Author : Queenmerh Category : Complete Novels
ba, saida ta gama gyaran ta fara kokarin dafa mashi coffee latte, da taimakon youtube da ammu tace ta duba ta samu tayi, tana gamawa ta wuto dakin lokacin wajen 6:50am ta gifta ana neman 7:00am, lokacin data shugo yana cikin bathroom yana wanka wannan ya bata damar shiga closet room ta bude wajen inda yake ajiye kayayyakin daya ke yawan fita dasu cikin kwanakin ta kwaso mashi su sannan ta futo daga dakin ta ajiye mashi kan gadon yanda dai take mashi idan zai shirya, tana gamawa ta futo zuwa kitchen ta sake reboiling coffee din kafin ta zubo mashi cikin mug ta daura shi kan saucer ta fito, fatanta allah yasa yasha.
Lokacin data shugo yayi daidai da fitowarshi daga closet cikin shiri, shi baima san ta ajiye mashi kaya kan gado ba don haka ya nufi closet ya dauka kayanshi ya saka, saida ya karaso tsakiyan dakin yaga kayan, saikuma gata a tsaye tana kallon na jikinshi, taji wani iri a ranta amma haka ta kauda komai ta karaso inda yake, daman yace mata karta sake taba komai daya danganceshi so idan bai saka ba batada right din jin haushinsa.
Har fargaba tunkarar shi takeji da zarar taga fuskanshi, da hes lively yanxu kuwa kwaa kwata fuskar na nan yanda take kamar bai taba fara’a ba.
“Sabahal khair didi…”
Daga bayanshi ya jiyo muryarta, kokarin zipping jakarshi yake amma ya dakata, ya dauka wajen minti biyu a tsaye bai motsa ba saida ta sake cewa “bismillah ga coffee”
Juyowa yayi ya kalleta kafin ya kalli coffee din hannnuna nata, yama rasa me zaice mata, duk maganar da zai fito daga bakinsa
Bamai dadi bace ba saboda duk waennan abubuwan da takeyi haushi suke bashi musamman idan ya tuna da wasu abubuwan, bai ce mata tak ba ya dauki jakarsa ya fuce saga dakin.
Saurin runtse idanu tayi jiki a mace ta futo daga dakin zuwa kitchen…
Da yamma ammu tazo nan ta shaida nata period dinta yazo, nan ammu ta bata yan dabaru da zatayi yanda bazai gane komai ba,sannan ta dakatar da ita da shan wannan maganin.
Yau kwana biyar kenan, babu abunda ya sauya tsakaninta dashi, zai tashi kota gaishesa baya amsa ta kwatakwata, magana ma bata shiga tsakaninsu, inama taga fuskar, hakan baisa ta fasa kyautata mashi ba, yanxu har abunci ma takeyi ta ajiye kuma yana gani amma bai taba koda kallon abunci ba kuma ya lura da batada hayaniya sosai, duk wulaqancin da yake mata bata nuna tayi fushi ko tashi haushi ko sau daya, yanxu har dare yana kaiwa bai dawo gida ba kuma da zarar ya dawo zai taddata zaune kamar wadda ke jiran dawowarshi.
Yaune rana ta karshe da period dinta zai dauke, daman dayazo karashe take yawan ciwon baya da kafa, gaba daya kafarta ta sage mata, tama kasa tashi, tun bayan aikin safe datayi ta dawo parlor ta zauna ta doka uban tagumi tana dan matsa kafar.
Tundaya futo daga wanka ya shirya yake kallon kofa, harya saba kullum zata shugo da coffee a hannunta yau da baiga shugowarta ba sai yaji kamar ya damu dukda yaki yarda da damuwar yayi, he’s enjoying yanda yake treating dinga bata nuna gajiyawarta da kosawarta, rai a bace ya miqe ya fuce daga dakin ya nufi sitting room nan ya taddata zaune a kasa ta tankwashe kafafu tana matsawa da alamu abun na damunta sosai, harya kauda idanu ya tunkari hanyar fucewa ya dan dakata yana mai fusantarta, yama rasa me zaice mata, baisan lokacin da bakinsa ya furta “where’s the coffee?”
