Advertisements
Chapter 65 Reading Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Matar Taj Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Complete Novels

Chapter   65 / 107

192K to 195K   out of 320.4K words

rai adan bace.
“Where can we find them?”
“How would i know? Shey i told you they never pay me my rent”
“How much is your rent, “50k” ya bashi amsa
Taj yayi tsuka, rai a bace jijiyoyin kanshi na tashi, kamar yaui hauka haka yakeji, salim ya bama landlord 100k suka bar wajen saboda hamami.
Tund asuka shugo mota taj ya dage kanshi, daga jiya zuw ayau salim ya gane wannan binciken yarinyar badan komai bane saidai so, duk yanda akayi mutumin nan son yarinyar yake, kuma ya hadu da ita a kasarshi ne.
“Sir zamu sameta insha allah, i still dont trust that jamilu, he definitely knows where to find her, ko kanaso musa hukuma a ciki?”
“No need for that, lets calm it a day”
Salim yaja motar sukabar wajen.
Suna cikin tafiya salim yace “sir ive assigned you the membership of the best gymnastic close to your home you can start anytime”
“Thank” taj ya amsashi gaba daya hes fed up, ya kasa thinking straightforward.

Wajen karfe hudu suka iso, salim ya saukeshi ya shiga ciki jiki a mace.
Laila data shugo part din anne ta a zuwa direct kitcen ta wuce wajen anty rabi, tana isowa tace “anty rabi ga lunch din uncle taj mami tace a kawo”
“Toh bari akai mashi”
Sabeeha dake tsaye tana yankan naman sa da aka kawo za a saka a fridge rabi ta kalla tacebar naman zamu cigaba nida basira kije ki kai wannan chan part din”
“Toh anty rabi”
Ta bata ansa tare da karbar tray din basira ta bita da harara, ita maisa baza ace takai ba.

Akan idanun laila sabeeha ta wuce part din taj, sai kawai tayi murmushi ta wuce part dinsu tare da daukan wayarta ta kura maya, “baby girl, kina ina ne? What are you doing?”
“Sleeping..”
Ta amsata kai tsaye, “ya muke ciki ne da bet dinmu? Banga wani sauyi ba?”
“Kina doubting dina ne?”
“No kawai dai na tambaya ne, naje part din anne nakai Favourite abunci sa da mami ta zuba mashi shine na tuna da bet dinmu”
“Meysa baki kirani ba????”
“Woo, kai masa zakiyi?“
“Yea…”
“Haba dai…you’ll not do that, irin waennan abubuwan ba kince yan aiki ne ya kamata sunayi ba,”
Banza tayi da ita amma ta qulu sosai ba kadan ba, “waye kika bama zai kai?”

“Sabeeha, i heard that aykin part dinshi ya koma hannunta,“
Kitt maya ta kashe wayar jikinta na bari ko dankwali bata saka ba daga ita sai wata yar vest da tight tayi packing shegen gashinta da ko ribbom din bai kamasu sosai.
Kamar zata fadi haka take tafiya gaf gaf gaf har zuwa part din, ko knocking batayi ba ta bankade kofar, adaidai lokacin ta tadda sabeeha na jera abuncin a dining, maya na ganinta ta daka mata tsawa “keeee me kikeyi anan?”
Da mamaki sabeeha ke kallonta, “bake nakema magana ba yar matsiyara me kike anan?”
Banza tayi da ita maya ta hasala “dan…”
“Karki sake ki zageni,aikina ya kawo ni nan ba fada dake ba,”
Daga yau karki sake shugowa nan?”
“Idan ke nakema aiki ki hanani”
Tana fadin haka ta juya abunta ta futa daga gidan kota kanta batabi ba, maya kamar ta shaqo ta ta kashe haka takeji, lokaci gida taji shes insecured gaba daya.
Sabeeha na futa sai gashi ya sauko kasan, sanye da armless riga da gajeran dogon wando kamar zaije gym, tundaga sama yake kallonta da mamaki,”wannan yarinyar is she okay?” Ya tambayi kanshi.
“What are you doing here?”
Ya tambayeta babu wasa, “uhm uncle taj, daman mami ne tace na kawo maka breakfast”
Tund aya mata kallo daya bai sake kallonta haka ba badan komai ba saidai kwata kwata babu abun burgewa a tattare da kallon nata,
“You may find your way”
Murmushi tayi tana gyara tsayiwarta harda kwarkwasa oho shi baima san tanayi ba,
“Uncle taj, are you going to gym? Can i come along?”
Ay baiyi tunanin anan ma akwai marasa kunya ba sai yanxu,,
“You may find your way” ya sake fada yana mata nuni da hanya this time around babu wasa, jiki a mace ta juya ta futa.
Sai yaji abuncin ma ya fita aranshi baici ba ya fuce.

