Author : Queenmerh Category : Complete Novels
ya dosa, why is he acting up like din, “are you deaf?” Ya sake daka mata tsawa,
Bakinta na rawa ta soma magana “nida barad ne kawai mukaje garden wallahi,”
“What where you doing there? Kinsan daga waye juice din yake da zaki sha? Are you going to act dump just to risk your life and my childs? Eh!!!”
Ya sake daka mata tsawa kamar yasan ana kokarin cutar da ita ko cutar da ita za ayi,
Kamar zatayi futsari a tsayen nan haka takeji, “dan allah kayi hakuri didi…I’m sorry bazan sake ba”
“Listen to me, daga yau karna sake ganinki waje, stay here, and dont you ever take anything from anyone, i repeat anyone..understood”
Yana fadin haka cikin hanzari ta girgiza mashi kai, “understood!!!”
“Yes..” ta amsashi,…
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 75
A fusace yabar dakin gaba daya ranshi a jagule yake, tundaga ranar dayaga sonata na kokarin cutar da ita ya kasa samun natsuwa da kowa bama ita kadai ba, the biggest threat to her will be fadwa, fadwa batada kama, kuma yasan how obsessed she is with him, yaga yanda hanaklinta ya tashi muraran lokacin dataji sabeeha nada cikin shi, tsoron daya karsu illata cikin jikinta harda ita dinma.
Tunda yabar gabanta jikinta ke bari sosai, babu abunda take sai innalillahi a cikin zuciyarta, yaudai taga fushinsa muraran, a hakan ma bataga komai ba,
Dakyar ta iya takowa bakin gado ta zauna, tare da dafe kirjinta dake bugawa fat fat… shuru tayi tana hasashen abund aya faru dazu batama san lokacin da hawaye ya soma zarya akan fuskanta ba..idan har zaiyi fushi akan haka ya zata kasance idan ya gano babu cikin shi a jikinta? Anya zata iya kuwa? Tana jin kamar ta yaudareshi ta mashi karya, karya da ciwo, musamman akan abunda ya shafi mutun, hes beginning to love abunda doesn’t exist, cikin nan babu shi, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, “ya zanyi?,”
Budo kofar dakin ya sakeyi, ya tako har inda take, bata ankara dashi ba saida ya miqa mata ruwa faga glass cup daya debo daga kitchen, saida ya futa ya shaki fresh air tukunna ya danyi sauqin bacin ran dayakeji, sai a lokacin ya tuna yanda ya barta, ta tsorata muraran and its not good for a pregnant woman.
Dago da idanunta da hawaye ke sauka tayi ta kalleshi tare da kallon hannunsa dake miqa mata glass cup din, hannunta na mazari ta dago zata karba ya hade hannaeysu gudun karta yada glass cup din.
Da hannunshi nashi da nata yakai cup din bakinta ta dan sha kadan kafin ya cire cup din ya ajiyeshi a gefe, ganin irin kallon da yake mata yasa ta sauke idanunta kasa.
Saurin runtse idanunshi yayi ya bude, baya son ganin mutun na hawaye abun yana breaking dinshi, gashi bai iya lallashin mutun ba balle ya fara akanta.
Samun kanshi yayi zama gefen da take zaune, yana zama kawai ta sake fashewa da kuka, sunkuyawa tayi tsakanin cinyoyonta, juyowa yayi yana mai kallon bayanta, hannunshi daya ya daga ya dora a bayan nata ya fara dabbin bayan nata ahankali cikin lallashi, ya dade yanayi sai kuma chan yayi gyaran murya “uhm…”
Ya dan dakata yama rasa me zaice mata, sorry zaice ne ko menene?, for the second time ya sake gyaran murya wannan yasa ta dago da fuskarta tare da turo bakinta tana kallonshi, wata iriyar shagwababbiyar fuska tayi a daidai lokacin wanda hakan ya kusa sashi murmusawa, abun ya bashi mamaki, how did you come up with something like that with her face, “why are you crying?”
Wata iriyar harara ta galla mashi batama san tayi ba, harda kauda idanu, zaro idanu yayi waje tsabar mamakin abunda tayi, “whats that?”
Ya mata nuni da idanunta,tasan harar tashi da tayi yake nufi amma ta basar kamar batama san tayi ba.