Da mamaki sabeeha ta dago take kallonsa, tayi mamakin jin furucinsa kamar a mafarko, tama manta da ciwon da kafarta keyi tsabar murna tayi saurin miqewa tace “yana kitchen bari na kawo”
Ta shige kitchen din tayi reboiling,tana murmushi, saitaji wani irin dadi aranta daya tambaya, ashe yana sane da ita, yana gama reboiling ta futo fuskanta harta sauya annuri ya bayyana akanta tace “bismillah” kallon don hannunta yayi kafin ya amshi coffee din, yakai bakinsa yadansha kadan ya tabe baki ya miqa mata,”disgusting” yana fadin haka ya miqe ya fuce daga parlorn, amaimakon taji haushi sai kawai murmushi ya kubce nata, ita wannan achievement ne a wajenta, yau da kanshi ya buqacu avu daga hannunta ba karamin dadi takeji ba, shi bangarensa tunda ya fuce ya fara wasi wasi da tuhumar kansa na tambayrta coffee din da yayi yanxu saitayi tunanin wani abun, tsaki kawai yayi yana mai jin haushin kansa for doing that.
Borin kunya😂
Yana isowa gym ya nufi wardrop ya ajiye jakarshi daidai nan mutalib ya shugo wajen,suna hada idanu ya suakeka taj din murmushi kafin ya miqa mashi hannu, kallonsa taj yayi irin who are you dinnan, ganin haka yasa mutabblb cewa “salam alaikum”
Yana jin sallamar musulunci da yayi mashi yasa ya miqa mashi hannu suka gaisa, suna gama gaisawa yabar wajen zuwa wajen gym, mutabbli ya biishi da kallo.
Tunda ya fara workout mutane ke kallonshi, matan dake wajen ko kasa duake idanunsu sukayi akanshi, hes so charming and charismatic, macen data sameshi wannan ta gama samun komai a wajen namiji, kyau, aji, uwa uba kana ganinshi kasan kudi ya zauna, tsakanin lokacin daya dawo ahyyacinshi zuwa yanxu ya sauya sosai, physically ma, ya maida jikinshi na da yanda yake a baya, kamarma yana neman yafi da din, hes so cute and handsome at the same time…
Cikin mutanen dake observing dinshi garda mutabblib daya karba membership din wajen saboda ya samu kusanci dashi, yau kwanansa biyar kenan da zuwa wajen, duk yanda yazo ya samu kusanci dashi avun ya gagara saboda he’s not opeb kwata kwata,bai karaya ba don haka ya cigaba da approaching dinshi.
Takowa yayi inda taj yake zaune yana warming thighs dinshi, yanxu haka ma sallama ya sake mashi, dakyar taj din ya iya amsa mashi don shi bai fiye son mutane suna shiga harkarshi ba, bashida sakewa kwata kwata, shake din da mutabblib ke miqa mashi ya duba kafin ya maida dubanshi ga mutalib din daya soma cewa “bismillah!!!”
Kai tsaye ya amsa shi da “no thanks”
Yana kaiwa nan ya miqe daman ya gama yabar wajen.
Yana futowa ya shige bathroom yayi wanka ya shirya kafin ya futo da jakarshi, ya fuce daga wajen.
Harya shiga motarshi yayi reverse ya soma jin horn daga bayan motarshi, da farko ya dauka bashi akema ba sai daga baya ya lura da motarshi akema horn, daidai nan mutallib ya karaso da tashi motar ya zuge glass yana mai fuskantar taj din ya miqa mashi airpod dinshi daya mata a cikin gym din, “sir ka manta da wannan, I believe naka ne”
Kallon airpod din taj yayi sai a lokacin ya tabbatar nashi ne don haka yayi saurin miqa hannu ya karba tare da cewa “thanks”
Yana fadin haka mutalib ya sara mashi ya figi motarshi yabar wajen, shuru taj yayi yana wani nazari, yanajin kamar ya taba ganin fuskarsa saidai ya rasa a ina ya taba gani.
Ahankali yaja motar yabar wajen shima, yaron black dake binshi kuwa yana biye dashi a baya, ya lura da motar dake bin nashi ba tun yanxu ba, shi abunma yanxu ya maidashi wani joke, for almost over 2months kenan ana bin nashi, kwata kwata baya jin wani darr ko tsoro kwata kwata.
