Author : Queenmerh Category : Complete Novels
nazari,”idan har da gaske kike ba yarki bace ba to zaman uban me takeyi mana agida? ki futar da ita daga gidan nan bana kaunar ganinta”
“Wallahi na maki alkawari duk abunda kikeso shi za ayi, zan futar da ita cikin gaggawa”
Tsaki maya tayi ta futa daga dakin hadiza ta fara safa da marwa, ya zatayi ta futar da sabeeha daga gidan nan? Ta wace hanya zata futa da ita?
Ay batasan sanda ta zari mayafinta ta futo daga gidan, kusan karfe biyar ta dan gifta,ko takalmin arziki babu a kafarta, kwana biyu tana kiran jamila ma bata dauka.
Ba ita ce ta isa dutsen habuja ba sai wajen karfe shida, kamar daga sama jamila ta ganta shugi duk a burkice.
Tana gaban reshow tana girki, “lafiya dai hadiza kamar an wulloki? Da magariba? Mutuwa akayi?
“Jamila ba lafiya ba, inda mutuwa akayi da sauki, inna kira wayarki bata shiga.
“Ina zata shiga wayarce ta fada masai”
“Taso jamila”
Kashe reshow din jamila tayi suka shiga uwar daka, ko wuta babu saida ta kunna touch light tukunna suka samu haske.
Cire mayafin dake kanta tayi tace “jamila na shiga uku, akwai matsala”
“Mecece matsalar?an gano ne?”
“Ana dai gab da ganowa, jamila shegiyar yarinyar nan tana neman shiga tsakanina da yata,ji nake kamar na kasheta wallahi na huta, kullum cikin tashin hankali nake da fargaba,“
Shuru jamila tayi kafin tace “me ya faru kimin bayani mana”
Take hadiza ta kwashi komai ta fada ma tun tuni yanda maya tsani sabeeha gashi kuma su bahijja sun dawo harda majeed”
“Jamila na kasa natsuwa, ina inuwa daya dasu,gani nake kamar za a gano komai,”
Jamila tace gashi wannan shegen yama daina daukan wayata,wai muje muji da matsalarmu shi ya samu na hannu, ke har barazana yamim wai wallahi wani yazo yana tambayarsa batun yarinyar nan amma ya rufa mana asiri yace taintota mukayi kina ganin akwai wanda yasan sirrin mu kenan? Ko akwai wanda kika fadamawa? Ke nifa dalilin dayasa na ki daga wayar ki kenan don wallahi ba faduwa tayi ba tsoro nakeji, ina zaune gani da yaya idan aka gano ai mun shiga uku.
“Haba jamila bazakice haka ba, taakanin mu yafi haka, ke kadai ce kikasan sirri na, kuma kema kinsan nasan naki sirrin.
“Shiyasa ay har yanxu bakida wadda takaini hadiza, yanxu ya za ayi ko saceta zamusa ayi?”
“Toh tayaya za a sace ta? In kika koma kice masu menene?”
“Ya zanyi jamila toh??? Eh ya zanyi?”
“Ki bata fiya fiya kawai tasha ta mutu,”
Shuru hadiza tayi ta rasa ya zatayi, “in aka gane kuma fa?”
“Eh haka ne kuma, ke kodai mu koma wajen boka? Wanda ya maida maki ita kamar ba mutun ba? Ya kulle maki bakinta?”
“Kinsan fa na daina bin bokaye, shika wanchan rabona dashi harna manta shekaru nawa? Tunda ta fara tasowa fa?”
“Ai kuwa aikin boka ne kawai zai kar ta cikin sauki ba tare da sanin kowa ba”
Shuru jamila tayi kafin tace “akwai wani takaddiri, amma gaskia aikinsa na kudi ne zaki nemo kudi masu yawa?”
“Zan nemo wallahi, a kassarata kawai, tayi mutuwar wulaqanci jamila”
“Bakida case, hankalin kowa ya huta, asirinmu ya rufu da hujja”
Suka kyalkyale da dariya harda tafi, “dadina dake akwai nemowa mutun mafita jamila”
“Haba waa hadiza kece fa, menene bazan maki ba a duniyar nan, zan rufa maki asiri har lahira indai bazamu ci amanar juna ba”
“Ay babu cin amana tsakaninmu tunda kowa yasan sirrin kowa, kai jamila kefa hatsabibiya ce, allah sarki alhajiji, haka kika kashe tsohonnan kikayi fuska kamar ba a yi ba, kinfi iyalansa ma kuka lokacin zaman makoki”
Wata bazawarar dariya jamila tayi tace “ay gadon filinsa dana samu har yanxu yana nan kuwa sheggun yayansa sunata bala’i akanshi har yanxu danaje aka rufe bakin sheggu tsit kikeji”
Suka sake tafawa, gyaran murya da akayi ne yasa sukayi saurin yi shiru.
