Author : Queenmerh Category : Complete Novels
so much respect.
“See you then may Allah blessings be with you as always”
“Insha Allah”
Sukayi sallama ta kashe wayar shima ya aje.
Yana gama shiryawa ya fito inda saleem ke jiranshi.
Suka gaisa asual suka fara zagayen da zasuyi, sun dade sosai kafin suyi branching a company baban salim na motocin ford da yake karban dealers.
Salim ya sanar ma babannashi daman taj din ya buqaci zuwa wajen, shi baban nasa baya kasar yayi tafiya so ya bama salim go ahead don yasan mahimmancin taj din tunda yaji daga inda yake dukda baisan shi din waye ba.
Sun zagaye wajen and taj is so impressed with yanayin yanda suke tafiyar da wajen, don ya banbanta da yanda sukeyi achan company, kuma duk varieties of different collections akwai saidai karancin colors ga pending orders da mutane keyi suggesting, a take yayi waya da merk yasa suyi approving duka collection din da baban salim ya nema daga kamfani.
Lokacin da wannan abun alkairi yazoma alhaji buba yayi murna kwarai ya kara tabbatar da zuwan taj alkairi ne, abunda sai a dauka shekaru kafin ayi approving sai gashi cikin awanni kadan ya samu kai abun yayi mashi dadi sosai.
Salim fa zuru yayi da idanu ganin yanda taj din yake zayyano wani turanci yana waya a take yayi signing wani deal dasu yayi approving a bude wani companying anan.
Wani abun mamaki daya kara gigita salim lokcin da suke zagayen motocin ya nuna interest akan wata ford sprt car, take taj yace mashi “are you into drift?”
Yace mashi yes, daga yes dinnan kawai yace “take it”
Salim kamar yayi tsalle don ko a mafarki bai taba tsammani ba, take wata natsuwa ta shigeshi yayi murna ba kadan ba kamar zai tsugunnama taj.
Shi taj dinma mamaki ya dungayi yanda yake mashi godiya don motar ba komai bace compare to latest collections dinsu na yanxu.
A haka sukabar wajen aka biyo taj din da wata dankararriyar mota daga cikin motocin.
Sai wajen 5 suka dawo gida, yayi sallah yayi wanka, baibi takan abunci wajen ba kwata kwata don yanxu ba komai yake ci ba.
Yana zaune mesaage din mutallib ya shugo mashi kamar haka.
“This is khaal, idan kayi receiving mesaage dinnan inason ka kira ni”
Take yayi dialing back tare da wani dogon tunani ba.
Call din na shiga akayi saurin dauka, taj yayi sallama.
Suka gaisa sannan suka dan tattauna, sun dade sosai suna magana kafin suyi sallama.
Har zai katse wayar khaal yaui saurin dakatar dashi.
“Tajudeen!!!” Khaal ya kirashi.
“Ka nemi mahaifiyar???”
Dam yaji gabanshi ya bada yayi saurin runtse idanunshi.
“This is the right time taj, shakarun da suka wuce a baya bazaka iya dawo dasu ba,its high time ka nemi mahaifiyarka, what you should have done years ago”
Jiki a mace ya dafe kanshi dayaji ya sara mashi jikinshi ya mutu yace “I don’t deserve to be with her, khaal,ban chanchanci bayyana a gabanta ba khaal,nayi babban kuskuren da bazai gogu ba khaal”
“Allah yana mana laifi munyafe masa, she will Accept you happily, HAJAR is one of a kind, and halinta ka biyo, baka da kamarta ayanxu, so face the consequences ka nemi yafiyarta, ka nemi albarkacinta saboda rayuwarka tayi albarka, saboda rayiwar ta inganta”
“Kodan hakkinta banajin zan taba samun kwanciyar hankali a rayuwata khaal, banida bakin kiranta a matsayin mahaifiyata, na cireta daga babin rayuwa ta nayi dana sani khaal, i was foolish and stupid and manipulated into thinking bata buqata na a rayuwarta”
“Ba laifinka bane taj, ba laifinka bane..KADDARARKA kenan,bazamu iya maida hannu agogo baya ba, so try and fix your past, try and clean your relationship with your mother, ka gyara alaqarka da mahaifiyarka, nasan guilt ke dakatar dakai, amma inason ka sani lokaci na kurewa karkazo kayi regretting”
“Insha Allah khaal” da haka sukayi sallama ya kashe wayar
Ya zauna yana tunanin rayuwarshi ta baya, wallahi babu ranar da zata gifta a rayuwarshi da kalmar mahaifiyarshi bazatayi crossing kind dinshi ba, wallahi an cuceshi matuqa, ace kana raye kuma mahaifiyarka na raye wadda ta tsugunna ta haifeka amma anyi distancing dinku, kuma bai gani laifin kowa sai laifin kanshi, bai ganin na iyayenshi da suka rabu a daidai lolacin dayafi kowa buqatarsu har hakan yayi sanadiyar gurbata rayuwarshi ya shiga wani traumatic stage at a very young age.