Bangaren sabeeha tun bayan ya futa take fama da wani irin matsanancin ciwon ciki, gashi yau ya kamata period dinta ya tsaya balle ace shine, kaffaunta duk sun sage sosai, ta dauka ciwon normal ciwo ne kuma zai daina saitaga akasin haka, don kamarma gaba gaba yake mata sosai, tun bayan data futo daga wanka ta kasa koda saka kaya ne, batama san lokacin data hau kan gadonshi ba ta kwanta tsabar azaba.
Karfe sha biyu ya shigo gidan, tunda ya shugo part dinsu ya soma jin kuka qasa qasa, bai kawo itace ba saima mamakin daga ina kukan ke fitowa daya dunga yi, cikin bedroom ya nufa nanfa yaji sunan ya tsananta cikin hanzari ya bude kofar ya shige daga ciki nan ya ganta zaune a kasa ta tabkwaro kafafunta daketa faman karkarwa saboda zugin da suke mata, take hankali ya tashi amma ya danne ya karaso inda take muryarshi a kaushashe ya soma magana “ke!!! Ke!!”
Sama sama ta soma jin muryarshi wannan yasa tayi saurin dagowa tana kallon shine tayi saurin miqew tsaye take kafarta ta amsa wand ahakan yasa ta sake zubewa a kasan,jini ya soma sauka daga kasanta kuma tana jin yanda yake zuba dukda ta saka pad a jikinta, jikinta gar tsuma yake, fatanta daya allah ya jefo mata ammu don batasan irin karyar da zatayi mashi ba idan yaga jini gashi ta kasa tabuka komai saboda azabar da take ji, kamar da wasa kuwa ya fara hango jini wajen kafafunta bai tabbatar da hakan ba saida ta sake wata yar kara ta zakusa gefe saboda murda nata da cikin yayi take yaga jini kwance akan hijab dinta harya bata hijan din nata sosai, take ya zaro idanu tunawa da research din da yayi inda akace idan har jini ya ballema mai ciki to zubew zaiyi, take hankalinshi ya tashi sosai, ya tsugunna gabanta hama rasa me zaice mata, “hey!!! Hey!! Whats wrong with you?meke damunki?”
Ay gaba daya batama san me yake cewa ba tsabar azabar da takeji sosai,lokaci guda ta furgice ta sake fashewa da wani kukan baima san lokacin daya sanya hannunshi ba ya dago da fuskarta ganin yansa take kuka shabe shabe he can see yanda takejin wahala inda baima san daga ina bane ba, tsoronshi daya karya zama cikin ne, gashi ta kasa fada mashi abund akw damunta,
Dagoda idanunshi da zaiyi ya sake ganin jini na saukowa a kafarta take hankalinshi ya tashi sosai babu abunda yake sai innalillahi a zuciyarshi yaka rasa mai zaiyi mata, daidai nan aka budo kofar, hankali a tashe ammu ta shigo dakin ta tunkari sabeehar, taja karasowa itama taga jinin, take hankalinta ya tashi sosai, saboda daga ganin wannan jini ansan bana lafiya bane, gashi taj na tsaye a wajen balle ta tambayeta ko dama haka take idan tana period, tama rasa me zatayi saida ya dago ya kalli ammu din yace “whats wrong with her? Whys she bleeding like that? Pregnancy dinne?”
Tambayoyin daya jero ma ammu kenan, ganin itama ta rude yasa ya kinkimi sabeehar gaba daya hankali a tashe yace “muje asibiti”
Hankali a tashe ammu ta zaro idanu tana kallonshi harya nufi hanayr futa da sabeehar a hannunshi, dan dole ammu tabi bayanshi cikin hanzari suka sauko kasa daidai nan su afiya suka fito ita da sonata, ganinshi da sabeeha a hannu yasa kowa ya visu da kallo cikin mamaki, har sonata zatabi bayansu afiya ta dakatar da ita,
“Saboda me zaki hanani binsu”
“Kina tunanin idan kika bishi zai saurareki ne? Bakiga yanayin da take ciki ba,”
Da mamaki sonata ke kallonta fuskanta da alamun tanbaya tace “ban gane ba”
“Looks like kamar cikin ya zube bakiga yanda suka fito ba ga kuma jini a jikinta”
Sonata najin haka ta waro idanu take wani irin dadi ya ziyarceta mata misali, batama san lokacin sata rungume afiya ba, su sunma qayyade cikin ne ya zube, take afiya ta doka fadwa da hidaya kira a waya.
