Advertisements
Chapter 12 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 107

33K to 36K   out of 320.4K words

babu damar guduwa saboda parlorn babu haske, na biyu kuma saida taji takun tafiyarsa da bude kofar da yayi ta tabbatar mata ya dawo kenan, ''na shiga uku'' ta fada a xucicoyar, wani irin tsoronsa kawai taji ya durar mata take ta tuna lokacin da suna asibiti, tana hango abubuwa da dama a idanunshi a lokaci wanda ta kasa gane ko menene.
shiko yanda yake tafiyar nan kamar yana ganinta dukda akwai haske yana zuwa daidai inda take tsaye yace ''who d hell are?, ke wacece?''
kuri sabeeha tayi jikin na bari don da zafi zafi ya taho, ''speak up!!!!'' ya daka mata tsawa, ay batasan lokacin da jikinta ya fara kyarma ba, dukda tsoron da taji hakan baisa tace tak ba ta soma yin baya ahankali ahankali, ko taku biyu batayi ba kawai ya cimmata kamar dama chan yana kallonta ya kamo damtsen hannuta ya rike gammm cikin nashi kamar ya kama hannun yar yarinya dake hannun nashi nada girma sosai, kamar zai balla, tayo gaba,a cikin duhu suke kuma baya ganin fuskarta don bazai iya tantance yanayin halittarta ba amma a kanshi yana hango gaba dayanta kuma jikinshi ya bashi itace wadda ke addabar kanshi, itace wadda yake gani a memory dinshi dukda ya kasa gane fuskanta, tunda ya kama dan hannunta ya rike yana kallon haske kwalla idanunta komai ya tsaya mashi chakk, tabbatacciya ce ta faru a wajen don a lokacin ya tabbatar da ita dince,sai kawai memry dinsu ya sake zuwan mashi inda yake shan wahala tana kula dashi, yana kuka tana kuka, yana farin ciki tana farin ciki gaba daya sai yaji jikinshi yayi sanyi, baima san lokacin daya saki hannunta ba yayi baya, sabeeha na samun dama kuwa tayi sadf sadaf ta fuce daga parlorn, tana rufo kofar wutan ya dawo…..



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 64

Update!!
tunda ta samu ta fuce daga dakin ta wuce dakinta dake kasa,zama tayi ta dafe kirjinta,muryarshi na yawo kanta, ko'ba a fada mata ba ta fuskanshi ya tuna wasu abubuwan,kuma yanxu abun ke mashi zafi sosai, yanda yake magana kadai ya tabbatar mata da dacin da yakeji a cikin ransa.
washe gari da safe duk kowa ya hallara akan dining, babu yanda ammu batayi ba da sabeeha ta futo taqi futowa, da yake yau weeknds ne hidaya da kanta ta aika a kirashi ya sauko sukayi breakfast dashi, tun daga sitting room suka soma jin shewar afiya da sonata, fadwa data kafeshi da idanu tana jin muryar sonata kawai tayi murmushi.

sanye suke da dubai abayas masu kyau, flight din safiya sukabi tun wajen six sai 8 suka karaso, da yake trip din bashida nisa tsakanin dubai da saudi, kowannensu ya sauko da gashin nan har gadan baya babu koda kallabi ne, afiya na gaba sonata na biye da ita a baya har suka karaso sitting room suka yada zango maids na biye da boxes dinsu.
 
