Author : Queenmerh Category : Complete Novels
magana.
“Didi please ka yarda ni ban shigo rayiwarka dan na cutar dakai ba, ni bance dole ka karbeni a matsayin matarka ba, i just want us to friends yanda muke a baya, baka min fada”
Dan murmushi yayi ta gefen baki,kai komai ma kyau yake mashi dukda yanayin bai chanza ba babu alamun wani expression daya sauya a tattare dashi ya miqe tsaye itama ta miqe.
“Okay”
Wani irin dadi kuwa taji aranta
Ya nufi hanyar futa tace “zaka fita?”
“Yes do you need anything?”
Kamar mai nazari haka ta tsaya tana tunani chan tace “yes ka sayo mana chocolate”
Girgiza kai kawai yayi ya futa.
Ita kuma ta koma bedroom ta gyara mashi ko’ina harda closet da bathroom, sai yanxu ta samu natsuwa ta tuna da maganar da ammu ta mata na korar sonata da tayi, wata iriyar dariyar mugunta ta dungayi su sonata an kara gaba.
Bangaren taj bai tsaya ko’ina ba sai gym nan suka hadu da mutabblib nan yake tambayrshi ashe abunda ya faru kenan,shi baima gane me yake nufi ba saida ya nuna mashi instagram yanda family name dinsu ke trending da mutuwar tareeq, yayi mamaki sosai ba kadan ba, anyways shi abunda ya shafi fadwa da shi tareeq din ba damuwar sa bane abu daya ne yafi bashi mamaki inda ta bada report din cewa basa tare for over a year, wannan kowa yasan karya ne, tayi hakan ne don tayi protecting image dinta, hmm this will be one of the reason da zaisa bazai taba trusting dinta ba.
Bayan few hours ya fito daga gym ya wuce mall ya sayo mata variesties of choclate kamar hauka ya jidosu sannan ya dawo gida. Yana parking ya kwashi abunda zai kwasa ya wuce sama direct.
Koda ya shugo dakin tana zaune kan sallaya don anyi salla, cikin sauri ta miqe da dan sauri ta ta karaso gabanshi tace “welcome back didi”
“Thanks” ya amsata a gajerance tare da miqa mata ledar hannunshi ta amsa tana murmushin dake bayyana kyau na fuskanta mai melting zuciya tace “wowww ashe ka sayo min thank you didi”
Ya shagala da kallonta har yaja kumatunta irin yanda akema yara yace “cute”
Yana fadin haka yabar wajen ya wuce closet yabarta da smiling like mumu😂😂 she can’t believe dis.
Coffee ta hada mashi mai zafi da fruits ta kawo mashi har bedroom ta ajiye sannan ta shiga closet ta fidda mashi da kaya marasa nauyi sannan ta futa donta bashi waje.
Yana futowa yaga kayan yasan ita ta ajiye ya saka sannan ya zauna
Ammu hidaya da afiya kiran duniya sunma fadwa bata picking calls dinsu, su hankalinsu harya fara tashi ma musamman ammu da afiya hidaya kam datasan ta bata wani damu ba.
Sai bayan sati guda tukunna ta dawo gidan, normal normal har wani irin kyau ta kara da qiba batada wata sauran damuwa saita taj.
Haka rayuwa ta dunga tafiya a kwana a tashi babu wuya, tsakaninta dashi yanxu sai kusanci, yana kulata sama sama idan tayi magana, sannan duk wani hidima nashi tanayi babu gajiya, akwai ranar da yana wanke gashinsa ma tayi requesting taimaka mashi, aiko ya kwanta a bathtube face dinshi na facing nata ta taimaka ta wanke mashi yanda sukeyi alokacin da baya cikin hayyacinsa, abun gwanin burgewa.
And he allowed her, bai kawo wani tunani aranshi ba just positive energy🙈
Idan yaga ta dauka abu mai nauyi haka zai hanata, lundry datake masu shida ita ma ya hanata.
Ciki dai baya gaba baya baya, baya girma, hakan yaso ya sashi zama worried amma kuma dayayi reserch saiya gano wasu matan haka nature dinsu yake ciki baya nunawa, ammu kuwa duk sati saita jata sun fita a sunan zun tafi zuwa asibiti nanko ba nan suke zuwa ba.