Acahn asibiti kuwa suna isowa aka wuce da sabeeha emergency room, taj dai ya kasa natsuwa kwata kwata, ni kaina na rasa gane yanayin da yake ciki, deep down fargaba ce kunshe a cikin zuciyarshi, sai a yanxu yasan jini ba abun wasa bane, take ya soma jin haushin kansa, idan wani abu ya samu wannan cikin he will be devastated, ya kasa natsuwa kwata kwata, ammu na ganin yanda ya zama restless lokaci guda, take taji wani irin rashin dadi a zuciyarta ko ba a fada mata ba kuka d ayanda yake kauda kai hakan baisa ta ta hango yanda lokaci guda ba ya sauya gaba daya, ayau rana ta farko ta hango tsantsar furgici a cikin idanunshi tarw da fargaba, “those that mean ya damu da cikin kenan?”
Tambayar da ammu ta tunda ga ma kanta kenan, so its true dayace he will responsible for it kenan.
Shuru ammu tayi taba nazari, yanda sukayi nisan nan batajin its time to give up, ayanxu ma da basu samu damar fayyace mashi komai ba kenan, dole she has to rwmove all of teh emotions dake zuwan mata.
Wannan yasa ta fuce daga wajen, takai wajen 30mins kafin ta dawo cikin asibitin, tana dawowa ta tsaya daidai nan likita ta futo ta buqaci ganinsu.
Taj din na daga gaba suka shiga office din doctor suka zauna, suna zama doctor ta dubi ammu ta miqa mata hannu, karbar hannunta ammu tayi kafin doctor din tace “congratulations ma’am, you dont have to worry, the baby is perfectly healthy”
Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yana jin kalaman doctor din na karshe, har zaida ammu ta jiyo sautin, murmushin yaqe ammu tama doctor din kafin tace “thank you doc”
Miqewa taj din yayi baima tsaya ba ya fuce daga office din.
Yana futa doctor ta dubi ammu tace “hauwa..gaskia this is risky, meysa zakiyi wannan karyar, yanxu badan ina duty ba ya zakiyi kenan?kinsan dai this ai illegal ba”
“Im sorry doctor farhana, bazaki gane dalilin dayasa na tsaya akan wannan maganar ba, wannan yarin da kike gani maraya ne, dana ne, wannan ne kadai gatan da zan mashi wanda nake fatan yayi nsanadiyar kubutar dashi daga ukubar da yake ciki”
Jinjina kai kawai farhana tayi kafin tace “shikenan hauwa i trust you, maganar yarinyar wannan maganin dana baki data sha dinnan shine ya jawo mata over glow during period dinta, ya kanata ta dauna sha haka karya mata illa”
“Ay ta gama sha ma”
“Zataji sauki, na bata injections dazai dakatar da flow din zaku iya tafiya ma yanxu, akwai pain relievers dana mata allurarsu zaisata barci sannan zai haifar mata da kasala”
Mikewa ammu tayi itama doc farhana ta miqe auka rungume juna ammu tayi mata godiya sosai kafin su fuce zuwa dakin sabeehar, suna fitowa suka hango taj din yanata faman waya, hidaya ce daman ta kirashi, ammu na karasowa inda yake tace “bari na fito da ita mu tafi, doctor tace zata iya tafiya”
Jinjina kai kawia yayi ya maida hankalinshi ga wayar da yakeyi, “zamu dawo yanxu” yana fadin haka baima saurari amsarta ba ya kashe wayar, da mamaki hidaya ke kallon wayar daya katse mata ko sauraronta bai gama yi ba, lamarinshi gaba yakeyi sosai.
Chan asibiti kuwa ammu tabfito tare da sabeeha suka nufi motarshi lokacin yana daga zaune a gaba, kayan jikinta an saya mata su zuwa wasu sabbi anan asibitin, dake farhana tasan ammu sosai wannan yasa akayima sabeehar arrangement.
