Author : Queenmerh Category : Complete Novels
lokaci ba ya shiada masu abunda yakeso da plans dinshi son ganin kamfanin ya tsaya, dake abune na harkar kudi inda sukasan zai kawo masu daukaka da kudi nan zasu bi wannan yasa suka mashi alkawarin suna bayanshi.
So far wajen 60% shareholders din sunyi na’am da sauyin daya kawo masu sai jiran lokaci kawai.
Gida ya nufa direct bayan ya bama gangs dinnan kwakwaran warning kan su bama khaal proper safety karyaji otherwise, sannan ya banka masu account dinsu da kudade sosai, sudai sun samu sabon oga, kuma duk abunda yakeso zasuyi mashi babu second thought.
Fitowa yayi ya nufi cikin gidan, yana shiga bai tsaya ko’ina ba ya tunkari stairs, daidai nan fadwa na shirin saukowa tana ganinshi tsoro ya dabaibayeta, amma ta danne sosai, tasan a irin lokaci kamar haka yana ganinta yake kaucewa saitaga akasin haka, kallonta yake daga sama har kasa sannan ya tunkareta tana baya kadan kadan doj tayi tunanin ko shaqeta zaiyi.
Yanda ya matso dab da ita nunfashinau na gogan na juna tayi saurin rufe idanunta tana jiran shaqa taji akasin haka, bakinshi yakai saitin wajen kunnenta ya soma magana “kinga ghost ne?,” saurin bude idanunta tayi tana mamakin tone din dayayi mata magana dashi, so soft and cool, suna hada ido kuwa ya danyi wani murmuahi ta gefen bakinsa trying as much as possible to tone down his anger towards all of them “thank you”
Da mamaki take kallonshi fa irin sosai, kamar bashine ya shaketa ba dazu, yanxu kuma he’s thanking her for what?”
“You’re my life savior, and I’m sorry for misjudging you”
Yana kaiwa nan ya wuceta yna wani makirin murmushi ganin ta sandare da mamaki fal akan fuskarta, aaurin juyowa tayi harya bude sitting room dinshi zai shiga ta kama hannunshi ta rike, kamar ta zuba mai wuta haka yaji wallahi amma ya daure.
“I’m i dreaming? Yanxu ka yarda dani kenan?”
Girgiza kanshi yayi irin baiji dadin nan ba yace “banyi tunani kece me sona tsakani da allah ba sai yanxu, i was blinded my whole life, kinata kokarin nunamin abubuwa amma na kasa yarda”
“Oh my god!!! I’m so happy, daman na fada ma, hidaya bata sanka batason ganinka,tayi attempting kasheka countless of times,” ta rungumeshi sosai tana sambatu yayi baya,
“Ni kadaice nake sonka, and I promise to protect you, lets take her down together, i have evidence da yawa danake ajiye dashi, nayita kokarin ganin na tura maka kayi blocking dina”
Wow, cin amana kan amana kenan, uwa daya uba daya balle kuma shi da suke step, duk yanda akayi hidaya trusted her shiyasa take samun damar harharda evidence.
hannu daya yasa ya fiddota daga jikinshi yana jin wani kyan kyami kamar zaiyi amai.
“Zan iya yi maka komai baby taj, yarda dakayi dani ka gama min komai, taj, i will give you the whole world taj,”
Yatsine fuska yayi yace “I’m tired let’s talk tomorrow, duk abunda kikace nayi zanyi, i want to fully trust you, sannan karki boyemin komai please FADYY”
Kai kan fadwa kamar zai fashe, har wani zut zut takeji a jikinta, itafa ta gama mace mashi gaba daya, “yes bazan taba boye maka komai ba, zan baka komai, you my life my world my everything, takardun inheritance dinka ma duk zan baka su, i have them with me, and don’t forget to unblock me okay”
Shuru ya danyi yana nazarin maganar takardu datayi, yayi tunanin suna wajen hidaya, but mey zai kaisu wajen fadwa anyways wannan bashine matsalarsa ba hasalima ta kawo mashi sauqi ne, komai is going according-to his plan, just the way he planned it.