Sai yaji wani irin dumm a kanshi, hoton ta daya karba wajen khaal har yanxu yana jikinshi akoda yaushe duk inda yake.
Maganganunsu da khaal ya kara bashi wani irin courage.
Har wajen magrib yana zaune jiki a
Mace kafin ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito da alwala yayi sallah, cikinshi ya soma qugi amma yaqi cin komai.
Yana zaune yana addu’oi akayi sallahr isha’i ya tashi yayi sallah yana idarwa a gaggauce ya shirya cikin irin farar jallabiyan nan ya saka kundura akanshi ya nadota saiya dawo sak balarabenshi dashi Masha allah.
Kai masha allah masha allah…tsarki ya tabbata ga wanda yayi wannan halitta, sai buga kamshi yake yalwatacce, ya dora agogo a hanunshi da zobunan azurfa a yatsunsa.
Yana gamawa ya fito daga dakin cikin kamewa ya sauka kasan, yana sauka kasan ya karba keys din sabuwar motar daga wajen valley keepers sannan ya shiga ciki, wajen dashboard ya bude kamar yanda ya buqaci permit da documentation duk an hada mashi a ciki karkashin sunan alhaji buba incase.
Kunna motar yayi sannan ya kunna wayarshi tare da dialing number anne, ana dagawa ya buqaci address ta fado mashi sannan yasa a map ya kama hanya.
Lokacin wajen karfe takwas da yan mintuna kadan, anatse yake driving yanabin map dukda baisan hanyar ba cikin ikon allah cikin abunda baifi 20 mins ba ya iso gwarinpa.
Daga nanma ya dunga bin map din har zuwa santuraki’s creasent avenue, yana shugowa lighing din wajen ya bade ko’ina ya soma slowing motar ganin securities at ko wanne end, bakinsa ya soma matsawa a hankali don banjin abunda yake fada harya karasowa gate din tafkeken mansion din.
Yayi bayanin inda zaije da sunansa kai tsaye babu wani tambaya aka barshi ya shiga, saiyama rasa ina zaibi wanne part zaije, daidai babban dake tsakiya ya tsaya wajen parking lots yayi parking.
Hamad dayayi parking shima yana kokarin kwasar paper bags din dinkunan dayayi tun daga shugowar motar yabita da ido.
This is the first time yaga irin motar a cikin compound din.
Ya dauka wajen minti biyu bayan ya kashe motar bakinsa na motsawa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fito daga motar yabi ko’ina da kallo har idanunshi ya sauka kan hamad dake shirin shiga main house.
Dan dakatawa yayi ya karaso inda taj din yake ya miqa mashi hannu da mamaki suna kallon juna.
“Asaalamu alaikum”
“Wa alaikum salam wa rohmatullah”ta ya amsa shi fuskansa ba yabo ba fallasa sai yalqi take Masha allah, ga wani cikar haiba da annuri dake kwance kan fuskar.
Hamad kwata kwata bai kawo shine baqon anne ba wanda tabi ta ishesa da zancensa da take cewa kusan halinsu daya very soft and calm guy.
“Hamad Abdullah”
“Tajudeen abdullah taheel”
Suida yaji sunansa tukunna hamad ya gane shine expected guest din kenan, shine wanda ya tafi karba kaya da anne tasa ayi masa daga babban kamfanin the boss ateliar suna dinkin manyan kaya da yadidika hadaddu.
Murmushi hamad ya mashi sannan ya mashi iso suka nufi hanyar main entrance.