“Mutun sai fada kawai, my old didi baya fada, hes so calm and sweet”
Ta fada ahankali, “what did you say?”
Saurin miqewa tayi tsaye ba tare da ta kalleshi ba tace “ni bada kai nake ba”
Har zata bar wajen yayi saurin kamo hannunta, chak ta tsaya, wani irin taji a jikinta kamar yau ya taba kama hannunta, jawota yayi baya ta zauna bakin gado kafin ya saki hannun nata.
“Fatima..”
Ya kira sunanta a natse.
Ahankali ta dago da idanunta ta kalleshi ganin he’s very serious,
Kamar mai tsoron magana ya soma cewa “plea..se be careful next time,”
Kallon bakinshi ta dunga yi, tund aya fara magana harya gama, saitaji wani iri aranta, tasan duk wannan abun da yakeyi sbaoda cikin nan ne da babu shi.
Sauke ahiyar zuciya tayi tare da dakewa ta soma magana
“Insha Allah, kayi hkuri didi bazan sake ba Insha allah”
Tana fadin haka ta sauke mashi murmushi, har yana hango braces din dake maqale da hakoranta, kauda idanunshi yayi tare da miqewa tsaye,
“Zaka futa ne?” Ta jefo mashi tambaya,
Bai juyo ba chan kasa kasa ya amsa da “yes”kafin ya fuce.
***
Tafiya yake anatse a cikin motarshi babu gaggawa, sanye yake cikin casual dressing dinshi as usual,bai tsaya ko ina ba sai inda zasu hadu da mutabblb bayan ya daukeshi suka nufi kamfanin property agencies da suka saya gidan khaal daga hannun government, suna isowa yayi parking kafin ya futo, mutabblib shima ya futo,suka shiga cikin Kamfanin a tare. anan suka tadda lawyer da mutabbli ya masu hiring wanda zai zama shaida sannan zai kawo legal papers wajen reception suka tsaya mutabbl yayi magana da mutanen wajen kafin su shige daga ciki wajen MD din.
Mutabblb ne ya bude kofar ya shiga kafin taj ya biyo bayanshi.
Gaisawa sukayi da MD din ya basu damar zama wajen mazaunin baqi, ba tare da wani bata lokaci ba suka gabatar da kansu inda mutabbl ya wakilci taj din wajen mutumin don shine zai saya gidan amma karkarshin sunan mutabblb.
Property documents din gidan mutumin ya ajiye masu so that they can go through sanna suka fara reviewing, suna gamawa a take sukayi sighning deal,taj na daga zaune yana kallonsu, shi zai saya gidan amma vaya son asan shine ya saya,shiyasa ya saka mutabblb a cikin, har zuwa yanxu yana mamakin yanda ya yarda dashi, abunda bai taba yi ba kenan, which shi a wajen is very risky, bai sanshi ba baisan asalinshi ba abota ce kawai ta hadasu, this is the first yake irin wannan kasadar, bayan wannan ma this is like a test, ta hakan zai gane idan mutabblb din can be trusted ko akasin haka.
“Thank you mr Mutalib abdallah!”
Hannu shima ya miqa mashi suka gaisa kafin suyi exchanging signature bayan sun bashi original copy din papers din.
Atare suka futo suka nufi cikin motarshi, suna shiga ya kunna motar tare da dan nunfasawa, juyowa mutabble yayi ya kalleshi kafin ya miqa mashi papers din ya karba yana mai kallon takardun.
“Thankfully basu saka gidan a kasuwa ba amma sir meysa ka dage saidai a saya gidan da sunana?ni a ganina yafi dacewa ace tunda kai ka saya ya zamana sunanka ne a wajen”
Shuru taj yayi baice komai, nazari kawai yake yanda zai nemi iyalan khaal, sai ayanxu yake dana sanin rashin yin zumunci da kowa, khaal dinma don yana yawan bibiyar rayuwar sa ne,yama rasa dalilin dayasa ya saya gidan, saidai yanajin hakan shine daidai.
Ganin yayi nisa cikin tunani yasa mutabbl gyaran murya yana mai fuskantar taj din, “yadai sir?”
Nunfasawa taj yayi sannan ya dubeshi, “thank you!”
