Author : Queenmerh Category : Complete Novels
wajen, shima mai kasimbar bai zauna ba ya miqe yabar wajen, ya nufi ind ayayi parking motarsa yana shiga ya rufo kofar ya zauna, dake motar full tinted ce baka hango wanda ke ciki kwata kwata,
Ajiyar zuciya ya suake kafin ya zare facing cap din sannan ya soma cire kasinbar dake kan fuskarsa, take fuskarsa ta bayyana, mutallib ne ya badda kama gaba daya bazaka taba gane shi ne, kallon envelop din yayi kafin ya soma warwareta, tunda ya dara karantawa yanayin fuskanshi ya sauya sosai, tsoro furgici tashun hankali duk ya bayyana akan fusknshi, “khaal yana raye!!!!!”
Ya furta ahankali, take komai ya soma warware mashi gaba daya ya shiga rudani lokaci guda, tabbas akwai alamun tambaya a tattare da mutuwar khaal, maisa bai lura da hakan ba sai yanxu? Tunda akace an tsinci gawar khaal a cikin ruwa sannan aka kayyade suicide ne ya kasa yarda da komai, shi zargin daya dunga yi har zuwa yanxu shine kashe khaal din akayi,kuma tricking dinshi akayi dubaga sharrin saka aka yi mashi, da karyayyakin da aka shirya mashi, sai yanxu ma ya kara tabbatar da abunda yake gani a gabanshi gaskia ne, zoben khaal da aka gani a jikin gawar da aka tantace tashi ce bashine zai tabbatarda khaal dinne ba, na farko dai zobe za a iya cirewa a saka ma wani don ace khaal dinne sannan za a iya yin irinshi dukda zobene mai shegen tsada ne sosai, bayan wannan ma yanda aka dunga covering up komai da kayyadar da mutuwar shi da akayi cikin gaggawa abun tambaya ne.
Kallon paper yasakeyi yana karanta forencis result din na asali, wato wanchan da aka fitar ma duniya fake ne, rubutu ne akan paper din daga ofishin forensics examination inda result din ya bayyanar da asalin gawar, inda aka tabbatar ba gawar khaal bace, which means khaal na raye kenan,
Shuru yayi yana nazari, daman tun bayan accident din daya afku lokacin daya dauko sabeeha da taj zasuje asibiti bayan ya fuskanci binsu ake a baya yasan shi hidaya ke hari, wanna yasa lokacin da accident din ya faru ya fice daga cikin motar ya gudu.
Dukda yayi laying low hakan baisa yayi binciken lafiyar fatima da taj dinba bayan accident din inda ya gano cewa basuji wani mummunan rauni ba, don a ranar saida yaje asibitin ya tabbatar hankalinshi ya kwanta, dukda shi yaji rauni sosai sanadiyar accident din kuma yasan hidaya bata fasa nemanshi ba, don yaji labarin wajen yaronshi dake mashi aiki karkashinsa yanda tasa a buncika asibitici dukdan a kamashi, yayi jinyar wajen wata guda kafin ya samu sauki sannan ya cigaba da buncikensa don bazai yuwu ya koma gidan ba donta gane fuskanshi.
Yanxu ma haka yana tailing dinta ne inda ya fuskanshi tana zuwa island dinnan kusan duk end of the week, duk binciken dayayi don ya gano inda take zuwa ya kasa ganewa don gaba daya maaikatan dake wajen kamar ta saye su, babu wanda yake bude baki balle yayi magana, duk bribing dinsu daya dunga yi ba a dace ba, karshe ma dai dayaga dukkansu they are loyal to her gudun karsu zargi wani abun yasa ya daina tambayar ya zuba idanu don samun chan din making move don ya tabbatar akwai abunda take yi achan din.
“She must be hiding something over there……”
Yana fadin haka ya sake duban paper din take ya zaro idanu, abund azuciyarshi ke raya mashi ya kasa yarda da hakan, dole ya tabbatar da gaskiyar lamari.
Cikin hanzari ya juya akalar motarshi yabar wajen….