“Ah ah hadiza kece a gidan namu da dare haka?”
“Hmm jamilu ba dole ka ganni ba kasan idan matsalata ta ciyo ni banida abokiyar shawara sai jamila”
“A sani cikin hirar mana indai ta samun arziki ce”
“Jamila ta hade rai ganin zai zauna tace “ka shiga ka huta mana muna sirrin mu zaka zauna.
“Kya bari mu gaisa dai ko?”
“Haba jamy kyaleshi mana, ya kasuwa jamilun jamy” ta fara tana kanne mashi ido, jamila bata lura ba taba kokarin kashe touch light don an kawo wuta tace “bari kiga nasa sanwa karya kone” ta fada tana miqewa, ay kuwa tana futa jamilu matso kusa da hadiza yace “ina shugowa naji kamshinki, hadiza uwar ruwa”
“Kaifa dan iska ne?”
“Kin fini iskanci ne,kwana dai zakiyi ko?”
“Yanxu zan tafi”
“Dan allah karki tafi haka ki kwana”
Shugowar jamila yasa yadan gyara zama yace “wai tambayarta nake zata kwana ne tace ah ah ga dare yayi”
“Dama baka bata bakinka ba dole ta kwana ay ina zata samu motar cikin gari yanxu, an kira sallah ka tafi masalaci”
Miqewa yayi yana yaqe ya futa ya barsu zaune.
Wajen bayan isha’i saigashi da tsire, wai ya kawowa hadizq bakuwa, jamila bata kawo ranta ba wannan yasa tace “ an gode”
Kusan a tare ta zuba masu tuwo sukaci, suna hira, banda shi data sashi cin tuwon a daki, koda wasa jamila bata wasa da zanjen jamilu da wata macen koda kuwa hadiza ce, tasanshi da zalama, musamman da kwanaki taji yayi wata magana data tada mata hankali ba tare da sanin sa ba, kuma ba sau daya yayi mata haka ba amma bata kawo komai aranta ba.
Suna cikin kwanciyar aure kawai sai ya dunga kiran hadiza dije… kinyi ruwa dadi, tasha jinshi yana fadin haka data tambayeshi sai yace mata ay sunan uwarshi yake kira kuma dadinta ne yasa yake haka, kai namiji da yaudara😂😂batasan abunda yake shukawa ba.
Dare nayi jamila ta mata shimfidar kwana anan parlor, saboda dakin yaran akwai zarni saboda futsarin kwance da sukeyi.
Achan gida ko sai wajen tara su bahijja suka dawo, suna dawowa ta wuce dakin maya ta taddata kwance, tashin duniya ta mata maya kamar gawa ko motsawa take gabanta ya soma faduwa, juyawan da zatayi kuwa kawai taga kwayoyi jibge gefen gado, hannunta na karkarwa ta duba taga sleeping pills ne, jikinta gar rawa yakeyi, ne maya keyi da sleeping pills ay bata gama shiga tashin hankali ba saida taga wani maganin a gefe, tana dagawa taga family planning, wannan yafi rukitar da ita, daddy na knckimg dakin tayi saurin boyewa a bayan hannunta, “wifey… “
“Yes daddy, barci takeyi ashe muje karmu tasheta”
Ta fada tare da futowa tabi bayanshi.
Kwana bahijja tayi tana kuka, ay a daren tabtura letter din retire, akan yarta ta lalace ga hakura da aikin, daman fadan da sukeyi da dady kenan, yayi retirw already kuma ya kawo mata shawarar su dawo gida gaba daya ta nuna bazatayi hakan ba aikinta nada amfani.
Bangaren taj ko a wajen nanna yayi dinner sun dade tare kafin ya koma part dinshi da tunanin fatima.
Itako fatiman gaba daya bata cikin natsuwarta, ganin irin kallon da maya ta mata yasa duk ta fita hayyacinta, gashi hadiza tasha mata warning.