“Haba ba damuwa, yanxu saika fadi sunan da kakeso ya koma kan property din saina fadama lawyer din yayi processing komai”
Dan nisawa yayi kafin ya dubi mutabbln din yace “a report din daka tura min naga ance iyalanshi sunbar kasar nan ko? Inason nasan inda suke saboda ya koma wajen su, saidai bansan inda suke ba”
Saurin runtse idanu Mutabblb yayi, shi kadai yasan yanda yakeji aranshi, wani irin farin ciki yakeji hade da emotional feelings, da khaal na raye sai yafi kowa alfahari da taj, ashe zaiyi mashi halarci dukda baisan abubuwan da khaal din yayi dominshi ba da yanda yayi protecting dinshi, kaf familyn nan babu wanda yayi kokarin taimakon iyalan khaal din harma wajen wanke sunan khaal din, karshe ma cireshi daga family history dinsu sukayi gudun kar laifikanshi ya shafesu, kuma yayi ruining masu company image dinsu, kaicho dan adam, lokacin da iyayensu suka rasu shi kadai ne ya tsaya akansu, ya kula dasu amma yanxu ga sakayyar da zasu mashi,daman ance bazaka taba sanin mai qaunarka ba sai baka raye kabar iyalai.
“Gaskia bazan boye maka ba kanada zuciya mai kyau, duk wannan illegal laifukan da akace yayi da tuhumar shi da akayi harda zarginsa da akayi da sa hannu wajen kidnapping dinka, hakan baisa kayi neglecting iyalanshi ba?”
Yana karashewa ya maida dubansa ga taj din,
Idanunshi na kan papers din yace
“I have to do this..”
“Why?” Mutabblb yayi saurin jefo masa tambaya,ganin yayi shuru bai bashi amsa ba yasa mutabblb yayi murmushi kawai,
“Sorry sir.. baikamata ina yawan tambayarka abunda ya shafeka haka ba, karna tsallake boundaries, but duk abunda kake buqata i will
Gladly help you”
Girgiza mashi kai kawai taj yayi kafin subar wajen.
Saida ya fara sauke mutabblb inda suke haduwa bayan sunyi sallar zhur tare kafin ya nufi gida kai tsaye, yana parking motarshi daidai nan tayi parking nata arniyar motar, cikin saurin ta fito ganin yana shirin fitowa shima.
Lokacin dayayi parking ya hango shugowarta don a gefen motarshi tayi parking wajen parking space.
Rufe motarshi yayi tare da hade fuskarnan tashi babu wasa ya nufi hanyar shiga ciki ko kallon kirki bata isheshi ba.
Tana kallonshi ya wuce ta gabanta babu abunda take sai binshi da mayen kallo harya bar wajen, wani irin makirin murmushi ta sauke kafin ta mara mashi baya.
Sama ya wuce direct, tsayawa yayi tsakanin walkway din dazai sadashi da part dinshi, maido da dubanshi yayi ga part din hidaya, yanason shiga shiga ciki amma zuciyarshi na hanashi,kauda kanshi kawai yayi ya wuce part dinsu.
Ahankali ya bude kofar dazai sadashi da sitting room, kamshi ne mai dadi na bakoor ya mashi sallama tare da sanyin ac saida ya sauke ajiyar zuciya kafin ya rufe kofar ya wuce ciki.
Bude kofar dakin yayi tare da sallama kasa kasa, idanunshi bai sauka ko’ina ba sai kan makeken master bed dinshi da take kwance abunta, sakin handle din kofar yayi bayan ya rufe sannan ya fara takowa cikin dakin.
Sauke ajiyar zuciya yayi shigarshi bathroom, wani irin ciwon kao yakeyi cikin kwana biyun nan, bayan ya rage kayan jikinshi, ya watsa ruwa… yana gamawa ya fito, lokacin it’s past 3pm,
Daure yake da towel din daya fito dashi, bai tsaya ko ina ba sai kan gado ya kwanta chan gefen tare da janyo duvet din data luluba dashi ya lulube jikinshi dashi shima saboda sanyin ac dakin.