Afiya dai idanunta na kansu su biyu, tayi laying low saidai fa tasan abunda take kuma tayi alkawarin saita gano koma menene suke boyewa.
A daki ko tare suke kwana shida ita a gado daya, yana daga chan gefe itama tana daga chan gefe, da asuba ko shike tashinsu suyi sallah a tare.
After 2 weeks…
Sabeeha ko tabdage sai janshi take a jiki, harda hira, sannan duk wasu funny event daya faru tsakaninsu saita labarta mashi, haka zatayi ta dariya shidai saidai ya girgiza kai, abu daya daya lura da ita, her life is just about him him him, batada magana sai nashi lokacin da baya cikin hayyacinshi its seems like sunada shakuwa sosai shida ita.
Don ta gama saninshi ciki da waje abunda yake so da wanda baya so, kuma yana hanko taantsar affection a tattare da ita game dashi.
Ahankali ahankali yake gane asalin so da kauna tsakanin mutanen dake around him..sabeeha dai she’s extraordinary, she’s selfless, she’s a happy child, and she takes his happiness first before nata, idan taga yayi shiru daman yana da irin wannan habit din sai yayi shiru gaba daya komai na duniya ya dameshi, mood dinshi gaba daya ya sauya, tana ganin wannan duk zata damu, haka zata dunga tambayarshi meke damunshi? Kotayi mashi wani abu? Ko an mashi wani abu? Kai she’s just extraordinarily different, she cares alot..wanda hakan ke sashi ganin shi he doesn’t have a seamless heart, his heart is like a rock.
Yau ta kasance friday…
Wajen karfe biyar fadwa na zauna a bedroom dinta gaba daya ta gama isolating kanta daga yan uwan nata afiya ta shugo.
As usual intazo dakinta zama kawai takeyi hakan kuwa akayi, fadwa na ganinta ta daga mata gira daya don batayi expecting dinta a cikin bedroom dinta ba.
“Yadai?” Fadwa ta tambayeta
“Kin gama boye boyen naki na kunyan auren scammer, inace kece kemin gori, bansan me nake ba? Bansan me rayuwa ke ciki ba,”
Wani irin kallo fadwa ta mata sai kawai ta dan dara harda tafawa kafin tace “tabbas bakisan me rayuwa ke ciki, kina tunanin bansan abubuwan da yake ba na aureshi?duk wani movement dinshi harma da affairs din da kuke dake dashi”
Da mamaki sosai afiya ke kallonta,harya bayyana akan fuskarta, she was so shocked to the extent that ta kasa cewa komai bakinta yayi gumm.
Murmushi kawai fadwa tayi tace “anyways ba wannan ba meyya kawoki? Hope it’s something that is worth my time da kikazo kina batamin?”
Gyara zama afiya tayi, dake itama yar ayi ce saita basar da maganar tace “i need your help”
“What help?”
Hotunan dake hannunta ta fito dasu ta watsa kan gado, kafin ta soma mata bayanin yanda sonata tabar gidan da yanda suka sama sabeeha abortion pills the next day basuga wani sauyi a tattare da ita ba da futar da sukeyi ita da ammu a sunan zasuce check up yanxu haka hotunan nan ma ta dauka ne inda suka fito kuma basubi hanyar asibiti ba.
“Ina ganin babu ciki a jikin yarinyar nan kuma ammu tasan da haka they are just fooling us, nayi kokarin nayima ukty maganar taqi ta saurare probably tana tunanin zan hada baki da sonata nayi poisoining danta”
Daukan hotunan fadwa tayi ta kallesu gaba daya, “recently akayi hotunan?”
Ta tambayi afiya
“Yes jiya”
Kallo daya fadwa tama sabeeha ta karanceta gaba daya babu wani sauyi a tattare da ita da za ace na me ciki ne, kwata kwata ta dauke attention dinta daga yarinyar shiyasa bazata iya tuna when last ta ganta ba.
Wani irin murmushi tayi na gefen baki daya kafin tace “daman babu yanda za ayi ta yarda dake idan har baki kawo health report dake nuna cewa bata da cikin, anyways kibar komai a hannu na.”