Tunda ta shiga motar tare da ammu a baya babu abunda take sai layi, gaba daya she’s weak saboda allurar da akayi mata, babu ahunda ammu ke mata sai sannu, shiko sau daya ya dago ya kalleta ta mirror kafin ya dauke idanunshi har suka karaso, suna fitowa daga cikin motar ammu ta shigewarta cikin gidan ta barshi da sabeehar, tana sane daman tayi hakan, ya dade sosai a zaune yana kallonta ta jikin mirror yana tuna irin fargabar daya shiga dazu, zai iya kiran abun da fargabar rasa something new thats part of him, sai kawia ya fara imaging da ace cikin ya zube fa ya zaiyi? Baya ma fatan tuna wannan don haka ya futo daga motar ya nufi baya inda take zaune ya bude kofar ya zubama fuskarta idanu sosai, kanta ne ya nemi langwabewa yayi saurin tallabota da hannunshi daya take fuskanta yayi lapping akan palm dinshi, she looks so innocent, take kawai yaji tausayinta ya darsu a zuciyarshi, he has a very soft side daya kasa sanin yana dashi sai akanta,ya dade yana kallonta babu ko kiftawa kafin ya sanya hannunshi duka biyu ya dagota nan take tayi yuuu ta fado jikinshi ya dauketa da hannu daya ya rufo kofar motar kafin ya shige daga ciki.
Yana shiga ya tadda sonata a taaye tana tsumayen ganinshi, itafa gaba daya murna takeyi dontama ji a jikinta cikin ne ya zube, hangoshi da take yana rike da sabeeha a hannunshi ba karamin takaici taji ya tsaya mata arai ba, for now bama wannan ba tukunnan, so take ta tabbatar babu cikin ko akwai don hka ta tunkareshi, “hey! Babe”
Ko kallon inda take baiyi ba saima jin kalmar ta karshe da yayi data sanya shi wullo mata wani mugun kallo
“Oh noo!! I’m so sorry babe cikin ne ya zube ko?”
Daga yanayin yanda ya kalleta ta tabbatar da akasin haka, take jikinta ya soma kyarma kamar mazari, bai sake kallon inda take ba ya nufi sama da sabeeha a hannunshi, fadwa data futo daga dakinta tana hangoshi da sabeeha a hannunshi take komai ya dauke mata.
Da kafarshi ya budw kofar dakin ya shiga daga ciki, dakin yayi wani dimn kadan babu yalwar haske sosai, ga kamshi mai dadi dake tashi kadan kadan, an gyara dakin fess fess wanda ammu ce tasa ayi kafin su iso,
Gado ya nufa da ita a hannunshi, yana kokarin kwantar da ita ya sauke idnaunshi akan fuskarta, ta nanikeshi gaba daya kamar wadda za a kwace shi daga jikinta, batasan ma tanayi ba saboda effect din allurar da akayi mata, dakkyar ya samu ya kwantar da ita ya gyara mata kwanciya, yana kokarin mikewa ta kamo gaban rigarshi wanda hakan yasa yayi mata runfa gaba dayashi, fuskanshi na gab da tata har goshinsa na bugun nata, kallon fuskarta ya soma yi daga kan hular asibiti da aka saka mata wadda ta dan zamo gashin kanta ya bayyana kadan zuwa ga gashin baby hair dinta dake kwance a goshinta ga girarta da idanunta dake rufe kawo wajen bakinda dake bude kadan ga pink braces dinta ya fito, kusancin dake tsakaninsu yayi yawa sosai don nunafshinsu har gogayya yake da juna,gashi sai sake matso dashi takeyi zuwaga jikinta kamarma sanyi takeji ko zazzabi ne ke neman rufeta, sun dade a haka kafin yayi saurin zame hannunta ya mike tsaye ya wuce bathroom yayi wanka.
Ya dade sosai a bathroom kafin ya fito ya sauya kaya zuwa marasa nauyi sannan ya wmfuce zuwa kitchen,yana karasowa ya tadda casserole akan tray da alamu abunci ne a ciki, harya dauka chocolate zai futa yadan dakata, ya nufi wajen da casserole din suke ya bude, pasta ne tayi