Author : Queenmerh Category : Complete Novels
kasa gane wane iri ne, jikinsa yayi sanyi kau kamar kankara har wani green green yakeyi ga jijiga, kuma duk aykin maganin ne alamun ya fara zama worst a jikinsa kenan, wannan fentalyn din is very addictive and deadly drug, yanada hadari sosai musamman idan akayi abusing maganin ba ta kan ka'ida ba, sabeeha dataga yana wannan jijigar ta dauka ko zazzabin ne ya haifar masa da wannan jijigar, haka suka kwana a zaune tana ta faman shafa masa warm water a jikinsa da towel,sai wajen asuba ta samu jikin nasa ya lafa sosai wajen doshin asuba.
Basu ne suka tashi ba sai wajen karfe sha daya na safe, itace ta fara tashi don haka ta shige bathroom kai tsaye tayi wanka ta sauya kaya kafin ta futo zuwa bedroom dinsu, yanda ta barshi haka ta taddashi a kwance yana barci, ta dade sosai tana kallon fuskanshi datayi fayau sosai ya rame,ta shagala sosai tana kallon fuskanshi tana tunanin yanda ya dunga jijiga a daren jiya gashi jikinsa yayi sanyi kau, alamarin shi is getting worst kullum gashi ta kasa gane meke damunshi, ta kasa ganewa, bai taba irin haka ba sai jiya,abu akanr almara, yau lafiya gobe baby lafiya, ita abund ayafi damunta yanxu yanda ya sauya gaba daya kamar ba taj ba, hes not happy at all, kamar wanda hes depressed baya magana saidai ya dunga kallonta, gaskia dole tasan yanda zatayi taga jamid koda sau daya ne,tunda aka dawo dashi daga asibiti bata saka shi a idanunta ba, barad ma ya daina zuwa bangarensu balle ta tambayeshi lafiyar jamid din, ita da ba kowan kowan ba bata isa ta tambayi dalilin rashin lafiyar tashi ba don haka batama sani ba, ko ranar daya fadin ma bata sani ba don suna part dinsu ita da taj din,
ta yanda taji ma
suma su afiyar yanxu tafi wajen sati biyu bata ji duriyarsu ba musamma sonata dake yawan zuwa part dinsu, ita rashin zuwanta ma sauqi ne a wajenta don fa gane yar iska ce.
Sauke ajiyar zuciya tayi tare da gyara mashi duvet din ta futa daga dakin.
Tana futowa ta nufi bangaren hidaya, gabanta na faduwa tunda suka qala mata sharrin sata ta kiyayi bin muhallunsu, yanxu ma don ta ras ayanda zatayi ne yasa ta soma bude handle din kofar ta shige ciki, yau ne rana ta farko data taba shigowa part din, parlor yayi kyau sosai kamarma har yafi nasu kyau sosai.
Sallama ta dunga yi shuru, saida tayi wajen sau uku babu wani response harta juya ta hango nurse din dake kula da jamid din kwance tana sharbar barcinta hankali kwance, yanda take barcin nan ya tabbatar ma da sabeeha hidaya bata gidan, kamar zata juya wata juyar ta ingizata da shiga kofar dakin dake facing parlor, tattara courage dinta tayi ta nufi dakin zuciyarta na bugu ta bude kofar tasa kai ciki tare d akaro kofar a hankali.
Bin dakin ta somayi da kallo, daki ne mai fadin gaske har idanunta ya sauka kan wani gadon marasa lafiya, ganin mutun a kwance yasa ta sake bude idanunta da kyau ta tako gaban gadon, saida tazo dab da gadon ta tabbatar da jamid ne kwance, ya rufe idanunshi, ya rame sosai kamar bashi ba, saiya bata tausayi sosai, cikin abunda baifi sati uku ba ya sauya sosai gaba daya, bakinsa daya karkarce ta kalla, bata kawo komai a ranta ba kawai ta sauke idanunta
“Allah ya baka lafiya uncle” ta furta tana mai juya ta nufi hanyar futa daga bedroom din, kwata kwata
Juyawa tayi har zata fuce daga dakin ya bude idanunshi, bayanta yabi da kallo lokacin tana gab da futa daga dakin, rigar jikinta daya gani da yanayin jikinta ya tabbatad mashi da sabeeha ce, tuni jikinsa ya soma tsuma, yanaji yana gani ta vude kofa zata futa, bakinsa dake karkace ya bude ya soka kiranta, “fa…ti..ma”
Inaaaa kamar ma baya futar da sautin kwata kwata, yanaji yana gani bashida damar tsaidata, bashida damar kiran sunanta ko ya shaida mata taj yana cikin hadari, tana rufe kofar kuwa ya runtse idanunshi sai hawaye.