Afiya na tafiya fadwa ta tattara hotunan ta ajiya sannan ta dauka wayanta ta soma dialing wata number..
Misalin wajen karfe tara na dare bayan sun gama dinner hidaya na study room dinta tana duba files fadwa ta shugo.
Kai tsaye ta samu waje ta zauna, saida hidaya ta gama abunda take kafin ta fuskanceta.
Nan fadwa ta baje mata komai abubuwan da afiya ta fada mata da hotunansu da ammu data dauka da yanda suka bama sabeeha abortion pills.
Saida ta gama jInta tsab ta duba hotunan sannan ta kalleta tace “so???? Me kikeso nayi akai kenan? Inma cikin babu shi time will tell”
Fadwa tayi mamaki sosai jin amsar data bata, “theres no time ukty, what if yayi consumating aurensu? What if ta samu cikin?No never i will..i will never allow that”
Hidaya tayi mamaki react dinta saidai bata kawo komai ba tace “do you have a medical prove”
“Tunda bakida shi i dont have time for this..abubuwan dake gabana sune a gabana”
“Ukty its seems like kin manta agender dinmu gaba daya, kina tunanin you have wrapped him around your arms ko? Kin manta abubuwan da muka mashi ko? Ko kina tunani bazai iya karbar taheel ba aduk sanda yaso?naga kinyi sanyi sosai well let me remind you idan kin manta…”
Saurin dakatar da ita hidaya tayi da hannunta sannan ta dubeta tace “ya isa haka…yanxu me kikeso ayi kenan”
Wani irin makirin murmushi fadwa tayi sannan fidda wayarta ta danna wani video, videon da tareeq yayi fabricating shida sabeeha lokacin daya nemi yin lalata da ita taqi bashi hadin kai, a lokacin daya nuna ma fadwa tayi saurin airdroping video din ba tare da sanin sa ba sai hotunan data dauki sabeeha da tareeq ranar da suke backyard ita da barad,
“Tunda babu yanda zamuyi proving fooling din kowa sukeyi ita da ammu why don’t we use this against them..musashi ya tsaneta har ya fara kokwanto shin cikin nashi ne ko ba nashi bane daganan dole ayi bincike harma da DNA”
Girgiza kai kawai hidaya tayi ta dan murmusa.
Washe gari ta kama saturday morning, kowa ya hallara akan dining, taj, ammu, fadwa , afiya barad sai kuma hidaya.
Tunda suka zauna kowa kecin abunda ke gabanshi, har suka gama.
Hidaya ce ta fara tashi kafin ta dubesu tace, “ina sitting room idan ka gama inason magana dakai”
Girgiza mata kai kawai yayi sannan ta futa, fadwa ma ta miqe tabi bayanta follow by afiya sai daga baya after ya gama shima ya miqe, kusan a tare suka fito shida ammu daga dining din zuwa sitting room din, daman sama zata wuce wajen sabeeha sai kuka ta dakata ganin sun zazzauna.
“Lafiya dai?”
Ammu ta fada tana tunkarar inda suke zazzaune, hidaya dake zaune ta hade girar sama da kasa kamar an aiko mata da sakon mutuwa ta dubi ammu tace, “zaki iya zama kema,”
“Toh allah yasa dai lafiya”
Ammu na rufe baki saiga sabeeha ta sauko da head maid dataje ta kirata.
Wallahi ganinsu zaunen nan saida gabanta ya yanke ya bada wani irin dammm da kyar dai ta daure ta karaso ammu tayi mata nuni da kusa da ita ta zauna.
