Author : Queenmerh Category : Complete Novels
mata aka cire tana kokarin miqewa zaune ta kasa saboda cuffs din da aka saka mata.
Discharging dinta akayi security suka rakata zuwa dakinta, tana shiga wani visiting call din yazo mata.
Duk a tunanin ta fadwar ce ta sake dawowa don bata kawo ko afiya ce ko wani family member ba daban.
Security suka rakota har wajen visiting area kafin su barta a tsaye dago da kanshi yayi ya sauke akanta, saurin yin baya hidaya tayi wuth so much shock, karara akan fuskarta, hannunta ta sanya kan fuskarta ta mutsuka idanunta don tabbatar da jamid ne a gabanta, mikewa yayi tsaye ya tunkari inda take tabi kafafunshi da kallo har zuwa hannyanshi daya sanya ya kamo nata ya zaunar da ita sannan ya dawo wajen zamanshi ya zauna.
Saurin kauda shock din dake fuskanta tayi ta kauda idanunta irin kamar batayi mamakin ganinsa ba.
“You must have work hard on your self, Yaushe ka samu lafiya?”
Girgiza kai yayi, this is hidaya, bazata taba chanzawa ba.
“You must be happy to see how i end up here,…mind you i still don’t regret my actions, i still stand on my grounds duk abunda nayi a baya”
“Nasani, babu wanda zai fadi ko wacece hidaya saini, amma inaso ki sani duk abun dayake faruwa dake yanxu baikai kwatankwacin pains din da kika saka yaron nan a ciki ba, and alhakin sa ke binki, baku hakura ba saida kukaci galaba akanshi, ay bakiga komai ba ma tukunna you contributed in destroying alot of peoples life, dukdan saboda power, saboda arzikin da zamu mutu mu barshi, saboda hatred, kin mance kema uwace, kin haifa kema, idan naki ne yayi experiencing abunda kikayi ma yaronnan…”
Ya dan dakata jin wani irin daci a zuciyarsa kafin ya cigaba, “yanxu ina arzikin?ina power din?
Idanunta ne yayi jaa sosai, tsakanin kwanakin datayi a wajennan yasata reflecting abubuwa da dama, musamman da fadwa tayi threatening dinta akan danta, bata taba regretting abubuwan datayi ma taj ba sai yanxu, ta dandani zafin cin amana musamman ga wanda ka yarda dashi.
Shida ta nemi wulaqantawa, shida ta nemi salwantawa rayuwa ta rabashi da kowa hatta mahaifiyarsa ta karfi da yaji ta maishesa kamar wani dan kwikwiyon da take juyawa san ranta, kuma ya yarda da ita sosai, ya bata matsayinda ko mahaifiyarsa bai bama in return tayi betraying trust da yardar daya bata da girman daya, infact bata taba considering dinshi matsayin dan uwanta ba ko sau daya, dukdan saboda mahaifinsu ya auri mahaifiyarsa.
Wani abu ne ya soma sauko mata a fuska kamar hawaye, she couldn’t believe hawayen takeyi, wannan hawayen nata ya bama jamid answers din da yake nema, ko zata kwana tana denying batayi nadamar abubuwan datayi a baya ba yasan yanxu tayi.
Saurin gogewa tayi ta dubeshi, “are you done?” Tana fadin haka ta miqe tsaye zata bar wajen yayi saurin dakatar da ita.
“You’re a victim as well, Its not too late to repent, its not too late to make things right,”
Dan dakatawa tayi kafin ta juyo, ta kalleshi, “khaal yana raye! Bai mutu ba?”
“Bai mutu ba? Yana raye?”
“Kwarai da gaske,” ya bata amsa
“He was never dead to begin with,”
“Wa kenan????” Hidaya ta tambayeshi kamar bata sani ba
“yar uwarki fadwa, !!!”ya bata amsa kai tsaye,
“I was one of her victims, itace sanadiyar paralyze dana samu, tana amfani dake ta hanyar cinmma burinta da boye duk wani sirrikanta.
Shuru hidaya tayi tana wani nazari, mamaki ya gama cikata sosai.
Kamar an tsunguleta ta dago ta kalli jamid tace
“Barad…!!! He’s in danger,ka daukeshi ka boyeshi,”
“Barad??” Ya kalleta ganin yanda gaba daya ta nemi rikicewa.