“I will unblock you Kije zan huta”
Ido daya ta kashe mashi sannan ta futa daga dakin, wallahi kamar tayi kyautar duniyar gaba daya haka takeji.
Tana fita yayi smirking,a tunaninta zaiyi tunanin fada mashi sirrikan hidaya datayi zaisa ya yarda da ita, well she’s another villain on another side, yayarshi da zata nemeshi da zina ay nata makircij dabanne, halinta ne da kudirinta ya riga na hidaya futowa.
Wanka yayi da ruwa mai shegen zafi sosai sannan ya fito daure da towel.
Wayanshi ya dauka yayi unblocking dinta, kamar jira take kuwa ta fara turo mashi mesaage yayi banza da ita saida ta tura mashi recordings dun datayi ita da hidaya tukunna yace mata “goodnyt”
Bangarensu khaal around karfe sha biyu na dare yana zaune ya jingina da bango mutallib ya shugo dakin don ya leka shi, akwai wani likita da suka kawo ya mashi allura yanata barci throughout sai wajen yanxu ya farka.
Mutallib na ganinshi zaune yayi saurin karasowa inda yake ya mashi sannu da jiki,ganin har zuwa lokacin hankalin khaal ba a kwance yake ba yasa mutallib ya soma mashi bayanin komai
Bayan karyar mutuwarshi da akace yayi da yanda ya shiga gidan ya badda kama ya hadu da sabeeha sannan ya shida mata komai, da yanda hidaya ta ganoshi ta nemi a kamashi cikin ikon allah aranar ne kuma sukayi accident daya sa taj ya dawo hayyacinshi, ya warke.
Bai boye mashi komai ba ya fayyace mashi yanda yayi approaching taj din, da yan bayanai daya samu daga taj din gameda zaman takewar da yayi da sabeeha da yanda tabar gidan.
A karshe ya shaida mashi yanda yayi hanya aka turata domestic workers organization har sukayi locating agents din da suka kawota aka kaita gida, saida ya tabbatar ma da khaal taje har nigeria cikin koshin lafiya.
Sai a lokacin khaal yaji sauqin abund ayakeji aranshi, bayanan mutallib sun sashi cikin salama, gashi ya zayyane mashi yanda taj ya karbo mashi gidanshi ya saya da kudinshi sannan ya tashi tundaga nan saudi ya wuce Egypt har wajen iyalinshi ya basu hakkinsu sannan ya masu tara ta arziki, jin wannan kadai saida yasa khaal hawayen farin ciki, yana taisayin taj, yaro baijiba bai gani ba ya shiga kuncin rayuwa.
Waya mutallib ya aje mashi doj ya samu ya kira madam dinshi don har yanxu bai shaida mata ba.
Mutallib na fita kuwa ya kasa hakura saida safe yayi dialing number ta, wajen sau uku yana kira ana hudu ta amsa cikin barci dontayi tunanin wani abu ne ya faru da taj don suna communicating sosai da mutallib.
Tana jin muryarsa bazata taba mantawa ba, muryarda tayi bankwana da ita har abada, me zatayi banda hawaye in full shock, don kafin tayi barcin nan saida tayi hawayen rashin mijinta, “ban mutu ba madam, ina raye”
Babu abund atake sai innalillahi tana jin abun kamar mafarki, saida ya kwantar mata da hankali and bai shaida mata komai ba gameda abunda ya faru yadaice mata she should trust him kawai, its was a sweet and emotional moment, yayi ta lalashinta tana kukan shagwaba na kewar dan tsohonta lol😂
The very next day, taj na tashi yayi wanka ya fito bayan ya gama shafe shafenshi saiga knocking, sannan aka bude kofa, to his greatest surprise yaga fadwa ko kayan barci bata cire ba ta karaso har inda yake, ta nemi kissing din kumatunshi ya dakatar da ita.
“Not today please”
Murmushi kawai tayi ita idan har zai dunga sauke mata murya haka ay ya gama mata komai.