Toh bangarensu hadiza, sai wajen goma sha daya duk suka kwanta, jamilu da baya barcin wuri sai gashi ya kwanta tun tara, su jamila suka hirarsu kafin ta mata sallama ta wuce daki, har hadiza na mata tsiya, “dan allah karku tada mim da hankali ina kusa da kofar daki, nida ba aure ba shekara nawa banji dadin namiji ba”
“Shegiya badai kin tsaya kwadayin na mijin wata ba”
“Kwarai kuwa kuma wallahi nan bada jimawa ba zan mallakesa, bari wannan damuwar tawa ta wange kiga abunda zai faru” sukayi dariya jamila ta shige ciki ta karo kofa.
Chan wajen karfe biyu dare hadiza ta soma jin ana tabata, kamar da wasa taji ana jan zanin ta, tuni ta bude ido, ga mamakinta wa zata gani jamilu, yana mata wasu abubuwa.
“Dan girman allah ki barni na dan dana”
“Baka da hankali ne? Jamila fa na ciki?”
“Toh se me? Ke wallahi bana iya barci in banji ki luntsum ba hadiza, dan matso mana..”
Toh da haka dai duk yanda taso ya kyaleta yaki karshe dai tace mashi toh su fita bandaki suyi acahn kar ajiyo su yace to, yaja jela yabita har toilet.
Ahankali jamila ta soma laluben dare, ay maganar da hadiza tayi da ita ta kwana dama kwana biyu basuyi ba, jin wayam yasa ta bude ido, ta kunna fitila, ba jamilu ba labarin jamilu, tashi tayi zaune ta gyara daurin kirji datayi ta haske dakin tass babu jamilu, ta dauka bandaki ya shiga wannan yasa ta koam ta kwanta, ah ah minti goma ta wuce babu jamilu babu motsinsa, haka kawai jikinta ya bata ta tashi kawai, ta bude kofar dakin ahanakli ta futo, kallon katifar hadiza tayi ganin kamar mutun a kwance yasa ta sauke ajiyar zuciya da batasan tayi ba ta futa ahankali tana bude kofa, hanyar bandaki ta nufa daidai nan aka kawo wuta, hasken bandakin ya bayyana, takowa ta somayi tun bata kaiga kofar ba ta soma jin wani irin sauti, da nunfarfashi, sai kuma muryar jamilu data biyo baya ahankali ahanakli “wayyo hadiza dadi, kinfi jamila, wai zuma kike zubawa a wajen ne? Bude min dakyau, na shiga chan chan wayyo dadii wayyo”
Kafarta na rawa ta karaso bakin bandakin tana jin sautin muryar hadiza tana wasu abubuwa, “shiga jamilu wayyo dadi,alkah ya tsinewa jamila, ashe dadin da take ji kenan?”
Jikin jamila na karkarwa ta doso bandaki ga bakin kofar ta dan tura kofar taji a rufe, cikin sauri ta tafi wajen tagar bandaki tana bude daman akwai dan dutse a wajen ta hau kan dutse take ta hangosu tsirara turmi da tabarya sai faman kumi sukeyi, tuni jikin jamila ya fara rawa ta toshe bakinta tana kallonsu, har suka gama tasss akan idanunta, “Kai nayi missing dinka wallahi, rabona dakai tun ranar nan fa danazo, haka ka zazzage min ruwan dadi ka barni da juye juye da daddare”
“Kedai bari, dana hau kan jamila sainaji lamii shuru, gata a bushe wallahi babu kumarin arziki, yanxu nasan na ci wallahi, hadiza badai dadi ba”
“Ni din wasa ce, ka futa kaje wajen matar karta tashi tunda ka sallameni”
“Mu dan kara mana” ya fada yana juyata jamila ta sauka kan dutse, ta bude har kafarta na jini ta danyi yar kara bai futo sosai ba ta toshe bakinta ta arce zuwa daki, hadiza tayi zumbur tace “qara naji ko bakaji ba?”
“Ban jiba wallahi ina zanji ni jamilu ina kwasar dadi”
“Kaga jela duba jamilu”
Dole ya kyaleta ya futo yana gyaran wando ya shiga daki, yana shiga jamila tayi saurin jan barko ta rufe fuskarta yayi tsaki ta hau kan gadon.
Jamila na kuka cikin bargo tana zazzaga ruwan bala’i aranta.
“Bura uban chan, hadiza kin je inda bai kamata kije ba, ni nan jamila saina jawo maki masifarda saikin kwana dubu kina kuka, tunda har kikaci amanata wallahi saina tona asirinki shegiyasa asararriya”….