Har cikin babban parlor hamad ya jagoranceshi ya zauna, babu kowa cikin parlor din sai kamshi yake ga sanyi ac.
Gaban taj daketa faduwa tun amota sai yayi doubling kamar ana lugude, and its something different da bai taba experiencing ba kwata kwata.
Har yana dafe kirjin nashi don kamar zai fito, yanajin kusancin wani abu daidai da bugun zuciyarshi.
Saukowa hamad yayi ya zauna tare dashi suka sake gaisawa sannan ya shaida mashi ya sanar ma da anne zata sakko yanxu.
Jinjina kai kawai taj yayi shi kadai yasan me yakeji.
Cikin yan sekanni kadan sai ga anne ta sakko cikin shiga ta alfarma, idanunta sanye da farin glass ga fara’a kwance a fuskanta.
Daidai nan anty fadila ta shugo tare da laila don anne tace yau duk anan za ayi dinner, (mijin anty fadila baya nan yayi tafiya)
Yana ganin saukowar anne yayi saurin miqewa murmushi kan fuskarshi shima ta karaso parlor ta zauna ya tako har inda take ya kama hannunta kamar yanda yakema ammu da khaal ya sumbacu hannunta cikin larabci ya gaisheta ta amsa.
Su anty fadila sai suka zama yan kallo, wannan ne baqon anne din, tsantagwaran balarabe? Shin ina ta san shi kuma? Meya hadashi da ita tambayoyin da suka dunga yima ka su kenan.
Su laila sai aka fara sunne kai anga kyakyawa, ta kasa daina kallonshi don baka iya resisting, allah allah take maya tazo ta ganshi, ita ta rikice qila maya sai sumewa.
“Zauna tajudeen”
Ta mashi nuni da kujera ya zauna.
Daidai nan uncle sameer ya shugo shima, shida anty mubina da yan yayanta, anty laila ko itada batasan shiga cikin dangin miji cewa tayi zazzabi takeji bata iya futowa, sai su abal ne suka biyo bayan daddyn nasu.
Gana daya yaran wajen cikin harshen turanci suka gaishesa ya amsa masu da yar fara ar shi.
Anty fadila ma ya gaisheta, uncle sameer ko musabaha sukayi.
“Masha allah tajudeen welcome to my home, and waennan family na ne”
Da mamaki sosai yake kallonsu su duka don wallahi bai taba tsammanin shes blessed with such a wonderful family ba.
“This is my first sameer, and this is my second fadila, thats her kids i have one more, she’s in london”
“Masha Allah” ya furta ahankali yana murmushi.
Su uncle sameer sai jinjina shi suke aransu don abun mamaki ne ace anne ta kawo stranger to their home definately yayi mata wani abunda bazata manta ba.
“Laila ja yaran nan kuje dining”
Laila ta jasu su duka ya rage sai iyayen nasu kadai.
“Sameer wannan shine tajudeen, shine wanda ya taimakeni badan jiba da tuni bana nan zaune a kusa daku”
Da mamaki duka suka juyo suka kallon anne meysa zatayi wannan furucin,….duk suka zuba mata idanu gaba dayansu suna jiran amsa.
“Muje muyi dinner ko”
Tasan son karin bayani suke amma ta katse su suka miqe tayi gaba suka bita a baya.
Aka zazzauna, what a happy family daya shiga cikinsu sai yaji kamar he’s among.
Uncle sameer ya dunga janshi da hira don yana kusa dashi.
Anne babu abunda take sai murmushin jin dadi kawai.
Ana gama cin dinner suka dawo sitting room, anne taso fada masu komai amma saitaji this is not the perfect timing gashi nanna bata nan, taj daya lura da hakan shima baiyi kokarin cewa komai ba.
“Anne tace daga saudi kake? Meysa kawo ka nigeria? I must say business right?”
“Yea business..and some personal stuff”
“Masha allah what are you into?” Sameer ya sake tambayarshi.
“Cars..i am the founder of…”
“Assalamu alaikum…”
Daga ciki da sukajiyo sallamar suka amsa da “wa alaikum salam..nanna”
Driver ya biyota da akwatin nata, duk suka juyo suka kalleta don bata idasa karasowa ba hamad yayi saurin karban box din anty fadila tace “ah ah baki tafi ba?”