Takardun data shugo dashi ta miqa mashi a hannun shi kuma original copy ba fake ba tana murmuaahi tace “as promised,”
Karba yayi ya karance tass, kuma yasan original ce, “wannan ce original copy, ukty batasan cewa she has the fake one all this while,”
Girgiza kai yayi yace “ya akayi bata sani ba”
“Nayi bribing lawyer dinta”
“Wow..so batasan original din na hannunki ba”
“Yes..” ta bashi amsa tana kama hannunshi,
“Let’s hangout”
“Sure by the night” ya bata amsa
Kamar ta huga tsalle haka taji “oohh i love that”
Tana kaiwa nan ta fuce, duk da tunaninta wani abun zasuyi da dare mahaukaciya.
Wayarshi yayi saurin dauka ya kira merk ya shaida mashi su fara proceeding transfer of inheritance dinshi saboda ya samu original copy din transfer din da hidaya tayi.
Yana kashe wayar kawai ya girgiza kai, yau dinnan zai tada masu da babban bomb dinda basu taba expecting ba.
By 12 ya shirya yin live press da reporters yanxu its about 8 na safe a gaggauce ya gama shirinshi sannan ya futo haduwa iya haduwa Masha allah.
Fadwa ana zaune kan dining tana jiranshi hartaci wanka batasan yayi fucewarshi.
Hidaya ta kirata yafi sau nawa taqi dagawa.
Wajen khaal ya fara zuwa, lokacin yana barci don an sake mashi allurar nan wannan yasa basu sake haduwa ba, sai mutallib da suka dan zanta ya shaida mashi plans dinshi, mutallib baiyi tsammanin taj will be this tough ba sai yanxu, and he’s so happy daya gane komai tun ba’a zaunar dashi bama.
10 yabar wajen su mutallib ya shigo taheel
Company, bai tsaya ko’ina ba sai office dinshi merk ya shugo da professional lawyer shi da sukayi hiring ya shiada mashi sun gama processing komai.
Lawyer na tafiya merk ya bashi recovered cloud dinshi da password daya buqata.
Ya saka a dayar wayarshi take komai ya dawo, hannunshi na rawa ya shiga last message din da aka tura, sallamar merk yayi sannan ya soma playing recordings din, magnagnun fa sosai from unknow source don bai san dawa hidayar ke magana ba don an chanza voice din other party din.
Saida ya gama tass sannan ya aje a gefe ya dafe kanshi.
Wallahi baisan time yaja ba sosai don its almost 12, merk yayi knocking ya bashi umarnin shugowa, nan ya shaida mashi its about time, jinjina mashi kai kawai yayi ya miqe ya dauka suit dinshi ya saka kan white pale rigan jikinshi sannan ya kwashi wayoyinshi duka ya fito a natse, bai tsaya ko’ina ba sai hall din da suke press conference.
At that last minute hidaya taji labarin journalist din da taj ya tara unexpectedly without her knowing, kiris ya rage bata kori secretary dinta ba wanda yaqi fada mata da gangan, jiya jiyan nan merk yayi making deal dashi yanda taj ya umarta akan yayi considering wani path zaibi, inda yasan cewa aikinshi tare da ita is not guaranteed ko kuma yayi considering deal din da suka zo masu din ya basu hadun kai, dake yasan hidayar ciki dabai wannan yasa ya zauna yayi dogon nazari sosai.
Kamar yanda ya qayyade 12 daidai babu ragin lokaci aka bude hall din ya shugo gefenshi merk ne da lawyer shi, gaba daya wajen ya karade da kyass kyass kyass anata faman daukanshi hoto, masuyin live harsun fara dauka manya manyan gidan tv stations duk an dauka.
Bakin stand din ya tsaya merk ya gyara mashi mic din gabanshi sannan ya dago ya kalli ilahirin reporters, da journalist din dake zazzaune,ba tare sa wani bata lokaci ba dukda sun sanshi ya gabatar da kanshi with full confidence sannan ya nemi su bashi aron hankalinsu gaba daya zaiyi wani quick revelation.