Bangaren sabeeha haka ta futo daga bangaren jiki a mace, tana tunanin me ya sameshi haja ya rame sosai, kwata kwata bataji kiran da yayi mata ba taya ma zataji shida sai an kai kunne saitin bakinsa ake jin abunda yake fada,data dan tsaya koda na yan seconds ne qila data ankare ya bude idanunshi.
Tana futowa ta lallaba ta fuce daga dakin bayan ta tabbatar babu wanda ya ganta.
***
Taheel company…
Shuru kakeji kowa yayi jugum cikin office dinta suna sauraron ta, saida ta gama bayani tass kafin ta jinkirta, daya daga cikin waenda ke managing finances din kamfanin ne ya soma magana cikin dattako da ladabi, “madam I’m afraid kudi masu yawa kamar wannan idan aka ciresu daga account din company lokaci guda zai iya jawo mana bankrupt, if aka samu matsala da production din
new business din ni ina ganin karmuyi gaggawa mu bari sai mun samu kudin investment din da mukayi siging da investors dinmu tunda bazamu saida shares dunmu ba, idan akayi gaggawa zai iya jawo mana bankrupt kuma sales yanata dropping saboda bamuda investors da yawa,”
“Are we low on budget?, manyan investors din da muke dashi fah? Daga kasashen waje?”
Ta tambayeshi kai tsaye
“No ma’am, but this is very risky, wannan kudin kamfani ne, investor kuwa zasu iya dakata da investment dinsu duk sanda kukaga dama and hakan zai iya…. “
“No but” ta katseshi, tana mai dubanshi tace tace “i the ceo approved of this duk wanda bai amince ba should deal with it, I’m conviced this is for the companies achievement”
Shuru kowa yayi, yana sauraron ta, wannan decision din nata duk wani professional business owner yaji haka sai yasan its risky, kwata kwata bata tunanin ma abunda zai biyo baya, kudin da za a samu kawai take hange, basuda ikon hanata don haka suka barta Tayi signing approval.
Suna fita ta maida dubanta ga wayarta daketa faman vibrating, tun jiya take ganin ana turo mata messages taka dauka ko spam ne, ganin messages din yaqi karewa yasa ta bude don dubawa, zumbur ta miqe tsaye, take wata zufa ta fara keto mata, idanunta na kan wayar ko shugowar fadwa bataji ba, fadwa dake ta bunta da idanu takai wajen minti biyu a tsaye, sai kawai tayi murmushi tace “ukty! Ukty”
Sai a lokacin hidaya ta dago ta kalleta, tana kallonta cikin faduwar gaba, dakyar ta samu ta tartara kuzarinta tace “yaushe kikazo!”
“Yanxu ta bata amsa, tana mai zama kan kujerar dake facing dunta kafin ta soma koro mata bayanin daya kawota, ganin hankalinta baya tattare da ita yasa ta cewa “ukty kina suararona kuwa?”
“Come again please!”
Jinkirtawa fadwa tayi aranta tace “ay bakiga komi ba ma tukunna,ko ya zatayi idan ta gano ko suwaye investors din da take taqama dasu hmm”
Wani notification din ne ya sake shugowa wayar hidaya wanda ya sata miqewa kawai ta zari jakarta, tana daukar jakar tata ko kallon inda fadwa take batayi ba ta fuce daga office din.