Da daddare kowa ya hallara for dinner, hamad da nanna da maya banda anne data kasa suakowa saboda kafa.

Daga kitchen rabi ta dubi sabeeha tace “dan allah jeki kai pepper soup dinnan nan,“
“Toh” sabeeha ta fada tana kokari daukan warmer din, ta tunkari dining area din.
Da sallama dauke a bakinta ta karaso, hamad ne ya fara dagowa jin muryanta mai sanyi, ya dade bai ganta sai yaga ta sauya gaba daya tunda sukayi hutun school.
“Sannu ku da hidima” nanna tayi magana tana kallonta.
Murmushi kawai sabeeha tayi ta aje abuncin kan dining, harta juya ta tsaya chak kamar ruwa yacita “taj, ga pepper soup a zuba maka?”
“No nanna, this is okay” ya fada da larabci.
Kirjin sabeeha kamar ana lugude, yanda kasan ana buga guduma haaka take ji, ta kasaa juyowa ta wuce kitchen jikinta na bari, so take ta juya amma ta kasa, kafafunta kamar ba a jikinta suke, muryan taj taji ko kuwa kunenta ne da kwalwalwarta ke kokarin yi mata wasa da hankali.
“Kai its impossible mai ze kawo taj nan gidan? Shida yake saudi She must be mistaken”
Basira ce ta kalleta dataga shugowanta tace “kizo mu karasa kin barni ni kadai inata fama da tukwane, duk wani abun arziki sai a wani sakaki aikin banza saikace ance ni bazan iyaba,”
“Yi hakuri basira”
“Ki daina ban hakuri dan allah, kizo mu cigaba na gaji zan kwanta,”
Hannu sabeeha ta sa mata hankalinta baya jikinta kwata kwata.
Basira dake kallonta ta gefen ido ce tace “kinga balaraben nan? Dan nanna yanada kyau ko?”
Balarabe? Sabeeha ta nanata aranta, “kai wallahi allah yayi mashi kyau, inama ace zai aureni wayyo, hmm bari na daina haukan nan nasan achan kasarsu saudiyya akwai zillaziyas hadaddu ba kamar ni ba gaja” harda yar dariyarta
Chak sabeeha ta tsaya da scrubbing din da take jikinta har tsuma yake ta juya ta nufi wajen futa daga kitcehn din, daidai wajen walkway din barrier din dayayi iyaka da kitchen din ta tsaya don tana iya hango duk wanda ke dining din, adaidai lokacin ya moqe tsaye bayan yayi ma nanna sallama zai koma part dinshi.
Wani irin jiri ta soma ji kamar zata fadi tsabar shock, babu abunda take sai “innalilahi wa inna ialaihi rajiun, “ har muryanta na dan futowa, she’s shock and confuse at the same time, juyowa yayi da hanzari don yaji tayi saurin shigewa saqon wajen ta boye fuskanta…



✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊

MATAR TAJ (destined with you🩵 🤍)
Written by
Queenmarh✍️
Book2
PAID
Chapter 99/100
Cikin sauri ta fuce daga wajen ko ganin gabanta batayi kirjinta na bugawa tayi saurin saka hannunta dake rawa akan kirjin nata, ji take kamar zuciyarta zata fado, marin fuskanta ko tayi yayi wajen sau biyu ko zata tashi daga mafarkin da take tunanin shi takeyi.
Samun waje tayi a backyard din ta zauna yar a kasa, hawayen dake sauka kan fuskanta ko batama san tanayinsu ba.
“Tajudeen ta gani yanxun nan? A cikin gidan nan ? Kuka shine dan nanna?”
All this while tana tare dashi cikin gidan nan batasan shine ba?duk zamanta a saudi bata taba sanin cewa mahaifiyarsa yar nigeria bace, tadai tuna lolacin da ammu ke bata labarin yanda yazo gidan, an rabashi da mahaifiyarsa tun yana kankani, shiyasa ya taso bashida mahaifiya a tare dashi sai hidaya daya yarda da ita sosai.
Harta fara jin emotional feelings na ganinsa datayi, tunawa da abubuwan da suka faru achan saudiyya yasa lokaci guda ta daqo sense dinta.
Take duk abun da ya faru ya soma dawowa akanta, rayuwar da sukayi shida ita achan da abubuwan da suka faru tsakaninsu da yanda tabar gidan, duk Kokarin datayi na ganin ta danne zafi da dacin abun kasa wa tayi kawai ta fashe da kuka, harga Allah ta cireshi daga rayuwarta ta, kuma bata fatan ta sake hada hanya dashi har abada, ta binne rayuwar datayi a saudi gaba daya kuma bata fatan wata rana ta tono shi, amma yanxu da suke inuwa daya ta ina zata fara?? Kai wannnan wace iriyar kaddarar rayuwa ce? Rayuwarta juyawa kawai takeyi yanda bata so kuma bata tsammani, ba haka takeso ba.
Ta dade zaune bata ma san da mutun a gabanta ba saida taga inuwarshi a gabanta yasa tayi saurin yin baya gabanta na faduwa.
Handkerchief din dake hannunshi mai kamshin gaske ya miqa mata yana kallin cikin idanunta, yanayin yanda wajen keda haske kamar hasken rana saboda wutar lantarki yasa ta gane yanad ne a gabanta,
“Please wipe your tears”
Samun kanta tayi da sauke kanta kasa ta kasa karban hanky din sai jinshi tayi kan fuskanta kamar ana sharewa, da sauri ta dago fuskanta ta kalleshi “meysa kike kuka fatima? Meke damunki?”
Kasa magana tayi saboda yanda takeji aranta kamar tayi pouring out komai ko zataji sauqi.
“Fatima!!!” Ya sake kiran sunanta a natse, “meysa kike kuka?An maki wani abu ne? Bakida lafiya ne?”
Girgiza kanta ta soma yi ahankali taqi yarda su hada ido dashi.
Shuru shima yayi gaba daya yayi sanyi sosai ganinta tana hawaye haka.
“Ko baki fada min fatima i see loneliness in you, i see pain in your eyes, please share your pains and burdens with me, I’m willing to listen to you”
Sama sama ta soma sauke ajiyar zuciya, hawayen fuskanta kuwa sunqi tsayawa tana sauraronsa, “dan allah ki fada min damuwarki, bana son ganinki cikin damuna kinji..”
Nanma shuru tayi ta kasa cewa komai tana kokarin daidata kanta.
“Fatima i…i…”
Saurin karban hanky din hannunsa dake dab da fuskarta tayi ta share hawayen dake fuskan nata idanunta har sunyi jaa sosai kafin ta miqe tsaye shima ya miqe yana kallonta.
Murmushi ta kakalo da kyar tace “ya hamad babu abunda ke damuna kaina ke ciwo ne shiyasa”
“Baki iya karya ba,”
Surprisingly ta kalleshi ya kureta da ido tayi saurin dauke nata tace “ba karya nake ba ya hamad”
Dan murmushin da bai shirya yi ba yayi yace “shikenan, but please inason ki sani, im here for you okay? Idan abu na damunki don’t hesitate to tell me”
“Meysa ya hamad? Niba kowa bace a wajenka, ni yar aiki ce kawai, babu dalilin da zaisa ka damu dani”
“Waya fadi maki haka? I care for you, i can see alot thru you, don’t keep it to your self okay?”
Yaqe kawai tayi tace “nagode ya hamad” tana fadin haka tabar wajen da sauri.
Maganr haya ce ta fadi mata akanshi, haya keeps telling her that yanasonta ita kuwa bata fatan karama ka ta wani bala’i,she wants to stay on her limit don yafi karfintaa and she has had enough.
Wanke wanken da bata karasa ba kenan ta wuce dakin rabi, ta roketa ko zata iya kwana dakinsu basira tunda bilki ta tafi kuma akwai extra gado tace mata eh.
Koda ta fada ma hadiza bata wani damu ba tace mata taje.
Aiko kwana tayi kan sallaya tana kai kukanta ga Allah, akan ya nema mata mafuta.

Jamila na komawa gida dahiru yayita faman kiranta, karshe ma dai kashe wayar tayi ta aje.