Barci dai har wajen karfe shida na yamma babu wanda ya farka cikinsu, barcine sukeyi cikin annushuwa ba tare da saninsu ba sakamakon gangar jikinsu daya hade dana juna kwata kwata batasan a jikin mutun take ba,haka zalika shima, its been long rabonshi da barcin yamma irin wannan, bayayi ma kwata kwata sai yau daya farayi, 3hours a jere nonstop nunfashinsu na gogan juna cikin duvet din, dake ita ta fishi dadewa dayin barci wannan yaza ta fara bude shanyayun idanunta da suka mata nauyi sosai harta saukesu akan fuskanshi dake dab da tata cikin duvet din, gaba daya ta dauka mafarki takeyi, rufe idanun nata ta sakeyi ta sake budewa taga fuskanshi, still believing mafarki ne, wannan yasa ta daga hannunta ta dora kan fuskanshi tare da shafa fuskar tashi da yatsunta, wani irin taushi da laushi taji a skin din nashi, ahankali ta soma motsa bakinta kamar kalmomin bazasu fito ba in a whispering voice tace, “di..di..na”
Kamar an doka mashi haka yaji muryarta a kunnenshi, tar ya bude idanunshi ahankali, saurin runtsesu yayi ya sake budesu akan fuskanta dake gab da tashi, shima dai ta bangaren nashi ya aza mafarkin yakeyi, bai gama tantance ko mafarkin bane ba ko zahiri ne ba yaji tace “ka..na..da kyau” a rarrabe ta karashe with her marvelous calm voice, saida ta sake magana ya tabbatar da zahiri ne, ya kasa kifta idanu sai kallonta yake da jajayen idanunshi, at the same time yana tuna kusancinsu lokacin da akayi kidnapping dinsu shida ita, yanda ya dunga shiga jikinta da yanda ya dunga cikwikwiyeta, take yaji wani abu ya darsu a zuciyarshi da gangar jikinshi, nunfashinsa ya soma rushing ahankali ahankali, har tanajin duminsu da kamshinsa akan fuskanta, kusancinsu yayi kusa sosai, he can barely sense her breath, take ya tuna sanda dunga shafa kirjinta yana saka kanshi tsakaninsu,idanunshi ya karade yayi jaa, he’s having erected feelings at the moment, abunda yakan jima baiji ba, shi ba mai mu’amala da mace ba balle, its not like bashida lafiya saidai shifa a tsaye yake, he’s not the type that loose control anyhow, amma yanxu ya gaza tsaida zuciyarshi daga karatun da take mashi, ya gaza hana kwakwalwarshi da tuna mashi wannan abun, hankalinshi bai fara tashi ba saida ta gangaro da hannunta wajen gashin bakinsa daya zagaye fuskanshi gaba daya shima ga laushi ta soma wasa dashi, magana take ahankali ahankali dake arousing dinshi, abunda bai taba experiencing ba. “wannan yana maka kyau sosai didi..i love it”
Tana fadin haka ta maida hannunta wajen gashin kansa, ta luma yatsunta cikin soft silky gashinsa,
Tunda ya kafeta da idanu ya kasa daukewa, itako sai lumshe ido take.
Bata gama tafiya dashi ba saida ta sauke hannunta dake wajen gashin bakinsa zuwa ga kirjinshi unknowingly to her hannunta ya sauka wajen nippy dinshi, bata murza ba haka zalika bata dauke hannun nata ba ta soma magana..”didi ka zama kato yanxu..” tana fadin haka ta suake ajiyar zuciya saboda zafin nunfashinsa da takeji akan fuskanta.
Cikin hanzari ya runtse idanunshi kafin ya budesu a fizge don ji yayi gaba daya kamar zai zauce, hannun nan nata dake kan kirjinshi yayi hanzarin kamawa yana fiddanunshi sama sama yayi hanzarin juyowa da ita ya zamana tana facing sama shi kuma jikinshi na fizga ya hau kanta, ya zamana yana samanta tana kasanshi, idanunshi na cikin nata yayi locking dinsu waje daya, saqe tayi a cikin mafarkin nata da take tunanin shi takeyi yi, baiyi wata wata ba ya dan duko saitin fuskanta ta yanda bazai sauke mata nauyi ba..