bai wani ci abuncin kirki ba coffee ne kawai yasha ya dauka savage ya goge bakinshi ya danyi relaxing bayanshi, saida ya jira hidaya ta gama ta miqe tana mai dubanshi tace ''inason magana dakai''
girgiza mata kai kawai yayi tayi gaba ya bita a baya, fadwa ta korasu da harara, yana daga bayan hidayar suka karaso sitting room daidai nan afiya ta dago ta kalleshi shima ya mata kallo daya, baima lura da sonata dake kokarin kwance igiyar takalmin ba saida afiya tace ''babes…''
''uhm..'' sonata ta amsa ta tana dagowa, karaf kuwa idanunshi ay sauka kan na sonata, daidai nan ammu ta taso daga dining din itama ta tunkaro wajen, sonata na ganinshi tayi saurin miqewa fuskanta a washe ta taho da sauri tana tunkaro inda yake batayi wata wata ba kawai ta rungumeshi, …''oh my gawdddddd…my zaddy is back, oh my..oh myyy i missed you so so much, youre back''
saqe yayi kamar an dasa shi don mamaki yama kasa daga matsar da hannayenshi, gashi ta wani kanainayeshi, gaba daya daga ammu harsu fadwa da suka karaso binshi suka dinga yi da kallo harma da sonata din, daidai nan sabeeha ta fito daga bedroom dinta, tana fito ta tsaya daga mesa tana hango ikon allah, ''yar iskar ta dawo kenan'' ta furta tana tabe baki, 
kallonshi hidaya tayi nan take idanunshi ya shiga cikin nata baima san lokacin da ya cire sabeeha daga jikinshi ba, ayfa batahakura ba dukda ya tureta haka ta sake koma mashi zata rungumo shi ammu ta zagayo inda suke ta kalli sonata tace ''what sort of nonesens is this, wacece wannan kuma? daga ina haka''
karaf fadwa ta amshe da , ''thats his ex fiance, ay shi ya santa tunda ya mata alkawarin aure''
sonata najin haka ta soma murmushi daman plans dinta kenan, dataji afiya tace mata ya dawo hayyacinshi a shirye tazo don zatayi komai don taga ta sameshi, da gangan tayi maganar nan saboda tasan tabbas sai anmu ta kwarkware komai a wajen,daman tanata neman yanda zatayi ta dakatar da hidaya kan maganar da zatayi mashi yanxu.
bata ma gama rufe baki ba ammu tace ''ita baku fada mata cewa yanada mata already ba? hartake buyoshi inda yake?'' 
damm gabanshi ya fadi, hidaya naji haka itama hankalinta ya tashi, ba ta haka taso yaji maganar ba, me ammu ke shirin yi kenan, 
''AURE kuma?'' baima san lokacin da kalmar ta fito daga bakinshi ba, ''yes….ba…''
''ammu…'' hidaya ta dakatar da ammu daga magana, wani irin kallo ammu ta mata kafin tace ''wai boye boyen me akene da baza a futo fili a fada mashi komai ba, he needs to know everything''
 tunda ammu ta fara magana yake kallonta yana kokarin prosessing abunda kunenshi ya jiyo mashi, hannunshi ta kama tace ''yes khaal ya aura maka macen datafi duk wanda kenan sanin damuwarka, wanda tasan kuncinka tasan damuwarka kuma wadda ta tsaya maka a lokacin da ba kowa ke ganin ka a matsayin mutun ba, a lokacin da….''
''ammu… hidaya ta sake dakatar da ita, tana mai kallon taj din da gaba daya ya sauya lokaci guda, idanunshi sunyi jaa sosai, ko sauraronta ammu batayi ba har zuwa lokacin yana gabanta ta cigaba da magana ''kafun khaal ya mutu…''tundaga wannan kalma ta karshe data fada bai sake jin komai ba kuma saboda kunneshi dayayi wani dummm, hidaya dake tsageruwa ce sai kawai tajashi baya ta fuskanshi ammu tace ''bakiga yanayin dayake ciki bane?, we cant just tell him everything lokaci guda saboda zai iya samun confusion,''
ammu na kallonta kiriri tana karya, neman hanya kawai take na ganin ba a fada mashi gaskia ba, ammu na kallo hidaya ta jashi zuwa sama hankali a tashe,su kuwa waenda ke parlor sunyi saqe, sabeeha dake labe bakin kofa kaf abunda ya faru ta saurara, batayi tunanin ammu zata zama bold haka ba lokaci guda ta fada mashi, sai kawai taji dadi aranta koba komai yanxu akwai hope din cigaba a nan gaba, kuma hidaya ta samu daidai da ita, ammu kuwa hidaya na barin wajen kawai sai tayi mrumushi aranta tace ''wayace maki ke kadaice kika iya makirci, du gudun da zakiyi dole watarana sai kin turgude''
tana kaiwa nan ta maida dubanta ga afiya ''ke kuma daga ina haka?,''
afiya data san halinta tayi saurin karasowa inda take ta rungumeta tana murmushi tace ''ammuuu….i missed you yaushe kika dawo''
''yayan bariki kenan, hmmm'' ammu ta fada aranta, kafin ta murmusa tace ''yau sati na guda a cikin gidan nan'' tana kaiwa nan ta wullama sonata wani irin mugun kallo tayi saurin dauke idanunta don daga gani yanda ammu ke magana zatayi jaraba.