Tana fita fadwa ta bita da idanu, kafij ta suake murmushi ta mike tsaye ta tako zuwa kujerar da hidayar ta tashi ta zauna akai tana mai junuya kujerar ta lumshe idanunta, “so this is how it feels to have a power, ukty kenan ashe haka kikeji, shiyasa kika kasa bari yaron nan ya dawo hayyacinsa, you want all of this to your self ko, hmm, lets see how it goes”
Tunawa da abunda ya kawota yasa ta miqe ta fuce, daman document ta nema na list of manyan investors din kamfani kuma ta samu ta hanya mafi sauqi, batasha wani wahala ba saboda itama tana cikin shareholders, dukda karbar information din investors ba abu ne mai sauqi ba, kowa boye cigaban kamfaninsa yake baya yarda ya futa koda wasa, sanin ko ita wacecec yasa ta samu cikin sauqi kuma ta gano abunda take son ta gane.
Hidaya na futa daga office dinta ta shige motarta tare da kiran black,in ka ganta zaka ga tsantsar furgici a tattare da ita na ganin abubuwan da aka turo mata.
İnformation dinta ne aka tura mata na dirty ayyukan da take sawa ayi mata duk sirrikanta gaba daya tare da threatening dinta da akayi wanda take zargin wannan sai agent din khaal dinnan, sai a yanxu ta tabbatar duk wani plans dinta na rawa, shi kanshi mai tura mata is a big threat to her, gashi ta kasa gano koshi waye,kuma a ina zata samesa, yanxu dataga wannan hankali ya kara doubling wajen tashi.
Bazata taba samun sukuni ba saita kama ko wanene wannan da ya zame mata baban threat din da zai iya jawo mata matsala.
Aikin da batayi ba kenan a ranar,warning kuwa babu wanda bata sheqawa black ba akan saiya nemo koma wanene wannan behind this.
After 2days
Futowa tayi afurguce daga bangaren su, its past 10 am na safe, duban duniya tayi mashi anan saman part dinsu bata ganshi, hankalinta ba karamin tashi yayi ba don jiya aman jini ya dunga yi,yau da safe kuwa taga sauyi a tattare dashi don kwata kwata gudunta ya dunga yi kamar yaga abar tsoro.
Kasan ta sauko tana dubanshi, babu kowa a a kasan, duk inda tasan zata ganshi anan kasan bata samu ta ganshi ba, ai fa sai a lokacin hankalinta ya sake tashi, ina ya shiga? Wai meke shirin faruwa ne? Anya kuwa ba ciwon shi ne yake neman dawowa ba? Tayi ma kanta tambayra tana futowa daga cikin gidan “didi didi…” ta cigaba da kiranshi, “dan allah ka fito, inma buya kayi,hankali ya tashi wallahi”
Hanyar garden ta nufa wajen sakon dake connecting garden din da entrance futa zuwa dayan compound din,
Jan hannunta da akayi yasa tayi saurin dagowa, tana mai kallon mutumin dake rike da hannunta, cikin hanzari ta warce hannun nata tana mai kallonshi tace “who are you?, meysa zaka kama min hannu”
“I’m sorry..dole ne yasa nayi hakan”
“Fatima right?” Ya tanbayeta
Da mamaki take kallonsa, bata taba ganinshi ba, muryarshi ce dai kawai dataji ne yayi mata kama da muryar data taba ji kuam ta kasa mantawa, “listen to me carefully”
“Bazan iya maki dogon bayani ba, but ina rokonki, please plase you need to trust me”
“Meysa zanyi trusting dinka? Ya akayi ka sanni?” Ta sake tambayarsa, ganin kamar zata bashi wahala wajen hadun kai yasa shi cewa “saboda ni na kawoki gidan nan a matsayin yar leken asiri”
Gabanta ne ya bada dam, tabbas wannan muryar bazata taba mantawa dashi ba, muryar wanda ya kawo ta leken asiri gidan nan, take jikinta ya soma tsuma ta fara yin baya baya saura kiris tayi tuntube ya dakatar da ita,
“I need you to listen to me fatima, tabbas nina kawoki gidan nan bisa ga umarnin khaal,wanda shine ya kawoki gidan nan, kuma kudirinsa badan kiyi leken asiri bane sai dan ki taimaka ma tajudeen, his life is in danger not only him harma dake, jamid bazai iya protecting dinku ba saboda ya samu paralyzed, we are running out of time, shiyasa nake son ki bani hadin kai don nayi fulfiling last wish din khaal”
Hawayen ne ya soma zarya akan fuskanta hannunta na karkarwa ta soma magana “how can i trust you? What if karya ne duk wannan?”