Washe gari, tun wajen karfe shida da rabi duk suka fito domin daura sanwar breakfast, gaba daya kana ganinta zakace bata da lafiya she looks so pale and sick, rabi ta tambayeta meke damunta tace ciwon kaine kawai.
Haka suka gama komai rabi tace suje su jera komai kan dining, tsoro da fargaba ne ya durar mata, yanxu the least abunda zata bari ya faru shine yasan tana nan, wanda bazata taba barin haka ta kasance ba, gashi batada dalilin da zatace bazata kai ba.
Wata dabara ce tazo mata ta kunce dan kwalin dake kanta dake yanada girma sosai wannan yasa ta yafashi suka soma futarda warmers din, woof datakai zata dawo, lokacin har sun fara saukowa, dake yau weekends kowa na gida.
Laila da maya ne suka fara saukowa kasan don a dakin maya laila ta kwana jiya, hayaniyarsu ce kawai ke tashi, shugowarshi ce tasa sukayi tsit gaba dayansu, maya da kaudi tace “good morning uncle taj”
Laila ta gaishesa ya amsa su a taqaice kafin ya wuce sama, sabeeha dake labe wajen shugiwa dining din tana jin muryarshi ta dakata gabanta na faduwa, saida taji laila na cewa “da alamu dai yau nanna a sama zatayi breakfast”
Daga mata gira daya maya tayi kafin tace “gashi nan ya wuce sama, anya maya zaki iya…?”
Hade rai maya tayi sosai tace “kisa ido mana kigani idan ban sa hankalinshi ya dawo gareni ba”
Dakatawa tayi da maganar tare da yima sabeeha wani mugun kallo, laila ko tsoron yima sabeeha magana take kar mayan taji haushi.
Abunda ta kawo ta aje zata juya maya tace “kinga zobenki kuwa? Naji dazu kina nema, kinsan gidan ne yanxu a cike yake da masu hannun bera”
Bude baki laila tayi da mamaki jin karyar da maya ta zugo dukdan ta kunsa ma sabeeha itako tayi wucewarta ko takanta batabi ba.

Dawowa kitchen rabi tayi tana kallon su suna wanke abubuwan da aka gana amfani dashi, yau gaba daya qnai zazzabi zazzabi takeji sosai wannan yasa ta barsu da sauran gyaran.
“Sabeeha..dan allah ga warmers din bangaren nanna nan kije kikai sama, ta buqaci yin break a sama yau”
Dam gaban sabeeha ya vada, tabbas dazu taji muryanshi kuma taji sanda laila ke cewa da alamu a sama zaiyi breakfast, yanxu ya zatayi kenan? What if ya ganta kai bazata bat hakan ta kasance ba.
“Anty rabi bari na karasa wanke wanken basira takai saman”
“Ah ah ke zaki kai, ita ta cigaba da aikin”
Basira kamar ta hadiye zuciya dan bakin ciki, ta wullo ma rabi wata iriyar harara kamar idanunta zasu futo.
Hankali a tashe sabeeha tace “toh”
Rabi na komawa daki gabanta ya tsananta, ya zatayi yanxu?.
Juyawa tayi ta koma daki ta dauko hijab dinta ta futo ta dauka tray din ta nufi hanyar futa, har zuwa lokacin gabanta faduwa yake, su maya na breakfast basuma lura da wucewarta ba kwata kwata.
Haka ta bi stairs dinnan kamar karta kai karshe tsabar fargaba ta nufi part din nanna.
Kafun ta shiga tayi saurin jawo bakin hijab din nata wajen bakinta ya zamana iyakacin idnaunta kawai ake gani ta gyara tsayuwarta kafin tayi knocking.
“Yes come in”
Akayi maganada daga ciki,runtse idanunta tayi ta bude kofar tare da sallama ciki ciki,
yana zaune kan kujera idanunshi na kan wayanshi kamar yana karanta abu, kwata kwata bai dago ba, itako tana arba dashi taji kamar tray din zai kubce mata, ya sauya gaba daya kamar bashi ba, tana hango kwanciyar hankali a tattare dashi gashi ya wani irin kara kyau sosai, kamar ba taj ba wallahi.
Ajiyar zuciya ta suke abubuwa da dama na yawo akanta ta nufi dining ta aje ta soma jera komai.
Gaba daya attention dinsa baya ga wanda ya shugo, yana replying messages din dake wayarsa, harta gama jerawa ta juya zata futa daidai nan nanna ta futo.
“Har an kawo breakfast din” nanna tayi magana don batasan wacce daga cikin yaran ta kawo ba.
Gyaran muryanta tayi kamar wadda ke mura yanda baza a ganeta ba tace “ eh ina kwana nanna”
“Ah ah yarinyar kirki yau kece kika kawo min breakfast din,”
“Eh,”
“Toh sannu”
“Ya Naji muryarki haka, ko mura kikeyi?”
Kamar mai tsoron magana dukdan karya gane tace “eh”
“Toh kunsha magani kuwa ko a kaiki asibiti?”
“Eh nasha” ta fada muryanta na breaking ganin ya dago ya mata kallo daya tayi saurin sauke kanta kasa ta kawar dashi gefe.
“Toh allah ya sawaqa”
Ko ameen din bata iya fada ba ta juya kafarta na harde ta futa daga part din.