ammu na barin wajen ta hango sabeeha dake labe, dakinta suka shige suka zauna ammu na kallon ta ganin yanayinta ya sauya yasa tace ''maysa baki fadamin sun kawo wannan mai zubin karuwar ba''
sunkuyar dakai sabeeha tayi tace ''na dauka ta tafi ne ammu''
''hmm akwai aiki a gabanmu, da alamu sunyi babban shiri kuma basu taba tsammanin zan kawo maganarki ba, daman tsorona daya karki zama target dinsu nasan yanxu zata fara tunanin duk yanda zatayi donta bataki a wajenshi, zatace komai tunda halinta daya da uwarta, she will do anything worst, amma karki damu kinji daidai nake dasu gaba dayansu, ive prepare for them''
tunda ta fara magana sabeeha kanta na kasa batace uffan ba..

acahn sama kuwa hidaya na janshi bata tsaya ko'ina ba sai part dinshi,suna karasowa ta jashi bakin gado suka zauna, yana fsukantar tana fuskantarshi, daga yanda yake kallonta kadai yasa taji a jikinta ya fara suspecting wani abu don yanda ammu tayi magana dazu har tana cewa boye boyen me akeyi, tasan tabbas zai zarga wani abun, kuma tana hango yanda ya damu da sanin rayuwar da yayi a baya, tun tana boye mashi saboda tasan he will never questioned her wataran tasan saiya tunkareta, ay batama gama tunanin ba tajiyo tambayoyinshi kamar saukar aradu akanta, ''DA GASKE NE ABUN DA AMMU TA FADA?, WACE IRIYAR RAYUWA NAYI A BAYA?, WHAT HAPPENED TO ME?, KHAAL YA MUTU?'' cikin natsuwa ya jero mata tambayoyin amma fa ita hankalinta a tashe yake, kamar an kama mai sata haka ta fara kame kame, haka kawai takeji kamar ya gano komai tunda har ya iya tattara courage din tambayarta to tabbas akwai matsala.
gashi ya kafe ta idanun shi da taji lokaci guda ya cika mata idanu.
'' me kike boyemin?,''
ay batasn lokacin data waro idanunta ba waje, da zai taba wajen zuciyarta da yaji yanda yanayin bugun zuciyarta ya sauya, option daya ya rage mata dole ta nemi backup, 

''TAJ listen to me, i'm doing all of this for you, saboda nasan you will be hurt''
saurin rintse idanunshi da suka jaa yayi ya bude su, shifa kawai yanason yasan komai, shi kanshi ya kasa gane dalilin da yasa ake boye mashi, yanxu hakan ma da kyar ya tattara courage dinshi ya mata magana, ''inason nasan komai, what hppen to me a year a ago, how did i end like that? ''