Zaro idanu tayi ahankali ta fara kokarin jujuya bakinta daya kafe da idanu,, “di……”
Bai bata damar karasawa ba a zafafe ya dora bakinshi kan nata, take nunfashinta ya daga yayi sama, buda bakinta ya soma yi da harshenshi cikin kwarewa har yayi nasarar tura halshenshi cikin mole din bakinta, ya ila’i, chak ya tsaya ya kasa komai, wani irin dumi yaji a cikin bakinta, gaba daya yama manta da wani braces dake bakinta saboda warmth’ din dake ciki, wani irin sanyi sanyi yakeji a jikinshi kirjinta na mashi falshing akanshi, dukda a cikin duhu yake ganin memory din hakan baisa idanunshi sun hasasho mashi yanda suke ba.
He couldn’t kiss her for so long ya zame cire bakinshi daga nata saboda yanda yake kokarin fighting abun, trying to remind himself wannan fa maid dinshi ce, kuma she used him, dan dagawa yayi yana mai kallonta, gaba daya ta sandare,wanne wane irin mafarki ne mai kama da zahiri.
Idanunshi ya maida kan boobs dinta, ga kaya dai a jikinta amma shi naked yake ganinsu, cause har ya gama hasashensu.
Zuciyarshi yaudararshi take and he will never believe or agree with her, da kyar ya samu ya rinjayi zuciyarshi ya yaye duvet din tare da miqewa cikin bacin rai ya sauka daga kan gado, wani irin baqinta yake gani a wannan lokacin, haushinta kamar an dasa shi a zuciyarshi at the moments, saiya fara tunanin daman abunda takeso kenan, ta wani bangaren takaicin kanshi yakeji da baqin cikin abun kunya dayaso yaui, he will never agree that the got erected saboda yarinyar nan, he felt intimate with her…
Haka ya wuce bathroom cikin bacin rai yana kallon jikinshi daya amsa kira.
Bangaren sabeeha tashin hankali, fargaba kunya tsoro babu wanda bataji ba lokacin data tabbatar da zahiri ne ba mafarki ba, “innalillahi wa inna ialaihi rajiun… na shiga uku”
Ta furta a hankali, hawaye na zarya akan fuskanta, what just happen? What did she do just now?” Tambayar data dunga yima kanta kenan.
A furgice ta miqe zaune tana zare zaren idanu….
**
Bude kofar bedroom dinta yayi ya shugo kai tsaye,ranshi gaba daya a bace yake amma haka ya danne, gaba daya katin banki data bashi tayi blocking dinsu kaf,daga yawonshi yake na banza da wofi a wani hotel, yazo biyan service yana bada card akace anyi blocking card din, allah yaso da cash a jikinshi, he was so embarrassed, har yana fada da receptionist din akan ko yasan koshi waye.
Daman cikin kwana biyu ba shiri suke ba shima ya fita harkarta, idan ta nemeshi fine idan bata nemeshi ba wannan matsalarta ce.
Baima tsaya wani knocking ba ya bude kofar ya shugo, alamun saukar ruwa dayaji ya tabbatar mashi tana bathroom wannan yasa ya dan dakata yana jiran fitowarta don jin dalilinta na yin haka.
Yana cikin nazari idanunshi ya sauka kan jakarta da wasu file a gefe, har ya kauda kanshi tunawa da sharadin data bashi na taba mata abunda ya shafeta chan kuma ya kasa kauda kai ya tunkari wajen jakar tata ya dauka file din, aggauce ya soma budewa don karantawa, take wasu hotuna suka zubo a kasa, tsugunnawa yayi ya kwaso su duka, hankali a tashe ya zaro idanu yana kallon hotunanshi kala kala a hotels, harda wani hoto ma da baisan anyi ba, gashi ga budurwa kan gado yana barci ta daukesu hoto, babu ma kaya a jikinshi, abundai so nasty, bude file din yayi, da divorce paper yaci karo daga court, ond atayi filing neman saki daga wajenshi, na biyun file din kuwa evidence ne na safarar kwayoyi da yakeyi a boye, na hudu kuwa report ne na drugs, inda tayi piling evidence din drugs dayayi shekarun baya, wanda ya boyeshi don idan akasan mutun na drugs to fa shekara goma ce a gidan yari.. jikinshi har bari yake yana karanta papers din.
Yanajin alamun kashe ruwan tap ya tabbatar futowa zatayi wannan yasa ya tattara komai ya maida su inda ya gansu kafin yayi hanzarin futa