Ganin tana neman furgice wani tunani yazo mashi ya bude wayarshi ya danna wajen hotuna ya miqa mata wayar, hotonshi ne gashi da khaal a zaune ranar eid ya duakesu hoto, next hoto ya sake nuna mata lokacin tana aikin gidan khaal, yana gama nuna mata ya soma bata labarin yanda ya bama jamid daga farko har karshe har zuwa lokacin da khaal ya bashi amarnarsu a ranar da aka tsinci gawarsa.
Kuka dai wiwi haka ta dunga yi dataji farkon labarin har zuwa karshensa, how can someone be this wicked? Ashe daman waennnan azzaluman ne sanadiyarsa ta zama haka? Wanna. Wace iriyar kiyayya suke mashi?, laifinshi ne da iyayensa suka haifasa? Tambayar data dunga yima kanta kenan tana hawaye, Sun shafe wajen 30mins a tsaye a wajen, saida ya tabbatar shes convince tukunna kafin ya soma tambayarta,
“Ranar litinin sha hudu ga wannan watan Jamid bai baki komai ba??baku hadu dashi ba?” Ya tanbayeta yana mai fatan allah yasa file din na hannunta
Nazari ta soma yi kafin tace “ah ah bamu hadu dashi ba”
Nunfasawa yayi kafin ya sake cewa “innalillahi wa inna ilaiahi rahiun, ina fatan allah yasa yana wajenshi, ta wannan hanyar ne kawai zan iya kubutar daku, listen to me fatima, inason duk yanda zakiyi kije ki samu jamid, kice mashi mutalib, idan kika fada mashi sunana zai gane abunda nake nufi, wannan file din idan yabar hannun jamid akwai matsala dole kiyi wannan kokarin wajen ganin kin karbo, amma cikin sirri saboda akwai hadari, nayi badda kama ne a matsayin driver saboda idan aka gani identity dina asirin mu zai tonu kinji”
Motsin da sukaji ne yasa shi saurin barin wajen baima idasa karashe abunda yake son fada mata ba…
Tareeq da tun saukowarta yana hangenta daga bakcony din part dinsu yayi saurin fitowa yabi bayanta ba tare da saninta ba, gaba daya duk discussion din da sukayi kaf ya gama jinsu daga a-z, bai bari sun ganshi ba yabar wajen immediately, yana kokarin processing abunda kunnenshi ya jiye mashi.
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2 paid book
Chapter 58
Tun bayan wucewar mutalib da kyar ta iya daga kafarta tabar wajen, har zuwa lokacin hawaye baibar sauka akan fuskanta ba, kalamanshi na echoing a kunnenta tunda taji yace rayuwar taj na cikin hadari,bama shi kadai ba harda ita kuma jamid bazai iya protecting taj din ba saboda ya samu paralyzed,badan taga hotunan daya nuna mata ba da kuma bayanin da yayi mata wanda ta gamsu dashi ba, bazata yarda ba,at that point batajin akwai wanda zata iya trusting yanxu kaf gidan.
“Innalillahi wa inna ilaiahi rajiun ta furta, kafarta har wani rawa rawa take tsabar furgici, tama manta da neman taj din da ta sauko yi, cikin hanzari ta koma cikin gidan harda gudu gudu, saman ta wuce bata tsaya ko’ina ba sai part din hidaya, tama manta bata rufe kofar ba, gabanta na bugun uku uku, batare da wani dogon tunani ba ta bude kofar tasa kai cikin dakin don ta tabbatar da abunda mutalib din ya fada mata na cewa jamid ya samu paralyzed, ya akayi bata gane ba lokacin data shiga dakin ta ganshi a kwance, she didn’t even noticed kwata kwata.