kauda kai hidaya tayi tare da cije leben ta, batason nuna mashi isa da tuni ta dakatar dashi saidai tana tsoron kar ya gano wani abun, tana cikin wanna tunanin sai kawai dabara tazo mata, ''kana son kasan komai ko?', well listen to me carefully', you had a tragic accident which lead to ko samu dissociative amnesia, 1year ago bakasan inda kanka yake ba, kuma khaal yayi using lalurar da ka samu donya samu abunda yake nema,…..''
gaba daya abunda ya faru ta juya mashi zancen ta maidashi kamar khaal ne mugu, kuma shine ya kulla komai don ya karbi komai na kamfaninsu harda yar kwallarta, ''da yake allah yana tare da mai gaskia ba aje ko''ina ba asirinshi ya tonu, munyi mamaki sosai don bamu taba tunanin sonda yake mana bana tsakani da allah bane, gaba daya muyagun ayyukan da yakeyi behind doors sun bayyana, yayi laudering kudaden kamfani, and he attempted to…'' ta sake fashewa da wani kukan kamar da gaske zaka rantse gaskiya take fada, ''i had to protect you all this while, didnt want to tell you all of this saboda nasan zakaji zafi sosai, a fili ya nuna yana sonka amma a zahiri ba hakan bane, he was selfish, ashe all this while kamfani yakeso shiyasa ya damu saika dawo saboda akwai abunda ya shirya, wannan yarinyar daya aura maka is part of his plan, ya aura maka ita ne saboda yayi amfani da ita wajen karbar duk wani shares and property din da ke karkashin sunanka''
tana kaiwa nan ta miqo mashi wayarta ta nuna mashi documentation din da khaal yayi wanda ya maida sunan sabeeha a matsayin next of kin dinshi sai properties dinshi,nayi kokarin raba auren saidai khaal ya nuna min fin karfi dole na hakura na barta don banida right din haka, yanxu kaji irin rayuwar da kayi a bayan ko?,''
tunda ta soma magana harta gama kallonta, yama rasa me zaiyi, yarda da kalamanta zaiyi ko kuma opposite din abunda zuciyarshi da kwakwalwarshi ke nuna mashi, 

''yanxu daka dawo hayyacinka nasan you will never accept this, ka fadamin duk abunda kakeso ayi, naqi korarta ne a gidannan saboda nasan rana irin tayau zata zo, kuma gashi tazo,just tell me me kakeso?''
shuru yayi ya kasa cewa komai, ganin yayi shuru yasa ta sake cewa ''nasan youre shock and surprise, dont overthink your self kaji, banason wani abu ya sameka, specialist consultant dinka yace you shoud not overthink, saboda zai iya jawo maka wata matsalar ko confusion, yanxu komai yazo karshe, ka kwanta gobe zamu cigaba da magana okay?''
girgiza mata kai kawai yayi harta fuce baibar mamaki ba,shi rayuwar da yayi ba a cikin hayyacinshi ba bata dameshi ba kamar maganganun data fada mashi game da khaal, he cant beleive this ya kasa yarda da hakan, kaf abunda ta fada mashi zuciyarshi na raya mashi opposite, kuma yana ji a jikinshi ba haka bane, sannan yarinyar da ake maganar khaal ya aura mashi ita, indai ita yake gani cikin memory dinshi to ba hakan bane, he was happy a memories din daya gani tare da baquwar fuskar da bai sani ba, har yanxu yana tuna sanda yake kuka itama tana kuka, da lokacin da yake dariya, he can see how close he was with koma wacece, toh kodai confusion din da hidaya tace zai samu idan yayi over thinking abun?, no defeinately there's something, dole yayi buncike akan komai.

kanshi ba karamin ciwo yake mashi ba, yanxu shine yayi rayuwar shekara guda baya cikin hayyacinshi?, kuma kamar yaro? tuna wannan kadai daci yakeji aranshi.


a daren bai samu yin barci ba kwata kwata, haka ya kwana yana duban wayarshi, duk abunda hidaya ta fada mashi akan abubuwan da khaal yayi ya gani a internet abu daya ne ya gani wanda bata fada mashi ba kidnapping da akace khaal yayi na heir din taheel, akan headline din news dinma ya gani, he cant believe har zuwa yanxu yaqi yarda da komai, sai a lokacin ya tuna lokacin dayaje gidanshi yaga an kafa SAMA saudi arabia monetary authory, (masu kamen kadarar wanda yayi satar kudaden kamfani ko na banki'')
har zuwa lokacin he could not believe komi dukda ga shaidu.