“Uhm fadila bazan iya ba da delays din flight dinku na nan nigeria, ive been stranded for about 3 hours, sun gama zaunar damu hamad yayi min booking wani flig…”
Chak ta tsaya tana karasowa sitting room din, kuma a daidai lokacin idanunta ya sauka akanshi, bugunda kirjinta keyi lokacin data shugo estate din bana wasa bane.
Daga kan wayarta zuwa files din dake hannunta duk wani abu daya kasance yana hannunta gaba daya sakinshi tayi kasa wanwas ji kake passs pass a kasa, take idanunta yayi jaa sosai ta soma yin baya baya jikinta na karkarwa jininta ya soma yin kasa sai jiri daya soma dibanta, fadila data lura da yanayinta tace “nanna!!!! Nanna!!!!” A daidai lokacin ya dago da idanunshi ya sauke cikin nata mug din tea din dake hannunshi ya sake gaba daya ya malale a kafanshi gashi da zafi sosai, shima cup din ya fashe.
Jikin nanna ya fara vibration kamar wadda zata shide tayi luuuuuuuu ji kake timmm a kasa.
“Innalillahi wa inna ialaihi raji’un suka miqe gaba dayansu sukayo kanta harma da taj da baisan ya taka mug dinnan ba ya karasa fashashi ya fasa mashi kafa, yana zuwa gab da ita ya kasa karasawa hotonta na flashing a fuskanshi yayi saurin rintse idanunshi ya bude ya sauke akan fuskanta da idanunta ke rufe, ya wani irin dafe kanshi cikin hanzari ya tura hannunshi cikin aljihunsa ya zaro hoton nata, duk kachaniyar da suka a gabamta duk sun zagayeta bayajin kwata kwata abunda suke fada abu kamar an
Toshe mashi kunne da basira ya kasa tabuka komai sai kallon hotonta da yake da fuskarta wani irin zazzabin ya saukar mashi mai zafi sosai ba kadan ba.
Ruwa aka yayyafa mata amma ta kasa dawowa daidai karshe ma nunfashinta daukewa yayi gaba daya.
Sameer yayi saurin cewa “anne bata nunfashi, bata nunfashi”
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun sameer ku kira barau ku kira ambulance karna rasa yar uwata, innalillahi wa inna ialaihi rajiun” ta dafe kanta daya soma sara mata.
Sai a lokacin taj ya dawo hayyacinsa wallahi bayaji baya ganinsu gaba dayansu, gaba daya ya koma kamar jan kosai, jijiyoyinsa suka fito rado rado.
Ya tsugunna ya dauko nanna gaba daya ya rungumeta zuciyarshi na kuna, wasu irin strong mixed feelings na shigarshi ga radadin da yakeji a zuciyarshi, ya nufi hanyar fita da ita.
Bata nunfashi inaga maganar kiran ambulance, wallahi bayajin me suke cewa kwata kwata yayi reverse da motar baibi takan kowa ba ya figi moatar, allah yaso akwai keys a jikin hamad wannan yasa suka shigiga cikin moatar sukabi bayan tashi.
Gudu yake ba karamin gudu ba kamar zai tashi sama,kiris ya rage baiyi causing accident ba har suka iso deeda.
Suna isowa ya zagaya baya kamar his life depend on her ya daukota ya shiga da ita, take nurses suka karaso da gado a da sauri aka sakata yabisu, aka dakatar dashi.
Aka kira doctors har uku don ta shiga critical condition, dasun shiga sun fito saiya miqe daidai nan su anne suka karaso, wani doctor ya sake futowa taj ya riko hannunshi kamar zai ballashi sai zufa yake gaba daya ya futa hayyacinsa yace “please save her…dan allah ku ceceta, i need her in my life”
Gaba daya kallonshi suka dunga yi, ya gama shiga tashi hankali gaba daya.
Anne da sameer da fadila suka karaso harda hamad suka zagaye doctor din anne tace “barau whats going on? Me yar uwata ke ciki? Ku rifa min asirin don allah ku ceceta”
“Hajiya calm down.. you need to make her calm down saboda idan hankalinta ya tashi its risky” barau ya karashe yana kallon sameer, anne tace “barau explain to me what is happening to my sister”
“Hajiya shock ne, which result to jininta ya sauka, yanxu nurses zasu kawo blood daga blood bank na asibiti, insha allah babu abunda zai sameta ku mata addua”
Daidai nan nurse ta karaso jiki na bari tace “sir can i have a minute with you”
Yadan matsa ta mashi magana kafin ya juyo, idan har ya bayyana masu babu blood type dinta a asibitin nan zai iya zame masu matsala don a gaskia family santuraki manyan client dinsu ne.
