayuwarshi, balle kuma fuskarta, curiosity din da yake ciki yasa komai ya soma bashi haushi haka kawai ranshi ya fara bashi.

Amnesia memory loss-mutun na samun amnesia ta hanyoyi daban daban, daya daga ciki shine accident din daya jawo buguwa akai wanda hakan ke affecting ma'ajiyar kwakwalwa, inda mutun ke manta abubuwan daya faru a cikin rayuwarsa na yan lokaci, wasu yakan zame masu har abada basa iya tunawa da rayuwar su a baya saidai su dasa wata, wannan amnesia din yana janyowa wasu su zamto sun manta rayuwarsu daga lokacin da suka girma sai ya zamana sun dawo kamar kananun yara masu koyon abubuwa (dissociative amnesia), wasu daga cikin mutane idan suka warke lokaci guda suke tunawa da komai da wasu kuwa basa iya tunawa kwata kwata shekarun da sukayi rashin lafiyar ya tafi kenan, wasu kuwa sukan tuna ahankali ahankali har su gano irin rayuwar da sukayi daga baya,wannan ce lalurar da taj ya tsinci kanshi a ciki, ayanxu daya dawo hayyacinshi gaba daya ya mance da komai,rayuwar da yayi shekara guda data wuce, sabeeha ta shigo rayuwarshi a daidai lokacin da yake fama da amnesia shiyasa ta kasance ita kadaice bai gane ba kuma bashi da memory dinta gaba daya…. 

washe gari ta kasance saturday, kowa da irin kwanan da yayi daren jiya, wasu sunyi shi da farin ciki wasu kuwa sunyishi da bakin ciki, musamman hidaya data kasa zaune ta kasa tsaye, ko rintsawa batayi ba, abubuwa da dama sun mata yawa kamar zatayi hauka, jamid dai tunda ta shigo dakin bai bude idanunshi bama balle ya kalleta, saidai ya lura she looks so restless, ga wayoyin daketa faman shugowa wayarta, karshe ma dai fucewa tayi daga dakin nasu ta wuce study room dinsu, bai sake ganinta ba saida safe lokacin har nurse din dake kula dashi tazo.
Bangaren su fadwa cikin tashin hankali sukayi shi don ba karamin cin mutunci tayi ma tareeq ba, saida ta sakashi a mazauninshi ta saita mai hankali tukunna ta nuna mashi idan ya sake abunda yayi jiya koda makamancinshi ne saita wulakantashi ta koreshi, tuni ya dawo hayyacinshi, haka ya kwana yana lallabata, bangaren fadwa bakin ciki da takaici ne yasa ta sauke duk wata masifa akan tareeq din, hankalinta ba a kwance yake ba kwata kwata saboda dawowar taj din, tana hango tsantsar tsanarta a idanunshi wanda ta tabbatar ya tuna abunda ya faru dashi da ita bayan ya dawo, she can see tsantsar qiyayyar da yake mata a idanunshi, kiyayyarsa bazaisa ta sauya ra'ayinta akanshi ba da yanda takeji game dashi.

ammu ma kwana tayi da zancen da kunenta ya jiyo mata lokacin da sabeeha da hidaya ke magana, babu abunda take sai nazarin maganganun sabeeha data fada ma hidayar, sai ayanxu ta kara tabbatar da akwai magana a kasa kuma ta kudirci koma menene saita bunciki alamarin don ta gano gaskia tsakanin hidayar da sabeehar, harga allah bawai tana son sabeeha ba saboda sufa larabawa daga nasu sai nasu basa son bare kwata kwata ita kuwa sabeeha tasan bare ce dukda khaal yayi kokarin convincing dinta wajen cewa sabeeha is the best decision for taj kuma yarinyar is special don haka kawai take kauda idanu, saidai yanxu zata sa ido sosai donta fuskanci kowa.