Kallonshi tayi ganin ya yi saurin aje wayar tunda ta futo, ba tun yanxu ba tayi sensing kamar akwai abunda ke disturbing dinshi kuma bata takura don ya fada mata ba amma tanason sanin koma menene.
“Ga breakfast ko? An kawo”
“Okay oummi”
Suka zauna suka fara cin abunci bayan nanna tayi serving dunshi, janshi take yi sama sama da hira musamman hiran business haka.
Suna gana karyawa zai wuce nanna ta dakatar dashi.
“Zauna tajudeen”
Ya zauna sitting room itama ta zauna tana fuskantarshi.
Shuru ne ya biyo baya kafin ta tattara courage dinta tace “ina kawunka? Banji kana maganarshi ba?”
Khaal take nufi kenan, shuru yayi yama rasa me zaice mata, bayason tasan komai ayanxu tukunna sai yayi resolving komai.
“Yana nan lpy,”
“Are you sure babu abunda ke faruwa tajudeen? Is there something that i need to know? Meysa kazo nigeria”
“Saboda ke oummi”
“Nasani amma…”
“Oummi please…zan fada maki komai amma ba yanxu ba,”
Sauke ajiyar zuciya tayi ganin haka yasa tace “toh shikenan, inason ka hadani dashi, its been ages rabona dashi”
“Insha Allah” ya amsa ta kafin ya mata sallama.

Bayan fitar sabeeha cikin gaggawa ta wuce part din shi wai don tayi using wannan opportunity din tayi gyaran part din kafin ya dawo.
Allah yaso babu wani datti a part din da zaisa ta wani dade, gyaran gado ne kawai da wankin bathroom sai kuma vacuuming da zatayi.
Da dakin ta fara cikin gaggawa ta wanke toilet din kamar tayi tsuntsuwa ta gama haka takeji tana gamawa ta futo zuwa sitting room, goge gogen ko’ina ta fara ta saka humidifier saannan ta kunna ac parlor din, tana tsaka da kashe electric vacuum din taji karar kofa, ta zaro ido waje, abunka da batada wani yawa tayi saurin juya baya ta duqa a gaban vacuum cleaner din kamar zata dauka abu.
Shidai yaga mutun a tsugunne ga karar vacuum cleaner sai yayi tunanin ko wadda ke zuwa gyaran part din ne.
Bai bama wadda ke wajen attention ba don bashi time din wannan ya tunkari stairs tanajin tafiyarshi har zai hau sama ya dakata, tare da juyowa yace “are you done???”
Tasna da ita yake and bata son raising anything da zaiyi suspecting itace ko ya gane ita ce wannan yasa tayi saurin girgiza kai.
Shi ganin abun yayi ma kamar rainin wayo sai yayi tunanin ko kurma ce, ya wani juya bai sake kalon inda take ba ya wuce sama.
Cikin sauri ta dafe kirjinta tare da janye hijab din data rufe kusan duka fuskanta dashi saboda nunfashinta dataji yana neman dauke.
Ay ko second daya bata sakeyi ba ta arce hartana tuntube.
Yana gama abunda yake ya futa daga gidan shima.
Yauma neman jamilu suka koma yi, gidan ma a rufe yau suka taddashi an saka kwado.

Sabeeha ko tana komawa daki ta samu waje ta zauna ta doka uban tagumi.
“Anya bazata hakura da karatun nan ba? Saitaji dama maman nata ta maida lafiyan kawai,“


Misalin wajen karfe hudu na yamma jamila ta dawo, mai shagon saka chargy dake gefen gidan na ganinta ya

65 / 107