With the kind of look da yake basu yasa taj cewa “take my blood..”
Gaba daya juyowa sukayi suna kalonshi, with annoyance hamad yace “please stay on your limit, allow them to do thier work”
Ko kallo inda yake baiba yace “i said take my damn bloood…idan wani abu ya sameta saboda delay dinku i will Make sure that asibitin nan bai sake anfanuwa ba”
“Bubu yanda za ayi a diba blood dinka bamusan kokai waye ba”
Sameer yayi magana cikin bacin rai don shi tun daya dauki nanna ya fice da ita ranshi ya baci.
Wallahi baima san sunayi ba kwata kwata ji yake kamar ya shaqe doctor din.
Anne ta katse su tace “doctor barau what is the issue”
“Hajiya im sorry bamuda blood tupe dinta”
“Ku diba nawa”
“You’re not compatible hajiya batada wani da ko jika? Wanda blood dinshi A ne?”
“Please take my blood and save her”
Sai a lokacin barau ya kalleshi yace “qre you related to her and what’s your blood group sir?”
“I AM HER SON!!!!!”
Dammmm gaban anne ya bada, ay itama saita samu wani hawan ruwa a take.
Fadila da sameer banda kallonshi babu ahunda suke with so much shock.
“Doctor doctor the patient is having pulsing tana jijiga”
Wata nurse ta fito hankali a tashe.
Ay ko kallon inda suke taj baiba ya afka dakin doctor barau yabi bayanshi.
Yabar su uncle sameer da anty fadila da suman tsaye, uncle sameer zai bishi don a tunanin shi ko ya haukace ne anne ta dakatar dashi.
“Tabbas dan hajara ne wannan babu makawa, tajudeen dan nanna ne ita din mahaifiyarshi ce, wadda ta tsugunna ta haifeshi tayi rainon cikinsa wata tara allahu akbar” sai hawayeeee😭😭😭😭😭
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 92-93
After an hour..
Gaba daya jugum sukayi a zaune, fadila da hamad na zaune kusa da anne while ya sameer yana tsaye yana safa da marwa tsakanin wajen.
Suna cikin wannan yanayi doctor barau ya futo, lokacin wajen misalin karfe 10 ta gifta ana neman sha daya,inda anne ke zaune ya nufa suka miqe tsaye.
“Alhamdulillah hajiya,…an kara mata jini and she’s stable now zaku iya ganinta, amma agaskia bazamu sallameta yau ba sai zuwa gobe”
Janjina kai anne tayi tare da sauke ajiyar zuciya suka dunguma doctor yayi masu jagora zuwa dakin da aka kwantar da ita.
Anty fadila na rike da hannun anne don jiri jiri takeji,kai yau sunga karamin tashin hankali mai tafe da abun alajabi da mamaki.
Suna shiga daga ciki suka taddata kwance, harda oxygen, ga jinin da aka saka mata a hannu, gaba daya lokaci guda harta fada sosai tayi fayau abun tausayi.
Zagayeta sukayi, gaba daya tausayinta ya dabaibaye su.
Su anty fadila har zuwa lokacin shock baibarsu ba, dayan hannunta da babu canula a jiki anne ta kama jiki a mace,wani irin tausayin kanwar tata ya gama shiganta, dole ta shiga shock, abunda ta dade tana dakonshi aranta, tana jiran baiyya a gabanta, lokaci guda unexpectedly sai gashi.
Chan kasan zuciyarta tanajin wani irin farın ciki mara misaltuwa, sai a lokacin ta tuna da taj ta dubi doctor tace “shi yana ina?”
“Yana lab, he insisted on giving enough”
“Thank you doctor”
Sameer ya rakashi kofa ya futa kafin ya dawo dakin, gaba daya kowa yayi shuru kamar ruwa yaci su, anty fadila ta kalli sameer suka hada idanu har zuwa lokacin kansu a kulle yake da wannan al’amari.
Muryar anne ce tasa suka maida