Wani cafe dine ya nufa kai tsaye inda zasu hadu da yaronshi, yana shugowa ya tunkari seat din dayayi masu reserving, yana kokarin wucewa sukayi karo da wani, cikin hanzari mutallib ya duga ya tattara mashi wayarshi da key din motarsa, “i’m sorry!!!” Ya fadi haka ya dago donya miqa ma wanda ya buge din, take idanunshi ya sauka kan fuskar taj, yanda yake kallonsa haka yake kallonsa, muryar taj dinne ta dawo dashi daga tunanin daya shiga with shock surprisingly yake kallonshi, “its okay”
Yana fadin haka ya karba keys dinshi ya fuce daga cafe dine din, yabar mutalib saroro mamaki ya gama cikashi sosqi, yakai kusan 2mins a tsaye ya kasa motsawa, kamar wand aaka tsungula ya juyo ya nufi hanyar futa daga retaurant din daidai nan taj din ke shirin shiga motarshi, ya kunnata, yana yin reverse yabar wata mota tabi bayan motarshi, ba karamin mamaki yayi ba don da farko ya dauka mai kama dashi ya gani, saidaga baya ya tabbatar shi dinne fa, “ya samu sauki kenan? Ya dawo hayyacinshi? Maysa baiyi bincike ba? Fatima fa?” Tambayoyin daya dunga ma kanshi kenan, tun bayan daya tabbatar da lafiyarsu lau ya maid ahankali wajen ganin ya samu duk wani evidence dazaiyi amfani dashi against hidaya.
Bangaren taj tunda ya shiga motar hannunshi nakan steering babu abunda yake sai tunanin abubuwa da dama, dagowa yayi yana kallon mirror dake hasko mashi bayanshi, ya kura da motar dake biye dashi a baya, tunda ya fito daga gym ake binshi cikin motar.
Redish Lower lips dinshi ya kama ya cije shi sexily har yana jaa sosai kafin ya sake shi a hankali ya shafa kanshi ahankali ya daura dayan hannunshi kan steering ya juya kan motar, dake sport car ce tuni ta kece ma motocin dake gabanta kan kace me gaba daya ya bace ma wanda ke biye dashi, saida yayi nisa sosai ganin ya bace ma motar dake binshi ya rage speed ya sauke wani side smirking ya nufi gida.
Yana parking ya futo da bag dinshi yayima motar key ya nufi cikin gidan, wani irin azababban ciwon kai yakeji sosai yau dinnan,cikin gidan ya nufa kai tsaye, tundaga kofar shugowa ya soma jin muryar sonata da afiya, koda ya iso wajen sitting room din ko kallon inda suke baiyi ba ya nufi hanyar stairs, sonata kuwa tana hangoshi tayi saurin miqewa tabi bayanshi,afiya ta bisu da harara, tunda tabiyoshi a baya tana kiranshi kota kanta baibi ba ya nufi part dinshi, yana saka konshi cikin sitting room din ya maida dubanshi ga couches din dake wajen, kamar wadda ke tsumayar ganin wani abu a wajen, har sonata tabi wajen da kallo itama ganin babu kowa a wajen yasa ta maida dubanta gareshi, “babe! Ka kulani mana,”
Bai amsa ta ba ya shige cikin sitting room ya tunkari bedroom, yana bude kofar ya shige, nanma bin dakin ya soma yi da kallo sonata na biye dashi a baya,gaba daya tama mance warning din daya ja mata na shigo mashi daki,
“Dan allah babe, muje dinner date yau, i will not ask more than this plea…” bata kaiga karaswa ba sabeeha ta fito daga bathroom, shigarta kenan, tunda tasha maganin da ammu tace tasha take ta faman zaryar bandaki, gaba daya indomie dataci ta dawo,gaba daya wani irin weak takeji a jikinta,tun daga nesa ta hangoshi sai sonata dake biye dashi a baya, tunda ta hangita taji wani irin makokon baqin ciki ya tokareta tama rasa dalilin dayasa da zarar ta ganshi tare da sonata take jin haka, kodan tana tuna lokacin data so yi mashi isknacin nan ne,
Kallo daya ya mata ya dauke idanunshi daga kanta, a cikin kallo daya nan ya karanci yanayin fuskarta, saidai shi wannan ba damuwarshi bane don haka ya karaso bakin gadonsa ya ajiye jakarsa akan gadon, sonata tubda taga sabeeha ranta ya baci, idanunta nakan cikin sabeeha, ayanda take ganinta a gabantan nan da tanada dama zata shafeta har lahira, ta zamo mata katanga tsakaninta da taj din, ga wannan cikin da take ikirarin nashi ne idan ta tuna da wannan kamar ta haukace.