Toh mun kwana nan allah ya kaimu zuwa gobe😂drama iya dramaa akwai bala’i a gaba
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 105
Jamila dai kwana tayi tana kukan bakin ciki takaici, da zafin cin amana, idan za akwana ana ce mata ga abunda hadiza keyi da mijinta zata rantse karya saboda ta yarda da hadiza sosai, ta maidata kamar yar uwarta ta jini, ta iya ta musanya yarda bata da alhakin kowa duk don hadizar ta bukaci haka kuma bata waiwayi mai zai biyo baya ba tsabar tsantsan kusancin dake tare dasu, amma ta rasa abunda zata saka mata dashi sai wannan? Kuma akan idanunta ta shiada hakan? Wannan cin amana ko a lahira bazata taba yafe ma hadiza ba, kuma tayi alkawarin saita nuna mata ba a taba jamila a zauna lafiya, dukda tasan hatsabibancin hadizar ita kanta baisa taji tsoro ba, saidai su kanshe kansu don wallahi saita baqanta mata yanda taci amanarta, ashe sunyi shekaru sunayi? Bama tun yau aka fara ba, ranar nan ma ashe raina mata hankali sukayi, kuma wallahi saida taji a jikinta amma ta basar wai ita tana ganin babu wadda takeda kusanci da aminci kamar hadiza, kai kota mutu zata iya barin yayanta wajen hadiza bazataji darr ba saboda tsabar yarda amma haka sukaci amanarta, shi jamilu bai wani dameta ba don tasan zaije waje ya nema, kuma yana bin mata wannan ta sani tun tuni, shine bin kananun yara yan talla shine bin yan 2k one night, dayayi ta’asarsa ita ke bi taba kwashewa amma wannan karan kam abun ya mata zafi, gashi kwance gefenta bayan ya gama maganganu marasa mutunci akanta da wulakanci, wai gata a bushe, wayam babu dadi, kam’bala’i badan tana danne zuciyarta ba sannan kuma tana tunanin yayan dake tsakaninsu ay wallahi data daba mashi wuka ta kashe shege ta huta dan buran’uba.
Safiya nayi ta riga kowa tashi, duk yanda taso ta danne abunda ke cinta a zuciya, kasawa tayi idanun nan a kumbure ta futo har ta wuce hadiza daketa sharar barci, ta dora tafashen ruwa, allah allah kawai take ya tafasa ta kwarawa shegiya, wata zuciyar ta haneta, “tunda har kika iya kaiwa har safiya bayan kinga cin amanar da suka maki ra’ayul ayni ai zaki iya dakawata ki hukuntata yanda zata wulaqanta, yanxu kika watsa mata ruwa taci banza,daure jamila danne” haka zuciyarta ta dunga raya mata.
Haka nan ta hkura ta dora sanwar safiya, indomie ma ta aika aka suyi mata don su halifa sun tashi, sheggun ne suketa barcin asara, tana gama dafawa ta zubawa su halifa suka tafi makaranta ita kuma ta juye masu a tray.
Daidai nan jamilu ya futo,sai faman wage baki yake da asuwaki, kauda kanta tayi ko mutunci gaisuwa bai samu ba saida ya fito daga bandaki yana dariya ta kalleshi tace “ba haihuwa ba ko yaya dari mukayi dakai saina hukuntaka jamilu,”
“Ina kwana mijin jamilaaa ikon allah” jamila ta fada tana kashe murya, sakin baki yayi galala yace “lafiya lau uwar halifa, abunci fa?”
Daman haka yake kiranta dashi, indai bai kirata da jamila ba.
“
Gashi nan na zuba mana gaba daya, hadiza ta tashi kuwa?”
Kanshi har waji rawa rawa yake yace “bari na dubo ta” ya shige daga ciki jamila ta bishi da wani kallo, kai kana ganin irin kallon nan kasan suna ruwa😂
Cikin parlor ta shiga daidai nan hadiza ta tashi, tana hamma, kallon jamila tayi tace “ina kwana aminiyas”
Saida jamila ta dan dakata kamar ta shaqota kafin tace “lafiya lau, sauko muci tare na zuba mana duka”
Ko kuskurar baki hadiza batayi ba suka zauna, jamila taja kayan kwanciyar data kwanta dashi suka fara cin abunci.