Kofar dazai sadata da dakin ta bude, cikin ikon allah kuwa bata tadda nurse din dake kula dashi ba don haka ta tunkari wajen gadon nashi, yana kwance idanunshi a rufe, ganin shi da tayi yanxu a haka ba karamin karyar mata da zuciya yayi ba,mutun mai lafiya ace rana daya ya tsinci kanshi a haka, hannunta na karkarwa ta daga tana kokarin tashinsa sai kawai ya bude idanunshi, suna hada ido hudu dashi ya soma kokari motsawa, “uncle..uncle innalillahi wa inna ialaihi rajiun”
Bakinsa dake karkarkace ya soma juyawa, alamun yana son magana, jikinsa har tsuma yake sosai, hannunsa dake karkarwa ta kama tace “uncle meysa sameka haka?”
Dakyar ya iya furta “TA..J…TAJ…..” struggling sosai yakeyi yanda zata jishi, jikinsa sai karkarwa yake, kwata kwata bataji me yake fada ba, saika kallon bakinsa dake karkace take sai hawaye, saida ya sake maimaita sunan tak ta gane, take taji gabanta ya fadi, sai ayanxu ta gaje yana son ya fada mata abu game da taj din, gaba daya tama rasa me zatayi, “taj? Taj???uncle mai zai faru da taj? Ka fada min”, yana kokarin sake yin magana daidai nan sukaji muryar hidaya daga sitting room ta shugo, tuni cikin sabeeha ya duri ruwa, shima kanshi jamid din hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, bazia iya motsawa ba gashi babu baki balle ya fada mata ta boye.
Sabeeha data tabbatar da muryar hidayar ce dai kunnenta ya jiyo mata hankalinta bai gama tashi ba saidata ji takun tafiya wajen kofar shugowa bedroom din, tabbas idan hidaya ta ganta anan alwai matsala, gashi bata samu ta tambayi jamid maganar file din da tareeq yace mata ta tambayeshi ba, rarraba idanu ta dunga yi Har idanunta ya sauka wajen curtains cikin hanzari ta saki hannun jamid ta karasa wajen ta shige cikin curtains din tana shigewa jamid ya sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya dukda gabansa na faduwa, shi kanshi bazaiso hidaya ta ganta anan ba, daidai nan hidaya ta shiga part din rai a bace,gaba daya kana ganinta zakasan bata cikin natsuwa, tana karasowa tsakiyar dakin ta kalli bangaren jamid dayayi saurin rufe idanunshi, kallon dakin ta somayi ganin nurse din dake kula dashi bata nan, saukan ruwan dataji daga bathroom yasa ta cewe “ke!!! Step out this instant”
Tuni cikin sabeeha ya duri ruwa, babu abunda kirjinta keyi sai bugu, harta daga kafarta dake rawa zata futo tayi saurin dakatawa jin abunda hidayar ta fada, “akwai wanda ya shugo nan dakin ne?”
“No madam” nurse din data futo daga bathroom ta amsa hidayar,
“Ya akayi kofar entrance din shugowa ya kasance a bude?baki iya aikinki bane yanda ya kamata?”
“I’m sorry ma’am, na manta ne ban rufe ba”
“Are you insance?this will be my first and last warning,idan bana gidan nan karki sake kibar kofar nan a bude sannan karki sake kibar kowa ya shugo part din nan har sai na dawo understood?!!!” Hidaya ta daka mata tsawa.
Jiki na bari nurse din ta amsa ta “yes ma’am kafin tayi gaggawar fucewa daga dakin.
sabeeha dake tsaye duk ta tsure,, duk a tunaninta ta dauka ta hangota ne cikin curtain din saidata ji maganar da sukayi da nurse yasa ta sauke ajiyar zuciya.
Nurse na futa hidaya ta karaso inda jamid ke kwance,kamar kullum yauma rufe idanunshi yayi, ta lura da hakan da yakeyi, ko zata kwana tana magana bazai bide ido ba balle ya kalleta koya bude ma tsantsar kiyayyar da yake mata take hango wa cikin idanunshi, ita wannan bama damuwarta bane don qiyayyarsa bazata hanata yin abunda ta kudirci yi ba,duk threat din datake mashi yaqi bayyana mata inda file din yake,tasan shi da taurin kai sosai, kuma tasan bazai fada mata cikin sauqi ba shiyasa ta dage da manipulating dinshi da maganin da take bama taj, tana