Saida kowa ya zauna hidaya ta fidda hotunan dake gefenta ta watsa su gaban taj, daukansu yayi daya bayan daya yana duban hotunan da mamaki, tabbas idan zai tuna ranar da kayan dake jikinta lokacin da suka fito ita da barad ne har yace mata kar ta sake fita babu hijabi, abunda yafi daure mashi kai shine har a yaushe tareeq ya isa gareta har yana mai janyota jikinshi don jikinsu yayi kusa da juna sosai saboda angle din hoton, karban hotunan ammu tayi tace “menene wannan din”
Shuru tayi ta gama ganin hoton kafin tace “zancen banza, yaushe akayi wannan din, daman nasan wannan taqaddirin yaron babu alkahiri a tattare dashi daman ta taba fadamin yanda yake kai mata hari,kudai wallahi da kwashe kwashen ku, ke kin kawo barauniya kw kuma kin kawo dan iska scammer”
Fadwa dake bakinta baya shuru take “kedai kawai kiyi shuru ammu bakisan komai ba,“
daukan remote dake gabanta hidaya tayi already sunyi screen mirroring daga waya zuwa tv,ta kunna nan take video ya bayyana, wallahi wallahi saika rantse ba fabricating video akayi ba da gaske ne, komai sak da jikin da fuskar hasalima dai babu wanda zaice ba sabeeha bace a jikin video din.
Cikin sauri sabeeha ta miqe hankali tashe tana mai duban taj da ammu at the same time,
“Yanxu wannan yayi kama da shike kai mata hari? Dama chan yar hannu ce dataga shima irinta ne shine take binshi,”
Afiya tayi charaf..”wama yasan irin abunda sukayi a cikin gidan nan, kai wallahil azeem zan rantse maku cikin dake jikinta ma bana taj bane na wannan dan iskan ne don babu yanda za ayi ace wanda baya cikin hayyacinshi har ya iya kwanciya da mace ya biya mata buqatar ta, as far as we know tunda suke tare tun lokacin da aka kawota babu wani abu tsakaninsu iyakacin ta kula dashi.”
Cikin hanzari ammu ta daga mata hannu rai a bace tace “wannan bashine zai baku damar yi mata qazafi ba,”
“No ammu stop it…stop defending her she’s fooling us all..idan baki yarda ma ki saurar wannan”
Nan fadwa ta danna wani voice record shima dai muryar sak ta sabeeha suna conversation ita da tareeq wai har tana cewa itafa leken asiri aka kawota gidan nan kuma zata iya yin komai, idan yana buqatar kwanciya da ita duk sanda yakeso a shirye take saboda ta saba da harkar abundai babu dadin ji, dirty and disgusting talks.
Tunda fadwa ta danna voice din idanunshi suka soma jaa, kanshi ya fara sara mashi yanayinshi ya sauya gaba daya kamar bashi ba ran maza yayi mugun baci yakai kololuwa
Saurin runtse idanu ammu itama tayi ganin yanayinshi, tana mai dubansu da kyau, lallai dole tayi wani abu yanxu kafin su cimma kudirinsu, har ammu zatayi magana hidaya tayi saurin dakatar da ita tace “ammu stop it please…duk wannan shaidun dake gabanki da magnganun da muka ji duk karya ne? Ko kirkira za ayi?”
Ammu kamar zatayu hawaye ta dubi taj da yayi shuru ya kasa magana tace “tajudeen yanxu ka yarda da wannan, bai kamata kuyi saurin yanke hukunci ba daga jin magana babu kwakwarar hujja, ku ya akayi kuka samu wannan din?”
Tunda ammu tayi magana afiya ke neman yi mata rashin kunya, “wama ya sani ko kinsan cewa cikin ba nashi bane amma kike kakkareta”
Rai a bace ammu tace “how dare you afiya…kinsan da wa kike magana kuwa?are you insane ina matsayin kanwar mahaifinki?”
Sabeeha da hawaye suka gama wanke mata fuska taoro da fargaba sun gama mamayeta tayi saurin cewa “wallahi wallahi sharri ne..wallahil azeem babu abunda ke tsakanina dashi, shine ke bina,”
“Shuttt up disgusting slut” fadwa ta daka mata tsawa, “wannan yayi maki kama da karya? How dare you sleep with my husband? Under my nose you have the audacity”
“Wallahi azeem ban taba magana dashi makamancin haka ba, shike bina kuma dana nuna mashi cewa zan tona mashi asiri shine ya kulla min wannan sharrin”
Wani irin buga table da akayi ne yasa duk suka dago suna dubanshi, idanunshi sunyi jaa kanshi yayi rado rado “shut up!!!!!!!!!!”