“Me zai samu barad?”
Dubansa tayi dakyau hannunta gar karkarwa yake, “fadwa ba kanwata bace, fadwa yar abdul basit ce”
Confusely yake kallonta, “ni take hari,kuma zata iya yin komai don ganin ban bayyana wannan sirrin nata ba, you need to take barad, ka boyeshi, karta cutarmin da daa”
Gaba daya jamid ya shiga confusion, yanxu wannan ne babban sirrin nata daman?….
Nigeria….
Karfe 5 daidai suka dawo gida, as always duk sun fita itace last, tana fitowa ta rufe motar saida ta jira hamad ya kashe motar ya fito kafin ya zagayo ya tadda ta tsaye, laptop din dake hannunshi ya miqa mata.
“Kiyi presentation din dashi”
Da mamaki take kallonshi don kwata kwata batayi maganar presentation dinba ya akayi ya san zata buqaci laptop?
Ganin ta tsaya yasashi “ko na aje abuna?”
Cikin hanzari ta karba murmushi ya kubce mata tayi saurin sunkuyar da kanta tace “thank you ya hamad”
“You’re welcome muje ciki”
A tare suka shiga main house ya bude kofa ta shiga kafin ta shiga, saida tazo wucewa part dinsu ta sake juyowa ta dubeshi bakinta ta dan motsa ahankali tace “thank you” sautin muryanta bai futo ba amma yanda ya kura mata ido ya gane abunda ta fada, tana fadin haka ta wuce ya bita da kallo, ya sauke wani murmushi ahankali, he just loves to seeing her smiling.
Saida yaga ta shiga ya juya ya futa daga main house din.
Da sallama ta shiga dakinsu, hadiza na zaune tana ninke bras da panties din maya datasa sabeehar ta wanke da asuba.
“Ina wuni mama”
A daqile hadiza tace “lafiya” kafin ta miqe da kayan datake ninkewa ta futa.
Sabeeha ta bita da kallo tana tunani wani abu ranta.
A gurguje tayi wanka tasa doguwra rigar da aka bata cikin kayan laila kafin ta fito zuwa kitcwhn, tana shugowa rabi dake tsaye a kitchen din tace “har kun dawo?”
“Eh anty rabi yanxu muka shugo”
“ga abuncin ki nan,”
“Tohm akwai aikin da za ayi?
“Ah ah jeki huta abunki kawai”
Murmushi sabeeha tayi tace “toh”
Daukan abuncin tayi ta fita rabi ta bita da kallo, haka kawai take tausayin yarinyar, babu ruwanta ga respect
Da sallama anne ta shigo bangaren nanna dake zaune da laptop kan cinyarta, zakayi tunanin aiki takeyi saidai gaba daya natsuwarta bata wajen kwata kwata.
Sallamar da nanna tayi ne yasa ta dawo hayyacinta bayan ta amsa.
Zama anne tayi suka gaisa anne ta mata ya jiki, “badai aiki kike ba hajara keda akace ki huta”
“ alhamdulillah naji sauki ay anne”
“Inason zamuyi magana” anne ta fada tana kallonta.
Nanna tasan maganar dazatayi mata wanda a yanxu dai bashi takeson ji ba kwata kwata, amma haka nan ta daure tace “ toh yaya allah yasa lafiya”
“Tajudeen zai dawo nan gida da zama, zamanshi a hotel bai daceba, ina amfanin zaman hotel ga gida na bari ne daman ki samu sauqi tukunna”
Take nanna ta hade rai kamar bata taba dariya ba tace “zaman me zaizo yayi anan? Bazai zauna anan ba, idan ya gama abunda ya kawoshi ya koma chan inda ya fito”
“Hajara kinsan me kike fada kuwa? Na kasa gane maki? Wannan wani irin kafiya ne? Danki ne fa? Shekara nawa kina mararin ganin danki?”