Nan ya soma masu bayanin accident din daya faru dashi shekara biyu da suka sannan ya shaida masu halin daya shiga which result to amnesia daya samu, wanda yayi sanadiyar loosing memory dinshi gaba daya kuma kwakwalrshi ta koma ta yara.
Tun kafin su fara mashi tambayoyi ya dora da ayanxu haka da yake magana dasu ya samu lafiya bashida any health issues,”
Yana kaiwa aya wani ya miqe baima nemi izini ba yace “zamu iya sanin yaushe ka samu lafiya? Gaba daya ko wata bamuyi ba muka samu labarin baka warkeba”
Murmushi taj yayi yana kallon screen yasan hidaya na kallonshi ayanxu haka,
“Na dauka zaku fi buqatar sanin yanda akayi nayi accident babu report din yanda abun ya kasan ce, whether its a hit or run or it’s not”
Nanfa waje ya kachame, views suka karu, yabar mutane cikin curiosity, “yanxu zaka karbi kamfanin ne?”
“Yes idan akwai buqatar hakan”
“Shin kana tunanin na kusa dakai suna da sa hannu cikin rashin lafiyarka?”
“Kamar wa kenan?”
“Khaal” wani ya amsa shi kai tsaye, “saboda shine mafi kusanci dakai da zaiyi hakan, bayan laifufukanshi da suka bayyana,
“What if shima and tricking dinshi ne? I have never had a terrible relationship with him, he will
Be the least person da zanyi suspecting, and i believe you’re all mistaken, but i will take legal action and the truth shall prevail”
“And lastly, I’m here to compete, to build and to bring the best out of the taheel company,i have pass down my inheritance to my self”
Yana gama magana ya sauko kasa ya fito daga wajen, yana sauke ajiyar zuciya, people still think and suspect khaal for hidayas wring doing amma yayi alkawari saiyayi clearing sunan khaal da zarar ya samu duk wani proper evidence.
Ana gama wannan press conference din aka kira board meeting, gaba daya shareholders sun hallara kowa da kowa duk an fifito, shida ya kura meeting din shine last to enter the hall, ana zazzaune saiga hidaya ta shugo walking majestically yau ko tashi tsayen da suke mata basuyi ba.
“What is this meeting for without my consent”
“Please have a seat mrs hidaya”
Daya daga cikin major shareholder ya mata magana, tun kafin ta zauna take kallon taj wani irin kallo mai wuyar fasaara, tana zama suka soma bayani.
“Concerning our fears and concerns about the company m, we have come to conclusion that munason new management”
“Wait what??? “ ta daka masu tsawa
Mai magana bai dakata ba ya cigaba “yes madam, the rightful heir to this company ya samu lafiya, bakida sauran excuse, we need you to step down madam”
Tana daga zaune taba sauraronsu, kwata kwata batayarda ta nuna masu ta wani damu
Ba tace e “and kuna tunanin kunada right din yin haka?”
“Yes madam,” suka aje mata papers din transfer of inheritance da taj yayi, ya maido da komai
Nashi daga wajenta.
Surprisingly take kallon papers din masu kama da original copies”
“Those are fake!!”
Sai alokacin yayi magana yana kallon idanunta “those are original, and by the way i don’t see any reason you’ll Be against this, koda kuwa they are fake i have the right to have whats rightfully mine”
Girgiza kai tayi ita kadai tasan abunda takeji aranta, tayi sake mugun sake ma, she underestimated him, she was shocked dataga live press din da yayi, but yanxu shes more shocked with this, anyways babu yanda ya iya, he can never have the company.
Nan aka fara vote, aka ajiye box kowa ya rubuta suna kan wani card suka rufeshi sannan aka jefa cikin box din, shida ita na zaune, sai faman jujuya kujera take tana kallon cikin idanunshi.
Bayan an gama wanda ke announcement yace “gobe zamuyi announcing wanda ya chanchanci zama chair-leader.
Daga nan aka watse aka barsu shida ita.