Ya daka masu tsawa gaba daya kowa tasha jinin jikinta, hidaya dake jin tana da authorities yin magana kuma ta tsaya tace “dole ayi dna test..to confirm wannan cikin nashi ne, bazai yuwu ace akwai bastard acikin family nan ba bazan taba yarda ayi tarnishing image dinmu ba never.
baima tsaya ya karasa sauraron magnganun hidaya ba ya miqe afusace ya wuce sama.
Ammu babu abunda take sai girgiza kai ko ba a fada mata ba ya gama yarda da magnganunsu, tabbas babu ciki jikin sabeeha saboda haka duk wannan sharri ne kuma tasan sune suka kullashi amma yanxu ya zatayi ta fayyace mashi? Komai? This is not the best moment, bata taba tsammanin they can go to this extent ba ya ilahi ta dafe kanta.
Da sauri sabeeha ta miqe tabi bayanshi hankali a tashe,
Kallon juna sukayi gaba dayansu suka murmusa don sun dana ma ammu tarko bama ita kadaiba harda sabeehar dole yanxu su fito da kansu su fadi gaskia, dna ko sai anyi shi idan aka tabbatar da akwai cikin kuwa dole su juya abun nanma suyi fabricating results din a maidashi dan tareeq ne.
Sabeeha data hawo saman kasa bude kofar shiga bedrrom din tayi hannunta na karkarwa haka zalika jikinta.
Dakyar ta tattara kuzarinta ta ta tura kofar, yana Zaune bakin gado ta karaso har ibda yake ta duqa har kasa nesa dashi ta soma magana “didi…ka yarda dani, wallahil azeem sharri ne, bani bace cikin video din”
Ta karashe tana rarrafowa kusa dashi ta fara kokarin kama hannunshi yayi saurin janyewa ya miqe tsaye yana kallonta disgustingly ya juya mata baya, “get out of my sight”
Ya fada cikin bacin rai, he really needs time for now, yayi processing komai, tabbas yasan halin fadwa da kudirinta akanshi, and anything that will come from her ba abun yarda bane saidai wannan ya dan taba shi, ya rasa dalilin dayasa gaba daya komai ya dagula mashi lissafi, zuciyarshi na boiling yana jin wani irin zafii sosai,
“Didi ka yarda dani dan Allah listen to me please”
A zafafe ya juyo rai a bace ya kamo hannunta ya dagota tsaye rai a bace yayi baya da ita har jikin bango yaka manta da wani batun ciki, hes just blind yace “i said get the hell out of my side are you dumb? “
Ya karashe yana saurin zame hannunshi daga nata disgustingly ya juya yabarta a tsaye feeling so shattered and scared ta futo daga dakin ta sauka kasa wajen ammu, tun kafin ta kaiga sauka kasan fadwa da afiya suka tareta, fadwa ta damqe hannunta idanunta sunyi jaa sosai ta soma “wallahi wallahi saina wulqantaki, tunda kika shiga gonata, saikinyi regretting zuwa gidannan, tana kaiwa nan ta hankadata gefe rai a bace, cikin hanzari sabeeha ta kama hannunta inda fadwa ta rike, hawaye na gangarowa akan fuskarta, ita bata su take ma, suna bari wajen ta tunkari dakin ammu.
Fadwa da afiya suka kalli juna fadwa ta zaro syringe din data deba jinin sabeeha dashi, ashe rikon data mata jininta suka diba.
Sabeeha data shiga dakin ammu bata lura da jinin dake dan disa ba daga hannunta.
A tsaye ta tadda ammu tana safa da marwa, tayi saurin Karasowa inda take tana kuka tace “ammu wallahi wallahi sharri ne”
Kama hannunta ammu tayi tace “basai kin fada ba sabeeha, nasan sharri ne kuma karya ne, zancen ciki da suke cewa nashi ne nida ke munsan cewa babu ciki a jikinki”
Sai a lokacin sabeeha taji sanyi aranta “amma ammu shii…didi baya son ganina yace na fita..ya yarda kennan? Ya zanyi ammu?”
“Kwantar da hankalinki, just leave him alone he needs time to think trust me kinji fatima?”
Misalin wajen karfe sha daya ammu da sabeeha suka soma jin hayaniya anan kasa, cikin hanzari ammu ta fito tare da sabeeha dake biye