, dukda bashi da kusanci da khaal yanaji a jikinshi he's not that kind of person, saboda ya nuna mashi so sosai, ya nuna mashi ya damu dashi sosai,ya nuna mashi how sincere he is shiyasa yake jin difficulty din yarda da abunda ya yaji kuma ya gani da idanunshi, maganar hidaya ce ta fado mashi inda tace ay duk yana komai ne don ya karbe kamfani shiyasa ya damu saiya dawo daga london don ya samu ya karbe share dinshi da property dinshi dake shiyasa ma ya aura mashi wata yarinya

 don ya cika kudirinshi na ganin ya karbe kamfanin taheel su, shi kamfanin nan baya gabanshi ma kwata kwata, idan harda yasan kamfanin yake hari ay daya fada mashi shi kwata kwata bayason komai daya danganci kamfanin, ko dawowarshi daga london baiyita da niyar shiga family business dinba.
yarinyar da hidaya tace khaal ya aura mashi ce ta fado mashi arai,nothing is clear to him abaout her, dole yayi buncike akan abunda zuciyarshi ke raya mashi akanta, meysa yake ganin memories dinshi da ita is opposite abunda hidaya ta fada mashi?, idan har zuwan yarinyar don a cutar dashi ne baiga hakan ba a cikin memories dinshi……



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 65
The next morning….
Kwata kwata bai samu yin barci ba daren jiya sai wuraren karfe shida, ya kasa relaxing mind dinshi kwata kwata, abu daya ya yanke aranshi wansa ya kudirci saiya nemo answer tambayoyinshi.
Ahankali ta soma bude dakin naki, sanye take da wata arbiyar nighties red,blonde gashinta har gadan bayanta, dukda babu wani hasken arziki a dakin hakan baisa ta hango kyakyawar fuskarshi ba saboda hasken bedside lamb, ga dan hasken dake lekowa ta wajen curtains, wani irin makirin murmuahi ta sauke tare da takowa har bakin gadon ta tsaya akanshi tana binshi da mayen kallo, yanda take kallonshi kamar idanunta zai zazzago tsabar masifa da jin shauqi, rayuwarsu a baya take tunawa, rabuwar da sukayi ta shiga damuwa sosai, duk yanda taso su dawo yaqi bata chance, kuma tasan yana sonta sosai, kirsa irin ta mata babu wadda batayi ba, gangancin ta ne ma ya jawo ta bari ya gano ta da wani, don a gidan sa ne ma incident din ya faru, da yake shige da fucenta a gidan shi ba wani abu bane don har pin dinshi tana dashi, duk sanda taga dama tana zuwa daman su turawa ba ruwansu da wannan, kwana ne dai bai yarda tanayi a cikin gidansa ba ko yana nan ko baya nan, toh a ranar yayi tafiya zuwa jamaica, da yake yace mata sati guda zaiyi shiyasa tazo apartment dinshi ta kwana ba tare da saninshi ba kuma tasan baya so,da safe shine ta futa zuwa gym din apartment din nashi, anan ne ta hadu da guy din har tayi mashi tayin zuwa apartment din boyfriend dinta, shiko ya bita suna hawa saman salon ya chanza, shi kuka bangaren taj daman wani business ne yaje yi a jamaica, branch dinahi dake chan ne aka samu matsalar importation kuma dole saiyazo shine yaje,yana zuwa dayake shi workaholic ne baima tsaya yin komai ba ya warware matsalar dake chan din ko kwana baiyi ba ya hau flight din dare, washe gari da safe yana suna isowa ya wuce gida direct.
Sauke ajiyar zuciya tayi tana mai kallon faffadan kirjinshi dake bude yayi unbuttoning din rigar jikin nashi,ga wani kwantaccen gashinsa dake kwance a wajen kadan, hannunta ta sanya ta soma shafa mashi karjin nashi har zuwa wajen cibiyaraa, kamar a mafarki ya soma jin tafiyar da ake mashi a kirjinsa, da yake light sleeper ne yana jin motsi ko yaya ne yake farkawa,

ahankali ya soma bude idanunshi, harya sauke su akan sonata dake shafashi, muryarta chan kasa kasa ta soma magana tana juya idanu, “good morning zaddy” tana fadin haka tayi saurin rankwafowa ta rungumeshi, cikin hanzari yayi saurin tashi zaune ya zareta daga jikinshi, fuskan nan nashi a hade,yana mata wani irin kallo mai tattare da kyama da tsana,ita kallon da yake

12 / 107