misalin karfe tara daidai kowa ya hallara a dining area, fadwa, tareeq ne suka fara zama kafin ammu ta fito, gaisheta sukayi yanda akeyi a kowani gida idan babba yazo kafin ta zauna, tana zama saiga barad ya shigo shima, yaron ya zama shuru shuru, kamar wanda ke cikin damuwa, ya daina wannan faran faran din nashi gaba daya, baima san amu tazo ba saida ya ganta yanxu, aiko da gudu ya tafi wajenta ya rungumeta, itama rungumeshi tayi tare da sumbatarsa sannan taja mashi kujera ya zauna gefenta ya gaishe da aunt fadwa da tareeq.
basu jima da zama ba hidaya ta suako, idonta wiki wiki har wani baki baki undereyes dinta sukayi saboda rashin barcin da bata samu ba daren jiyan, tana karasowa ta gaishe da ammu sannan ta hakimce akan kujera su fadwa suka gaisheta.

ammu dai na kallon ikon allah, babu wanda ya taba abuncin nan saida hidaya ta karaso, tana karasowa suka fara kokarin zuba abuncin ammu ta dakatar dasu, ''ya zaku fara?, ay sai magajin gidan ya suako na dauka shi kuke jira ay''
kallon juna tareeq da fadwa sukayi kafin su maida dubansu ga hidaya data kai hannunta kan spoon din dake gabanta ta dakata jin abunda ammu ta fada, dagowa tayi ta kalli ammu din kafin ta ajiye spoon din tace ''ammu ko kin manta wacecec head of the family?''
''ya za ayi na manta, taju..''
shugowarshi da kamshinsa ne ya dakatar dasu su duka harda ammu dake kokarin yin magana, damm gaban hidaya ya bayar ganinshi kawai datayi, gaba daya ya gama cika masu idanu how huge he is, wallahi gaba daya ya sauya, daga yanayin tafiyarsa, fuskarsa har wani walqi takeyi, kasa dauke idanunsu sukayi akanshi harya karaso dining area din ya tunkari inda hidaya take, yana karasowa ya dan rankwafa ya sumbaceta a kuma cikin calm husky voice dinshi ga breath dinshi na fita mai dadin kamshi yace ''good morning first love''
fuskarshi na nan yanda take, kwata kwata baka iya karantar yanayinshi a hakan ma saboda hidaya na wajen kenan, da kyar ta hadiye wani mugun miyau ta fidda murmushin dole datayi forcing kanta dayi tace ''morning big T, how are you feeling now?, hope youre okay?, tell me idan wani abu na damunka okay?''
ya danyi mamaki ganin how soft she is, normally idan ya gaisheta haka saidai tace mashi morning shikenan, bai kawo komai aranshi ba ya sauke mata murmushinsa mai tsadan gaske yace ''hamdullah''
sai a lokacin ya maida ya dubansa ga ammu data yi kasaqe tana kallon ikon allah, takowa yayi ya karasowa inda take ya kama hannunta ya sumbaceta sannan yace ''sabahal khair mufaddal ammu''
yar harara ammu ta mashi kafin tace ''sai yanxu ka ganni''
dan murmusawa yayi kadan ta gefen baki wanda hakan ya kara mashi kyau sosai, tare da cije lower lips dinshi yanda yakeyi koda yaushe, wannan nature dinshi ne,kuma ba karamin kyau hakan ke mashi ba kai ya allah so sexy and attractive, fadwa dai kasa dauke idanunta tayi akanshi harya zauna kusa da hidaya, barad na daga gefen seat din, tunda taj din ya shigo ya kasa dauke idanunshi akan uncle din nashi dayaga ya sauya gaba daya, tsoron mashi magana ma yake saboda hidaya ta hanashi zuwa inda yake, taj na ganinshi ya daga mashi yanda suka saba idan yazo hutu daga london, ''hey buddy''
cikin hanzari kuwa ya daga hannunshi suka tafa, yaron yanata mamakin uncle din nashi da sauyawarsa ba kamar yanda yake ba, tareeq ko dan neman magana yayi saurin gaishesa, ko kallon inda yake baiyi ba ya gyada mashi kai kawai, ran fadwa idan yayi dubu ya baci ba kadan ba,

7 / 107