Sabeeha na daga tsaye yabi ta gefenta ya wuce bathroom abunci ko kallonsu gaba daya bai sakeyi ba.
Sabeeha saida ta tabbatar ya shige bathroom din wani abu ya raya mata arai, “yau zan koya maki hankali karamar yar iska”
Tana fadin haka ta tunkari inda sonata take, taba karasowa sabeeha ta kalleta daga sama har kasa kafin ta murmusa tace “an biyoshi kenan? Ke baki gajiya ne? Kullum kina biye dashi kamar mayya,Ina pride dinki…oops why should i even ask someone that doesn’t even know what that is, youre ao cheap….”
Tunda takai karshe sonata ke kallonta, gaba daya da turanci take maganar kuma grammer djnta na fita yanda ya kamata, ba karamin tainata sonata tayi ba sai yanxu ne take ganin yarinyar nan A ce itama, a haka kana ganinta kamar batasan abunda take ba, maganarta na karahe ba karamin sosama sonata rai yayi ba idanunta yayi jaa sosai, bata gama shanye takaicin maganar sabeehar ba ta sake jefo mata wata maganar data kara qular da ita.
“kinga banbancin dake tsakanina dake kenan ko? Kince ni matarshi ce a lokacin da baya cikin hayyacinshi, kuma bazai taba accepting dina ba ko? Well yanxu i have his child in me, and I’m still standing as his wife, and you? Tell me who you are to him?Hmm?…you’re nothing but a leach, saidai ki bishi amma bazaki taba samun abunda kike nema ba a wajenshi, and lastly let me warn you, nan ba wajen zuwanki bane duk sanda kikaga dama,karki sake shugomin bedroom nida mijina haka kai tsaye, idan shi zakibi yanda kika saba idan ya futo saiki sameshi, karamar yar iska” ta karashe da hausa, ran sonata idan yayi dubu ya baci sosai, harta daga hannunta zata sauke akan sabeeha ta daga ganin taj a tsaye yana goge kanshi da towel, idanunta ne ya sauka cikin nashi, daga nesa tana hango cikin kwayar idanunsa sai kawai ta cije lebe ta sauke hannunta ta juya ta fuce a fusace, sabeeha dake tsaye ta sauka hannunta zai sauka kan fuskarta, don itama a shirye take taci ubanta, saikuma akasin haka data gani, har sonatara ta fita bata bar mamakin hakan ba, koba komai dai ta shaqa sosai kuma daman hakan takeso.
Juyowa tayi karaf idanunta ya sauka cikin an taj din, yana mata kallo daya ya dauke idnaunshi, itama tayi saurin dauke nata ganinshi tsaye da towel, a kugunshi, gabanta har wani bugun uku uku yake ganinshi haka da tayi dukda kallo daya tayi mashi tayi hanzarin dauke idanunta, take cikinta ya sake hautsinawa tayi saurin tunkarar bathroom ta dunga kwara amai, yawanci aman ma na ruwa ne, duk wannan aman da takeyi daman don ya gani ne shiyasa ammu tace ta dunga shan maganin wannan zaisa ya kara zama convince akwai cikinshi a jikinta.