Ya miqe tsaye harya juya zai fita don ko magana bayajin yana da time din yi da ita, “i underestimated you tajudeen,”
Dan juyowa yayi ya sake kallonta, ta miqe tsaye tana tafiya a hankali, “i warned you not to play games with me, don’t be disappointed when you see what I’m capable of”
Zura hannunshi yayi cikin aljihun wandonshi yace “idan har ance min zamu kaiga haka zan karyata, and by the way i’m already disappointed in you, i trusted you with my whole life, i never knew it was a a disguise mask on you,”
“Hahahah…ta kyakyace da dariya, sannan ta shafa fuskanshi “oh noo, i don’t know what got into your head, but you’ll surely regret this, i will forget that we’re related, this company was mine and will forever be mine, a bastard can never inherit, kana tunanin idan sukasan you’re a bastard zasu yarda su baka responsibility din kamfanin nan?By now nasan so much has got into your head, and i don’t fucking care, that to show you how far i can go, listen to me carefully taj, i hate you, i hate the sight of you, i hate everything about you, kai wata annoba ce data shugo cikin rayuwarmu, ka tarwatsa farin cikin mu, and you expect me to open my arms for you?? Hahahah a bastard???? No neverrrrrr, baka wulqanta ba tukunna da saura,”
Word din bastard dinnan ya dokeshi sosai ba kadan ba, ya runtse ido ya bude ya kalleta, “why? Why? Saboda mahaifiyarku?,
Idanunta sunyi rudu rudu sunyi jaa
“Don’t you dare!!!don’t you dare, karka kuskuran sunanta ya kara futa daga bakinka, you bastard”
At this point abun ya kaishi bango,
“The sooner you accept the fact that i am the only heir to the taheel the better for you, and mind you i’m ready for all of you, i will make sure that you regret abunda kika yi ma khaal, ni zan iya hkura da abunda kikamin but khaal, i will clear his name bfr kiyi nasarar kasheni yanda kikasoyi shekara biyu da suka wuce”
Yana kaiwa nan ya futa ya barta tsaye hankali tashe, what? He found out?, ya gano komai? Did he find out she’s behind it?….
Yana barin hidaya ya futo ya shiga motanshi bai tsaya ko’ina ba sai hideout dinnan, yana zuwa ya tadda khaal zaune bayan sun gaisa khaal ke fada mashi yaga press conference da yayi, and he’s happy zai karba kamfanin saidai yana ji mashi hidaya, shi yasan hidaya ciki da bai, bazata taba yarda komai yayi mata slipping a hannu ba cikin sauki, wanna yasa khaal yake mashi fargaba.
Fadwa
Tunda safe tasha wasu kwayoyi take barci, kwata kwata batasan abunda ke faruwa ba, hidaya ta kirata yafi sau dari, har sauda ta dawo gidan ta shugo daki wajen karfe bakwai ta ganta a jeme.
Rai a bace hidaya ta tashe ta tashi furgigi, “har kinada time din yin barci wannan dan iskan yaron yayi trumbling akaina, he knows everything, and I don’t know iya adadin abunda ya sani, he wants the company”
Hamma fadwa tayi ta kalleta tace “shine zaki tada hankalinki ukty? Yanxu ni kin tadani daga barci na mai dadi nasan kuma at the end of the day you’ll find solutions to all of these problems”
Kallonta hidaya tayi ganin hankalinta a kwance yake saita tuna da takardun da khaal yayi presenting, how dis he get that?
Kama habarta hidaya tayi kamar zata shaqeta tace
“Fadwa tell me, is therw something that i need to know?”
“Ukty me haka zaki kasheni ne”
“Don’t play with me fadwa, i trust you the most”
Fadwa ta kalleta bayan ta cire hannunta a wuyanta tace “yanxu kina tunanin zanci amanarki ne? Kin manta ciki daya muka fito? Why would i do that?”
“You better not do that”
Tana kaiwa nan ta ja jakarta ta fuce.
Fadwa ta bita da harara tana duban time taga har wajen karfe takwas, plan dinta ya tuguje gaba daya saboda wannan shegen baccin, ta masu reservation ita dashi around 6-8 yanxu kuwa