Jamilu sai faman wage baki yakeyi don hardashi,normal normal suka fara hira, don kwata kwata jamila batayi gigin nuna masu ta ga wani abu ba, su ko a wajensu sun maisheta shasha sha saisu kalli juna su kanne ido, jamila sai kawai murmushi tayi.
Wuraren wajen karfe goma sha daya hadiza tayi wanka ta shirya, zasuyi sallama jamila tace “toh maganar kudi ya za ayi kenan?”
Shuru hadiza tayi kafij tace “ni yanxu gaba daya dubu dari uku ce a wajena, kudin albashin mu kenan na wata uku, kinsan dubu hansin hansin wannan tsohuwar ke bamu nida shegiyar yarinyar nan”
“Toh ki turosu duka kuwa don wallahi dakyar idan zasu kai ma, ba ayi maganar kudin mota ba wannan mai sauki ne don zan biya da kaina”
“Allah sarki jami, allah yabar min kawata”
Dariya jamila tayi tace “Ameen kawata”
A take hadiza ta tura dubu dari uku zuwa account din jamila, sannan sukayi sallama kan duk yanda akayi jamilar zata kira hadizar ta shaida mata.
Tana futa jamila ta daura kafa daya kan daya tana kallon alert dun kudin, “hadiza kenan…”
Chan banagaren maya bata tashi bafa saboda over dose tayi ma kanta, bayan kwayoyi data sha har yar kwalba ta kofa, allah baiyi bahijja zata gani ba, haka su laila suka wuce school ita bata samu taje ba, koda daddy ya tambayi mummy maisa batajeba nan ta shiada mashi baqon watan ta ne yazo shine ta mata allura ta huta.
Yadai je a zancen nata a haka amma bawai ya yarda bane, don tsakanin jiya zuwa yau gaba daya yanayin bahijjan ya sauya koda ta shaida mashi tayi retire yayi mamaki sosai don yanda ta kafe bayajin zata iya hakura da wannan aikin nata, don tana son taimakon rayuka, koda yake anan ma zata iya yin hakan ba sai lallai achan ba.
Ya rasa dalilin da Nigeria gaba daya ta fita ranta, taki jinin dawowa, saitayi shekara biyu uku a jere bata yi tunanin zuwa gida ba abun yana bashi mamaki, kuma batun yanxu abun ya faro ba tun bayan data haifi maya.
Misalin wajen karfe goma sha daya ta farka, kanta yayi mata wani irin nauyi sosai, ta dubi time ganin 11 yasa hankalinta tashi, gaba daya batayi aiki da tunani ba, what if dady yaganta a wannan yanayi? Take gabanta ya fara bada dam dam, sallamar bahijja yasa ta sola gyara natsuwarta yanda take taoron dady bata tsoron mummy kwata kwata, its easy to fool mummy amma dady a take yake rafko ta.
Murmushi bahijja ta mata hannunta rike da bowl ta karaso ta ajeshi gefen bedside maya ta wani kauda ido, bahijja ta zauna gefen gadon tare da kamo hannunta tace “baby babu gaisuwa”
“Good morning” ta gaisheta a takaice, “morning baby, kanki na ciwo ko? Ga soup nan na kawo maki”
Kallon bowl din maya tayi kafin tace “thank you”
Miqewa tayi ta wuce bathroom ta wanko bakinta kafin ta futo, bahijja ta kalleta tace “kinyi alwala?”
Girgiza kai mayan tayi ta juya zuwa ga bathroom din.
Agaban bahijja ta futo bayan ta shunfida mata sallaya ta bata da hijab ta tada kabbarar sallah tana kallonta.
Kai ko a cikin sallar mayan ma aikwai dan gyara, at that point bahijja ji tayi ta tsani kanta gaba daya wallahi tsabar takaici.
Mayan na idarwa ta miqe tsaye ta nufi bakin gadon ta zauna ta dauka bowl din, bahijja na kallonta batace mata uppan ba, ta shanye tass, saida ta gama bahijja ta kalleta tare da aje pills dinnan a gabanta ta soma magana “when did this start maya?yaushe kika fara shan different kinds of dangerous pills? Me kikeyi da maganin hana daukan ciki maya?”
Shuru maya tayi ta kauda kanta gefe, tgaba daya tsoro ya gama baibayeta, indai mummy ta gani to tabbas dady ma ya gani”
Sai kawai ta fara hawaye, ta kamo hannun bahijja tace “mummy please don’t tell daddy, please bazna