“Yaya, banida da, na dade da ajiye zama uwa a gareshi, tunda har banida mahummaci a rayuwarsa”
“Ya isaa!! Ya isa haka nan, saurareni da kyau hajara,karki sake ganin laifin danki na qin waiwayarki dayayi,kin tafi kin barshi yana da kananu shekaru ba tare da tunani wani hali zai shiga ba dukdan saboda laifin ubansa, mey laifinsa? Ya za’ayu bazaiyi tunanin kinyi abandoning dinshi ba? shin kinsan irin rayiwar da yayi achan? Kinsan ya childhood dinshi ta kasance achan? Wannan abun da kikeyi ba komai bane face huce takaicin tsohon tabon dake dan qare aranki ya hanaki moving on shekaru wajen nawa ya hanaki yin aure, tun wuri ki dawo hayyacinki ki rungumi danki karki tafka babban kuskuren da zakiyi dana’sani,”
Kuka sosai nanna keyi anne na mata fada yau ko tausayinta bataji ba don furucinta ya bata mata rai.
Ganin yanda take kuka sosai yasa anne kama hannayenta ta rukosu tace “haba hajara kamar bakida tawakkali? Mene laifin yaron nan? Eh??ki godewa allah daya sa zaku sake ganin juna kuma wannan dama ce allah ya baki na zama uwa a karo na biyu, duk wani abu daya faru dama chan haka allah ya kaddara saiya faru bamu isa mu chanza shi ba”
Kallon ta anne tayi tare da bata qwarun gwiwa, “danki na buqatarki hajara,ki zame mashi uwarda ya rasa tun yana shekara bakwai, ki bar komai ya wuce, ko zamo mai karbar kaddara duk yanda tazo maki, ki mance da baya kamar ba ayi ba”
Runtse ido nanna tayi kafin ta bude idanunta ta dafe kanta anne na ganin haka ta fara kallon gefen gadon ko zata ga maganinta idanunta ya sauka kan bedside drawer dake bude, taci karo da hotunan taj din, yana baby da lokacin daya fara tafiya, har zuwa lokacin daya girma ya zama saurayi.
Murmushi kawai anne tayi ta balla mata magungunan tace “dadai aje wannan kafiyar kikayi kikaja danki daya fi maki, don wallahi idan har kikayi watsi da wannan damar taki ya koma zuciyarki ce zata buga, wllah ya sawaqa”
Tana fadin haka ta fita.
Gaba daya nanna ji tayi jikinta yayi sanyi sosai, dukfa wannan abun da take a baki ne, tunda ya rike hannunta ranar yana kuka a gabanta gaba daya ta sare, ta fara blaming kanta for komai, what kind if a mother zata tafi tabar danta ba tare da tayi wani difon tunani ba tunawa da wannan kadai da abunda mahaifinsa ya mata kesata karaya.
Anne na fita daga part dunta ta wuce nata ta soma dialing number taj, cikin ikon allah kuwa ya dauka cikin gaggawa, kwananshi biyu kwance yana zazzabi saida salim ya kawo mashi doctor ya dan samu sauqi.
Ko jiya da sukayi waya da anne kasa fada mata yayi abunda ke damunshi.
Yana dagawa suka gaisa ta soma magana kamar haka.
“Inason gobe ka dawo gida, ina dana ina zaman hotel, come back home kaji ko”
Shuru yyi gabanshi na faduwa sosai, “oummi??”
“Karka damu tajudeen, tana nan tana jiranka tajudeen, allah yayi maka albarka yasa muga aurenka da yayanka tajudeen, ni zan aurar dakai ma” ta fada tana murmusawa, maganar aure datayi saida gabanshi ya fadi.
Amma ta wani bangaren ba karamin dadin kalamanta yaji ba datayi na kan cewa oummi na jiranshi, ahankali ya furta “Alhamdulillah, take yaji duk wata ragowar rashin lafiyarshi ta kau gaba daya, saidai kuma gabanshi ba karamin bugawa yakeba sosai at the same time kuma lokaci guda sabeeha tazo ranshi.
✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊
MATAR TAJ (destined with you🩵🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 95
Saudi…
Jamid baibar detention center dinnan ba saida hidaya ta fada mashi komai, asalin fadwa yanda ta kashe tareeq saboda shine ya fara sanin sirrinta da kuma bacewar taj, da yanda ta dunga amfani da ita don cinma burinta, dukda itama tana da nata kason a cikin duk abubuwan da suka faruwa.