Ta dade sosai tana aman kafin ta futo daga bathroom din, lokacin data shigo bathroom din ya wuce closet din room, idanunta ne ya sauka kan jakrshi dake kan gadon, daukar jakar tayi ta tunkari closet din ta kwankwasa kofar, yana kokarin sanya rigar jikinsa tayi knocking din,kamar bazaiyi magana ba chan kuma ya rage murya kamar wanda ke kyashin yin magana yace “yes”
Kwata kwata bataji ba saida ta sake kwankwasa kofar, sannanta bude kofar, lokacin harya gama saka kayanshi ya juyo, ya dubeta, idanunshi ya suaka akan jakar shi dake hannunta, tana jin saukar idanunshi a jikinta kanta a kasa ta tunkari inda taga yake yawan ajiyewa idan ya dawo ta ajiye mashi, takalmanshi daya cire a wajen suka ta tattara su ta ajiyesu wajensa ya kamata, tunda ta fara wannan hidimar yake kallonta yana nazarinta, “shi abubuwan da takeyi ma gani yake kamar pretending takeyi, kwata kwata bai yarda da itaba, she must be up to something” take maganganun dayaji sunayi da sonata ya zo mashi akanshi, daidai nan ta dauki towels din daya ajiyesu a kan island harta nufi hanyar fita zata kaisu toilets tajiyo muryashi a kausashw har saida gabanta ya amsa.
“Stop!!!!!!” Ya dakatar da ita kafin ya tunkari inda take ya zagayo ta gabanta yana fuskantarta tana fuskantarshi, tunda ya tsaya agabanta kamshinsa dake fisgar duk mai shaqa ya shammaci hancinta, saida ta runtsw idanunta sosai, she can feel his presence agabanta kamar anyi magneting dinshi da zuciyarta, ta kasa gane dalilin dayasa takejin zuciyarta na karata da zarar taji kusanci dashi, towel din dake hannunta ya warceshi daga hannunta sannan ya dubeta fuskarshi babu wasa ko kasan idanunshi sunyi kifi kifi ya danyi jaa sanadiyar ciwon kan da yakeji yace “karki sake taba anything that is related to me, I don’t ask that from you, ban buqaci hakanba,i made it clear dazu, you’re nothing but a maid don’t pretend or act like a wife,understood”
Tunda ya soma magana ta dago da idanunta tana kallon cikin idanunshi, idanunta sun mashi wani irin kaifi sosai,yar tsuka yayi ya fuce daga closet din ba tare da ya sake kallonta ba.
Yana futa ta sauke ajiyar zuciya jiki a mace, he’s so tough to deal with anya zata iya abunda ammu tace kuwa, ta yaya zata samu kusanci dashi idan ya hanata kyautata mashi, ta dade sosai a tsaye anan kafin ta fito jiki a mace, ko kallon inda yake batayi ba ta wuce sitting room ta zauna.
Ta dade a zaune ta kura ma tv idanu babu abunda take sai tunanin maganarshi, har wajen karfe biyu, daidai nan ya futo daga bedroom din ya shige kitchen, tana kallonshi ta gefeb idanu ya shiga ya fito da chocolates a hannunshi da yawa ya kwaso su.
Saida ya shiga daki ta sauke ahiyar zuciya,sai alokacin ta tuna da wanda ta dauko dazu da safe, yana nan ind ata ajiye kan table, dauka tayi ta bude ledar, tund atake bata taba ganin hadaddrn chocolate irin wannan ba, take taji miyau ta ya tsinke ta kai baki ta gutsira kadan taci, saida ta lumshe idanu ta bude,ta cigaba da tauna, tana cikin tauna ta dan dakata jin kanar ta tauna abu kanar gyada kuna ga kamshinta, cikin hanzari ya duba chocolate din da kyau wajen inda ta gutsira taga peanut a ciki, cikin hanzari ta zaro idanu batasan lokacin data yarda wanda ke hannunta ba cikin hanzari ta mike ta nufi dakin nata cikin sauri harda dan gudunta, tana bude kofar ta hangoshi zaune ga laptop a gefenshi da alamu aiki zai fara, hannunshi ta maida idanunta a wajen take tahango exact same chocolate din data sha yanxu harya bare ledar yana kokarin kaiwa bakinsa budo kofar datayi da gaggawa yasa ya kalli inda take, gaba daya ta gama tsurewa, yana ganin itace ya kauda idanunshi akanta ya maida kan laptop din dake lap dinshi yakai chocolate din bakinsa, kamar