Abunda yafi bama jamid mamaki shine asalin fadwar, ba yar taheel bace? All those years haka suka dunga venting akan taj, Hating on him, ganging up on him, suka kusa salwantar da rayuwarshi, kuma ba kowa bane kan gaba sai hidayar, ashe shine asalin dan uwanta, fadwa ce outcast cikin su, ta haramtacciyar hanya ma aka sameta, mahaifiyar tasu da suke duk waennan abubuwan saboda ita ashe itace aje masu abun kunya.
wannan babbar ishara ce a garesu gaba dayansu musamman hidayar data dauka tsanar duniya ta dorama taj, ta wulaqanta rayuwarshi ta kusa salwantar da rayuwarshi saboda tsana, bai tsareta da komai ba, yanxu gashi komai ya juye mata, yar uwar datake tunanin itace jininta ta kasance batada alakar ubantaka da ita kuma ta zame mata babbar barazanar.
Shima kanshi bata barshi ba, dukdan sabod aya tsayama taj, yayi protecting dinshi, saboda hakan ta maidashi kamar wani enemy dinta yana matsayin mijinta.
Tunda ya samu paralyze kuwa ya zame mata mara amfani ta fiddashi daga gidan nan ta turashi kasar waje neman lafiya bata sake waiwayarsa ba, Batama san yanda akayi ya samu lafiya ba har yazo gareta yanxu haka, duk tsawon wannan lokacin bashida tunanin daya wuce na taj da sabeeha, saboda shi kadai zai iya fadin wahalar da suka sha a wajenta, makirci iri iri daban daban dukdan akan abun duniya, dukdan saboda taj karya gajesu.
Babu irin maganganun da jamid bai fada mata ba cikin bacin rai sosai, ta kasa magana kwata kwata gaba daya saboda she’s guilty of everything, he vent so much of his anger akanta sannan ya nuna mata ay bataga komai ba, kamar yanda ya fada mata bazata taba sanin zafin abunda tayi ma taj ba sai ya samu nata gashi nan ba a je ko’ina ba saboda abubuwan datayi a baya zai shafi dansu, an innocent child daman duk abunda kayi sai anyi ma naka,, a karshe ma dai fada mata yayi idan har wani abu ya samu dansu bazai taba yafe mata ba.
Aranar daya dawo yaji labarin kamata da akayi tunda abune ba boyayye ba kama ga matsayinta a kasar, ko’ina zai dauka don zai shafi kamfanin su, yayi mamaki sosai, wannan ne yasa yazo don ya tabbatar ma idanunshi don hidaya can never give up so easily he wanted to see why tayi sanyi batayi amfani da tricky connections dinta ba, don zata iya yin komai akan kamfaninsu da kuma ganin duk wasu abubuwa da takeyi bai fito idon duniya ba, ashe ashe ga dalili, ga kuma labarin bacewar taj.
Haka ya futa yabarta zaune, jiki a mace tayi la’asar kamar ba hidaya ba, ta kasa tabuka komai, komai ya juye mata gaba daya bata cikin natsuwarta saboda danta, da tanada hanyar maida hannun Agogo baya da batayi abunda tayi ba a baya, sai hankalinta ya sake tashi sosai, don tabbas fadwa zata iya illatar mata da danta dukda ta bata abunda take nema.
Jamid na barin detention center din, gabanshi na faduwa sosai ya wuce school dinsu direct.
Gaba daya school din yau is busy saboda hutun end of the terms da akayi kuma iyaye nata zuwa daukan yaransu.
Dukda yasan makarantar akwai tsaro sosai wannan baisa gabanshi faduwa ba,at the same time har zuwa lokacin he’s in so much shock.
Ay bai gama samun shock of his life ba saida aka nemi barad a school sama da kasa aka rasa, home school teacher dake kula dashi ta shaida yana zaune a visiting area, don tun safe ake zuwa daukan student, on a blink of eye aka nemeshi aka rasa, jamid kamar zaiyi hauka, school gaba daya ta rikici aka fara duban cctv, abunda suka gani ne ya sake tadama jamid hankali, don footage din ya nuna wani mutumi ne ya shugarda barad din cikin wata baqar mota, home school teacher data gane ko wanene ta shaida masu ay driver din dake zuwa daukansa ne lokacin da yake zuwa day kafin a maidashi prep border…
Jamid was so confused don a lokacin yana kwance baisan meke faruwa ba, baima san wanenene driver ba, tsoronshi daya karya kasance driver nada sa hannu da fadwa…
Waya mutallib ya dauka yayi typing message kafin ya aje wayar ya maida dubanshi ga barad dake zaune, yaron yayi shuru baice qala ba,har suka isa hideout suna isowa mutallib ya bude mashi kofa ya futo.