an wullota haka ya ganta a gabanshi ta duqo daidai fuskarshi har nunfashinsa na gogaggay da nata tayi saurin amshe chocolate din dake hannunshi, sai faman haki take saboda dan gudun datayi mai tattare da tsoro da fargaba, da mamaki yake bin fuskarta da kallo, hazel idanunta kadai idan ya kalla wani iri suke mashi, sai yau ya samu ganin proper view din fuskarta saboda taba dab dashi, tana da fully lashes zaro zaro da suke karama eyeball dinta kyau,brows dinta ma kamar zasu hade tsabar cika, ga hancinta kamar ab tsaga kara, daidai fuskarta, saurin kauda kanshi yayi itama tayi saurin gyara tsayuwar ta tana fuskantarshi, gaba daya tama rasa me zata ce mashi, saida taji muryarshi, “whats the meaning of this”
Kuru tayi mashi da idanu tama rasa me zatace mashi, “daman naga akwai…”
Kasa karasawa tayi ganin irin kallon da yake mata sai kawi ta sauya magana tace “inason naci ne”
Wani irin kallo ya mata irin whats this?har zaiyi magana kuka ya fasa tunawa da she’s pregnant, yanxu haka zaman da yake ma buncike yake akan pregnancy, what to expect and what not to, ayanda buncikenshi ya bashi taste din mai ciki daban yake, musamman during early pregnancy,
Duban gefenshi tayi ganin babu mai peanut din a cikin wand aya kwaso sai wanda ta amshe yasa ta sauke ajiyar zuciya ta fuce daga dakin ya bita da kallo.
Tana futa ta nufi kitchen,ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya tace “innalillahi that was so close,”
Ta dade a tsaye tana tuna lokacin dayaci peanut dinnan yanda nunfashinsa ya dunga daukewa, ba karamin tashin hankali ta shiga ba,tunawa da yana dasu dayawa a fridge yasa cikin hanzari ta bude Fridge din ta soma bincike chocolate din gaba daya saida ta tsince mai peanut din tass kafin ta sauke ajiyar zuciya, “allah ya taimaka baici ba, inaga baisan akwai peanut a ciki ba,gwara na kwashesu duka kawai,”
Tana fadin haka ta kwasosu duka tavrufw fridge din ta nufi zuwa sitting room ga zauna, daidai nan ta dago idanunta ganin kamar an shiga bedroom dinshi, kauda kai tayi ta zauna ta ajiye chocolates din a gabanta, kwata kwata bata lura da wanda ya ajiye mata ba kan table.
Bangaren taj tana fita ya bita da idanu, yana nanata maganar datayi aranshi,samun kanshi yayi da daukar sauran chocolate din ya fita daga bedroom dinshi, yana fitowa sitting yaga bata nan, sai motsin daya soma ji a kitchen,tun kafin ya karasa cikin kitchen din ya jiyo muryarta inda take maganar peanut, chal ya tsaya yana nazarin maganar tata da mamaki, duban chocolate din yayi a take ya duba content din ingredients din dake ciki, take yaga peanut a ciki, yayi mamaki sosai don saida ya fadama workers din shop din daya sayo a wajen su bashi chocolates din da babu peanut a ciki kwatakwata saboda hes allergic to it, yanxu dayaci da shikenan zai iya shiga risk reaction sosai, take ya tuna yanda ta shugo daga dakin ta kwace daga hannunshi, daga yanda take magana ma ya gane ta karbe ne daga hannunshi saboda tasan hes allergic to it, kuka zaisha wahala sosai idanda yaci, ya dade sosai yana processing komai a wajen, kuma yana kallonta daga nesa, “why would she stop him? Meysa ta dakatar dashi?kuma maisa taqi fada mashi?”
Yanda ta shigo hankali a tashe da yanda ta tsorata lokacin da yana gab daci ne ya fado mashi arai
Ganin tana kokarin juyowa yasa ya juya ya shige bedroom dinshi, yana tunani, there’s something about this girl dayakasa predicting.
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 68
Tunda ya shigo bedroom din ya zauna babu abund ayake sai nazarin abunsa kunnuwanshi suka jiyo mashi, yana nan zaune ta shigo bedroom din, tunda ya dago yake kallonta ya kasa dauke idanunshi, yaqi yarda da abunda zuciyarshi ke raya