Dauko yaron baiyi ma mutallib wuya ba saboda yaron ya sanshi, ciki suka shiga yana fatan kar yaron ya tsorata idan yaga khaal don yanada wayo.
Cikin ikon allah Koda yaron yaga khaal bai nuna yaji tsoron ganin shi ba, saima tambayar khaal din yayi how is he alive? Mamanshi tace ya mutu bazai dawo ba, gashi kuma yanxu yana raye that means mamanshi karya ta mashi kenan? khaal ya rasa wani answer zai bashi…
Kallon khaal yaron ya sakeyi Sai kawai ya fara kuka sosai yana tambayar khaal da gaske an kama mamanshi? Friends dinshi sunce mamanshi is a kidnapper an nunota a tv, har bullying dinshi aka fara yi.
Tausayin yaron ya gama babaibayeshi,idan ya taso yaji abubuwan da mahaifiyarsa tayi a baya abun zaiyi affecting dinshi sosai…
Call din taj yasa mutallib futa daga inda suke don ya amsa, gaisawa sukayi kafin mutallib ya soma magana.
“Na kawoshi yana tare da khaal yanxu.”
Shuru akayi daga chan mutallib na jin yanda ya sauke ajiyar zuciya, “please take care of him”
Da mamaki mutallib ya soma magana, “duk abunda mamanshi tayi maka baisa kayi abandoning dinshi ba? Why?”
Daga chan taj ya bashi amsa kamar haka, “saboda he’s innocent,“
Murmushi kawai mutallib yayi yace “kamar yanda kayi hasashe, an saka kamfanin a kasuwa, next week za ayi bidding akan, kuma darajarshi ta sauka akwai possibility kamfanin B&B ne sukeson su saya saboda su kadaine tayi partning dasu kafin wannan scandal din,”
Shuru taj din yayi yana wani dogon nazari akai, saida mutallib ya sake magana kafin yace “i will call you back” ya kashe wayar ya soma dilaing number merk, yana daukan wayan ya soma mashi proper bayanin yanda abubuwan ke wakana a kamfanin, already yasan fadwa has take over tunda daman itace next to hidaya, at first ya dauka agenda dinsu daya da Hidayar tunda duk wasu abubuwa da sukeyi akan karya gaji kamfanin mahaifin nasu ne, kuma zasu iyayin komai akanshi sai yanxu ya fuskanshi ba hakan bane, nata plans din dabanne, daman he never trusted her tunda har ta iya cin amanar yar uwar tata, dubaga lokacin da aka kama hidayar ta futo ta nuna cewa kwata kwata basusan komai gameda abunda yar uwarsu keyi ba, kuma dalilin dayasa ta hanasu su kansu yan uwanta su shiga harkar business, ta juya komai akan hidayar, yanda dai sukayi ma khaal, lokacin da aka ce yana amfani da kamfanin wajen yin illegal abubuwa, ashe ita sayarda kamfanin ma takesonyi, kuma ga competitors dinsu.
Jamid na barin school fadwa ta karaso itama, tana zuwa neman barad din aka shaida mata ay driver yazo ya daukeshi, tana barin wajen ta shiga mota taja da mugun speed, tayi mugun sake da bata daukeshi ba tuntuni tun kafin ma tayi threatening hidaya dashi, dole hidaya will not sit still zatayi komai akan danta, musamman yanzu data gano komai tasan wacece asalin fadwar, hidaya has so much influence da zata iya yin hakan,ko zaman sati biyun nan datayi a detention center dinnan fadwa ce tasan yanda tayi duk wani lawyer yaqi daukan case din hidayar, dole hidaya ta zauna a ciki don tasan sirrinsu ita da mahaifinta, kuma idan har ta fito zata iya zame masu barazana shiyas ayanxu tayi deciding daukan barad don tasan shine weakness din hidayar shi zaisa taqi making any moves.
Nigeria…
Baze university abuja…
Suna gama debate presentation kowa ya futo daga class, excitedly, musamman haya da sabeeha sai wasu maza biyu da suka kasance a